Breaking News

Duk karfin Izzata Book 1 Page 16

Episode 16*

 

Idanta ya sauka, a kan shahram dake tsaye fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa babu alamar wasa a tattare dashi ” sakin diyana, tayi tana mai da nunfashi ” karisa shigowa ɗakin yayi yana faɗin get out yayi


maganar yana nuna Aunty Maryam ” kallan raini ta tsaya take masa daga sama har katsa dogon tsaki taja, tanunashi da ɗan ya tsa tace kai karamin marakunya ni kake chewa nafita to kashirya karɓan hukunchi ” shikam Shahram ko ajikinsa, dan daman bajin hausa yakeba bare yaji me tache, sai ma kallan Zahra dayayi yace all of U follow me yana gama faɗin hakan yajuya ya koma bakin kofa ya tsaya ” wuchewa Zahra tayi taje ta taimakawa diyana tamike ” Aunty Maryam na tsaye suka raɓa gefenta suka wuche, tanasan ta damkoh diyana tachi gaba da bugu kuma tana tsoron yadda taga fuskar Shahram ba wasa hakan yasa ta fiche a ɗakin a fusache ” Shahram ganin sun mike sun nufosa yasa yayi waje, suka bi bayansa bai tsaye wajen motochin gidan suka nufa da kansa ya buɗe musu marfin family car suka shiga gaba ɗayansu ” shima shiga yayi yaja motar da gudun gaske nan take security dake tsaron gate suka wangale masa gate ɗin ” dagudu ya danna hanchin motar yayi waje doguwar titi yamiƙa dasu gudu yake sosai chikin ƙanƙannin lokachi suka isa wani katafaren asibitin DON dake kan titin zoo road ” suna parking ya fito yabuɗe musu motar bayan sun fito yayi gaba suƙa bishi a baya ” diyana daker take ɗinkisa kafa ” hiyana kuwa goshi sai jini yake, gaba ɗaya jinin ya wanke mata face ” kai tsaye office ɗin baban dr yanufa ” security dake tsaye a bakin office ɗin suna ganin Shahram suka shiga sara masa kamar sunsan juna buɗe musu kofar office ɗin sukayi suka shiga ” babban dr naganin Shahram yamike yana miƙa masa hannu, miƙa masa hannu Shahram ma yayi suka gaisa san nan yakora mara bayani a kansu diyana ” da sauri dr peter ya ɗauki waya yakira nursing ” nursing na shigowa dr peter yabata umar a kan ta tafi dasu diyana tabasu gado gashi nan zuwa yadubasu ” har ɗakin da a ka kaisu sai da Shahram ya bisu sai da ya tabbatar sun fara samun kulawar Dr san nan yafito ya nufi motarsu yatayar yanufi gd

A bangaren Aunty Maryam kuwa tana komawa ɗaki ta ɗau’wayarta tafara kiran layin Aryan dan taji ko shiya aiko Shahram amma ba’a ɗagaba sai data kira miss call 10 amma ba’a ɗagaba san nan ta hakura ta ajiyewayar tana ta surutai wlh Aryan kazo gaɓar da bazan kyalekaba, ina ruwanka dan nabuge yaran nan toma waya faɗamaka ina bugunsu dole na binchiko ta ina kasamu lbr, haka dai take ta surutun’ta

Yadda akayi Aryan yasamu lbr Aunty Maryam na bugunsu diyana har ya’turo Shahram

Lokachin da Khalid ke magana da Zahra yaji tayi shiru sai hello, hello kawai yake amma ba amsa har zai katse kirankuma sai yaji ihu, nantake hankalinsa yatashi yamike yanajin yadda Aunty Maryam ke bugunsu, da sauri yanufi ɗakin Aryan rike da wayarsa yana zuwa yamikawa Aryan wayar ” muryan Aunty Maryam sukaji tana faɗin nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana,” bai taɓa kirana a wayaba amma yau yakirani har sau 2 saboda ke ” a fusace Aryan yayi wurgi da wayar Khalid yamike, nan take fuskarsa ta Sauya idon nan suka chanza sukayi jawur dasu kamar an watsa barkono, wayarsa ya ɗaukoh sai huchi yake kiran layin Aunty Maryam ɗin yafarayi Amma shiru shiru har 3 time rai a ɓache yayi wurgi da wayar, yanufi hanyar fita ” da sauri Khalid yarikesa dan ya lura baya chikin hayyachen’sa inazakaje Aryan chewar Khalid ” Nigeria zanje mana ” dariyane sabo kuɓchewa Khalid amma sai yadanne yace ai kokatafi yanzu ba yanzu zaka isaba kafin kaje kuma duk abun da zai faru yarigada yafaru, yanzu dai kakira wani daga chikin security nan suje su kashe wutar, ai tun Khalid bai kai karshen magana ba “Aryan yanufi wayarsa da sauri ya ɗaukoh yafara kiran layin Shahram, ” Shahram nayin picking call ɗin ” Aryan yabashi umarnin yaje ka dakatar da Aunty Maryam daga bugun su diyana datake san nan ya ɗaukesu ya kaisu asibiti, yana gama faɗin haka ya katse kiran ya zauna a bakin gado ya dafe kai
Kusa dashi Khalid yazo ya zauna ya sa hannu ya dafa kafaɗarsa zaiyi magana ke nan sukaji sallamar DON

