Breaking News

Duk karfin Izzata Book 1 Page 22

Episode 22*

 

Sosai Aryan ke kallan chikin idon ta, kasa tayi da kai dan bazata iya chigaba da haÉ—a ido da shi ba, sake matsowa kusa da ita sosai yayi, ya matse ta da jikin,bangon “murya na rawa tace dan Allah yaya Aryan kayi hakuri,


maganar da tayin nan yasa yaji tamkar an chan ka masa mashi a zuchiya,da kyar ya iya buÉ—e baki kamar mai raÉ—a yake faÉ—in “wae banace karki sake magana ba, hannu tasa ta toshe bakin ta, a hankali ya haÉ—e fuskar su waje É—aya,hanchin su na gogan na juna rutse ido tayi dan baza ta iya kallan chikin idon saba,calmly yafara magana “daga yau karki sake kwalliya da daddare,kuma idan wani yasake yima ki magana kika amsa shi sai na É“ab’É“allaki, yau kuma ina É—an kwalin ki, a tsorache ta buÉ—e baki har kerma lips nata keyi tana faÉ—in kayi hakuri…bai bari ta karisa ba da sauri ya É—ora ya’tsansa a saman lips nata, yana girgiza mata kai yana faÉ—in “ae banche kiyi magana bako, kiyi shiru ki saurare ni, kawai, shiru ya É—anyi yana kallan yan da lips na ta ke kerma dan tsoro jiyayi tamkar yayi kissing nata, amma ba zai iya hakan ba itakuwa kara runtse ido tayi dan sai kerma gaba É—aya jikin ta yake, almost 10mnt suna saye a haka, da kyar ya iya buÉ—e baki dan yadda yake ji, ya chigaba dace wa “me yasa bakya jin magana tane eh? ko dan kinga ina damuwa da kirinÆ™a sa É—an kwalin shiyasa kike kin sawa, to shike nan zan fara hukun taki,a kan hakan,yanzu dai zo nan kifara tsallen kwaÉ—o yana kai karshen maganar a zafafe ya sake ta da sauri ya juya ya koma saman sofa ya zauna sai lumshe ido yake

