Duk karfin Izzata Book 1 Page 32
Episode 3️⃣2️⃣*
Da sauri ta juyo ganin jabir ne yasa ta Æ™ara É—aure fuska sosai, ta sunkuyar da kanta kasa, “my hiyana me ya same ki kikayi kuka? Chewar jabir Ya yi maganar yana matsowa kusa da ita, É—an ja da baya kaÉ—an tayi kasa kasa tace “ina kwana, batare da ya amsa gaisuwar nata ba ya sake mai mai ta mata tambayar daya mata da farko “me yasa meki ki kayi kuka? waya taÉ“amin ke?
Chikin sanyin murya tace “ni ba wan
da ya taɓani kawai nayi kuka ne saboda an mai da kanwata garinmu,
“Eyya to sorry kinji kije class idan an tashi break kizo muyi hira dan ina missing naki sosai, ko dai ke baki missing na ne? Ya karisa maganar yana É—an dukar da kai yana leka fuskan ta dayake ta sunkuyar da kan kasa, shiru tayi bata sake che masa komai ba, ganin bata da niyar magana ne yasa yace “to kije class É—in idan antashi sai kizo na kawo miki tsaraba
Bata jira ya karisa maganar shiba ta shige class nasu da sauri, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya juya ya nufi nasu class É—in
Sosai Bgs yake sauri kamar zai tashi sama taku yake irin na sadaukin yaki, yazo dai dai zai shiga É“angaren Aryan, yajiyo muryan Abba daga bayan sa yana faÉ—in “jirani mushiga tare, batare da ya juyoba ya tsaya har Abba ya kariso, wajen a tare suka jera zuwa chikin part É—in,
“Menene ya hana Aryan zuwa sallar asuba Abba ya tambaya yayi maganar dai dai lokachin da zasu haura stair case É—in chikin palon Aryan,
“Abba wlh nima ban saniba abun da nazo tambayar sa kenan, shiru Abba yayi bai sake chewa komai ba, har suka karisa betroom É—in, da sallama suka shiga a tare
Kwanche yake saman katafaren gadon sa,yana sharara barchin, da mamaki Abba ya juyo ya kalli Bgs wadda shima Abba yake kallo..
….Karisawa bakin gadon sukayi a tare zama Abba yayi a gefen gadon shi kuma Bgs ya haye saman gadon ya É—an jayye bargon da Aryan ya lulluÉ“u, zuba masa ido Bgs yayi sosai kamar mai karantar wani abu a kan face nashi
“Abba da alama É—an uwana bai yi barchi jiya da daddare ba koda kuma yayi to kaÉ—an ne, ka duba time fa yanzu Almost 8:5am amma yana barchi ko sallar asuba bai yiba, anya Aryan yana da lfy kuwa? Dogon numfashi Abba yaja kafin yace “kila akoi abun da ya tsare sa ya hana shi barchi da wurine.
Guntun tsaki Bgs yaja sannan yasa hannu yana É—an bubbuga hannun Aryan,
“Aa Safras ka barshi mana yayi barchin sa chewar Abba “aa Abba ya tashi dai kofa sallar asuba bai yiba ya tashi idan yayi Sallah sai ya koma barchin, shiru Abba yayi bai sake Magana ba, bubbuga Aryan Bgs yake yana kiran sunan sa “my blood, my blood
Da kyar Aryan ya iya waro ash eyes nashi nan, sun chanza sunyi jaa saboda barchi chikin muryan barchi yace “Bgs lfy? ÆŠaure fuska Bgs yayi kafin yace “zaka tashi kaje kayi sallar asuba ne ko dai sai na maka 1bloo 7 die,
Wani sallar asuban kuma? I Already nayi sallar ton asuba ɗin, yayi maganar yana kokarin miƙewa zaune, da kyar ya iya miƙewa zaune, da sauri yasa hannu ya dafe kansa dan ji yake kamar kan nashi zata faɗi kasa ga wani azaban chiwo da take masa, sai sara masa kan keyi kamar zai fashe,
Ganin Aryan ya dafe kai ne yasa Bgs saurin kai hannunsa saman goshin Aryan É—in yana faÉ—in “my blood lfy? Menne? Kai É—inne ke maka chiwo? Karisa hayewa gadon Abba ma yayi ya sa hannun’sa ya riko kan Aryan yana faÉ—in
“Aryan meke damun kane? É—ago jajayen idon sa yayi yana binsu da kallo ganin yadda suka ruÉ—ene yasa ya É—an kakalo murmushi gefen fuska, da kyar ya iya motsa lallausan red lips nashi ya furta “bb komai, a tare Bgs da Abba suka chire hannun su daga saman goshin nasa,
Aryan me yasa baka je masallaci da asuba ba? Chewar Abba yayi maganar yana sauÆ™a daga gadon, “Abba makara nayi wlh, lokachin da natashi already an gama Sallah “me yasamu wayar ka? na kiraka da asuba ai a kashe, Bgs ya tambaya yana kallon face nashi,
