Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bad Boys 48


048
___________________
Yanda gidan maƙura uwar Ambassador ya tashi da wuta ya cinye ambassador da uwarsa murmus ,yarima ya tsira da ƙyar,hakan yayi daidai da farkawar Mai martaba firgigit akan gado ,wani doguwar miƙa yayi ya rafka salati.
Auta neehla dake gefensa tana masa tofin Addu’a fashewa tayi da ihun murna taje ta faɗa jikinsa tana tattaɓashi“Abbana kana gani na? Ka gane Ni abbana? Nine autar ka ka gane Ni?”

Jinjina mata kai yake daƙyar sam baida ƙwari daɗewan da yayi a kwance cikin jinya ba ƙaramin nunar masa da jiki yayi ba sam muryarsa baya iya fitowa .

Nihla miƙewa tayi zata fice a ɗakin da gudu tayi yekuwa sarki ya farfaɗo tayi kaciɓis da yarima ya shigo ɗakin da sassarfa ƙafansa ba ko takalmi

Ruƙunƙumeshi tayi gamida jan wani ajiyar zuciya ,itama a hakan mai babbar ɗaki tazo ta rungumesu duka
“Allah na gode maka da ka saita mun gidana bayan ya idasa wargajewa Allah kaine abun godiya ,Allah mun tuba ga kurakuranmu da mukayi na baya da wanda zamuyi anan gaba ,tabbas wannan jarabawa ne mai kama da gyaran hali ,Ubangiji ka sake rufa mana asiri ka kare mu daga sharrin matsafa da bokaye”

***
Saida sarki ya kwana biyu yana shan ƙarin ruwa da magunguna sannan yayi sarai ya bada kwangilar gina mahaukaciyar fada mai girman gaske da kawatuwa haɗe da gidan Yarima Abbad ,gidansu Sulaim tuni an bugeshi an maida gidan zamani bene hawa biyu da rumfar motoci a tsakiya ashe dai ƙatoton fili ne ,talaucine da zubewar garuka yasa ya zama kango.

Baba da inna cikin sati uku sunyi sharr ,an turo masu kuyangi da jakadiya mai ma Sulaim hidima,Zuwa kafin ta tare,mai babbar ɗaki ita tayi kwangilar masu gyaran jiki tundaga sudan.suna gyare jikin amarya ana tsuma mata jiki da kayan ɗaa🤓 sirrin yarima ne🍌💋

Duniya ta dawo ma tsofaffin nan sabuwa ashe dama ba wasu tsofaffi bane can talaucine yake neman cusasu rami .
Gashi sanadiyyar su kafatanin unguwar an malala mai kwalta an jera solar .abunsu acafai acafai kamar unguwar masu kudi duk saboda Sulaim yarinya ɗaya tamkar da goma .

Sai bayan enginiyoyi sun gama gudanar da duk ayyukan su anyi furnituing ko’ina ,a sannan ne aka tara gagarumin bikin tarewar Sulaim kuma da nadin sarautar Abbad a matsayin Sarki ,a cewar mai martaba gwara a naɗa Abbad sarki kar yayi mutuwar gasken irin hakan ya daɗa faruwa .

Sabon gida ,sabon fada ga amarya Er talaka er ba kowa ba yau ta zama sarauniya ,Mahakurci mawadaci ba’a cira rai ga Rahman Ubangiji.

Dare nayi dangi sukayi wa Sulaim rakiya zuwa gidan angonta sabon Sarki Abbad kaci dubu sai ceto dashen Allah mai takama da ikon Allah an buga an Barka karike Allah kai ke da nasara👍🏼

Daren yau dai suma a barsu su shana ,kundai San yarima ba daga legs ,idan sun kwana hudu jiki ya saba da Iskanshi😂😂🍌Sai muje mu lekosu.

 

 

 

Lilisss🍌💋

0um Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Post a Comment for "Bad Boys 48"