ahankali ta duka yafara frog jump tana kewaye palon tana hawaye,tun tana kuka a hankali har tafara da É—an sauti, yana zaune yana jin ta sai faman runtse ido yake,yana chiza laÉ“É“an SA, dan har chikin ransa yake jin kukan nata, amma yazama dole yarin Æ™a hukun tata, kodan tarin Æ™a jin maganar sa, frog jump take sosai ga high heel a kafarta kamar an hanata chirewa, sai kuka take,kaÉ—an kaÉ—an tafara jin chiwon chiki,amma tana tsoran faÉ—awa faÉ—a masa, azaba yayi azaba,sae faman nishi take numfashin ta na fita da sauri sauri jinyadda take numfashine yasa Aryan É—agowa, ya kalle’ta,Subhanallah, da sauri yamiÆ™e yanufeta yana faÉ—in lfy kike kuwa sis,bai kai ga karisawa wajen taba yaga ta sulale kasa kamar bata numfashi,da sauri ya karisa wajen ya duka, a ruÉ—e yasa hannu ya tallabo kanta yana faÉ—in Ke,ke,lfy kike kuwa,É—ayan hannun’sa yasa,a saitin kofar hanchin ta dan yaji shin tana numfashi, jin bata numfashi alamar ta sume,ne yasa ya miÆ™e da sauri ya É—auke’ta chak yaÉ—ora ta saman sofa, yanufi freij ya É—auko robar ruwan Faro mai sanyi yadawo ya zauna a gefen ta, buÉ—e robar ruwan yayi ya tarbo a hannun’sa ya shafa mata a fuska,dogon numfashi taja, a hankali ya furta “ke kina lfy kuwa slowly ta buÉ—e idon ta a kan face nashi,da sauri ta sake runtse idon tana matsar kwalla, shiru yayi yana kallan’ta wasa wasa tafara juyi tana kara sautin kukan,”ke wae meke damun ki’ne,ya tambaya a É—an ruÉ—e dan a’yanayin dayake kallanta kamar period nata ne ke san zuwa chikin kuka take faÉ—in “chiki yaya Aryan chiki’na wayyo Allah,hiyana ta kizo zan mutu, da sauri yasa hannu ya chire hannu’ta daga rikon datawa chikin nata,ya dora hannun sa awajen,a sukwane kuma yachire hannun nasa dan wani irin shock da yaji, kallan face nata yake dan ya tabbatar da abun dayake zargi shin period ko dai nomal chiwon chikine, ita kuwa sae kuka take, bazai iya jure kukan nata ba, a zafafe ya miÆ™e ya koma chikin betroom É—in sa, jim kaÉ—an sae gashi ya fito riÆ™e da sirinjin allura,idon ta a lumshe sae kuka take tana juyi a saman sofan, a gefen ta ya zauna ya kama hannun ta a hankali,dan yasan in ta buÉ—e ido bazata tsaya ya mata allura ba,gashi tana bukatar alluran kodan period É—in yazo mata da sauki,chikin dabara ya É—aure hannun nata ya fara ne man jijiya,itakam sae kuka take dan ba tama san yana kusa da ita ba, gyara zaman’sa yayi da kyau, chikin dabara ya tsira mata alluran da sauri ya mata ya zare,sirinjin, a’sukwane ta buÉ—e ido tana ko’karin ihu,hannu yasa ya rufe bakin nata yana girgiza mata kae,”tashi kije É—aki ki kwanta yayi maganar yana zame hannun sa daga bakin’ta, chikin dashe war murya take faÉ—in “yaya Aryan wlh bazan iya tafiya ba,ta karisa maganar tana sakin wani,kuka mara sauti,dafe kae yayi yana faÉ—in”wae banace kukan nan ya isaba kiyi shiru haka nan,yana gama faÉ—in hakan yamiÆ™e,ya É—auke ta chak ya saÉ“a’ta a kafaÉ—ar’sa yayi waje da ita,da sauri sauri yake tafi kai tsaye É“angaren Ammi,yanufa da ita,da sallama ya’shigo palon babu kowa,a hankali yafara takawa izuwa É—akin su kamar bai san taka kasan, kodaya shiga sae daya sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya,dan ganin su Zahra sunyi barchi, saman sofa ya kwantar da ita, ta buÉ—e baki zata masa godiya da sauri ya juya ya bar É—akin,har yana tun tuÉ“e, chire takalman kafar ta tayi ta kwanta,ta dafe chikin ta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

Aban garen Aryan yana fita É“angaren Ammi É—akin sa ya koma,a gurguje ya shiga, toilet wanka yayi ya shirya chikin kayan barchi,riga zuwa goiwa mai igiya, gaban rigan a buÉ—e take faffaÉ—ar kirjin nan nasa awaje rigar fari ne tas,mai laushi sae kamshi yake zubawa fitowa palo yayi ya É—auki coffee É—in da diyana ta kawo masa,ya koma betroom,kaÉ—an yasha saboda coffee É—in yayi sanyi, ajiyewa yayi kan table É—in tsakiyar É—akin,ya haye saman katafaren gadan’sa ba jimawa barchi yayi awon gama dashi

Washe gari tun asuba su Ammi suka shirya, Ammi Aunty farida hiyana diyana Zahra yusuf Khalid Aryan da kuma DON, lamrat da amrat kuma Anbar su wajen Aunty mardiya “wasu dan Æ™ara dan karan, motochi masu numfashi guda 5 suka É—auÆ™esu zuwa Airport, ajere motochin suka jera har Airport, Ammi da Aunty farida mota É—aya suka shiga,DON da Aryan motar’su É—aya,hiyana diyana da kuma Zahra motar É—aya Khalid da Yusuf ma motar’su É—aya,É—ayan motan kuma sojoji ne a chiki,diyana sae murna take yau zataga yaya bello da innar yaya bello, Zahra ma sae murna take yau zataje kauye dan inba makaranta ba bata taba zuwa ko inaba,shiyasa ta dage sae tabisu, idan muka koma É“angaren DON kuwa kamar zai mutu dan bakin chiki sae wani É“ata fuska yake kamar anche masa kwasan kashi zaije,Aryan Khalid Yusuf kam ko ajikin su basu damuba,

