Breaking News

Duk karfin Izzata Book 1 Page 24

Episode 24*

A gurguje Aryan ya karisa É“angaren sa, kayan jikinsa yafara ragewa, ya rage da gashi sai shot ya nufi toilet dan yin wanka, after 45mnt yafito É—aure da towel ya nufi gaban morrow, wayar sa dake saman drawer mirrow ya É—auka yafara kiran layin Aunty


farida, budu É—aya Aunty farida ta É—aga tare da faÉ—in “hello bro, “Aunty babba pls ki turomin yarin yar nan bari na dubata “ok bari na kawota da kai na dan bazata iya tafiya ba tana ganin jiri, batare daya sake magana ba ya katse kira da sauri sauri ya shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada feshe jikinsa yayi ta haÉ—aÉ—É—iyar parfume nashi mai shegen kamshi da tsada, gyara haÉ—aÉ—É—en kuma lallausan bakin gashin kanna nasa yayi, ya É—aure a bayan ya zuba jelar gashin a bayan wuyar sa sai kelli gashin keyi,

zubawa mirrow sosai ido yayi yana kallan kansa, shiru yayi kamar mai tunani, jin motsi a pallo ne yasa ya juya da sauri yanufi dressing room nashi dan shiryawa,

da sallama Aunty farida ta shigo É—akin rike da hannun diyana sai faman lumshe ido take, ganin É—akin ba kowa yasa Aunty farida tace “my diyana jeki zauna a saman sofa ki jirashi kinji, “to kawai diyana tace tanufi sofan da kyar take tafiya saboda sarawan da kan ta ke mata, Aunty farida kuwa juyawa tayi ta fice daga É—akin,

Zama diyana tayi ta jingina da jikin sofar ta kwantar da kanta ta lumshe ido kamar mai barchi, Almost 12mnt tana zaune shiru,har barchi yafara É—aukar ta, wani fitinannen kamshi ne ya daki hanchin ta wadda yasata sauri waro ido karaf blue eyes nata suka sauka cikin ash eyes nashi, tsaye yake sanye da jallabiya Black colour zuba mata ido yayi sosai yake kallonta, da kyar ta iya buÉ—e baki tace “ina wuni yaya Aryan, juyawa yayi batare da ya amsa ba yanufi wajen drawer

A box ya É—auko ya dawo kusa da ita ya zauna,spirit and cotton ya fitar yafara mata dressing wajen, chikin shagwaÉ“a da murya kamar na mai kuka tace “yaya Aryan zafi ya’kemin sosai ta karisa maganar tana turo baki, subhanallah wani irin shock yaji saboda yadda tayi maganar, zuba mata ido kawai, yayi ya dakata da aikin da yake har takai karshen maganar, da kyar ya iya sai ta tunanin sa, ya buÉ—e baki murya kasa kasa kamar mai raÉ—a “sorry kinji dole zai miki zafi amma zan miki a hankali,

Sake turo baki tayi tana faÉ—in “to ni kawai kabari tun da akoi zafi “kinfi san ki zauna da chiwon ke nan, gyaÉ—a masa kai tayi alamar eh “bakisan yin kwalliya ke nan, da sauri tace “a’a inasan kwalliya “to in baki tsaya an miki magani ba to fiskan ki zai É“achi bazaki rinÆ™a kwalliya ba, chikin marairai chewar murya tace “to ayya yaya Aryan kamin a hankali kaji wlh akoi zafi, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, shiru yayi batare daya sake magana ba ya mai da hannunsa kan goshin’ta ya chigaba da dressing na wajen,

sai mutsu mutsu diyana keyi taki tsayawa zafi wajen ke mata sosai nan take tafara ruwan hawaye, dafe kansa yayi da hannun sa É—aya yana faÉ—in “kinsan ban san kuka ko kiyi shiru ae nakusa gamawa kinji, gyaÉ—a masa kai kawai tayi amma bata dai na hawaye ba “wai ba ke che kika che zaki auri soja ba,ya tambaya yana kallan face nata, da sauri ta É—aga masa kai alamar eh “to ai matan sojojin jarumai ne basa kuka, cikin shesshekar kuka tace “Allah yaya Aryan zafi yake yi mini ne shiyasa amma na daina kukan ta karisa maganar tana goge hawayen ta, girgizar kai kawai yayi ya chigaba da aikin sa sauri sauri yake mata dan karta chigaba da kuka bai san kukan nata ko kaÉ—an,in tana