Kallonsu DON yake sosai kamar mai nazarin wani abu a fiskokinsu wuchewa yayi ya zauna a bakin gadon ” calmly yafara magana me yake damunka Aryan wan nan shine tambaya ta karshe da zanmaka idan baƙa faɗaminba kasan sauran ” kakalo murmushi dole Aryan yayi yana faɗin wai meyasa kakesan saka wani tunanin banza a zuchiyar kane, nifa nafaɗama kwanan nan ina yawan fama da chiwon kaine amma bari namaka mai kankat wlh Allah nikam bawani abun dake damuna, kawai jinake tamkar a takure nake banajin daɗin ƙasar nan narasa meke min daɗin banda haka wlh babu wani abun ” jinjina kai kawai DON yayi batare dayache komaiba, dan yasan iya gaskiya ke nan Aryan yafaɗa masa dan bayadda za’ayi Aryan yayi rantsuwa a kan karya kuma tabbas zai iya shedan Aryan a ko ina baya faɗin maganar da ba hakaba, to amma tabbas yana da damuwar da shi da kansa baisan da itaba ” ganin DON yayi nshirune yasa gaba ɗayansu suka dawo kusa dashi, dafa kafaɗarsa Aryan yayi yana faɗin baka yarda da magana ta bane ” juyo green eyes ɗinsa yayi kan face ɗin Aryan tare da ɗanyin murmushi gefen fuska nayarda mana na yarda da duk abun da kafaɗa domin baƙa taba yimini karyaba matsalar ɗaya a nan shine tabbas akoi abun da kedamunka wanda kai da kanka bakasan meneneba ” zuba musu ido khalid yayi yana tunani a chikin ransa gaskiyane DON kachi su nanka Safras indai wajen basirane kai karshene ba abanza mai marbata ya dage sai kai za abawa sarauta’ba, yayi nisa chikin tunani sai yaji Aryan nataɓasa firgigit yayi ya ɗago yana kallonsu duk sun zuba masa ido ” lfy Khalid kodai kaima kana da damuwane DON yajefo masa tambaya ” aa bani da damuwar komai nikam kawai tunanin meke damuna ɗan uwana nake ” nifa babu abun dake damuna na faɗa muku ” DON zaiyi magana wayarsa tafara ringing hannu yasa chikin aljihunsa ya fitar da wayar, sunan Sadiq yagani ta bayyana a kan screen ɗin wayar dogon tsaki yaja tare da jefar da wayar a kan gado ” da sauri Khalid yasa hannu ya ɗauki wayar yana duba wanene yakira DON yake jan tsaki haka ganin sunan Sadiq yayi a kan screen ɗin bai yi mamakiba, dan DON yaki ɗaukar wayar Sadiq dan kuwa Sadiq yayi aure ” murmushi yayi yana kokarin picking na call ɗin kiran tayanke chire pin na wayar yayi dayake yasan pin na wayoyinsu dan ba abun dasuke ɓuyewa juna
Kiran layin Sadiq ɗin yafarayi wayar nafara ringing Sadiq yayi picking call ɗin yana faɗin yau wace rana nayi sa’a an ɗauki wayata ” dariya Khalid yayi san nan yace ai kasan shikam bazai ɗauki wayarkaba ” my Khalid ykk ” lfu lau ya amarya suhaima ” first dai yanzu albishirinka ” da sauri Khalid yace goro ” my baby ta haifamin baby boy yanzun nan daman shi nakira nafaɗa muku ” wow my man inatayaka murna bari nabawa Aryan ma yatayaka murna ” Khalid bai jira amsar Sadiq ba yamiƙawa Aryan wayar ” satar kallan DON Aryan yayi yaga bama su yake kalloba yasa hannu ya’karɓi wayar yawa Sadiq congrat san nan yace ga DON nan, kuma da gangan yayiwa DON ɗin haka dan yasan idan shi yamiƙawa DON wayar tofa dole zaikarɓa kuma gaskiya yanasan DON yataya Sadiq murna kodan halakchin da Sadiq ɗin yamusu, yanzu matarsa na aihuwa tun bai sanar da kowaba yafara sanar musu, aiko basaso dole zasu danne sumasa congrat ” karbar wayar DON yayi badan yasoba kawai dan bazai iya kwasale Aryan a idon kowa bane

