Breaking News

Bad Boys 42


042
*Bonus*
___________________
“Kinga mun yarima? This morning?”

“Nima shi nake nema ,mama hankali na a tashe yake ,I even needed to have some words with him ,yeah I Doubted if sarautar gidan nan har yanzu ta gado ne ,bai zama contesting akeyi ba a watsa tsaba mai rabo ka tsinta…”

“Auta baki da fatar alkahiri a rayuwar É—an uwanki ne? To ko ma menene da ke da sauran masu tunani irin naki su jira ,suna kallo yarona zai gaji karagar ubansa ,Abbad zai zama sarki na 4 da yardar Allah”
Kafin Auta ta kawo nata objections É—in ta wuce ta fuuu.

Zafi zafi taje ta ɗauko car key dinta Bata jira Driver ba ko guards ta shiga motar ta mata wani mugun key ta figeta da gudu tun daga parking lot ta nufi hanyar gate ,da sauri masu gadin ƙofa suke tale gates har guda duka ukun ,haka ta fice daga gidan a hargitse.
Ita kanta bazata taɓa iya tuna yaushe ne rabon da ta tuƙa mota da kanta ba ,zata iya cewa tun kafin sarki ya zama sarki. Tun sarki na yarima kafin babansa ya mutu ya gaji mulki.
***

“Sarki yana da É—a a wani waje,kuma Matsawar yana raye yiwuwar zaman ka sarki rabi da rabi ne ,ma’ana kowa yana jan Æ™arfin ikon gadon sarautar………! ”
Kalmar da kakan jabir ya soma gaya ma Yarima knn a sanda suke shiga daga cikin kogon.

Itama kuma mai babbar É—aki kalmar da bokanya ta soma gaya mata kenan a daidai sanda take rusune a gabanta cikin tashin hankali.

“Kana nufin akwai wanda zai iya zama sarki ba Ni ba?”

“Ko yayi nasara ko kayi nasara ,amma kayi Æ™oÆ™arin ganin bayan sa kafin ya shigo fadar nan ,saboda taurarinsa suna da haske …yana zafin halshe fiye da kai,yana makirci kamar mace ,da kayi sakaci ya shigo fadar zai tarwatsa maka gida kuma dole yayi sarauta.”

“How and why?,Mai Baki ya fi mai aiki? Munafuki yafi mai sarauta…ban taÉ“a ganin yanda banbaÉ—anci yafi zaurance ba”

“Yana da É“oyayyen Sihiri a tare dashi ….a taÆ™aice an tsumashi ,a shirye yake”

A hankali yarima ya maimaita “He’s battled ready,waye shi?”

“Kaje ka cigaba da roÆ™on mutanen ka gafara…Zaku haÉ—u Æ™arÆ™ashin inuwar wata budurwa,Allah yaba mai rabo Sa’a ,kar kayi sakaci da Addu’a yarima! Ina maka fatar Nasara.” yasa hannu yana shafa masa kai yana masa en Addu’oi.

***
Ambassador ne gurfane a gaban mamanshi ,baÆ™a baÆ™a Æ™irin da ita , mummunan gaske ,kana ganinta kaga shu’uma ,duk da yaronta yayi kudi baisa ta sauya ba tana nan a wahalenta.

Miƙa hannu tayi gefen ta ,ta kamo wani ƙwarya shaƙe da wani abu kamar jini ta miƙa ma Ambassador .
Jikinsa na rawa yasa hannu ya amsa

“Yarooo!”

A hargitse ya É—ago yina kallonta
“Shanye”

Watsa idonsa yayi cikin tashin hankali cikin ƙwaryar jinin Hannunsa.

“Ina bazan iya ba mama”
Tsawa ta daka masa wanda yasa tantabarun gidan yin kuka suka firfito daga kejinansu ,wanda suke tsube a ƙasa suna tsintar dawa suka tashi firrrr saboda firgita.

“Shanye nace! Ni zan ringa magana kanayi? Ni zan baka umurni kana mun jayayya? To waye silar dukiyar da kake taÆ™ama dashi? NINE! waye silar zamanka Ambassador? NINE! Yau ne ranar cikar girmanka,yau zan bayyanar da É“oyayyen takobin da na daÉ—e ina wasashi…yau zan gabatar ma maÆ™iyyiyata Lauje mai dafi da zai Zaro en hanjinta waje ,zaki fito gidan sarautar nan Ummi ,yau zaki bar gidan da na baki aro kikaci zamaninki a cikinsa Ni kuma ina raÉ“e cikin wahala Ni da É—a na,Yanzu lokaci na ne zaki bar mun gidana da uban É—a na mai martaba! Yarona zai zama sarki zai wulakanta mun ku…”

“Yaroooo” ta sake kiran sunan Ambassador cikin Hayaniya da fitina irin na gawurtattun matsafa

“Kaje ka kashe mun,yaron nata da take taÆ™ama dashi,ka Æ™wato mun kujeran babanka….yau lokacin girban haÆ™urinka ne,yau wanda suke maka gorin shege zasu san yarona ba shege bane da ubansa! Uban kuma maÉ—aukaki da yafi ubansu….taka a hankali É—an sarki jikan sarki ,sarki da kansa nan da sa’oi arba’in da Takwas ….ka tafi ina nan ina kallon duk abinda ke faruwa a cikin Æ™waryar tsafi na,Gabanin nan shanye mun wannan tsimin jiÆ™on tas! Don anan nasarar ka take”

Ɗaure fuska yayi Nan da nan ya rikiɗe ya zama wani kalar mutum mai suffar mugaye ,cikin ɓacin rai na tuno wulakancin da yasha a rayuwa ya kafa kanshi a kan ƙwaryan jinin ya ƙyanƙyame

“Hiihahahahahaahhaa” ta barke da wata mahaukaciyar dariya ,wanda yasa gurin ya fara girgiza kamar jirgin sama ne yazo giftawa.

“Oya Oya jeka fuskanci maÆ™iyinka..jeka Æ™wato mana mulkin da ya guje mana tsawon shekaru ,saboda makircin waccan bakar dagar(Mai babban É—aki, mahaifiyar Yarima Abbad)” a zabure ya miÆ™e yana gyara kwalar riga .

“Yes yarona” taje da sauri ta É—auki kaskon wutar dake ta É“ulÉ“ulo da hayaÆ™i ta na kewayeshi tana turare masa jiki da hayaÆ™in.

 

 

_A yawan lokaci muna tare da mugayen mutane bamu sani ba,kai dai ka kasance da Addu’ar safiya da maraici ka fice gida da Addu’a sai Allah ya kareka daga sharrin mutum ko Iska,wannan shine abokin Ya Sheikh wanda yake barinshi a gidansa a koda yaushe ,shine wanda yake son Sayyada a birne a Æ™asar zuciyarsa,shine wanda ya bayyana mata yana sonsa ta tozarta shi,a karshe ma ta gunmaci zaman gidan ya Sheikh da ta kula shi….Æ™araÆ™aÆ™a kaka_

 

Oum Aphnan
#Bad boys
09065990265
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaÉ—ai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuÉ—in ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

No comments