Breaking News

Bakar Ayah 2

Page 🖤02🖤 


Ƙwana uku baya…………

________________”Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za’ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaÆ™anci,saita Æ™wammaci bata shigo rayuwar mijina ba.
Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita.
JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaÉ—ai a faÉ—in duniyar nan,Æ™addarar sa ce ya zauna dani ni kaÉ—ai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga Æ™waina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan, saidai idan nina haifa shine zai gani,amma idan baniba babu wata Æ´a kuma.wannan alÆ™awarina ne ni LUBNAH Æ´ar URWATU”
“Shikenan yanda kika ce aikin bazai gagara ba,saidai kafinnan zaki ajiye nairah Miliyan É—aya da rabi kafin a fara aikin,dan zubar da cikin a yanzu zayyi wuyah,saidai a bari idan yakai matakin haihuwa sai a hanashi fitowa,koya kika ce toh”
“Hmmm idan hakan zaifi ayi hakan,amma ni da son samuna ne kafin na koma gida na sameta anyi filla filla da naman jikinta,babu wani abu dazai nuna itace,vazaka gane bane boka,natsani na buÉ—i idona na ganta a cikin gidannan,da wannan tsinannan cikin tana turashi,nafiso a kasheta irinnna waccar matar,kafin ma takai ga wani samun ciki”
“Kai……!! Tsiyata dake lubna gaggawa,inkika bi a sannu,kuma kina bawa Aljanu jinin da suke buÆ™ata,babu abinda bazaki samu ba,har matakin zaman ki na CEO ma duk zai cika nan da zuwa gaba.
Idan aka kawar da itama rufe idonsa za’a yi daga kan duk wata Æ´a mace da take doron duniyar nan,ke É—ai zai dunga kallo a duk inda idonsa ya sauÆ™a”
“Shikenan nidai duk yanda zakayi ma kayi”
“Amma fah akwai Æ™a’idoji da dole saikin kiyayesu,na farko;dolene kijata a jiki,ta yanda zata yarda dake har ki dunga sanin ya take ciki,na biyu kuma akwai wata Æ´ar tsana da zan baki,ki tabbatar kin saka jininta a jiki,lokacin da tazo haihuwa ki dunga karya jikin tsanar,zai zamo tamkar jikinta kike karyawa,daga lokacin da kika karyata tayi laushi,ita kuma sannan zata fuskanci tata mutuwar tareda abin cikinta”
“Naji wannan bayani naka,za’ayi yanda kace ba matsala,lokacin dazata dunga ihu sannan zuciyata zata wanke da zama min da tayi a cikin gidana.
Nagode gaskiya yau da gagarumin abinda ka bani,zan tafi,dan yau zai dawo daga taron daya tafi England”
Tashi lubna tayi daga ƙasan da take zaune tareda kaɗe zaninta tana murmushin samun nasara.
Hanyar fita daga wajen ta nufah mai matuƙar bada tsoro,amma hakan ko a jikinta,dan akan kishin mijinta babu abinda take ganin zai iya saka mata zani yarabata dashi.
Saida ta É—anyi tafiya mai nisa kafin tazo wajen inda ta ajiye motarta,Wai hausawa suna cewa SA KAI YAFI BAUTA CIWO.
Saida tayi tafiya mai nisa kafin ta shigo garin abuja,direct JAAN ESTATE ta wuce da baƙar motar ta.
Nufar babban get ɗin tayi cikeda ƙasaita da izzah,wanda hakan a jininta yake.
Titin dazai kaita apartment É—insu tabi,wanda take É—an ciki kaÉ—an da bakin babban get É—in.
Saida ta wuce nasu Hajiya Zeena kafin ta iso nasu part,shima da get É—insa mai zaman kansa,yana É—auke da part biyu,amma a haÉ—e suke ta tsakiyah,inda side É—in Jabeer yake.
Ba hanyar nata part É—in ta nufah ba,da alama wajen Hafsa zataje.
Fuskarta a murtuƙe take saboda tsanar baiwar Allahn,amma haka ta danne saboda zancen boka ta saki fuskarta kaɗan.
Da sallama ta shiga tangamemen falon,mai adon Green da purple,yayinda nata kuma yake fari da ja.
Haushi ne yakamata ganin kayan Alatun da mijinnata yasaka mata,tafison komai yazama ita kaÉ—ai take dashi bada wata matar ba.
“Assalam Æ™anwata kina cikine””
Hafsace ta fito daga É—aki da doguwar riga a jikinta marar nauyi tana tura zungureren cikinnata.
