Breaking News

Bakar Ayah 20


Page 🖤20🖤

 

 

“Nayi wa headmaster É—inku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roÆ™eshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana”
“Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga”
“Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene.
Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faÉ—amin wane abin arziÆ™i kikeyi guda É—aya da za’a shaideki da ita”
Yamutsa fuska Bombee tayi tareda tashi daga tabarmar mlm Ahmadu.
“To shikenan baba zanje nayi jarrabawar tunda haka kakeso,babu matsala”
“Yawwa uwata kin kyauta,gwanda kiyi karatu hakan zaifi kyau”
Tundaga wannan zancen mlm Ahmadu yayiwa headmaster maganar jarrabawar tata,ranar daza’a yi kuwa ta shiryah tasaka uniforma É—in da mlm Ahmadu ya É—inka mata,dan cewa tayi fafur bazata saka tsoho ba wanda aka aro mata a anguwa.
Dole sai sabon akayi mata,idan tasaka saita bawa innayi shi.
Fitowa tayi daga É—akinnasu ranar jarabawar,tasha sabon uniform da sandal da safa,sai goge kayan take da handkerchiep kaman gaske,kayan kuwa blue Burberry ne yayi mata kyau sosai.
A bakin ƙofar gida ta hadu da mlm Ahmadu yana zaune a majalisar dattijai,nufarsa tayi tana bubbuɗawa,kana ganinta kasan anyi marar ji,ga kyau irinna maciji.
Sallama tayi a wajen tareda tsugunnawa a gavan su.
“Baba zan tafi jarabawar,a bani kuÉ—in cin abinci,dan sai yamma nadawo”
“To shikenan kokefah uwata,hakan ai yanada kyau sosai,maza ki rubuta mai kyau saboda kiciyo makaranta mai kyau,nasanki da Æ™oÆ™ari dama”
Ɗari biyar ya ɗauko a aljihunsa ya damƙawa Bombee,tasa hannu biyu ta karba tareda yin godiya,kafin ta juya ta tafi.
“Ahh ikon Allah anya kuwa itace?”
“Mlm Audu baban su muruje yafaÉ—a yana jijjiga kai”
“Ita ce mana,girma ne yafara zuwa an fara hankali”
Mlm Ahmadu yafaÉ—a É—auke da murmushi akan fuskarsa,saboda jin daÉ—in yadda Bombee ta nuna hankalin nata a gaban dattijan. Addu’a yayi a ransa akan Allah yasa tacigaba a haka.
A bangaren mutuniyar kuwa tana shan kwanar gidannsu maimakon ta É—au hanyar gidansu sai tayi hanyar jeji.
A hanya tashiga wani gini ta sanja kaya,daganan kuma tayi cikin jejin kanta tsaye.
TadaÉ—e tana tafiyah a cikin jejin kafin ta iso wani gida a dokar jejin.
Hayaƙin dayake tashine mutum zai gane cewar akwai mutum a ciki.
Sallama tayi a bakim ƙofar gidan,muryar wata mata ce ta amsa mata dattijuwa.
“Bombee kece da hantsinnan,shugabannki baya nan yashiga jeji É—azu”
“Gabas yayi ko yamma?”
“Ahah Bombee bazaki bishi ba ke kaÉ—ai kina mace,kinfi ni sanin bayason kina shiga cikin dajinnan ke kaÉ—ai batareda shi ba”
“Haba Inno har yanzu na,babu indan bansani ba a jejinnan,bariki gani”
Tun kafin wacce aka ƙira da inno tace wani abu Bombee ta nausa cikin jejin da gudu.
Gudu takeyi ta hanyar gabas maso kudu a cikin jejin,daga yanda take gudun tana tsallake itatuwan da suke kan hanya mutum zai tabbatar tasan takan hanyar gaba da baya.
Catt taja ta tsayah tanacikin gudun,kaman wanda wani yabata umarnin hakan.
Shuru tayi na wasu Æ´an mintina tareda rufe idonta na É—an wani lokaci.
Sunkuyawa tayi har saida ta fadi a ƙasa,mashin dayazo ta samanta kuma yah caki a jikin bishiyar gefenta.
Tashi tayi tareda yamutsa fuska tana duba bayan rigarta da lakar wajen ta ‘bata mata.
“Haba shugaba,kasa na bata rigata a cikin wajennan”
Wani mutum ne mai tsantsan jiki,farin bafulatani ne,amma kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,duk cewa shekaru sun fara nunawa akan fuskarsa.
Dariya yakeyi tareda tafa hannyensa alamar jinjinawa.
“Da kyau ashedai bakya training a banza,menene yasa kika biyoni cikin daji,sannan ya akayi kikasan ina nan”
“Uhm na karbo kuÉ—in siyan nima kwari da bakata,tsawon lokaci ina tara kudi yau nagama tarawa…..tabb har yanzu bansan inda zan sameka ba,yau fah litinin,nasan dama tanan zaka iyo ai”
“Hmmm da alama ba iya idonki ne yafina sauran mutane fah harda jinki da kuma tunaninki,kinyi Æ™oÆ™ari dakika kaucewa harina,ya akayi kika lallami Babanki har ya baki kuÉ—innan”
“Uhm bani yayi na siyah kayan kwalliyah,shine na taho nan”
“Meyasa bakya son yin abinda iyayenki suka ce toh,kullum ina faÉ—amiki kinada lokacin sanja ra’ayi akan bin hanyata,saboda ke macece ba namijiba”
Shuru Bombee tayi baya amsa masa ba,shima dama yasan bazatayi maganar ba,duk sanda yayi mata maganar tasanja ra’ayi.
Abu ɗayane yasa bai koreta ba shine,yasan idan ya korata gida ma bazata haƙura ba,zatabi wata hanyar ne inda babu mai kallonta ballantana ya kulada itah. Shikuma haka kawai yake jinta a ransa kaman ƴar sa wacce shi Allah bai bashi ba.