“Eh Ni na kashe wayar jiya da daddare, to akan idan nazo barchi zan kunna sai na manta
Shiru Bgs ya É—an yi kafin ya chiro wayar sa daga aljihu wandon sa, ya kunna hasken screen É—in ya chire password ya shiga contact nashi, layin Fahad ya fara kira ringing É—aya Fahad ya É—aga
“Hello big bro, ina kwana, “lfy Fahad, baki buÉ—e Abba da yaya Aryan ke kallon Bgs tunani Abba yake wai daman Bgs ya iya amsa gaisuwa tab lallai Fahad yarone mai Sa’a ya chire tuta a gidan nan, kaiii
Yaya Aryan ma tunani yake anya na taɓajin Bgs yana amsa gaisuwar wani ko wata kuwa? Yayi iya tunanin sa duk bai tunano in da Bgs ya taɓa ansa gaisuwa ba kwata kwata, ko awajen Aiki yaran mu zasu gaishe sa sai dai ya ɗaga musu hannu ko kuma ya musu alamar yaji da ido, ashe daman yasan yadda ake amsa gaisuwar kenan? Lallai yaya prince sai dai nace Allah ya shirya min kai.
“Fahad ka kawomin coffee mai zafi ka haÉ—o da hot milk, ina É—akin Aryan yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran.
..dawo da green eyes nashi yayi kan Aryan dake zaune ya zuba masa nashi Ash eyes É—in shima yana kallon sa
“Aryan lfy kake kallo na haka? Kawar da kallon sa gefe Aryan yayi zai yi magana sai Abba ya rigashi da chewa “ba dole ya kalleka ba daman ka iya amsa gaisuwa? Dawo da kallon sa Bgs yayi kan face É—in Abba yace “na iya Abba “au ka iya shine idan aka gaida ka baka amsawa “wlh Abba bawai da gangan nake kin amsawa ba, kawai ni ban son magana ne Allah harchena nauyi ya kemin idan zanyi magana
“Ba shakka Safras nima shaida ne ba tun yanzu ba haka aka haifeka baka son yawan magana amma dai karinÆ™a daurewa kana Amsa gaisuwar yan uwan ka, shiru yayi bai sake chiwa komai ba
A hankali Aryan ya zuro kafar sa kasa kafin ya sauko daga gadon, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi toilet, wani irin jirine ta kwashesa batare da ya shirya ba kawai sai dai yajisa a faffadar kirjin Bgs, kara waro ash eyes nashi waje yayi, yana kallon face ɗin Bgs yayin da shima Bgs ɗin shi yake kallo
“Aryan baka da lfy ne? Abba ya tambaya yana karasowa wajen su, da kyar ya iya buÉ—e É—an karamin bakin nan nashi yace “aa Abba lfy na kalau kawai kai nane ke É—an min chiwo sai jiri da nake gani, É—an duÆ™awa Bgs yayi batare da yayi Magana ba ya saÉ“i Aryan a kafadar sa ya nufi toilet É—in dashi,
komawa gefen gadon Abba yayi ya zauna yana tunani ” lallai Aryan ai ka makara ita soyayya baa nuna mata jaruntar, ai san da zaka kawo kanka ma ba wan da ya sani, Ni kuma inshaa Allah sai na koyamaka sanin darajar mace sai kasan chewa mace halittace mai daraja Abba yayi nisa chikin tunanin sa, bai maga shigowar Fahad ba sai dai yaga mutun yana Æ™oÆ™arin hawa gado yana faÉ—in
“Abba ina kwana, murnushi Abba ya sakarwa Fahad kafin yace “lfy ka tashi lfy, fuskar nan a É—aure kamar bai taÉ“a dariya ba, da kaga Fahad ba sai an faÉ—a maka chewa kanin Bgs bane, zaka gane domin komai nasu iri É—aya, kaman nin su É—aya irin yadda Bgs ke haÉ—e fuska haka shima Fahad ke yi, rashin son maganar su ma irin É—aya komai dai na Fahad sak na Bgs, dan yanzu ma da Abba yace katashi lfy Fahad, bai amsa ba sai ma kara É—aure fuska da yayi ya zaro wayarsa yana latsawa, Abba kam ko ajikinsa dan gaba É—aya Æ´a’Æ´an sa ba wanda bai san halin su ba,
Hannun su riÆ™e chikin na juna Bgs da Aryan suka fito daga toilet É—in, da alama brush Aryan yayi, saman gadon suka haye, Bgs yace “Fahad ina coffee É—in, Fahad ba tare da yayi magana ba ya sauko daga gadon ya nufi table É—in tsakiyar É—akin ya É—auko kwakkyawar plate mai É—auke da haÉ—aÉ—É—un cups guda 5 kowani cup an rufeshi da É—an karamin plate mai kyau, bakin gadon ya dawo ya tsaya yana faÉ—in “gashi nan, É—ago green eyes nashi Bgs yayi yana kallon Fahad, da mamaki yace
“Fahad coffee da hot milk kawai nace ka kawomin ya naga cups har guda biyar?