Bayan ya kammala ya mai da komai ya rufe Box É—in ya ajiye a gefe ya miÆ™e ya koma bakin katafaren gadon sa ya zauna yana kallan ta, sai faman yamutsa fuska take tana turo É—an bakin. “me ya haÉ—aki da wanchan wawan mutumin har ya bugeki haka, yayi maganar yana É—aure fuska , dama kamar jira take tafara bashi lbr tun shigan ta gidan da yadda ya buga mata sandar duk sai data bashi lbr komai, tun da tafara magana ya kafeta da ash eyes nashin nan, ya kasa chire idon sa a kant, yadda take motsa lips nata nan jiyake kamar yamiÆ™e yaje yayi kiss na lips É—in ko zai samu sauÆ™i abun da yake ji a zuchiyar sa, da sauri ya kori sheÉ—an ta hanyar furta a’uzubillahi minasshe É—anir rajin kafin yace “to daman tun asali me tsaka nin ku kuna da dan gantaka da shine, “aa bamu da dan gan taka É—an yayan Inna che, “what kara waro ash eyes nashi yayi sosai a kanta, nan take ya Æ™ara É—aure fuska rai a É“ache yace “to daman kun taÉ“a samun matsala da shine a baya da har yake ikirarin zai kashe ki, “eh kullun idan inna ta aike mu É—iban ruwa sai ya tare mu ya zubar mana da ruwa, nan dai diyana tashiga bashi lbr duk abun da yataÉ“a haÉ—a su da buba from A to Z har fyaÉ—en da yaso yayi mata,

shiru yayi, nan take fuskar sa ta sauya kamanni idon sa suka sauya su kayi jaaa sosai, lokachi guda, a fusache ya furta “fyaÉ—e, a tsorace diyana ta gyaÉ—a masa kai alamar eh gaban sai faÉ—uwa yake dan ganin sauyawar yaya Aryan lokachin guda gawani huchi da yake duk jijiyoyin kansa sun tashi sosai, gawani zufa da yake kamar ba A.c a É—akin jikinsa har wani tsuma yake gaba É—aya ilahirin jikinsa É“ari yaÆ™e gashin hannun sa duk sun mimmiÆ™e,Sai faman chizan red lips nashi yaÆ™e da karfi kamar zai fasasu, kamar alluran sojan nashi ne ya tashi, nan take matsanan chin tsoran sa ya dira mata a rai, tunani ta shigayi anya bazan tashi in gudu ba kuwa karya bugeta,

dafe hannun sofa tayi É—akyar tamike wai dan ta gudu kar ya bugeta, cikin tsawa ya furta “ina zakije, jikinta sai kerma yake chikin wata iriyar voice kamar zatayi kuka tafara magana “dan Allah yaya Aryan kayi hakuri karka bugeni wlh ni bana san duka kaji ta karisa maganar tare da sakin wani marayan kuka mai ratsa zuchiyar mai sauraro, runtse ido yayi dan har chikin zuchiyar sa yake jin kukan nata, ya dafe kai,dan bai san kukan data keyi ko kaÉ—an sassauta sexy voice nashi yayi calmly ya fara magana “nache zan bugeki ne kimin shiru ki koma ki zauna, “yaya Aryan to kishi nake ji ina san in sha ruwa, Slowly ya waro ash eyes nashi a kan face É—in ta, sai hawaye take wani na bin wani “ok jiki É—auko ruwa a freij kizo, to kawai tace san nan tanufi palon tana jan kafa a hankali, ido ya zuba mata yana kallonta sosai har ta fice daga É—akin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke, kana yasa hannunsa yana yamutsa gashin kansa, wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa a hankali yafara magana “Aryan wai meke damun kane meyasa na kesan yarinyar nan ta rinÆ™a kasan chewa kusa dani, yanzu dache ta zauna me zan bata,anya ina lfy kuwa? meyasa nake É“ata rai na dan wani ya taÉ“a chewa zai mata fyaÉ—e? Meyasa zan bugi malamin makaranta su dan yache bazai dai na Son taba? why me ruwana da ita, shiru ya É—anyi kamar mai tunani,