“da private jet na yaya Aryan suka tafi,tun jirgin’su bai sauÆ™a ba motochi 6 daga gidan sarkin yola ke jiran’su a Airport karfe 10 na safe jirgin’su ya sauÆ™a, basu wani É“ata lokachi chikin jirgin ba suka fito,DON yafara fitowa fiskar nan tamkar wani mayin wachin zaki taku yake irin na jaruman maza,daka kansa kaga wadda akai wa zuwa dole,Aryan na biye dashi a baya,sai Khalid da Yusuf,Aunty farida rike da hannun diyana suma suka sau’ko Ammi na biye dasu Abaya,sai Zahra da hiyana,Shahram da Abdol ne karshen fitowa,kae tsaye wajen motochin suka nufa, da sauri Shahram da Abdol suka fara buÉ—e musu kofar motochin, Aunty farida da Ammi mota É—aya suka shiga,DON da Aryan motar su É—aya, Khalid da Yusuf suma motar su É—aya,hiyana diyana Zahra matar su suma É—aya,sai Abdul da Shahram suka shiga É—ayan motar suma,kamar dai yadda sukazo,a jere motochin suka bar Airport É—in da ma tsakai chin gudu,

kai tsaye kauyen jambutu suka nufa, wato kauyen su hiyana haka suka rinÆ™a keta dajin nan har kofar gidan su hiyana sukayi parking,na motochin, da yake yau kasuwar garine, shiru garin yayi ba jama’a duk sun tafi kasuwa,da sauri Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar, Shahram yazo ya buÉ—ewa Aryan, Abdol kuma ya buÉ—ewa DON,kafa DON ya zuro waje batare daya fitoba yana zaune chikin motar,yana latsa waya yana wani kwaÉ“e fuska, Aryan kuwa,fitowa yayi yana kallan yanayin garin,Ammi da Aunty farida suka fito suka jera zuwa chikin gd “Ammi nikam bari naje dubo yaya bello tukun nan chewar diyana tafaÉ—i hakan tana murnushi,”bazakije ba wuche ki koma chikin moto Aryan yafaÉ—i hakan chikin tsawa,”Ammi dake tsaye a dai dai bakin kofar shiga gidan su hiyana, tace “a’a ina ruwan ka da ita, kasan halak chin da bello yamusu ne jeki abun ki diyana muma muna zuwa ai,bari mu gama da nan tukun nan, Tun Ammi bata kae karshen maganar ba diyana ta kwasa Aguje ta tanufi hanyar gidan su yaya bello, kwafa Aryan yayi a zuchiyar sa yana faÉ—in zamu haÉ—une, hiyana da Zahra ma fitowa sukayi su kabi bayan su Ammi, “to ni dai tun da Allah ya kawomu kauye yau barinaje naga gari chewar Khalid da sauri Yusuf yace “a’a jirani muje tare jerawa sukayi tare sukanufi chikin gonaki, wani dogon tsaki DON yaja yana faÉ—in “ni gaskiya an chucheni wlh da akasani dole nazo garin nan, Aryan dake tsaye kusa dashi bai san sanda dariya ta kub’che masa ba dan yadda DON yayi maganar, wani mugun kallo DON ya watsa masa yana faÉ—in me kakewa dariya to “kai nakewa dariya mana yanzu dan Allah prince menene laifin garin nan, ae kodan albarkachin a nan aka haifi Ammi ka girmama garin koh, tsaki kawai DON yaja batare daya sake chewa komai ba