“Eh to ai naji kache kana É—akin yaya Aryan ne shiyasa na haÉ—o muku kai da shi ni kuma na haÉ—awa kai na black tea dan nima na taya ku sha, kaga cups 2 naka 2 na yaya Aryan, É—aya’n nan kuma nawa, girgiza kai Bgs yayi yana faÉ—in “to ai daman Aryan nace ka haÉ—awa coffee ba Ni ba Ni kataÉ“a ganina inashan coffee ne? Kaje ka ajiye a saman table É—in, bari mu sauko, juyawa Fahad yayi ya maida plate É—in saman table sannan ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1, yanan jiransu
Miƙewa Abba yayi yana faɗin sai kun fito fada sannan ya nufi hanyar fita, Aryan ne kawai ya amsa wa Abba da to
A tare suka sauko daga gadon suka nufi Fahad dake zaune saman sofa yana latsa waya.
A saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna da sauri Fahad ya miƙe ya ɗauko cup mai ɗauke da coffee ya miƙawa Aryan, sannan ya ɗauko cup mai ɗauke da hot milk ya miƙawa Bgs shi kuma ya ɗauki black tea ɗin sa ya koma ya zauna, shiru sukayi
A hankali Bgs ke ɗan korɓan hot milk ɗin haka zalika Fahad yana latsa waya yana ɗan kurban Black tea, Aryan kuwa ya riƙe cup ɗin ya kasa kai wa bakin sa yayi shiru kamar mai tunani
“Aryan me kake tunani? Meke damunka? Bgs ya jefo masa tambaya, ajiyar zuchiya ya sauÆ™e kafin yace “babu komai my blood bana jin sha coffee É—in ne bakina ba É—an É—ano
ajiye cup É—in hannun sa Bgs yayi sannan ya juyo da kyau yana kallon Aryan “Aryan wai nikam yaushe kadawo ragon namiji ne? Waro manya manyan ashe eyes nashi waje Aryan yayi a sukwane ya juyo da kyau shima yana kallon Bgs, da mamaki “rago ya mai mai ta kalmar chike da jin haushin dan gantashi da kalmar da Bgs yayi, nan take kuma yaji wani karsashi yazo masa, ji yayi duk wata damuwa ta gudu domin ba abun da ya tsana arayuwa iri amasa kallon ya gaza ko kuma yana da rauni ko dai ache masa rago.
