Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bakar Ayah 28


Page 🖤28🖤

 

 

 

Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa.
Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi.
Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi.
Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan.
A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya hau,saidai ba’a bashi gado ba gida suka dawo,tunda bayyi tsanani sosai ba.
Amma tunda suka dawo da la’asar har yanzu bai sake magana ba.
Runtse ido tayi lokacin da labarin ya riski kunnenta,babu makawa tasan itace silar hakan.
Saurin kawar da fuskar tausayin datake ciki tayi,tareda jan numfashi dogo kana ta furzarshi.
Kai tsaye cikin daji ta nufa ta mungun gudu,wanda kowa yakalli hakan yasan da gangan takeyi saboda ta gajiyar da jikinta,aikuwa abinda take nema ta samu,dan daƙyar da ƙarisa filin yin gwajinnata tana maida numfashi.
Idonta ne yasauƙa akan haidar wanda yake zaune akan reshen bishiya yana jin tuffah(Apple)a hannunsa.
“Wow irin wannan gudu haka kaman barewa,daga nesa fah nakejin ƙarar gudunki,anya kuwa ke mutumce,karfah nace da aljana nakeson yin abota”
Tubbbb ta tofar da wayu tareda watsa masa harara tace.
“Wai miye hadina dakaine,sannan da izinin wa kakeson shiga gonata?”
“Gona kuma,bakiyi shuka a wajen ba fah,in ma akwai ni bangani ba gaskiya”
Yakarisa maganar yana duban wajen a cikin fuskar zolaya.
Zaro ido yayi tareda matsar da kansa gefe guda,cattt kuwa ƙaramar wuƙar ta caku a jikin bishyar dayake kai.
Kafin ya dawo hayyacinsa sai ganinta yayi akan reshen a gefensa,fuskakokinsu suna tabb dana juna,ta zuba masa wannan fitinannun idanuwannata masu launin shuɗi a cikin nasa.
“Kutt kasheni zakiyi,sannan kuma yaushe kikazo wajennan iyeee?”
“Ba wannan na tambayeka ba,meyasa kakeson shiga rayuwata,wani ne ya aikoka? Sannan mai kake so dakake bibiyata,na daɗe ina kulada kai a wajennan tsawon sati guda,da farko banyi zaton nikake bibiya ba,sai daga baya na kulada hakan,waye kaiiiii?”
Tafaɗa cikin tsawa tareda dasa masa wuka a kan wuyansa.
“Habaaaa Bombee mai yayi zafi shiba wuta bane,babu abinda nake binki dashi,jarumtarki da kuma yanayinki ne kawai yake birgen,shiyasa nakeson ƙulla abota dake,bayan hakan kuma dama banga kowa a cikin wajenba wanda zanje wajensa”
“Daga ina kake?”
“Kaman yanda na faɗamiki sunana Aliyu,ni ɗan gidan General Muhammad Bello ne. An kawoshi nannne saboda wani case ɗin manyan yan fashi dayake wakana”
Gidanmu nacan ɗayar hanyar ba wacce kikebi idan zaki je gidan maharbinna ba.”
Sauƙowa tayi daga kan bishiyar ta soke wuƙar a kumkumin ta inda tacireta.
“Kaine mutum na farko daya tunkareni da niyyar abota batareda wani dalili ba,kodayake yanada nasaba da cewar baka sanni ba”
“Menene yasa baza’ayi abota dake ba,you are very “interested lady”
“Wanne yarene haka kayi magana dashi,uhm kaman yana kama da wanda malamai da copper ko kuma masu bibiyar wannan jejin suke magana dashi”
“Kutt bakisan turanci ba kina nigeria”
“Nasanshi yanda kayine yamin kama da ba irin na sauran ba”
“Hhhh inaga saboda ba a ƙasar nan nake zaune bane,nazo hutune na shekara guda shiyasa na biyoshi nan domin naga ya wajen yake. Baki amsamin tambaya ta ba,meyasa suke tsoronki”
“Kai baka gani ba,a ganina dai kaiba makaho bane,suna ganin kaman ni ba mutum bace saboda idanuwana”
Dariyah Haidar ya sheqe da ita,wanda hakan yasa Bombee binsa da kallon kaman yasamu tabin hankali.
“Wani blue iris ɗinki,da farko nayi mamaki kam sosai,amma kuma nida na zauna a ingland naga masu irin idonki da yawa,hmmm saidai gaskiya nasu baya shining kaman naki,amma duk wanda yagani yasan ai normal ne,akwai masu abubuwa rare da dama a duniyah”
zaro ido Bombee tayi jin daya faɗa mata cewar akwai masu irin halittarta a cikin duniyar nan a wani wajen nesa da ita,lokaci guda sai kwaɗayin da haɗu dasu yafara shiga cikin ranta.
Tambayoyi Bombee take yimasa yana bata amsa,wani yayi mata dariyah wani kuma kawai yabata amsa.
Lokaci ɗaya sai tasamu kanta da sakewa dashi batareda ta sani ba.