 

______****______***_____

Tun ranar da jarabawar su Bombee ta fito yake ta jelen wajen dubawa jarrabawar sa.
A zuwansa na ukune gidan headmastern,ganin abin yazama haka ya faÉ—amasa gaskiyar abinda yake faruwa.
“Mlm Ahmadu nasan kanason maryam (Bombee)tayi jarrabawa domin tayi karatu,amma fah ita ba karatunne a ranta ba,dan dama haka mukayi ta fama da ita lokacin tana gabanmu,tayin wani lokacin sati ma zatazo makarantar ba,duk lokacin data zo kuwa ba iya É—alibai ba,mukammu saita caja mana Æ™waÆ™walwa.
Badan mutuncinka ba dama bazata gama a makarantar muba korarta zamuyi,to yanzu ma zancen danake maka batayi jarabawar taka roƙa tayi ba.
Ko mai kama da ita bamu gani ba a wajen jarabawar,dan haka saikaje ka tambayeta da kanka.
Amma karka ce nina gaya maka,dan tace sai tayiwa É—ana duka idan na faÉ—amaka bata zoba,saboda nasan zata aikata yasa nayi shuru. Amma ganin yanayin daka shiga yasa na faÉ—amaka”
Yana gama faÉ—awa mlm Ahmadu haka yakoma cikin gida yabarshi a tsaye.
Haushine ya kama mlm Ahmadu jin abin Bombee tayi masa,wato dan iskanci babu wata makaranta da taje,shine harda karbar dari biyar babu ko kunya taje ta kashe.
Hanyar gidannsa ya nufa yana saƙawa yana kuncewa. Dabb dazai shiga gida dabara ta faɗo masa. Murmushi ganin yasamu mafitar tunanin dayake ciki.
Yana shigowa gidan yau ko sallama bayyi ba idonsa ya sauƙa kan Bombee,wacce taketa wurga sakwarar da inna laari tayi musu da ranar.
Daneji da Laari kwanonsu É—aya tare suke ci,sai innayi kwanonta daban itama Bombee haka,da farko tare sukeci,tashi É—aya Bombee ta tada tsiyah sai an raba musu kwanon abincin.
Masifah mlm Ahmadu yafara,ta inda yashiga batanan yake fita ba,kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai.
“kee Bombee yanzu dan zabar baki É—aukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?”
“Danajene an gama shiyasa”
“Hmm to shikenan,ki rubuta ki ajiye,aure zan miki kawai na huta dake,tunda kinÆ™i karatu saiki tafi gidan miji?”
Ƴar dariyar tayi irin bata ɗauki maganar da ɗumi ba kafin tace.
“Aure kuma baba abokaina ma fah ba amusu aure ba?”.
“Su suna da hankali,sun É—auki iyayensu da mutunci,sannan kuma dasuka sakasu makaranta sunyi,basuyi taurin kai ba kamar ke,dan haka ko kinÆ™i ko kinso aure zan miki da É—an gidan Jauro da suke Æ™auyen gefenmu,BUBA,dama yace yana sonki nace karatu zakiyi,shima kuma É—an tijarane kaman ke,saiku haÉ—u kuyi da rayuwa tare har lokacin nutsuwa yazo muku.