sai jin voice nata yayi tana faÉ—in “yaya Aryan in tambaye’ka, É—ago ido yayi yana kallanta dan bai ma san ta dawo É—akin ba, mamaki ne ya kama shi wai wan nan wace iriyar yarinya che yanzu nan fa take kuka a nan wai daga fitan ta palo ta dawo shike nan takoma fara’ar ta, jin yayi shiru yasa diyana sake chewa “yaya Aryan kasan me nake son tambayar ka bata jira amsar shi ba, ta chigaba da chewa, mata ma suna aikin soja ne? Tsaki Aryan yaja yana kawar da kansa gefe, dan ya lura in ya biyewa diyana zata chaza masa Æ™waÆ™walwa “ke ban sani ba tashi ma ki tafi É—aki yayi maganar da É—an tsawa, miÆ™ewa tayi da kyar ta kama hanyar fita, har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo karaf suka haÉ—a ido dan kuwa ita yake kallo, a shagwaÉ“e tace “yaya Aryan to pls ka faÉ—a min mana idan mata na aikin soja nima zan shiga ne dan Allah ina san riÆ™e bin diga kuma kayan sojoji na burgeni, ido kawai ya zuba mata ba tare daya bata amsa ba, ganin bai da niyar magana yasa ta fara bubbuga kafa ta turo baki tana yarfe hannu tafara magana “dan Allah yaya Aryan ka faÉ—a min kaji kodai zaka bani naka kayan sojojin da bindigar kane nasa nima, kallan ta kawai yake dan ya kasa magana tunani yake wai anya wan nan mutunche yarinya bata da tsoro ko kaÉ—an jiba yadda take min magana, “yaya Aryan na tafi tun,da bazaka faÉ—a min ba bari naje na tambayi wan chan mai kama da hiyana, yama sunan shi wan nan da baya dariyan nan, tayi maganar tana É—aga kai sama kamar mai tunani, jin ta ambachi zataje ta tambayi DON ne yasa Aryan saurin chewa “mata basa aikin soja sai dai susa uniform É—in mazajen su, wai bakin che kema soja zaki Aura ba, da sauri ta gyraÉ—a masa kai alamar eh “to kibari idan kin Auri sojan sai ki rinÆ™a saka uniform nashi, “to shike nan natafi ta karisa maganar tana ficewa daga É—akin, girgiza kai Aryan yayi yana faÉ—in “da kinje kin tambayi DON kuwa da baki sake yiwa kowa magana a gidan nan ba, dan ina da tabbachi hakoran ki ko É—aya ba zai rage a wan nan É—an bakin surutun ba, wai yarinya’ne ba zaka ga baki ba sai magana, yayi maganar yana karisa hayewa saman gadon sa, ya kwanta tare da lunshe ido yana sauke ajiyar zuchiya.

YOLA

almost 30mnt inna na kwanche takasa miÆ™ewa sai nishi take da kyar da kyar, a wan nan yanayin bokan nata ya shigo ya same ta hannunsa riÆ™e da wata bakar kwarya mai É—auke da wani jan ruwa a chiki, kanta ya É—ago ya kafa mata kwaryan a baki yafara É—ura mata maganin, bashi tafara ha’É—iyewa sai da ta shanye tas san nan yasaki kanta, ya miÆ™e ya fita ya koma wajen tsafe tsafen sa ya zauna jim kaÉ—an, sai ga Inna tafito da kwarin ta, tazo gaban sa ta zauna tana faÉ—in “zan iya tafiya, wani mahaukachin dariya yayi ha,ha,ha, kafin yace “eh ammafa gidawo bayan sati É—aya dan kiji saka makon aikin ki “to tache tare da miÆ™ewa tanufi hanyar fita har ta kai bakin kogon zata fita sai kuma dai ta juyo tace “zan iya zuwa anjima musake yin abun da mukayi É—azun, wani dariyar mugun ta yayi a zuchiyar sa yana faÉ—in aiki ya fara kamaki ke nan abu yayi kyau kinshigo hannu, a fili kuwa che’mata yayi “eh idan kina soma yanzu ma ai sai muchi gaba, da sauri ta juyo ta nufoshi tana faÉ—in “eh ina so, sake kwashewa yayi da dariyar mugun ta kafin yace “to shiga chiki ina zuwa, tun bai karisa maganar ba ta shige chikin É—an kewayayyen wajen nashi, ta chire mayafinta ta haye kan yar figaggi yar katifar nashi,

ba jimawa shima ya shigo zindir babu kaya ajikin sa hayewa kanta yayi sai wani faman murmushi take, shima murmushi yake sai dai shi na mugunta yake, chire mata kaya yayi yafara aiki, awan nan karon ma sosai ya nemeta gaba da baya sai dai bata ji zafi kamar na É—azun ba hakan kuma ya samo asali ne, saboda maganin daya bata, awan nan karon tare suka murji juna sai wani nishi suke dukkan su biyu,