Diyana kuwa da gudu ta faÉ—a gidan su bello ko sallama babu tun a kofar gida take faÉ—in “yaya bello ina kake yaya bello ina kake, bello da buba suna zaune a kan tabar ma a tsakar gida innar bello na girki, inna buba bata nan, hasana matar bello tana Shara,a tsakar gd, da sauri bello ya miÆ™e jin muryan diyana,dan kuwa ko mutuwa zaiyi ya dawo bazai manta voice na diyana ba, da gudu diyana ta kariso chikin gida kai tsaye wajen yaya bello tanufa zata rungume’sa kome ta tuna sai kuma taja birki, tana kallan sa shima ita yake kallo chike da farinchi yace “diyana kece? diyana baki yaki rufuwa sai dariya take tace “yaya bello ina….bata kai karshen maganar ba ta sake wani ihu sakamakon san dar da bubu ya buga mata a goshin’ta, kan kache me jini ya wanke mata fuska ihu take sosai shi kuwa buba kamar mahaukachin ya sake É—aga sandar ya buga mata a kafa, nan take ta faÉ—i kasa tana ihu, a zafafe bello ya É—amki sandar yana kokarin kwache wa buba kuwa yaki saki nan take suka kaure da faÉ—a, da gudu innar buba tafito daga kichin tana salati, hasana kuwa jefar da tsintsinyar hannun ta tayi tanufi É—aki da gudu dan tsoro, ganin buba da bello sun kaure da faÉ—ane yasa diyana ta miÆ™e da kyar, tanufi hanyar fita daga gidan,asukwane buba ya sakarwa bello sandar yabi bayan diyana da gudu yana faÉ—in yau sai na kashe’ki shegiya, diyana kuwa ganin buba na zuwane yasa ta tattara iya sauran karfin ta ta watsa da gudu tayi waje tana ihu

Jin ihun diyana yasa Aryan É—agowa a’sukwane, ganin diyana na gudu ga jikinta duk jini yasa Aryan ya nufe ta da sauri, da gudu su Ammi ma sukayo waje jin ana ihu,

Diyana na kokarin faÉ—uwa Aryan ya karisa a zafafe batare da ya damu da jinin dake jikin taba ya rungumeta a kirjin’sa yana faÉ—in “lfy me yasa me ki eh.. bai kai ga rufe baki ba sai ga buba ya fito da gudu yana faÉ—in “sai na kashe ki ni zanyi ajalin ki a zuchiye Aryan ya saki diyana tana tangal tangal zata faÉ—i bai ma luraba idon sa ya rufe gadan gadan ya nufi buba,da gudu Aunty farida ta kariso wajen ta riÆ™e diyana dake kokarin faÉ—uwa,ta rungumeta suka koma chikin gidan su hiyana na, bello daya biyo bayan buba dan ya dakatar dashi kar ya bugi diyana ganin dasu Ammi tazo yasa ya koma gefe ya harÉ—e hannu a kirji yana kallonsu, DON kuwa yana zaune ko kallan inda su diyana suke bai yiba bare ma ya tanka sai latsa wayarsa yake, dayaji hayaniyar jama’a na damun sa sai ya É—auko bluetooth yasa a kunnen sa ya kunna kira’an Al qur’ani mai girma na minshawi ya kure volume ya jingina da kujerar motar ya lunshe ido

Buba ganin Aryan ya tin’karosa gadan gadan ga fiskar nan tasa kamar wani,mayinwachin zaki, a’sukwane buba ya juya zai koma chikin gd, sai dai ina taku biyu Aryan yayi ya dam ki wuyar’sa ta baya É—agashi sama Aryan yayi, yayi wurgi dashi gefe wani ihun azaba buba ya saki, gadan gadan Aryan ya nufeshi dam kar wuyar sa yayi ya kai masa wani naushi a fiska nan take wajen ta kunbura, ihu buba yake kamar makoshin sa zata fashe, baji ba gani Aryan ke kai masa bugu ta ko ina, jin yadda buba ke ihu da kyar muryar sa ke fita ne yasa Ammi ta nufesu da sauri dan kar Aryan yayi kisan kai, daga É—an baya Ammi ta tsaya,a tsorache tace “Aryan ka kyalesa haka ya isa, Aryan bai ma san tana yi ba dan baya ji baya gani bugu kawai yake kai wa buba duk ya fashe masa jiki ga fuskar sa ta kun bura sun tum,