Kallon Lubna take da mamaki,dam yanda taga murmushi akan fuskarta abune da bata taba gani ba a faÉ—in rayuwarta,a ranta addu’oi take jerowa duk wacce tazo bakinta.
“Lafiya Æ™alau Anty lubna,sannu da dawowa ya hanya”
“Hanya Æ™alau,har zan shige nace bari nazo naga ko lafiya kike,nasan babu kowa a gidan saike kaÉ—ai,ga Honey ma bayanan,an barki ke kaÉ—ai ga ciki”
Ƴar dariyah Hafsa tayi,har sannan bata share tantamar inaga antynnata ba lafiyar ta Æ™alau ba,dan in ana neman rashin imanin matar to a tambayeta”
“Ayyah ba komai anty,akwai Alawiyyah ai Æ™anwata,tana taimaka min da abubuwa,Hajiya ma kuma tana shigowa akai akai”
Mintsine bakin lubna tayi tareda cewa “munafukar tsohuwa” a ranta.
“Ohh kinga shaÉ—af na manta da hakan,dama saidai ta hakan ai,akwai abincine ki bani,yanzu na fawo gashi banci komai ba”
“Ah….ehhh barina duba kitchen É—in,ki zauna akan kujera naje na dawo”
Murmushin yaƙe Hafsan take dan kwata kwata abin bayyi mata a gaske yake faruwa ba.
Bayan tabar wajen tashi lubna tayi tana kalle kallle a cikin falon,yaune zuwanta na farkon wajen da niyyar arziƙi,saidai tazo tayi tijara ko kuma kashedi,dan haka har tazo ta tafi bata gane mai yake wakana a wajen sai yanzu.
Tana cikin kalle kallenne Hafsa ta dawo É—auke ta plate a hannunta,ta rufe da wani a sama.
Karba lubna tayi tana murmushi tareda cewa.
“Yawwa nagode Æ™wanta sosai,amma zan iya tafiya dashi saina kawomiki plate É—in?”
ÆŠaga mata kai Hafsa tayi cikin ladabi.
“Lahhh ki tafi dashi Anty babu komai”
Daga haka lubna tajuya ta fita da plate É—in abincin a hannunta.
Tana shiga part É—inta ta buÉ—e kwandon shara ta zubashi a ciki,tareda jefa plate a É—in a wajen wanke wanke tana kaÉ—e hannu kaman ta dauki kashi.
Ɗaya daga cikin masu aikinta ta ƙwalawa ƙira.
“Bishirahhhhh!!!!!”
“Naaama ranki ya daÉ—e”
Ta karisa magana tana zurowa da gudu.
“Gyaran gidannan bayyimin ba kwata kwata,ku tabbar kun sake gyarawa kafin magriba”
Bayan ta wuce wacce aka ƙira da bishira ta samu waje ta zauna,tareda sakin wata ajiyar zuciya,banda neman na halali mai zai sakasu aiki a wajen wannan dujal ɗin.
Bayan ta fito daga wankane taji ƙarar motoci suna shigowa cikin apartment ɗinnasu.
Shafe shafe tafarayi,dan tasan mai gidanne yadawo daga taron shekara da sukeyi da sauran companies..
Har lubna ta gama shiryawa ana ta ƙiran Sallah amma bata ga Jabeer ya shigo ba,abinne yafara bata haushi,dan tasan yanzu haka yana sashen Hafsa,saboda ita tana da ciki ita kuma batada shi.
A bangaren J.J kuwa yana fitowa daga motar muhimmin ƙira ya shigo wayarsa,ana nemansa da gaggawa,dan haka a take ya ɗau ƙaramar motarsa personal ya koma.
Bashi ya dawo gidanba sai bayan isha.
Sallama yafara a bakin falon lubnan,amma shuru bata kulashi ba har ya shigo cikin É—akinta.
A zaune take akan kujerar dressing mirror tana danna waya,tacika tayi famm kaman zata fashe.
Mamaki abin yabaww J.J,dan yasan babu abinda yayi mata kafin tafiyarsa,hasalima sanda ya fita daga gidan bata nan ta tafi gidan ƙawarta batareda yasani ba,shine ma yakamata yayi fushi,amma kuma wai itace dayin fushin.
“Lubna inata Yin sallama kinaji kaman ba musulma ba?”
“Hmmm banyi niyyar amsawa bane,dan tsabar rashin adalci wato,tun É—azu kashigo gidan amma kana wajenta,ita gamai haihuwa koh,sai nayi magana tsofi suce banida haÆ™uri”
“Ke suwaye tsofin,iyayena koh? Yayi miki kyau,wai yaushe zaki sanja haline kam,dawowa ta fah kenan,yanxune ma nashigo gida,hmmm ALLAH ya shiryeki,banida lokacinki tunda lafiyarki kalau fine,na sauÆ™e miki haƙƙinki,saida safe”
Yana gama faɗin haka ya bar sashennasa cikin bacin rai,tasashi kuwa sarai,idan yayi zuciya da ita ta ƙwammaci ya mareta daya tura mata aniyarta,dan sai yayi sati bai kalli inda take ba.
