Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Duk karfin Izzata Book 1 Page 13

Episode 13*


Tana ganin jabir ya ɗaga hannun zai mareta tafasa kara tafaɗi kasa tana birgima kamar mai aljanu ” bashiri jabir ya jabirki ya tsaya yana kallo ikon allah ” da sauri su hiyana sukayi kanta suna kiran sunanta ” chikin tsawa diyana ke magana ni basunana diyanaba ni sunana bilkisu, ha,ha,ha ta

kwashe da dariya ” a tsorace Zahra ke faɗin munshiga uku yaukam me kuma yasamu diyana ” hiyana kam ko ajikinta dan tasan iskanchin diyana yawuche hakan ” chikin tsawa diyana tace kai jabir zo nan ai nafaɗamaka daman niche zanyi magananin’ka ” jabir najin haka ya kwasa aguje yabar wajen ” Zahra kam tagama tsorata baya baya tafara jaa tana salati ” hiyana lamrat amrat kuwa ko ajikinsu saboda sunsan halinta daman ” diyana naganin jabir ya gudu tamike tana faɗin nizakawa iskanchi wlh nafika iyawa muzuba mugani ae kai karamin ɗan iskane ” a sukwane Zahra tamike tana kallon ikon allah ” mekuma kuke kallona haka chewar diyana tayi maganar tana kokarin mikewa, bayan tamike tsaye ta dubi su hiyana tace sai kutashi mutafi class ae tun da ɗan iskan ya gudu,
hanyar class nasu tanufa abunta tafiya take hankali kwanche, hartakai kusa da class nasu saikuma ta juyo yadda tabarsu haka tajuyo ta gansu ko motsi basuyiba Sun zuba mata ido ” murguɗa baki tayi kana tace kuchigaba dazama allah yasa yadawo yasameku nikam kunga shigana class tana gama faɗin haka tasa kai tawuche chikin class nasu abunta

Hiyana ta mike taje ta dafa Zahra tafara magana Aunty Zahra naga kin tsorata to wlh indai diyana che kaɗanma kika gani dan wlh abun dayafi wan nan zata aikata ” dogon nunfashi zahra taja haɗe da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya kana tace yanzu hiyana kina nufin kichemin ba aljanubane sukayi magana yanzu diyana che, kuma yanzu diyaya ita ta iya zama ta shirya wan nan wasan kwai kwayon ” shakka babu Aunty zahra duk abun da kika gani shiryashi diyana tayi ba gaskiya bane chewar hiyana ” shiru Zahra tayi tana tunanin itafa lamarin diyana yafara bata tsoro tayi nisa chikin tunani taji, lamrat ta taɓata tana faɗin Aunty Zahra muje dan idan kika biyewa Aunty diyana wlh yau bazaki shiga class ba jiki ba kwari Zahra tafara tafiya tana faɗin yanzu idan jabir yaganefa ” wan nankuma matsalarsu, che shida diyana tunda ita tamasa chewar hiyana ” lamrat kuwa chewa tayi wlh ninasan ko jabir yagane Aunty diyana zata nemawa kanta mafita ” ajiyar zuchiya Zahra ta sauke san nan tace to shike nan allah ya karemu gaba ɗaya tayi maganar tana kokarin shiga class nasu sai anjima sukawa juna hiyana ma tawuche nasu class ɗin suma su lamrat kowache tawuche class nasu

Karfe 3 na rana anbuga bell na tashi gaba ɗaya ɗalibai sun fito suma su hiyana sun haɗe kansu suka nufi wajen dasuke tsayawa sunajiran drivers nasu, suna tsaye suna yar hirarsu sai ga faria ma da fara’a suka gaisa da hiyana dakuma diyana lamrat da amrat kuma suka gaisheta ta amsa da fara’a ” daga bayansu sukaji an daka musu tsawa, a na faɗin ke nizakiwa karyan aljanu koh to wlh yau sai kin gommace da’baki zo duniyar bama da sauri gaba ɗayansu suka juya ” diyana zatayi magana sukaji jiniyar motochin ɗaukansu ” hiyana na ganin motochin ɗaukar’su, batasan lokachin datache alhamdulliah ba ” Zahra kuwa tun motochin basu gama parking ba ta zura a guje tabuɗe kofar motar tashiga tana sauke ajiyar zuchiya ” lamrat da amrat ma motar’su suka nufa da sauri sukabar hiyana da diyana tsaye awajen ” jabir naganin motochin’su yaju yabar wajen yana faɗin zamu haɗu gobene wlh zakisani inna rikeki ” diyana naganin jabir ya tafi ta murguɗa baki tana faɗin kadaɗe baka dau matakiba wlh ɗan rainin wayyo zanyi maganinkane allah yakaimu goben kagani nidakai wazaiyi winner ” baki buɗe hiyana ke kallan diyana tana tunani a chikin zuchiyarta wai diyana kam bata da tsorone a rayuwarta ” tayi nisa chikin tunaninta tajiyo muryan diyana na faɗin to kekuma me yatsayar dake inbazaki zoba saimu tafi mubarki da jabir ɗin ” mamakine yakama hiyana wai yaushe diyana ta barwajen nan jiki ba kwari tanufi motar drivers ɗin na tsaye suna kallonsu sunasan tambayatsu lfy amma suna tsoro dan hakan bata shafi aikinsuba ” hiyana nashiga motar suma drivers ɗin suka koma chikin motar suka tayar da’ gudu sukabar makarantar.