Bayan sun gama shike ayan sune ya kwanta a gefenta yana mai da numfashi, itama sai wani mai da numfashi take, sai misalin karfe 7 na dare Inna ta koma gida sai farinchiki da murna take tana faÉ—in “gobema komawa zanyi wlh irin wan nan abu haka, ko sallar mangariba babu bare issha batare da tayi wanka ba ta haye yar katifar chiyawar’ta ba jimawa barchi ya É—auke ta ko abinchi bata nema ba.

KANO

Misalin karfe 8 na dare gaba É—aya family Abba sun haÉ—u a palo ban da DON shi bai fito ba, gyaran murya Abba yayi, yana kallon diyana dake zaune kusa da Aunty farida tana chin ayaba, yafara Magana “naji duk abun daya faru zuwan ku Yola, sorry my daughter kinji ba zaku sake zuwa garin ba inshaa Allah. Shiru ya É—anyi kafin ya dawo da kallan sa Abba yayi kan Ahmad dake zaune kusa da Aiman, ya chigaba da Magana, “kai Ahmad kashirya daga gobe zaka fara hawa kujerer mulki gobe misalin karfe 9 zaka fita fada,waro ido waje Ahmad yayi yana san magana, amma ba hali dan idan Abba yana magana ba wan da ya isa ya tanka har sai ya gama,

É—aure fuska Abba yayi ganin yadda Ahmad ya zaro ido, dawo da kallansa kan Khalid yayi ya chigaba da magana, “kai kuma baba jibi Monday su Zahra zasu koma school kaje kamusu abun daya dace,

Shiru Abba ya ɗanyi yana mai da numfashi san nan ya ɗora dachewa sai magana ta gaba kuma, ke hiyana tashi kije ki kiramin Safras, ya karisa maganar yana kallan hiyana, mikewa hiyana tayi kamar zatayi kuka jikinta har ɓari yaƙe saboda tsoron DON, shi kanshi Abba ya lura da yanayin data shiga, amma dole ne taje ta kira masa DON dan haka sai ya shareta, tafiya take kamar wadda kyau ya fashiwa a ciki ta fito daga palon

Part na DON ta nufa tun a bakin kofar palon kasa take sallama, amma shiru babu wadda ya amsa chikin palon ta shiga babu kowa, a’hakali kamar bata son taka kasa tanufi stair É—in, ta haura a bakin kofar palon daman ta tsaya tasake, doka sallama, nan ma shiru, hannu tasa a hankali ta tura kofar palon, ta shiga shiru shima babu kowa, kofar betroom É—insa ta nufa a bakin kofar ta tsaya da murya kamar mai shirin fashewa da kuka tayi sallama shiru bai amsa ba, sake sallama tayi nan ma shiru bai amsa ba, shiru tayi tana tunanin, yanzu ya zanyi, in koma palo ne to idan ma na koma palo in che me, ban isa in che baya nan ba tun da sun san yana gida, to idan kuma na koma na chewa Abba na faÉ—a masa, kuma bayan ban faÉ—aba zasuji shiru bai zoba kar Abba ya masa faÉ—a shikuma ya hukun tani, idan kuma nashiga nan ma zai iya hukun tani, Almost 30 hiyana na tsaye tana tunanin mafita data ga dai tsayuwar ba abun da zai tsinana mata sai tayi shahada ta tura kofar betroom É—in a hankali ta shiga da sallama.