Ammi ta ruÉ—e sosai dan Aryan baya chikin hayyachin’sa kotayi magana bazai jiba gashi Aunty farida tayi chikin gd da diyana, bare ma tayiwa Aryan magana, da sauri ta juya tanufi wajen DON zaune yake a chikin motar idon sa a lunshe hankalinsa kwanche, dan yada Bluetooth bai ma san meke faruwa ba”kai katashi kaje ka dakatar da Aryan daga bugun É—an mutane Ammi tafaÉ—a tana kallo face nash, shiru DON bai amsa ba kuma bai buÉ—e ido ba, ganin hakan yasa Ammi tayi tunanin kodai barchi yake, da sauri tasa hannu tana É—an bubbuga Shi, slowly ya ware green eyes nashi a kan face É—in Ammi, da sauri ya chire bluetooth dake kunnensa yana faÉ—in Ammi lfy, “ina fa lfy ga Aryan chan yana kokarin kisan kai, katashi kaje ka dakatar da shi daga dukan É—an mutane, É—aure fuska DON yayi yana faÉ—in “to ni Ammi ina ruwana basu suka ja ya bugesu ba daman ai mutanen garin nan da dabbobi suke..wani birki ya jaaa da maganar asukwa’ne ya daÉ—a waro manya manyan green eyes nashi yana kallon Ammi, data É—aga yatsu biyar zata zabga masa mari sai kuma itama ta dakata tana kallonsa, chikin fushi Ammi tafara magana “to a nan aka haifi uwar idan mutanen garin nan dabbobi’ne to fa kasa har dani ina daga chikin dabbobi nima ko naso ko baka so nan shine tushen ka ta É“angarena kuma ina alfahari da hakan,idan kaga dama katashi ka dakatar da É—an uwan ka idan kuma bakaga dama ka barshi yayi kisan kai tana kai karshen maganar ta juya a fusache ta koma chikin gida,

dafe kai DON yayi yana faÉ—in “dan Allah Ammi kiyi hakuri na tuba, why why zan É“atawa mahaifiya’ta rai sosai haka, har take kokarin yin abun da bata taba kotan tawaba mari Ammi, kuma ni NO yau gaskiya na kure ta, sosai dole naje na nemi yafiyarta ya karisa maganar yana miÆ™ewa kai tsaye wajen su Aryan yanufa,yana taku irin na jaruman maza,
yana zuwa yasa hannu ya damki damtsen hannun Aryan ya jashi baya, a fusache Aryan yasake nufar buba gadan gadan, rikesa DON yayi yana faÉ—in “wai wan nan dukan na menene haka ya isa baka ganin ya suma ne wai ma me ya haÉ—aku kune, shiru Aryan yayi yakasa magana sai huchi kawai yake ga wani iska mai zafi dayake furzarwa daga bakinsa, hannunsa DON yaja har wajen mota, É—auko robar ruwa DON yayi a chikin motar ya buÉ—e bakin robar ya miÆ™awa Aryan, ansan ruwan Aryan yayi ya kafa robar a bakinsa ya farasha, ganin yakusa shanyewa’ne yasa DON ya É—auko masa wani yabuÉ—e yana jiran ya karisa shan’yewa, tas Aryan ya shanye ruwan, yayi jifa da robar, yasa hannu ya anshi wanda DON ke riÆ™e dashi ya duÆ™a ya zuba ruwan gaba É—aya a tsakiyar kansa,shiru yayi Almost 7mnt sai faman furzar da wani iska mai zafi daga bakin’sa yake, ganin Aryan bai da niyar miÆ™ewa yasa DON kamo hannunsa ya mikar dashi ya zaunar dashi chikin mota yana kallon face nashi “are U okey bro DON ya tambaya yana nazarin face É—in shi, jinjina masa kai kawai Aryan yayi batare dayayi magana ba “me ya haÉ—aka da mutanen kauyen nan,har ka masa irin wan nan duka, a zafafe Aryan ya É—ago kamar wadda akawa allura yasake miÆ™ewa yana kokarin nufar buba, da sauri DON yasake kamo hannunsa, yana faÉ—in “it’s ok zo kayi zaman ka ya isa haka kodai so kake ka É—au doka a hannun kane ya isa pls, da kyar DON ya shawo kan Aryan ya hakura ya kyale buba, shiru sukayi Aryan na zaune chikin mota DON na tsaye a kusa dashi yana kallansa, almost 15mnt san nan Aryan ya É—ago yana faÉ—in “ina su Ammi, wani dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace, thank God daka dawo chikin hayyachin ka, tsaki Aryan yaja kafin yace “ni bansan wulakanchi da che maka akayi bana chikin hayyachi nane pls ka faÉ—amin ina su Ammi “suna chikin gidan chan mana yayi maganar yana nuna gidansu hiyana da hannu, shiru Aryan yayi kamar mai tunani jingina kansa yayi da jikin kujerar motar ya lumshe ido, zuba mi shi wan nan manya manya green eyes nashi nan DON yayi yana ta kallonsa kamar mai son gano wani abu a tattare dashi.