Yau kwana biyar ke nan datafiyar su mai martaba Umrah

SAUDIA

Misalin karfe 10 na dare Aryan Aiman yusuf Ahmad Khalid suna zaune a palon hotel ɗin da suka sauka hirasuke gaba ɗayansu ban da Aryan daya zauna shiru kamar bashi a ɗakin ” Khalid ne ya ɗan taba shi ” a ɗan firgiche ya ɗago ash eyes ɗin nan nasa yana kallan khalid ” lfy meke damun ka gaba ɗaya naga kamar mood naka ya chanza chewar Khalid ” iska mai zafi Aryan ya fuszar daga bakinsa kafin yasoma magana babu komai kawai inatunanin intashi inje induba prince ne naga wunin yau shiru banji motsinsaba ” satar kallan yusuf Khalid yayi san nan yace ok to kaje kadubashi mana ” mikewa Aryan yayi yanufi staircase ɗin ya haura sama ” murmushi Yusuf yayi yana kallan Khalid ” harara Aiman ke wugawa yusuf tare da faɗin me kuke kullawa ” shima Yusuf yadawo masa da harara yana faɗin mekuma zamu kulla ” tsaki Aiman yaja san nan yamike yana faɗin zakusani dai kubi a hankali dankuwa idan ta kwaɓe muku kunsan sauran ” kallan sama da kasa Khalid yawa Aiman san nan yaja tsaki yace. To kayi rashin sa’a nine babba ba kaine babba a kainaba dazaka tsaya kana faɗamin zanchen banza ni wuche kabani waje hai ” tsaki Aiman yaja san nan ya wuche yanufi staircase ɗin ” dawo da kallansa Khalid yayi kan Ahmad dake zaune ya zuba musu ido to kaima mekake jira dabaka’wuche kabi husainin nakaba ” dariya Ahmad yayi san nan yace gulma natsaya jimana ai yau munraba gari da husainin nawa dannikam sainaji gulmar ” Khalid bai sake maganaba sai daima yachiro wayarsa yafara neman layin Zahra ” wayar nafara ringing yamike yana chewa Yusuf kasameni a ɗaki san nan yawuche ” mikewa Yusuf ɗinma yayi ya kyale Ahmad awajen yanufi staircase ɗin shima kai tsaye ɗakin Khalid yanufa da sallama yashiga zaune yasamu Khalid yana waya da zahra, hannu kawai Yusuf yasa ya amshi wayar kana yasa akunnensa yana jiyo hayaniyar, kannen nasu ” ina my baby abunda Yusuf yace da zahra ke nan ” da sauri zahra tace gatanan tamikawa lamrat wayar ” hello yaya Yusuf ina wuni ” lunshe ido Yusuf yayi san nan yabuɗe yana faɗin lfy my baby ya school ” alhamdulillah lamrat tabashi amsa ” shiru yaɗanyi kafin yafurta tsarabar me kikeso inkawo miki ” babu komai yaya Yusuf Allah dai yadawo daku lfy shine fatanmu chewar lamrat ” bakaramin daɗi Yusuf yajiba azuchiyarsa yafa tunanin yarinya karama da hankalin manya yana chikin tunani yajiyo muryarta tana faɗin allah yaya Yusuf kewarka nake sosai da sosai ” sake lunshe ido Yusuf yayi yana murnushi farinchiki kasa kasa yace my baby nima nayi missed naki sosaifa ” a shagwabe tace to yaushe zaku dawo ” Yusuf zaiyi magana Khalid ya amshi wayar yana faɗin inyamaka zafi kasaya mata nata wayar yayi maganar tare da mikewa yanufi waje ” murnushi Yusuf yayi san nan yafurta nice idea yana gama faɗin haka ya haye gadan Khalid yayi kwanchiyarsa