Congratulations inatayaka murna chewar DON ” da murna Sadiq yace thanks ykk y gd ” lfy yasu mom ” alhamdulillah Sadiq yabashi amsa ” ok kawai DON yace san nan ya katse kiran ya ɗago green eyes nashi yana kallonsu ” zuba mishi ido Aryan da khalid sukayi sosai suna kallansa Khalid na mamakin hali irin na DON ” kallon me kukemin haka ” murmushi Khalid yayi san nan yace kyau kamana mana shiyasa muke kallanka ” mikewa yayi yana faɗin to aiki yasameku kuda kukasanma me kyau yake nufi, yana gama faɗin hakan yayi waje ” dariya Khalid yayi sosai san nan ya dubi Aryan yana faɗin wai gaji DON baisan me kyau ba kajimin iskachi ” tsaki Aryan yaja yana faɗin kai ma kake biye masa ae, to daman inban da kai da neman magama ina DON yasan maka wani abu Wai shi kyau, ko kuma mara kyau ai shi inba Bom, bindiga, bullet,ba to bawani abun dayasani mai kyau ” mikewa Khalid yayi yana faɗin good night anjima kakira Shahram kaji ya ake chiki ” da sauri Aryan yafara lalubar wayarsa yana faɗin yanzu dai wani anjima kuma, wan nan ke nan