subhanallah kara waro blue eyes nata tayi sosai a kansa, kwanche yake saman katafaren gadon sa idon sa a lunshe kamar barchi yake, daga shi sai short a jikin sa faffaÉ—ar kirjin nan nasa awaje,ga wani bakin gashi mai kyan gaske kwanche a kan kirjin, lallausan bakin gashin kan nan nasa kuwa duk ya bar bazu a kan face É—in sa ya rufe masa ido, zubawa É—amtsen hannun sa ido hiyana tayi tana kallo kara waro blue eyes nata tayi da kyau a chikin zuchiyar ta yana faÉ—in “kai ai wan iri hannun na sa ai ya kusa chin yata, tab idan ya bugeka da hannun nan sai ka mutu, dawo da kallonta tayi kan faffaÉ—ar kirjin sa, gashin dake kwanche a wajen kawai take kallo tana faÉ—in, wow a chikin zuchiyarta, Allah ka bani miji mai kashi a kirji nima yana min kyau, sauko da blue eyes nata tayi izuwa kan chin yoyin’sa, wani bakin gashi ne mai kyau da sheki kwanche a kan chinyar nasa, sosai ta zuba masa ido tana kare masa kallo from head to toe, tana yaba irin kyansa da kyan jikin sa, tayi nisa chikin tunani sai taga alamar ya É—an motsa hannun sa, a ruÉ—e ta ja da baya ta koma jikin kofa, a tsorache tace “yaya Prince Abba na kiran ka, shiru bai amsa ba cikin tsoro ta sake mai mai ta maganar, batare daya buÉ—e ido ba ya furta “get out chikin tsawa, ai tun bai gama faÉ—eba tayi waje daman ita burinta kawai yaji sakon Abba, tun da yaji shike nan

da gudu tabar É“an garen nasa ta koma falon Abba, sai numfashi sama sama take, gaba É—aya idon mutanen falon ya dawo kanta ban da Aryan da Fahad abin chin su kawai suke chi “sister lfy kike numfashi kamar wadda tayi gudu chewar Yusuf ya yayi maganar yana kallon face nata, ita kam Zahra ko ajikin ta dan tasan dalili, Abba ma yasan hakan zata iya faruwa yasan sai DON ya kore’ta, da gangan yake aika ta daman dan yasan duka dai DON bazan duketa ba tun da yamasa gargaÉ—i a kan haka, dawo da kallansa Abba yayi kan su Yusuf yayi yace “kai ina ruwan ku da ita zoki zauna ki chigaba da chin abinchi ki kinji my daughter, É—aure fuska Aunty Amarya tayi dan taso jin me DON yawa hiyana take numfashi haka ko marin’ta yayi,

Zama hiyana tazo tayi awajen da ta tashi ta É—auki spoon a hankali tafara chin abinchin ta, shiru shiru DON bai zoba da har suka gama chin abinchin, Abba ya dubi Khalid rai a É—an bace yace “kai baba tashi kaje ka chewa Safras nifa na haife shi ba shi ya haifeni ba da zai ajiye’ni ina jiran sa, Khalid na kokarin mikewa, sai ga DON ya shi go sanye chikin jallabiya fari, yana taku irin na jaruman maza, fuskar san nan kamar bai san menen dariya ba sai wani kakkau da kai yake, gaba É—aya su Aunty Maryam kowa ya shiga taitayin sa, har da Aunty amaryan, kujerar dake fuskantar Abba yaje ya zauna da sauri kannen nasu suka fara É—aga masa gaisuwa, bai ko kalli inda suke ba bare ya amsa musu gaisuwar sai ma kara É—aure fuska da yayi, sai da suka gama gai suwar nasu sukayi shiru kowa ya nitsu suna sauraren suji abun da Abba zai che.

A hankali DON ya buÉ—e É—an karamin bakin nan nashi kamar bai san motsa lallausan lips nashi, ya fara gaishe da iyayen nasu, fiska ba yabo ba fallasa Abba ya amsa haka Aunty amarya da Ummi, Ammi kuwa É—aure fuska tayi sosai kafin ta amsa masa,Shiru yayi san nan ya sun kuyar da kai, shiru palon yayi gaba É—aya Abban ne ya katse musu shirun da chewa “Zahra kutashi kuba mu waje, tun bai kai karshen maganar ba Zahra hiyana diyana lamrat amrat suka miÆ™e suka bar palon,

dawo da kallansa kan su DON Abba yayi yafara Magana “abun da yasa na taraku a nan shine, duk kanku lokachi yayi da zakuyi Aure, a sukwane DON Aryan Fahad haidar Aiman da kuma Ahmad suka É—ago kai a tare suna kallon Abba kamar zasuyi ihu musam man DON Aryan Fahad Aiman,su nasu É“achin ran na da ban ne kamar wayan da aka chewa uban su ya mutu, Khalid Yusuf Umar kam ko ajikinsu, Aunty farida ma É“ata rai tayi sosai dan tasan wan nan maganar da Abba yayi ba karamin É—agawa su DON hankali zai yiba, dan babu hakan a tsarin su, tafiso a barsu sunemi mata chikin nitsuwa, dan idan akache za’a tilasta musu wlh duk wadda aka aura musu tashiga uku,