Shikuma ganin tasake tana maganar arziki dashi,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba haɗeda dauke kewa.
Basu ankaraba suna ta surutu sai gani sukayi rana tayi sosai.
Tashi Haidar tayi taga bakin ruwan dayake zaune ya kalli Bombee.
“Nikam barina tafi,sai anjima zan dawo,daganan zaki fara koyamun wasannan dakike da sanda”
Dariyah tayi tareda cewa.
“Lallai kuwa wasa,abinda nake yayi maka kama da wasa koh?”
“Komai dai menene nina tafi”
Ya juyah zai tafi saikuma taga ya tsaya,kasancewar ruwan take kallah batasan mai ya gani ba.
Muryar da bazata taba mantawa ba taji ya daki dodon kunnenta.
“Heheehhe iyeeee kice kin samu duniya kam,tunda har ɗan matashin saurayi kikayi bansani ba,da izinin wa kike gara rayuwarki haka”
“Da izinina mana,da dana wa zanyi,sannan menene ya kawoka inda nake?”
“Saboda na kwashi romon da bankai ga shaba kika katseni”
Ƴar dariya Bombee tayi tana kallon goje wanda yake tsaye tareda maza gudan huɗu ,bibbiyu a kowanne gefe.
“Ta yaya marar ƙafa zai hau tsani(bladder)? Uhm”
“Idan an hau masa ai ya wadatar,koda shi baxai iya hawa ba,a tunaninki dan bazan iya farmakarki ba shikenan zan bar abinda kikayimin ya tafi a banza ne,yau babu mai ƙwatarki a hannuna,saina maidake abun tausayi,abinda zanyi miki sai ya kafa tarihi a garinnan,dan ba’a taba yiwa wani mahaluƙi irinsa ba”
Yana maganar gashin bakinsa yana ɗagawa,sannan yana haɗawa da dariyar mugunta. Tashi Bombee tayi daga inda take tareda kallon Haidar.
“Haidar kabar wajennan yanzunnan kar abinda zai faru yashafeka,karka damu bazan bari su bika ba,kabi ta bayana ka gudu”
“Ke kuma fah,kina ganin zaki iya da wannan mutanen,su waye su ɗin,sannan me suke nema a wajenki”
“Karka damu dani,zancen suwayd kuma bazan samu damar baka bayani akai ba yanzu,amma idan na rayu ko mun sake haɗuwa za faɗamaka”
Tana gama maganar ta turashi ta bayanta tareda yimasa kallon umarnin dole ya bar wajen.
Yana tafiyah kuwa taji muryar goje yana cewa
“Iyeee kice dagaske ashe kina sonsa tunda har kareshi kike,karki damu babu abinda zanyi masa,zaifi ciwo ma idan yaga masoyiyarsa anyi mata fata fata,zan in yanada wayo shin zai ƙara sonki? Ku lahanta min ita tukunna mazaje”
Yafaɗa cikin gunji.
Farmakarta sukayi a tareda da nufin kaimata mungun duka,saidai cikin sa’a tasamu nasarar tsallakewa ta hanyar yin tsalle tareda riƙe rishen bishiyar da take samanta.
Wuƙar kunkuminta taciro ta sokawa ɗayah a gadon bayansa,aikuwa yafasa ihu yayinda yaji azabar ta ratsashi.
Komawa dabaya sukayi ganin an shafe kusan daƙiƙa ashirin basu samu nasarar tabata ba.
“Kai ogah yarinyar fah ta iya faɗa da alama,ya kake ganin za’ayi?”
“Kuje mata kuma salon dabara mana”
Suna cikin hakanne goje ya sanɗeta tajuya baya ya sake mata sanda a gadon baya,kasa jure zafin dukan tayi,dan haka tafaɗi kasa tana maida numfashin wahala.
Wani sandan goje yasake narka mata a ciki,tasaki kukan mai nuna Alamar dukan ya shigeta.
“Wai ke mai iya faɗa koh,birice ke yau taki taƙare”
Duka yacigaba da kaimata ta ko’ina,babu tausayi babu imani. Tun Bombee tana nishi har yazamo jin dukan take kawai yana shiga jikinta.
Tsugunnawa yayi saitin fuskarta yana kallonta ɗauke da murmushi mugunta akan fuskarsa.
“Kai tulezi ku buɗemin ita ku fara yimata fyade har saina ce ku daina tukunna”
Rufe idonta tayi kirif tana jira taji ta inda zasu shigeta su keta mata mutunci. Duk iya kokarinta wajen ganin ya motsa gabobin jikinta abin ya faskara,dan kamar basa karbar saƙonta ma ballantana su motsa ɗin.
Shirinyewa tayi ta saddaqar tata taƙare daga wajen,a sama sama tajiyo hayaniyar mutane da kuma sautin takalmansu,wanda ta tabbatar bana masu yimata aika aikar bane.
Sakin ta taji sunyi sun nausa cikin jejin,yayin da karar sawunsu yake yin nisa,ƙarar na wasu kuma ya dunfarowa inda take kwance………bata san shin masu cetonta bane ko kuma masu cutar da ita.
Ɗagata taji anyi an sakata a cikin wani abu mai tafiyah.

Sorry ayi hakuri a barshi haka,🤣🤣🤣🤣 bansan mai zance ba

 

 

 

 

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Post a Comment for "Bakar Ayah 28"