Nigeria DON hospital

Washe gari misalin karfe 8 dinaya na kwanche a gado da drip a hannu ” hiyana ma kwanche a nata gadon ansamata bandeji a goshi ” sai lamrat da amrat dake zaune gefen gadon hiyana, zahra kuma tana kan kujera plastic dake chikin ɗaki ” shiru sukayi gaba ɗayansu na tsawon lokachi ” sallama sukaji a bakin kofar ɗago kai sukayi gaba ɗayansu Shahram suka gani tsaye shida Dr Peter karisa shigowa chiki ɗakin sukayi suna tattaunawa ” mikewa Zahra tayi daga kan kujerar ta koma gefen gadon diyana tana kana tacewa Shahram, uncle have a seat ” thanks dear san nan ya zauna a kujerar ” miƙamasa takardar magani Dr Peter yayi san nan ya juya yanufi waje ” Shahram kuwa wayarsa ya ɗaukoh daga aljihun wandansa yafara kiran layin Aryan, har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan a ka ɗaga
Chikin girmamawa Shahram yafara magana hello sir good morning ” morning how are U ” am fine sir ” where is she da sauri Shahram ya mikawa diyana wayar ” hannu tasa ta amsa ta ƙara a kunne hello yaya Aryan ina kwana ” lfy y jiki ” da sauki ina Ammi dan Allah yaya Aryan kafaɗawa Ammi ta dawo dan Allah wlh tsoran Aunty Maryam nakeji, nikam Ammi tazo taje tasayar da shanun Bappa gaba ɗaya tasaya mana gida mukoma ” shiru kawai Aryan yayi yana sauraron’ta har ta kai karshe ” chikin sanyin murya yafara magana karki damu ae munkusa dawowa saura 9 days ne kawai kuma kinga nafaɗa miki Aunty farida zatazo next week idan Aunty farida na nan babu abun da Maryam zata muku, yanzuma bazan barku hakaba kinji bazata sake taɓakuba ” to shike nan Amma pls yaya Aryan ka haɗani da Ammi da Abba mana ” mezakiche musu idan na haɗaku ” zanfaɗamusu abun da Aunty Maryam tamana ” aa to bazan haɗakuba gaskiya ” ayya yaya Aryan kayi hakuri ka haɗamu tunfa shakaranjiya da Ammi ta kiramu ta wayar Aunty Zahra bamu sake maganaba, jiyama ina wanka naji su hiyana na magana da ita, kafin nafito kuma sungama magana pls ka haɗani da ita takarisa maganar kamar zatayi kuka ” to zan haɗaku amma saikin min alƙawarin bazaki faɗamusu komaiba gaisawa kawai zakuyi ” da sauri tace eh namaka alƙawari wlh bazan faɗaba ” ok to yanzu bawasu Zahra wayar bari naji yanasu jikin idan mungama magana sai na haɗaki dasu ” to kawai tace san man tamiƙawa zahra wayar ” karɓa Zahra tayi suka gaisa san nan tamiƙawa hiyana ” ansa hiyana ma tayi suka gaisa ya tambayeta jikinsu tace da sauki san nan yace to tabawa diyana wayar, miƙamata wayar hiyana tayi ” da sauri diyana ta ansa tana faɗin hello ” idan ruwan da a’kasamiki yaƙare Shahram zai maidaku gd, dan na chanza shawara zan ƙira mijin Aunty farida na faɗamasa ya bar Aunty farida tazo goɓe kinji ” to shike nan yaya Aryan amma kuma, kuyi sauri ku dawo dawuri tayi maganar a shagwaɓe ” meyasa kikesan mu dawo dawuri kodai kina san ganina’ ne ” eh ba kai kaɗaiba dukkan kuma inasan ganinku, gd babu daɗi dabaku nan ” shiru yaɗanyi kafin yace ok inshaa Allah munkusa dawowa ae ” to Allah ya dawo daku lfy tana gama faɗin hakan bata jira amsar shiba tamiƙawa Shahram wayarsa ” koda Shahram ya ansa wayar yasa a kunnensa, sai yajiyo Aryan na faɗin nima inakewarki my sister ina kewar coffee ɗinki mai daɗin nan” a sukwane Shahram ya miƙa mata wayar kallansa diyana ta tsaya take damamaki batare da ta ansa wayar’ba ” mikewa Shahram yayi yazo har kusa da ita yasa mata wayar a kunne ” muryan Aryan taji yana faɗin sister ba kyajinane ” hannu tasa ta ansa wayar tana faɗin inajinka yaya Aryan “to ae naji inata magane kinyi shiru ” eh dazun banji me kafaɗa’bane ” ok to shike nan Shahram zai jira idan ruwan da a’ka ƙaramiki ya ƙare zai mai daku gida, nurse ɗaya zata biku tachigaba da kula daku ” to yaya Aryan makaranta’fa ” makaranta sai kunji sauri ba naji kun gama exam bama ” laaa waya faɗamaka to ” zuchiyata mana itace tafaɗamin ” to zuchiyar’ka tafaɗi gaskiya mungama ” to bazaku sake zuwaba sai ranar da za’ayi hutu yanzu kam ku huta kuyi jinyar jikinku ” to ka haɗani dasu Ammi mana ” sai da daddare idan kun koma zankira layin Zahra na haɗaku amma karki karya alƙawari’fa ” to bazan karyaba ” ok sai munyi waya anjima koh, yana gama faɗin hakan ya katse kiran ” jin ya katse kiran yasa ta mikawa Shahram wayarsa,

Sai 12 :45 a ka sallamesu daga asibiti hiyana dai ba a chire mata bandejin’ba, saboda sosai taji chiwo a goshinta dan har ɗinki 6 a kamata awajen ” Shahram dakansa yabuɗe musu motan suka shiga tare da nurse ɗaya kai tsaye gd Shahram ya wuce dasu ” yana parking yafito ya buɗemusu motar suka fito, daka gansu kaga wayanda suka sha wahala, har ɓangaren Ammi Shahram ya rakasu sai dayaga shigansu palo tukun nan yajuya yakoma bakin gate
Suna’shiga ɗakin’su suka nufa wanka suka farayi ɗaya bayan ɗayan suka sanya dogayen riguna abaya baki ” hiyana kam dakyar tayi wankan saboda zafin da kanta ke mata shiru suka zauna ” jim kaɗan Zahra tamike tana faɗin ina wayata bari nakira masu aikin sukawo mana abinchi nanfa tashiga nemar wayar’ta, chan gefen drawer ta gano wayar, da sauri ta ɗauka ta duba taga wayar ta mutu ba charji jonata a charji tayi san nan ta kunnata tafara neman layin binta
Bugu ɗaya binta ta ɗaga Zahra tabata umarni kan ta kawo musu abinchi ”

