Breaking News

Bakar Ayah 25

 

Page 🖤25🖤

 


 

Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba’a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa.
Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa.
“Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari.
Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni koh,to inaga bakya bukatar sanin mai zai faru.
Yanzu nan zan aikata miki abinda nake aikata wa,saidai ke ta hanyar au…………”
Bata bari ya ƙarisa faɗin abinda yake shirin amayarwa ba tazage iya karfinta ta cankeshi a gabannasa,bayan ta tabbatar yagama sake lagonsa.
Giff ya rufe bakinsa baikai ga karisa maganar dayake mata ba,lokaci ɗayah abubuwa dayawa suka shiga kwakwalwarsa,Azaba,razana da kuma yanda abin yazo masa a bazata.
Kafin yayi wani yunƙuri ya sheme a kasa warwars ko motsi bai sakeyi ba na kirki. Babbar alama ta nuna baƙaramin lahani Bombee tayi masa ba,sanadiyyar dukan data kai masa.
“Yanzu sai naga wane abun zakayi mana abinda kake iƙirarin aikatawa ai,da tunaninka tun farko tsoronka nake,hmmm da alama baka je ka tambayi wacece ni ba,bayan ni nasan waye kai”
Tsugunnawa tayi wajen saitin fuskarsa ta wanke shi da mari tasss.
“Marina dakayi na rama,ina ka mutu ma bana binka bashi,dan hakan sai ya dameni,idan na tuna ka mareni ka mutu ban rama ba”
Mayafinta ta ɗauka yafa kafin ta dauki duk abinda tasan tana buƙata ta tsallakeshi ta bar dakin.
Batareda kowa yaganta ba tafita daga gidan sai cikin garinsu.
Lokacin data isa dare ya ɗan yafara.
Babu kowa a tsakar gidansu lokacin data shiga,dan haka kai tsaye ɗakinsu ta wuce,babu kowa a ciki da alama innayi tana ɗakin innarta.
Gadonta ta kaɗe hankali kwance ta kwanta.
Sai muce saida safe…………………

 

Da safe indo ce yauma takawo musu abinci kaman jiya,mamaki tayi ganin ƙofar wangale ko turata ba’ayi ba.
Har ta juya zata tafi sai kuma tagano kaman ƙafar goje yana kwance a tsakar ɗakin.
To shikuma yau kwayar kwanciyar ƙasa ta gara masa,hmmm ko ya murƙushe ƴar mutane har saida yagaji kai,maganinta ai ba ita marar kunya ba.
Ajiye kwanon tayi zata tafi,har ta bar ƙofar saikuma ta dawo tafara kiran Bombee.
Kira uku tayi mata amma shuru ba’a amsa mata ba.
Uhm barina duba koya jimaya rauni,ƴar mutane ta mutu mana mushiga uku.
Tura ƙofar ɗakin tayi ta leƙa kan gadon,amma babu kowa akai,sannan babu alamar an kwana ma akai,dan shinfiɗinsa yana nan rass.
Wajen banɗaki taje nan ma babu alamar mutum a ciki,hakanne yasa ta dawo ɗakin ta sauri domin ta tashi goje.
Shurarsa tayi taƙafarta amma shuru bai tashi ba,hasalima ko motsi bayayi,kuma numfashinsa ma baya fita kamar na mai bacci.
Jini ta gani yafito ya bushe a ƙasan gajeren wandonsa dayake mai haske ne.
Ihu ta kurma iya karfinta tana ƙiran inna daayi.
Jin ƙiran bana lafiya bane yasa ta taho da gudu zaninta ma a hanya ta karisa gyarashi,don ita duk a zatonta ma goje ne yayiwa Bombee aika aika,dan dama tun jiya sun saka tsammanin faruwar hakan.
Saidai tana zuwa wajen saita tarar sa’banin abinda take tsammani.
Indo ce akan goje har sannan tana jijjigashi amma yaƙi tashi,sai ihu take tana ƙiran sunansa.
Suna cikin hayaniya ne jauro yashigo wajenna su jin suna kiran sunan goje suna salati da kuma ihu.
“Yau nashigesu ni daayi,mlm zoka gani anya kuwa ba barayine suka shigo gidanann ba,shi yana kwance da alama dukansa akayi,itakuma Bombee batanan,kar ko ɗauketa sukayi kai?”
“Kinga bar wannan zaton,maza maza ɗakko mayafinki barina je wajen garba yazo da motarsa mukaishi cikin gari asibiti”
Cikin ƙanƙanin lokaci jauro yadawo suka ciccibeshi zuwa cikin motar sai asibiti.
Suna zuwa kuwa aka shiga dashi ɗakin gaggawa,zuwa lokacin ya farfaɗo,amma daƙyar yake motsi,kana ganinsa kasan yana cikin mawuyacin hali.