“No Abba No gaskiya kabar wan nan maganar ni babu mace a tsarin rayuwa kamin wani hukunchin dai amma banda batun mace pls Abba, chewar DON, ya karisa maganar chikin wata iriyar voice wadda da kajita kasan tsantsar kiyayyar macece a ranshi,ga fiskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa, shiru Abba yayi ya zubawa DON ido har yakai karshen maganar tashi, shi kanshi Abba yasan chewa mawuya chin abune DON Aryan su yarda da batun Aure, domin babu hakan a tsarin da sukayi wa rayuwar su,shiyasa ma bai takura musu ba tsawon lokachi ya bar su, to amma yanzu yazama dole suyi Aure dan chika sunnan ma aiki, kuma yafi son su kawo matan da zasu Aura da kansu dan idan yace zai Aura musu zaÉ“in sane, yasan matan sun shiga uku

sosai Abba yashiga tunani, gaskiya bai kamata nayiwa DON dole ba idan yayi haka tofa akoi babban matsala tsabar tsanar mace dayayi ne jiba agaban kannen sa yau ya buÉ—e murya haka yana magana har da chewa sorry mutumin da magana wahala yi take masa, lallai bai kamata na takura masa ba idan kuwa nayi haka zanyi dana sani mai girma, addu’a kawai ya kamata na masa.

Ganin Abba yayi shirune yasa Aryan chewa “Abba pls kabar maganar auren nan wlh ba muso babu mace a tsarin rayuwar mu pls my Abba kaji ya karisa maganar yana É—an dafa hannun Abba, chikin fushi Ammi tace “babu mace a tsarin rayuwar ku ko, to ku chiremu muma a tsarin rayuwar ku tunda muma matane tana kaiwa nan ta miÆ™e ta fiche daga palon chikin fushi da É“achin rai, dafe kai DON yayi a zuchiyar’sa yana faÉ—in jiya nayi É—aya yau kuma na biyu am so so sorry Ammi ammafa aure kam ba zan yi ba gaskiya sai dai duk abun da zai faru ya faru, miÆ™ewa Ummi tayi itama tana faÉ—in “ranka ya daÉ—e idan kun gama zaman ka kira malam mai rukiyya yazo ya musu dan ga dukkan alamu aljana che ta auri Æ´a’Æ´an nan, a sukwane suka juyo gaba É—ayan su suna kallon Ummi, É—aure fuska tayi kafin ta juya ta fice daga palon, kallan Aunty amarya Abba yayi tun bai yi magana ba ta miÆ™e ta fita tana É“ata rai dan taso jin me Abba zai che musu wani amsa zai basu, “Maryam salma mardiya kutashi ku bamu waje,chewar Abba yayi maganar yana kallon su, jiki ba kwari suka miÆ™e suka fita.

Palon ya rage daga Aunty farida, DON Khalid Yusuf Aryan Aiman Ahmad Umar haihar da kuma Fahad