Ganin yayi shirune yasa Bgs yace “me ya sauya kane Aryan? da alama fa yanzu kafara zama… da sauri Aryan ya sa hannu ya rufe masa baki bai bari ya karisa maganar ba domi ba zai iya jin taba, zuba masa green eyes nashi kawai Bgs yayi yana kallon face É—in sa
A hankali Aryan ya zame hannun’sa daga bakin Bgs san nan ya É—auki cup É—in coffee sa ya fara sha, juyawa Bgs ma yayi ya É—auki hot milk nashi ya chigaba da kurÉ“a a hankali, shiru sukayi ba wanda ya sake magana
YOLA
da sallama Inna habiba ta shiga gidan su buba, da kyar take iya jan kafarta, har ta karisa tsakar gida, inna yaya Bello da innar buba suna zaune saman tabarma guda, inna yaya Bello tana shafawa innar buba magani a kafarta daya kumbura sosai yayi wani green kamar ya ruɓe,
Saman ta barman Inna habiba taje ta zauna “sannun ki da zuwa habiba Chewar Innan yaya Bello, wani harara inna ta wurgawa inna yaya Bello, tana faÉ—in “to ai ba wajenki na zoba munafuka sai ki tashi ki bamu waje, ajiye robar maganin hannun ta innar yaya Bello tayi tana kokarin miÆ™ewa,
Da sauri innar buba ta riÆ™e hannun ta tana faÉ—in “aa innar bello dalla kiyi zaman ki, ki rabu da habiba, bata da hankali ne, waro ido waje inna tayi chikin tsawa tace “ke larai ni zaki chewa bani da hankali eh, au yanzu da wannan munafukar kika haÉ—a kai,kenan? “habiba ki daina zagin min yar uwa wlh idan ba haka ba zamusa yaranmu su miki duka tsiya,
Wani dariya Inna tayi har da shewa kafin tace yanzu ne kika san dachewa ita yar uwarki che ko? to wlh idan baki dawo chikin hankalin ki ba Allah sai na tona asirin duk abu da kika aikata wa yaron ta Bello, dariya Innar buba tayi kafin tace
“Ki tona mana, dan Allah habiba ki tona ni bani da wata damuwa idan kin tona saboda nasan bello da innar sa, zuchiyar su ba irin na dabbobi bane wlh duk kauyen nan babu mutanen kirki kamarsu ki duba duk kuntatawa rayuwansu da nayi hakan bai hanasu taimako na lokachin dana shiga halin mutuwa ko rayuwaba, alhamdulillah kuma ni nasamu na roki gafarar su kuma sun ya femin, ke ma wlh idan dai baki tuba ba to karshen ki ba zaiyi kyau ba, ko da yake ko kin tubama dole sai kin karÉ“i azaba da hukunchi, domin Allah baya yafe hakkin wani bawan, sai dai idan bawan shiya yafe maki da kansa, to kuma aina zaki ga bappa ki roÆ™i gafarar sa ina zakiga su hiyana da mahaifiyar su, duk babu wlh habiba kekam kinshiga uku
A fusache inna ta miÆ™e ta É—aga hannu zata zabgawa innar buba mari, chikin tsawa Bello dake tsaye a bayan su tun É—azun yace “wlh kina marin ta sai na shemeki da sandar nan, a tsorache inna ta juyo da sauri dan tasan Bello akoi shi da zuchiya sosai kuma idan yace zaiyi abu tofa zai yi ne “zo ki fita mana a gida Bello ya faÉ—a yana nuna mata hanyar fita da hannun sa, ba musu ta kama hanya fita tana jan kafa a hankali hankali har ta fice daga gidan
Karisawa yaya Bello yayi wajen su inna ya zauna gefen innarsa yana faÉ—in “innar buba kinsha maganin ki kuwa? “eh bello nasha ni dai ba abun da zanche muku sai dai in muku fatan alkhairin kuna da kyakkyawar zuchiya
“Ki daina faÉ—in haka Inna ai duk abun da muka miki yiwa kaine kuma ai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya faÉ—a chewa idan kana tare da mutun yana aikata abun da ba dai dai ba to karka kyamachesa karka gujesa ko da ka masa wa’azi bai jiba karka damu ka jashi a jiki kana masa alkhairin a hankali kana nuna masa abun da ya keyi ba mai kyau bane sannan kana binsa da addu’a, sai kiga Allah ya shirya shi ya chanza hali ya dai na, ba wai idan kaga mutun yana abun da bai dache ba sai kaje ka zauna kana zaginsa kana tsine masa a chikin mutane ba, yanzu ba gashi da muka jaki ajiki bamu je wajen kowa mun zage kiba bamuyi gulmar ki da kowa ba bagashi Allah da ikonsa ya shirya mana ke ba, kin gane gaskiya
Ajiyar zuchiya Innar buba ta sauke kafin tace “hakane Bello zancheka gaskiyane to Allah dai yasa itama habiba ta gane Allah É—aya ne, a tare innar yaya Bello da yaya Bello suka haÉ—a baki wajen chewa Amin,
Miƙewa innar yaya Bello tayi tana faɗin bari naje na ɗora mana girkin safe dan yau naga kamar hasana batajin daɗi,