Tun takwas suka kawoshi asibitin,sai wajen goma kafin ya farka sosai,shima dan anyi masa alluraine dakuma bashi magunguna da karin ruwa.
Dan sanda jauro yaɗakko domin abin dole saidasu a ciki,saboda ana buƙatar sanin wanda yayi masa wannan lahani har cikin ɗaki.
Tareda ƴan sandan dakuma jauro aka shiga ɗakin asibitin inda goje yake kwance.
Dare ɗaya har ya rame ya fita a hayyacinsa,silin yake kalla yayi shuru,da alama yatafi kogin tunani,cinyoyinsa kuma an ɗaɗɗauresu da wasu karafuna a jikin gadon.
Dan sandanne ya kariso inda yake a hankali cikin jimamin halin dayake ciki.
“Sannnu fah ya jikin,dan Allah idan bazaka damu ba shin zaka iya faɗamana mai yafaru?”
“Bbboombiiii”
Dukkansu zaro ido sukayi,dansun fahimci inda zancennasu ya dosa,dan dama likitan yafadamusu farmakarsa akayi a gabansa da duka,wanda hakan ya jawo masa matsala,har sannan basu gama gano mai yake faruwa ba.
“Wacece Bombee kuma,ko wacce nasani ƴar gidan mlm Ahmadu??”
“Eh ita fah,kuma matarsa ce jiya shekaranjiya aka kaita ɗakinsa”
“Tohh abin daban mamaki,yanzu dai muje gidannsu muji mai ya faru,dan bazata wuce gidan ba,tunda mungane ba wasune suka farmakesu ba”
“Hoɗan wannan yarinya anya kuwa mutum ce?”
Jauro ya faɗa cikin mamaki.
“Aiko aljanace sai tasan tayi wannan aika aikar,kuma fah babu itace a ɗakin wanda ta dakeshi dashi”
“Hakane kam inna,ita sai anyi mata hukunci daidai laifinta,ni da kasheta ma sukayi”
Inna daayi ce ta kwabe mata bako ganin dan sandan yana wajen.
Shawarar ɗan sandan suka bi,ita inna daayi da indo suka zauna a wajensa,shikuma jauro da ɗan sandan suka nufi gidansu Bombee.
Tunda ta nuƙo hayar kyauyennasu tashigo gidansu ,data kwanta ba ita ta tashi ba sai ƙarfe goma.
Buɗe ɗakin tayi tafito daga tana mika tareda yin hamma,alamar mutum yayi bacci ya more.
Da inna laari suka haɗa ido tana bakin ƙofar ɗakinta.
“Innalillahi wa inna ilaihi ra ji’un mai zan gani haka ni laari,ko gizo ne take min kai”
“Mai ya faru yawuro kike wannan salatin,gamo kikayi da safiyah”
“Malm inaga gamo nayi,Bombee fah nake gani tafito daga ɗakinsu,anya kuwa kalau nake”
Daneji dake daki tana shiryawa Addarta Hadiza kayansu zasu tafi,batasan lokacin da ƙirjinta yai wani daramm ba,duk da hakan ba abune da zata gasgata ba,saidai kuma hmmm Bombee ce fah?
Maryam ce tashigo ɗakin bayan ta ajiye butar hannunta tareda cewa cikin hausarta mai haɗe da fillansi.
“Inna Daneji dagaske fah take Bombee ce a tsakar gida,kuma daga yanayinta kaman a gidanann ta kwana,dan fuskarta yayi kama da wacce ta tashi daga bacci”
Tun kafin Daneji tagama jin ƙarishen maganar ta daka tsalle sai gata a waje.
Haɗa ido sukayi da Bombee wacce tayi saurin dauke idonta tana kallon kasa.
Shurune ya ratsa wajen na ƴan wasu mintuna,kowa yarasama mai zaice mata.
Ɗaga idonta tayi a hankali tana ƙarewa mutanen dasuke wajen kallo,ƴan gidannasu ne dukka inka ɗauke innayi datake makaranta,sai kuma ƴan uwan Daneji dasuke shirin tafiya a lokacin. Daga gefe kuma Hajiya Dadda ce yayar babansu wacce take zaune a taraba,itama shirin tafiyar take a ɗakin inna laari,tajiyo wani sabon batu wai amarya a gidan ta kwana,sai yanxu suka ganta kwatsam da safe.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana bayan yagama shurun takaicin.