Dawo da kallansa Abba yayi kansu DON ko’wannen su sai faman É—aure fuska yake sai wani chi chijewa suke, É—an gyaran murya Abba yayi kafin yafara Magana “ke farida na barki ne saboda bakin ku É—aya dasu ke che sirrin su basu taÉ“ayin wani abu batare da kin sani ba dan haka ku saurareni, “ni bazan tilas ta muku kuyi Aure ba, wani dauyayyar ajiya zuchiya DON Aryan Fahad, suka sauke a tare, har da É—an sakin fuska, ganin hakan yasa Abba murmushi yachi gaba da chewa “bazan takura muku kuyi abun da baku so ba, saboda farin cikin ku nake bukata, amma dai burina shine naga kunyi aure kun haifamin jikoki shine babba burina a duniya kuma farinchiki na, ni ina san farin chikin ku ban sani ba ko kuma kunason nawa, ban sani ba ko zaku iya chika min burina tun ina raye, É—an dakatawa Abba yayi yana satar kallon fuskokin su,a ransa yana faÉ—in nina haifeku ai baku kuka haifeni ba a chikin ruwan sanyi zanyi maganin ku, nan take fuskar DON da Aryan ya sauya sosai dan sun gano tarko Abba ke neman yima’su da kalaman sa, Fahad kuwa sai murna yake Abba bazai yimasu dole suyi aure ba, shiru Aiman yayi ya É—ora hannu a gemun sa yana kallon kasa yana nazarin magan ganun Abba, Khalid da Yusuf kuwa É“ata rai sukayi sosai dan su gaskiya Aure suke so kuma suna da matan da zasu aura, amma DON da Aryan suna neman watsa musu farin chiki, Aunty farida kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai jin kalaman Abba, tabbas Abba na da gaskiya yakama suyi aure amma banso Abba yabi musu ta wan nan sigar ba da an bi a hankali an bisu da addu’a inshaa Allah komai zai tafi dai dai

Ganin sunyi shiru kowan nan su yatafi tunani yasa Abba chewa, “nifa ban takura’wa kowa daga chikin kuba, burina da kuma farinchiki na kawai na faÉ—a muku, kuma ban che dole sai kun chika min burina ba koma me ni zan zama mai chika muku burin,kuma mai saku farin chiki a ko da yaushe, kuje ku zauna kunitsu kuyi tunani yana kai karshen maganar yamike ya shige betroom É—in sa,

chikin fushi da É“achin rai DON ya furta “never Abba aure fa, wlh I cannot do it I cannot do it gaskiya bazan iya chika maka wan nan burin nakaba, a fusache ya miÆ™e ya bar palon, da sauri Aryan ya miÆ™e zai bi bayan sa “ina zakaje Aryan Aunty farida ta tambaya, “Aunty farida baki ganin É—an uwana yana chikin É“achin rai ne ai bazan iya zama ba, yana kai karshen maganar batare daya jira amsar taba ya fiche da sauri, a fusache Aiman ma ya mike yaja tsaki yana faÉ—in “nima dai ba zan iya chika’wa Abba wan nan burin na shi ba sai dai in ku zaku iya bani da lokachin mace yanzu, yana kai karshen maganar ya juya da, sauri ya nufi hanyar fita dan bai dan Aunty farida ta. dakatar da shi

Girgiza kai Khalid yayi kafin yache “gaskiya a wan nan gaÉ“ar ya kamata mu chika wa Abba burinsa, domin duk wani abun da mukeso yana mana yanzu ki duba Aunty babba saboda bama son mulkin nan, Abba ya hakura da bamu mulkin duk dan muyi farin chiki, tun muna yara har muka girma har izuwa yanzu bamu taÉ“a chewa Abba muna bukatar abu kuma yaki yi mana ba, to meyasa mu kuma zamu rinÆ™a kin abun da yake so, yache zai bamu mulki munki ya hakura yanzu kuma kin fa ji auren mu shine kaÉ—ai burin daya rage masa a duniya da yake san mu chika masa,to why bazamu chika masa burin sa ba. É—an daka tawa Khalid yayi da magana yana mai da numfashi “Kana da gaskiya Khalid amma a hankali Ya kamata abi abun tun da kaga dukkan ku ba soyayya kuka taÉ“ayiba babu wata alaka da ta taÉ“a haÉ—aku da wata mace idan ba mu yan uwan ku na gida ba, SO kaga abune mawuyache lokachi É—aya a che zaayi muku maganar aure garama kai dasu Yusuf da sauki, amma kafini sanin halin DON da Aryan, basu san wani abu wai shi soyayya ba, bai da che amusu zuwa É—aya haka ba a hankali za’a shawo kansu, yanzu dai zanje in same’su dan musan abunyi tana kai karshen maganar ta miÆ™e tanufi hanyar fita, shiru Khalid yayi yana tunani, miÆ™ewa Fahad ma yayi yabi bayan Aunty farida, haidar da umar ma suÆ™a miÆ™e suka fita suka nufi É“an garensu palon ya rage Khalid Ahmad Yusuf.

*💫STAR LADY💫*

👑UK Writers👑

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

 

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

 

No comments