A É“angaren buba kuwa, a sume yake ga jiki duk jini, bello ya É—auke sa Chak ya saÉ“asa a kafadar’sa yayi chikin gida dashi, saman ta burman dake shinfiÉ—e a tsakar gidan bello ya kwantar dashi san nan yakira hasana, yace ta kawo masa ruwa, da sauri hasana ta kawo ruwan a kwano bello ya ansa ya É—iba a hannun’sa ya shafawa buba a fuska, shiru bai farfaÉ—o ba, sake É—ibar ruwan bello yayi yasha fa masa nan ma shiru, bai farfaÉ—o ba zuba masa ruwa mai É—an yawa bello yayi shiru buba ko motsi baiyi ba, dukar da kai bello yayi sai tin kirjin buba yasa kunnensa dan yaji shin mutuwa yayi ne, tabbas zuchiyar buba na har bawa to amma an zuba ruwa an zuba bai farfaÉ—o ba, shiru bello yayi yana tunani a wan nan yanayi innar bello tafito daga bayi ta same’su chikin ruÉ—u da kiÉ—ima ta nufe’su tana tana faÉ—in “bello me ka masa badai dukan’sa kayi ba “a’a inna bani na dake sa ba yan uwan’su diyana ne suka masa hukunchi “to yanzu bello ya zamuyi kasan, san dai bala’e mahaifiyarsa yanzu ko zamu tsallake inuwar mu bazata taÉ“a yarda ba kai ka bugesa ba, shiru bello yayi bai sake chewa komai ba ya zubawa buba ido .

A bangaren su Ammi kuwa zaune suke a tsakar gd diyana na kwanche a kan chinyar Aunty Farida tayi barchin wahala duk da an wanke mata goshin nata jinin bai daina zuba ba, miÆ™ewa hiyana tayi tana faÉ—in “Aunty Zahra kizo muje É—akin bappa,”to Zahra tace san nan ta miÆ™e suka nufi É—akin bappa, kamar yadda suka bar É—akin haka yake ba’a taÉ“a komai ba sai uban kura da datti da É—akin yayi, nan fa hiyana ta shiga kakkaÉ“e kurar ta fito ta É—auki tsintaiya a waje ta koma chikin É—akin ta hau gyaran É—akin

Gyara zama Ammi tayi tana fuskantar Inna tafara Magana “habiba kinsan kafin Ahmadu ya rasu babu Aure a tsakanin ku Koh, to yanzu mu ba wan nan che ta kawo muba, yanzu dai wan nan gida da kike chiki kirike mun barmi’ki, ki chigaba da zaman’ki a chiki da sauri Aunty Farida tace “Ammi ya zakiche kin bata gidan kuma ina che ae ba zai yiwu kiyi kyauta da dukiyan marayu, batare da izinin suba, murmushi Ammi tayi nasu irin na manya kafin tace “feeda wan nan dukiyar dakike gani bana su hiyana su kaÉ—ai bane har da nawa a chiki nima ina da kaso, dabbobi 60 baban mu ya rasu ya bari ga filaye da gonaki, ba yadda za’ayi nayi kyau ta da abun da ba na waba Aunty farida zatayi magana hiyana tafito daga É—akin bappa da gudu tana faÉ—in Ammi ki..

 

*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

*

 

No comments