Khalid kuwa yana fita kai tsaye ɗakin Aryan yanufa da sallama Khalid yashiga Aryan baya ɗakin dan haka khalid yafito yanufi ɗakin DON da sallama yashiga zaune yasamesu kan kadon, suna fuskantar juna da alama magana mai muhim’manchi suke ” jin sallamar Khalid yasa dukkansu suka juyo suna kallansa ” ƙarisa shiga chikin ɗakin Khalid yayi shima ya haye gadan ya zauna a nutse yafara magana
Aryan wai meke damun kane naga gaba ɗaya yau ka chanza ne gashi ka ɗan rame kamar baka da lfy chewar Khalid ” daga green eyes nashi sama DON yayi kamar mai kallan wani abu kamar kuma mai tunani ” zuba mishi ido Aryan da Khalid sukayi suna kallansa ” jimkaɗan ya sauke kansa tare da furzar da iska daga bakinsa ya tsare Aryan da ido sosai yake kallansa ” nantake Aryan ya mike kamar mara gaskiya yana kokarin sauka daga gadon kamar daga sama yaji muryan DON yana faɗin me kake ɓoyemin ashe akoi abunda bai kamata nasaniba a dangane da kai, kodai matsayina bai kai bane ” jin maganar DON yasa Aryan saurin juyowa yana kallansu shiru yaɗanyi kafin nan yace. Taya kake tunanin akoi abun da zan boyemaka dangane dani kai’nefa ni kuma nine kai SO bawani abun boye boye a tsakaninmu wlh kawai bana jin daɗine ni kaina bansan meke damuna ba kwata kwata nakasa samun nitsuwa ” shin akoi wani abu mai mahim manchin daka rabu dashine dazaisa kakasa nitsuwa DON yajefo ma Aryan tambayar bazata ” aa nikuma ina dawani abu mai muhim’manchi dayawuche kune ai kune kawai masu muhim’manchi a rayuwata ” Khalid dai ido kawai yake binsu dashi yadda suke maganar burgesa suke DON akoi kokolwa sosai akoi basira Aryan kuwa akoi wayau sosai shiyasa haɗin nasu yake bada chitta ” barchi nakeji kaina chiwo yake min zanje na kwanta chewar Aryan yayi maganar tare da juyawa yachigaba da tafiya har yakai bakin kofa sai yaji muryan DON yana faɗin idanma baka faɗamin yanzuba nasan dole gaba zanji ai ” shiru kawai Aryan yayi bai tankaba saima kara sauri dayayi yabar ɗakin

Dawo da kallansa DON yayi kan Khalid yana faɗin akoi abun dake damun ɗan uwana tabbas ba lfy yakeba ” murmushi kaɗan Khalid yayi a zuchiyarsa kuwa yace baridai ya ɗan latsa DON yaji yazasu kare ajiyar zuchiya ya sauke san nan yadubi DON yace kasani kodai yafaɗa soyayyane ” a zafafafe DON yace what ? hauka yakene kataɓa ganin yana magana da watane ma NO hakan ma bazai yuwuba ” mamakine yakama Khalid ganin daga maganar mace DON ya sauya kamar bashiba ” nantake ya kara ɗaure fuskar nan kamar baisan me dariyaba Khalid yayi nisa chikin tunani muryan DON takatse masa tunani ” Khalid i said get out ” kallon DON Khalid yake da mamaki ba musu ya sauka daga gadan dan yasan halin DON yanzu idan yace zai biye masa sai abun yakai’su ga ɓachin rai ” fitowa Khalid yayi daga ɗakin DON kai tsaye yanufi ɗakin Aryan

Da sallama yashiga zaune yasamu Aryan a tsakiyar gado ” ba karamin mamaki Khalid yayiba ganinsa zaune karisawa chikin ɗakin yayi ya zauna a bakin gadon ” sai lokachin Aryan ya juyo yana kallansa ” lfy bakayi barchiba aryan Khalid yajefo masa tambaya ” iska mai zafi ya furzar daga bakinsa calmly yafara magana nasaba da shan coffee kafin nayi barchine Khalid dazun nayi order coffee sun kawomin amma ɗan ɗanon bai minba kwata kwata na gida nake buƙata shiyasama kaga nakasa barchi ” hannu Khalid yasa a aljihun wandansa ya ɗauki wayarsa yafara kiran layin zahra dan kuwa yanzu yagane matsalar Aryan ” bugu ɗaya Zahra ta ɗaga tana faɗin yaya Khalid ɗazun muna hira ka gudu ” yanzu me kuke bakuyi barchiba Khalid yajefo mata tambaya ” karatu mukayi amma yanzu zamu kwanta ai tabashi amsa ” ok ina diyana ” gata nan inbatane chewar Zahra ” eh bata yayi maganar tare da mayar da wayar a H-free ” ansar wayar diyana tayi chikin voice kamar mai jin barchi tafa magana yaya Khalid shine baka nemeniba tun ɗazun inajin kana magana dasu zahra inasu Ammi ” suna lfy allah sarki na mantane amma ai gashi yanzu na nemeki Koh ” yauwa yaya Khalid daman inasan in’tambayeka chewar diyana ” ok tambayi ” wai a chan makkan wake kaiwa yaya Aryan coffee ” jin tambayar nata yasa Khalid ɗago ido yana kallan Aryan shima Aryan ɗin shiyake kallo ” dawo da kallansa Khalid yayi kan wayar san nan yace bari nabawa yaya Aryan ɗin sai ki tambayesa Koh bai jira amsar taba yamikawa Aryan wayan ” ba musu yasa hannu ya karɓi wayar yana sauke ajiyar zuchiya ” Khalid na mika masa wayar ya mike yace kuyi magana inazuwa yana gama faɗin hakan yafiche daga dakin da sauri yana murmushi