Chikin kankanin lokachi saiga binta tashigo da sallama, hannunta ɗauke da babban trey mai dauke da kulolin abinchi da plate a kai a tsakiyar ɗakin taajiye san nan ta gaidasu tafita ” saukowa kasa zahra da diyana sukayi ” Zahra ta dubi nurse ɗin tace kizo kichi abinchi sister, bamusu itama nurse ɗin ta saukoh ” kuma kunajiran saina kirakune? Zahra tayi maganar tana kallansu lamrat ” jiki ba kwari suka tsaukoh, ” Zahra da kanta tayi sarving na kowa kallan, hiyana dake zaune tayi ke bazaki zo muchi’bane ” Aunty Zahra nifa bazan iya chin komai”ba dan kaina chiwo yake min sosai ” aa hiyana karmuyi haka dake kawai ki saukoh ki daure kichi ko kaɗanne ” hiyana badan tasoba haka ta saukoh suka fara chin abinchin, jitake kamar magani takechi dan bakinta ba tes ko kaɗan
” Bayan sungama chin abinchi ne nurse ta basu magunguna san nan suka haye gado ” zahra a ita da hiyana a gadon’su, dayana da amrat da lamrat suma a gadon diyana ” nurse nasu kuwa suka kaita ɗakin’su amrat, suna kwanchiya ba jimawa barchin wahala ya ɗaukesu

SAUDIA

Wayarsa ya ɗauka yafara neman layin Aunty farida ringing ɗaya ta ɗauka ” hello my bro ” na’am lovely Aunty ykk ” lfy lau yasu Abba ya shirye shiryen dawowa ” alhadulillah ina junior ” yafita da baban’sa ” ok Aunty farida daman ina san magana da’kene “ok to inajinka ” sonake kije gd gobe ” ae sai ranar Monday zantafi amma meyasa kakesan naje dawuri ” Aryan zai sake magana idonsa suka sauka chikin green eyes wato DON tsaye yake a bakin kofar shigowa betroom ɗin, sanye yake da suite ash colour, bakaramin kyau yayi yatara gashin kansa ya ɗaure, fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa ya harɗe hannu a kirji ya zubawa Aryan green eyes nan nashi ” hello bro baka jinane ” sorry lovely Aunty inajinki wlh hankalina yatafi wajen DON ne ” ok to injinka meye dalilinka nacewa naje’gidan gobe ” babu komai kawai dai inasan kijene ” jinjina kai Aunty farida tai kana tace ok badamuwa zanyi magana da dadyn junior idan yadawo ” ok kawai Aryan yace batare daya jira kozatace wani abuba ya katse kiran ”
dawo da kallansa yayi kan DON yafara magana to meya tsayar da kai kuma a bakin kofa ” dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya a hankali yafara takowa izuwa chikin ɗakin gefen gado ya zauna yana fuskantar Aryan ” ayayin da Aryan ɗinma shiyake fuskanta shiru sukayi na ɗan lokachin suna kallan juna ” DON ne ya katse musu shirun dacewa munyi magana da Aunty farida tace tafara magana da Abba a kan maganar sarauta amma kanaganin Abba zai chanza ra’ayi kuwa ” gaskiya dakamar wuya Aryan yabashi amsa a takaice ” mikewa yayi ya kwanta a gadon yana kallan Aryan ɗin batare dayace kalaba ” Aryan kuwa dayaga kallanda DON yake masa kamar kallan tuhumane, sai yamiƙe yana faɗin bari na dubo khalid yanufi hanyar fita ” meyasa kake guduna ne yanzu Aryan ” chak Aryan ya tsaya kirjinsa na bugawa da karfi a hankali ya juyo idansa suka sauka chikin na DON dan kuwa ya tsaresa da ido sosai yake kallansa ” meyasa zanrinƙa gudunka kuma ” wan nan dai kai kasan dalilin amma dai ninasan ba haka kawaiba ” nibawani gudunka danake yama za’ayi kace ina gudun kane bayan tare muke komai, har chin abinchi, wanka da barchine kawai ke rabamu, ” ok to yanzu dakamike ina zaka, eh bawai bani da aikin yi banefa nabari nazo wajenka muyi hira amma ko kara bakaminba kamike wai barika dubo khalid
Shiru Aryan yayi yana tunani kuma yagane kuskuren dayayi nacewa bari yadubo Khalid dan haka sai yajuya ya dawo chikin ɗakin kusa da DON ɗin yadawo ya zauna yana faɗin am sorry bro ” jinjina kai kawai DON yayi batare dayayi maganaba ” shiru sukayi gaba ɗayan’su kowa da abun dayake tunani