Tsuka taja duk da taji tsoron fushinnasa,dan Allah ne kaÉ—ai yasan irin yanda take so tajishi a tareda ita,dan ita kanta shida ce shiÉ—in jarumin namijine a ta kowacce fuska,badai mace ta rainashi ba,saidai ma ta gaza.
Dama ƙarin haushinnata kenan,ba a sashenta yake ba,shiyasa take wannan kumbure kumburen.
Hafsa tana kan sallayah ya isa É—akin cikin fushi.
Sallama tayi tareda sake masa murmushi lokacin da suka haÉ—a ido.
Shima murmushin yayi mata,duk wani bacin rai da lubna tayi masa sai yaji yana sauƙa.
“Ka dawo lafiya ya hanya?”
“Alhamdulillah,ya zaman gidan da lafiyarku”
“Muna lafiya kalau,barina kawo maka abinci”
“Ahah ki barshi,barina yi wanka tukunna”
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa tareda shiga banÉ—aki.
Kafin ya fito ta fitar masa ƙananna kaya marasa nauyi.
Da safe suna cikin yin break fast lubna ta shigo sashen riƙeda plate ɗin jiya a hannunta.
Tasha wani matsatstsen lace kalar zinare da baƙi riga da skirt,ba laifi tanada yar ƙiba,amma kuma bayada kunkumi sosai mai cika ido,sannan ba fara bace,saidai sanadiyyar mayuka na zamani,tayi fari tass kaman fatalwa.
Wani shu’umin murmushi tasake mai,dauke da ma’anoni kala kala.
Hafsa ce ta gaishe da ita tareda yi mata bismillar abinci,Jabeer kam ko kallon ta bayyi ba,sauri yake yagama cin abinci yafita wajen aiki.
“Ayya wai break fast,naga kam kuna cikin nishadi sosai,plate É—in jiya na dawo miki dashi”
Ta faɗa tamkar mutuniyar kirki. Jan kujera tayi babu kunya a kusada Jabeer ta zauna tareda yimasa kallo ƙasa ƙasa.
Hafsa tana kallonsu amma ta kawar da kanta tareda zubawa Lubna itama abincin.
Bayan kamar minti biyune Jabeer ya ɗago ya zabgawa lubna harara,saboda yanda take ɗaga ƙafar wandonsa da kafarta ta ƙarƙashin tebur ɗin.
Har ya buÉ—e baki zayyi magana ganin bata daina ba ya fasa,saboda yanda Hafsa ta ajiye cokalin hannunta tana rike cikinta.
Tun kafin Jabeer ya taimaka mata,lubna ta riƙeta tareda yimasa magana ya ɗakko key ɗin motarsa.
Cikin sauri suka nufi asibitin da itah da gaggawa,sai bayan sun isa an shiga da ita É—akine tukunna suka samu damar Æ™iran Hajiyah zeenah,wanda cikin Æ™ankanin lokaci ta tashi hankalinta,sai gata itada Laylah,matar baffansu ABDULLAHI. Sayyada-tateen kam ba’a sanar mata ba,saboda kowa yasan halinta da surutu da É—aga hankali.
Safa da marwa suka fara a bakin labor room É—in,itadai luban kallonsu kawai take,duk sanda suka nuna damuwa Æ™ara bata haushi suke,musamman yanda jabeer yafasa tafiya ko ina,kowa addu’ar ta sauÆ™a lafiya yake,ita babu wanda ya kula da ita.
Ƙara wayarta tayi a cikin jaka,wanda hakan yasa ta nufi wani dan waje gefe da inda suke tsaye.
“Hello Hajiya na É—ebi miki jinin,yanzu zan fito daga ward É—in,sai ki bini zuwa nurse section na baki”
“Okay babu matsala”
Tana kashe wayar tayi murmushin mugunta tareda kallon inda hafsan take kwance,fitowa nurse É—in tayi kanta a sunkuye É—auke da test tube na jini ta nufi sashen su,babu wanda ya kulada ita,domin kowa yayi zaton abu zata kai wani wajen.
Lubna tana ganin hakan ta bi bayan nurse din,saida sukaje inda babu kowa kafin ta tsayah,
“Yawwa gaskiya kinyi Æ™oÆ™ari sosai,ai dama yanda kika faÉ—a cewar kin bata maganin naÆ™uda tasha da safe,shiyasa na shiga sashen domin na biyosu asibitin.
Aikinki ya cika,na tura miki miliyan É—aya acct É—in yanda mukayi nagode ni barina na tafi”
Lubna ta faÉ—a bayan ta karbi jinin tasaka a jaka.
“Kwanan ki ya Æ™are Hafsatuwa kema kaman É—ayar,nariga na faÉ—amuku,duk wacce ta rabeshi to kabarinta ta tona,koda kuwa wacece”…….!!!!!

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama’are

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

No comments