Ke kuma saiki fara shirye shirye,nan da wata É—aya zansaka bikin,yanxu haka ma wajensa zan nufah”
Yana gama faÉ—in hakan ya kaÉ—a babbar rigarsa ya nufi waje.
Daneji takai lomar abinci bakinta,bata ƙarisa taunata ba ta tashi a wajen cin abincin,abin duniyah duk ya isheta.
Zama tayi a bakin gadonta tayi shuru tana kallon tagar É—akin,rayuwar ta a baya tafara tunawa,yanda ta taso a gidansu cikin kulawa da kuma gata.
Bata taba tunanin zata tsinci kanta a irin wannan rayuwar ba,da farko batayi tunanin yin aureba ba acikin danginsu ba. Haka ta wayi gari tana wajenda babu danginta ko É—ayah,idan wani abu ya sameta,batada kafaÉ—ar dazata jingina tayi kuka,har yau ta gagara sabawa da kaÉ—aicin datake ciki.
Aka zo zuwa lokacin data samu ciki,farincikine ya kamata,ko ba komai zata bude ido taga jininta a gefenta. A haka tafiya tayi tafiyah lokacin guda ta buɗi ido ta kalli ƴar ta kuma jininta a hannunta,a sannan tayi tunanin wahalar ta yanke zata raini ƴar ta cikin gata da soyayya kaman yanda ta samu,Saidai bata saniba ashe tsugunne bata ƙare ba. Sai ƴar ta tazo duniyah ta wata halitta taban,wanda tun a lokacin ta fara hangon irin ƙalulabalen dazasu fuskanta itada ƴar tata,musamman daya kasance cewar dama bakowane ya yarda da ita ba,kullum cikin zargi take akan ita mayyace.
Cikin dadi da babu daÉ—i ta raini Æ´ar tata har zuwa girmanta,a tunanin idan Æ´ar ta jure wahalar yarinta watarana sai labari.
Tashi É—aya sai rishe ya juye da mujiya batareda tayi zato ba,sai yazamana abinda take gudun shiya afku.
Wato ƴar tata tayi nasara buɗe shaiɗanin dake cikin jikinta,wanda sukayi iya ƙoƙarinsu wajen binneshi a jikinnata.
Maimakon zaluntarta da yara sukeyi,sai ya zamo yanzu yaro idan bata ga dama ba ko fita daga cikin gidansu bai isa yi ba.
Abinda take gudun a ƙira ƴar ta dashi yanzu ya gauraye bakin mutanen garin.
“MAYYAH HATSABIBIYA”
To bayan wancan kuma ga wata sabuwar itama ta ‘bullo,auren rashin gata mijinnata ke shirin yiwa Æ´ar tata,duk da tasan laifin na Æ´ar tata ne,amma kuma zuciya babu Æ™ashi,takasa daure hakan a cikin ranta.
Yanzu fargabarta ma É—aya shine,shin Bombee zata yarda ta zauna a gidan auren idan ayi mata,babu abinda ya canza a halittar jikinta na Æ´an adam ta take fuskantar haka,inaga kuma ita a wani yankin daban.

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

No comments