YOLA NIGERIA ✈️

Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi sai tunani take tayi nisa chikin tunaninta taji ana Sallama a kofar gd, amsa sallahar tayi san nan tamike ta ɗauko mayafi ta rufa a kanta tayi waje, tana fita tachi karo da bello ” aa Bello kaine mai doka sallama haka to ya akayi ” eh nine inna inawuni ” lfy meyakawoka ” daman goggon’su hiyanace wadda ta ɗaukesu ta aiko wani yazo yafaɗamin intattara dabbobin’su hiyana na haɗa da nawa narinka kula dasu bayan Sallah zasu zo ” wani tsalle inna tabuga tana faɗin banga uban daya isa ya taɓa dabbobin nan ba wlh ” to inna ae’ga yan sakon nan basu tafiba sai kifaɗamusu ” juyawa inna tayi tana kallan inda bello ke nunawa, wasu sojoji taga guda 3 sanye da kaki, fuskar nan tasu babu alamar wasa aguje inna takwasa tayi chikin gida ” juyawa bello yayi yanufi garken dabbobin yana faɗin muje ” bin bayansa sojojin suka har zuwa wajen dabbobin ” ƙirga dabbobin suka shigayi bayan sun gamane “bello yadubi sojan yace a nawa lissafin dukka dabbobin banda kaji, da zabbin, nan iya shanu, da raguna, da awaki, 1007 ne amma kufa nawa kuka samu a naku lissafin ” ɗayan daga chikinsu yace 1005 nasamu dayanma yace 1005 ” kai kumafa bello ya tambayi ɗayan da baiyi maganaba ” amsata iri ɗayane danake 1007 shiru sukayi chankuma Bello yace to kozamu sake ƙirgawane ” aa basai mun sakeba a barshi a lissafinka domin ina da tabbachin shine dai dai, dan kafimu iya ƙirga dabbobi, nasan kana kirga wayanda sukafi wan nan yawa to ni da kyarma na iya irgawa wlh sai rikiitani suke ” murmushi kawai bello yayi san nan yace to muje wajen kajin nan kuma ” no kaji da zabbi madam tace ka ɗauka bata buƙata ” nan take fara’a ta bayyana a fiskar bello sai godiya yake zubawa har suka fito ” sojojin sukaje suka shiga motar’su suka kama hanya ” bello kuwa da sauri yajuya yanufi gd dan yafaɗawa innnar’sa abun dake faruwa

KANO STATE

Misalin karfe 4 hiyana ta farka daga barchi tana duba time da sauri tafa tashin’su Zahra dan ko sallar azhar basuyi’ba, koda suka tashi sai faman yamutsa fuska suke ” hiyana naganin sun tashi tamike tanufi toilet danyin alwala zahra kuma wayarta tachiro daga charji ta kunna wutar screen ɗin nanfa tasamu miss call kusan 17 yaya Aryan 4 miss call, yaya Khalid 3 miss call, Ammi 3 miss call, mai Martaba 5 miss call, yaya Yusuf 2 miss call, ” tunani tashiga’yi wazata fara kira saiga wata kiran tashigo tana dubawa taga yaya Aryan , da sauri tayi picking call ɗin tana faɗin hello yaya Aryan ina wuni ” daga ɗayan ɓan garen Aryan yace lfy ykk yajikinku ” da sauki barchi, mukayine shiyasa kakira bamu ɗagaba ” ok ina sauran’suke ” miƙawa diyana wayar Zahra tai” ta ansa taba faɗin wanene ” idan kinsa a kunnenki ae zakiji koma wanene Zahra tabata amsa ” kara wayar tayi a kunnen’ta tana faɗin hello ” ya jikin naki ” laaa yaya Aryan daman kaine jiki ba sauki gaskiya dan har yanzu zafi kaina da kirjina yakemin sosai ” saura kaɗan ya kwashe da dariya amma sai ya danne yace to inshaa allah zai daina yimiki zafi kinji ” diyana zata sake magana sukaji an turo kofar ɗakin nasu da farfi anshigo a razane suka ɗago ganin Aunty Maryam yasa diyana fasa…✍️

 

Pls more comments an share 🙏

 

 

 

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

 

No comments