Baikai ga cewa komai ba sukaji muryar Jauro a ƙofar gida,da kuma muryar wani mutum daban da basu wayeshi ba.
Fita yayi wajen gun sallamar,dan yasan bazai wuce ta dalilin Bombee ba.
Shigowa yayi dasu cikin gidan,dan inya tsayah yi musu magana ma bai san mai zaice musu ba,wataƙila ma sunfishi samun masaniyar abinda yake faruwa.
“To ga surukinki nan,saiki faɗamana meyasa kika dawo gida,kuma ma dan iskanci wai a gidana kika kwana ban sani ba,bayan na kaiki ɗakinki shekaranjiyah”
“Hmmm mlm Ahmadu kenan,ɗazu fah naji kururuwar iyalina,ina zuwa na tarar da goje a kwance kaman gawa. Nan muka ciccibeshi sai asibiti,da farko nayi tunanin wasune suka kawo masa farmaki.
Amma abin mamaki daya farfaɗo sai yake faɗamana wai matarsa ce tayi masa haka wannan aikin.
Zancen danake masa yanzu haka likita yabamu bayanin da ƙyar ya iya haihuwa,saboda dukan datayi masa a gabansa da daddaren”
“Meeee????”
Dukkansu suka haɗa baki suna kallon Bombee wacce ta cuno baki,lokaci ɗaya kuma tafashe da kuka kaman ba ita ba,ihu take jikinta har rawa yake,cikin marairaiciyar murya ta kalli babannata tareda cewa.
“Baaaba wlh kaman yanda nace muku na yarda ayi auren banyi niyyar yin komai ba. Ranar da aka kaini baidawo gidan ba,sai jiya da daddare yashigo min ɗaki yana maganganun maye na shaye shaye,bance masa komai ba yah wanka min mari,kaga ma wajen.” Ta faɗa tana nuna marin dayake kwance a fuskarta.
“Daga nan kuma yafara tahowa inda nake ina matsawa har jikin bango,ni bansan mai zaimin ba sai yacire wandonsa yana dariyah.
Abin mamaki yabani ganin babba yacire wandonsa,kuma sai ya fara maganar data bani tsoro.
Wai abinda yakeyiwa mata a gari nima shizaimin wato fyaɗe,cikim tsoro saboda na kare kaina nakai masa duka a wajen,saboda a ganina hakan zaisa ya ƙaleni. Bansan zai faɗi ƙasa ba aradu……kkkuma tsoro naji danaga yanda yayi wa Atika akace ta suma ankaita asibiti,shiyasa na kaimasa naushi,daga haka ban kwaɗa masa komai ba,inaga bayan na tahone saboda kar ya tashi ya rama,wani kuma yaje ya dakeshin….”
Ƙarisa maganar tayi tana share hawayen dayake fitowa a idonta.
Duk wajen a yanda suka saurari zancennata sun tabbatar,batada ilimi akan abinda goje ke shirin yimata,sannann batayi tsammanin dukan datayimasa zai masa illah haka ba.
Inna laari ce takalleta tareda cewa.
“Kina nufin kice bakisan abinda goje zai miki,shin ina maganganun dana faɗamiki kafin akaiki gidannaki?”
“Iyeee nifah banji mai kuke cewa ba a ɗakin baba rannan,dan kafin mu shiga na toshe kunnena,saboda kar naji abinda kuke faɗa nayi kuka. Ji nayi ana cewa wai duk wanda yaji abinda ake fada masa kafin akaishi gidan miji to zayyi ta kuka,nikuma banason nayi kuka shiyasa na toshe kunnena”

Toh fah ga wata katobarar ta kawo kai,Bombee bataji hudubar da akayi mata ba🤣🤣🤣🤣.

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

No comments