miƙewa yaya Bello ma yayi ya nufi ɗakin sa dan ya duba jikin matar tashi, suka bar innar buba ita kaɗai,
Maiduguri
Da gudu junior ya fito daga É—akin su diyana na biye dashi a baya tana faÉ—in “wlh idan na kama ka zakayi bayani da harchen larabchi, kai tsaye É—akin Aunty farida suka nufa,
Aunty farida na kwamche saman katafaren gadon tana shararan barchinta chikin kwanchiyar hankali, kamar daga sama taji diran mutane a kanta, a sukwane ta farka ta miÆ™e zaune, ganin Aunty farida ta miÆ™e zaune ne yasa junior ya faÉ—a jikin ta yana faÉ—in “na É“uya ai, dafe kai Aunty farida tayi tace “my diyana zonan ki zauna, ba musu diyana ta zauna kusa da ita ta zuba mata ido
“My diyana kina jina, gyaÉ—a mata kai diyana tayi alamar eh chigaba da magana Aunty farida tayi, “my diyana yanzu fa kin girma bai kamata kina wasan guje guje ba kinji ko? GyaÉ—a mata kai diyana tayi alamar taji, “good yanzu dai kutashi kuje palo ku fara breakfast ina zuwa, bari nayi wanka “Aunty farida yaushe zaki mai dani gida? Diyana ta tambaya
“My diyana ki saurareni da kyau kiji me zan faÉ—a miki, gida ba yanzu zaki koma ba, anjima dady’n junior zai dauke ki kuje yamiki registration a school nasu junior, ki fara zuwa school kinaji na ko? Turo baki diyana tayi kamar zatayi kuka tace “Aunty farida nikam ina son komawa gida Allah, ina son ganin yaya Aryan dasu Ammi,
“My Diyana yaya Aryan fa ya koma London, dan haka ki daina tunanin sa gida kuma zamuje nan da wata 3 kinji yanzu dai kuje Aunty jummai ta zuba muku abinchi kuyi breakfast ina zuwa,
Jiki ba kwari diyana ta miÆ™e ta riko hannu junior suka fito daga É—akin, ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke kafin tace “gaskiya ina da aiki babba kafin na sauya ki my diyana, dan ba abun da kika sani sai shirme da wasa
A hankali ta zuro kafar ta kasa sannan ta miƙe ta nufi toilet
KANO
Misalin karfe 3:10 dankareriyar family ka dake É—auko su hiyana daga school che ta kutso kai ta chika katafaren gate É—in gidan, kai tsaye parking space driver ya nufa, tun bai gama gashe motar ba hiyana ta buÉ—e kofar ta fito da sauri ta nufi part É—in Ammi,
Da sallama ta shigo palon betroom É—in Ammi ta wuche kai tsaye, da sallama É—auke a bakinta ta shiga
Ammi na zaune a bakin gadon ta, tana riÆ™e da littafin addu’oe, gaban ta hiyaba tazo ta tsugunna ta sunkuyar da kai kasa
da wanna zazzakar kuma sanyayyar muryan nata tace “barka da rana Ammi,
“Hiyana lfy bakije kin chire uniform ba eh? Ammi ta tambaya tana É—ago haÉ“ar hiyana da hannun ta, “Ammi daman nazo in roke ki ne dan Allah ni ki mai dani kauye sai ki dawo da diyana nan, kinji ni zan iya jure duk wata wahala, kuma zan iya hakuri da halin inna da buba, na san diyana bazata iya hakuri ba kome buba ya mata zata che zata rama kuma wlh Ammi dukan mutu buba yake mata tsoro nakeji kar su kasheta shiya gara ni ki kai ni chan sai ki dawo da diyana nan.
tsabar tausayi Ammi batasan lokachin da kwalla ya chika mata ido ba har yana kokarin zubowa, gaskiya hiyana mutunche, wadda samun irinta a duniyar yanzu akoi wahala ya Allah kasa ta zama matar É—aya daga chikin Æ´aÆ´ana
“Ki kwantar da hankalin hiyana kinji, diyana bata kauye, tana chan wajen wata kawata hajj fatima dake zaune a saudia, ammafa karki faÉ—awa kowa kinji ko an tambaye ki, kiche tana kauye
É—ago blue eyes nata tayi ta É—an saki murmushi har sai da dimple nata ya bayya, tace “to Ammi bazan faÉ—aba “yauwa my hiyana koke fa kinga yadda kika kara kyau da kikayi murmushi nan kuwa? To yanzu dai ki tashi kije ki chire uniform kiyi wanka kuzo kuchi abinchi, karki kara saka wata damuwa a ranki, “to kawai hiyana tace sanna ta mike da murnar ta har sauri take tanufi kofar fita
Tana tura kofar zata fita shi kuma yana shigowa karo sukayi kanta ya bugi faffaÉ—ar kirjinsa nan kasan chewar ya fita tsawo sosai, waro blue eyes nata tayi nan take tafara ganin jiri, baya baya tayi tana kokarin faÉ—uwa..
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
More comments an like pls
Post a Comment for "Duk karfin Izzata Book 1 Page 32"