Calmly Aryan yafara magana hello ” ina wuni yaya Aryan chewar diyana ” wani murmushi Aryan yayi kafin tace lfy y school ” alhadulillah tabashi amsa ” good yace saikuma sukayi shiru dukkansu ” chankuma sai diyana tace yaya Aryan wayake kawo maka coffee a makkan ” murmushi ya ɗanyi kafin ya burta babu kowa ” yanzu ke nan bakashan coffee ɗin ” eh bana sha yabata amsa a takaice ” Allah sarki da ina nan dana rinƙa kawoma ai ” Aryan baimasan san da dariya ta kubche masaba dan yadda ta furta Allah sarki bakaramin dariya tabashiba amma sai ya danne dariyar yace ashe kinaso na bansaniba ashe kina tausayina ” aa bana sonka inadai tausayinka chewar diyana ” to meyasa bakisona ” shiru ta ɗanyi san nan tace kai’ma ai bakasona ne shiyasa nima bansanka ” to wayace maki ni banasonki ” Allah yaya Aryan basai anfaɗaminba ni da kaina nasani baka sona dan inkana sona bazakache zaka harbeni da bindiga namutu kowa yahutaba ” shiru yayi yana tunanin sai yanzu yagane kuskurensa namata barazana da hakan shi yamata chikin wasa itakuma ashe tarike a matsayin gaske yayi nisa chikin tunani sai yaji tana faɗin yaya Aryan sai da safe su zahrafa har sunyi barchi sun kyaleni ” ok kawai yace da ita san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya kwanta bajimawa barchi tayi awon gaba dashi

Lokachin da Khalid yadawo ɗakin dan karɓar wayarsa yasamu aryan yayi barchi murmushi yayi a’fili yafurta ai daman ninasan meyahanaka barchi kai da kanka kake neman kashe kanka anfaɗa maka SO wasane ganin Aryan yana ɗan motsi yasa Khalid ɗaukan wayarsa da sauri yayi waje yana murmushi

Washe gari dawuri suka tashi sukayi shirin zuwa school kamar yadda suka saba haka suka fito yauma kai tsaye wajen motochinsu suka nufa da gudu drivers ɗin suka karaso wajen budemusu motochin drivers ɗin sukayi
Su diyana Suka shiga suna shiga drivers ɗin ma suka shiga da gudun gaske suka tada motochin suka bar gidan gudu suke sosai chikin kan kanin lokachi suka isa school ɗin awajen dasuka saba parking sukayi yauma fitowa su hiyana sukayi suka jera zuwa wajen tsayuwa suyi hira kafin a shiga class ” drivers kuma suka shiga motochin suka juya suka koma gd

Tsayuwa sukayi kamar dai jiya Suna hirar’su daga bayansu sukaji andaƙa musu tsawa ” ke zonan ni jiyazakiwa karayan aljanukoh to wlh sai kinyabawa aya Zakinta dan yau saina babbalaki a school ɗin nan ” gaba ɗayansu suka juya ganin jabir yasa Zahra ta kwasa da gudu abunta tayi hanyar class nasu ” diyana kuwa tsayuwa tayi kamar mai tunani ta harɗe hannu a kirji babu ko alamar tsoro a tattare da ita ” hiyana kuwa juyowa tai ta dubi’ su lamrat kasa kasa tace musu kuje class ” a tare suka juya suka nufi class ” jabir ganin alamar diyana ko tsorata batayi ba dajin maganar da yayi yasa ya nufeta gadan gadan ya duncle hannu zai kai mata naushi da sauri…✍️✍️

 

 

More comments an share pls 🙏

 

 

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️

 

 

*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

 

 

Post a Comment for "Duk karfin Izzata Book 1 Page 13"