Breaking News

Furar Danko 33

 

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

 

 

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

 

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

 

 

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣

 

 

 

…….Bai san ainahin Office ɗin nata ba, sai dai ganin motarta a harabar wajen ya sake tabbatar masa da tananan bata wuce ba. Tunanin zaman jiran fitowarta yayi, hakan ya sashi samun wajen zama a gurin securitys. Bayan gaisuwa a tsakaninsu bai sake kula kowa ba ya shiga sana’ar tasa ta game ɗin ball a waya. Biyar dai-dai babu alamar zata fito, tun yana ɗan ɗagowa ko zai hangota har ya fara sarewa ganin biyar da rabi har ta gota ma. Ga mafi yawan ma’aikata sun wuce dan motarta da wasu biyu ne kawai suka rage a harabar wajen. Ɗaya da ga cikin security ɗin ne ya dubesa tare da faɗin, “Abokina wanda kake jira har yanzu bai ƙaraso bane? Dan shida dai-dai ake rufe wajen nan fa”.

Wayar ya ajiye tare da ɗagowa ya dubi security ɗin fuskarsa a ɗan sake, sai dai ba murmushi yake ba. “Wadda nake jira tana ciki dan ga motarta nan, nima ina tunanin ko lafiya har iyanzu bata fito ba”.

“Kana nufin Madam Mawaddat Jiƙamshi?”.

Kai ya jinjina masa alamar ita. Shima security ɗin cikin nuna jimami ya ce, “Inaga dai yau aiki ne yay mata yawa gaskiya, dan a kullum zakaga idan bata zama ta farkon tashi ba to zata zama ta biyu. Nima kaina nayi mamakin rashin fitowar tata yau duk da dai naga wani aiki tasa a gaba kwana biyun nan mai muhimmanci. Amma bari na duba maka maybe bata san kana zaman jiranta bane”.

Kafin Smart ya samu damar cewa wani abu security ɗin yay gaba. Minti kusan uku sai gashi ya dawo. “Abokina inagafa kamar akwai matsala”.

“Matsala kuma? Tami fa?”. Smart ya faɗa ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Amma sai ya dake abinsa kamar babu komai. Security ɗin ya cigaba da faɗin, “Bawai matsalar bace a zahirance, na samu sakatariyarta ce kawai zaune cikin damuwar wai tun ɗazun data fita ta dawo ta shige office ta rufe kanta har yanzu bata fito ba. Ta mata knocking kuma yafi sau ashirin batako ji motsinta ba sai yanzu babu jimawa taji maganarta kamar cikin surutai”.

Ƙirjinsa ne yaji ya ƙara bugawa, ya kai yatsunsa biyu saman goshi ya ɗan murza. Basai ya nema ƙarin bayani ba yasan wani abu tasha. Sai dai bai taɓa tunanin har a wajen aikinta ma tana shan abubuwan nan ba. Ɗagowa yay idanunsa har sun kaɗa da ɓacin rai. “Kozan iya shiga office ɗin nata?”. Ya tambayi security ɗin.

“Ah eh mana mizai hana. Ai gara a je a duba mike faruwa ko?”.

Miƙewa kawai yay, security ɗin yay masa jagora har office ɗin. Sun samu sakatariyarta tsaye jikin ƙofar tana knocking da faman kiran “Aunty! Aunty Please ki buɗe ko kiyi magana dan ALLAH.”

“Kinga ƙyaleta idan da key bani”. Ya faɗa cikin dakewa. Cikar kamala da kwarjininsa yasa Zainab jin bazata iya musa masa ba. Duk da kuwa yau ne karo na farko data taɓa ganinsa anan ɗin. Sai kuma ganin harda security ya ƙara mata ƙarfin gwiwa. Muryarta a sanyaye ta ce, “Sai dai na duba ko zanga extra keys dan ta shiga da key ɗin ciki”. Kansa kawai ya jinjina mata, ta koma wajen table ɗinta domin bincikawa. Shi kuma ya jingina da bango tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa. Kusan mintina huɗu tana ta binci-bincike har dai ta samo keys ɗin da ƙyar. Gabansa tazo ta miƙa masa cikin girmamawa.

“Thanks” yace a hankali yana amsa. Koda ya buɗe ƙofar bai yarda ita da security ɗin sun biyosa ba sai da ya leƙa. Saurin rumtse idanunsa yay tare da yo baya, cikin ɗan furzar da huci ya gyara yanayin fuskarsa yanda zasu fahimcesa. “Inaga bata da lafiya ne, kun san halin ogar taku kuma maybe bata buƙatar kowa ya sani shiyyasa taya rufe kanta a ciki, ku barni da ita kar ku samu rabon faɗa kuma”. A yanda yay maganar dole ne ka gamsu, dan haka security ɗin yay murmushi dan kuwa masifar Mawaddat kowa ya santa, idan sukai sanya wajen buɗe mata gate kota saka wani aikin kai mata wasa sai ta tsefeka tas. Balle ma Zainab da tafi kowa sanin wacece uwargijiyar tata. Sallama security yay ya fita, Zainab kuma ta koma mazauninta ta zauna duk da ya kamata ace ta tashi, amma dai tafi yarda taga sai Mawaddat ta fito lafiya sannan. Ƙofar ya sake turawa ya shiga ya maida ya rufe tare da jingina jikinta kansa a ƙasa bai yarda ya sake kalloba. Kamata yay ya kira Zainab, sai dai baya son ta ganta a yanayin. Har yanzu tana kwance a tsakkiyar sofas ɗin da aka shirya dan zama bayan ta zamanta da wanda ke a gaban table ɗin nata. Ta ture Centre table ɗin tsakkiyar kujerun tana kan carpet ɗin gashinta yaɗan barbaje. Har yanzu idanunta na kallon p.o.p ɗin office ɗin, hira take da mamanta da idanunta ke gani ko nace ƙwaya take siffanta mata. Hawaye share-share a fuskarta ga murmushi. Tsaiwarsa gurin shiru na wasu sakanni ya sashi ɗan jin soki burutsunta. A karo na farko ya ɗaga kansa ya dubi p.o.p ɗin shima jin tana faɗin, “Mammah karki sake tafiya ki barni kinji. Kiyi zamanki muyi hirarmu, inma bazaki min magana ba ni zan na miki murmushinki ya wadatar dani. Kar kiyi kuka a kaina bana son ganin hawayenki ki bari Please ki bari…” ta faɗa cikin wani irin sanyin murya sai kuma ta fashe da kuka. Da farko bai ɗauki surutun nata komai ba sai shirme irin na masu shaye-shaye, sai dai Mammah da take ambata ya tsaya masa a zuciya. Ganin yana ɓata lokaci ya sashi furzar da ƙaramin iska tare da cigaba da takawa cikin office ɗin, ƴan dube-dube yake yi duk da baiyi tsammanin zai iya dacewa da abinda yake neman ba. Dama baiyi tsammanin ganin ba ai. Fita yay inda sakatariyarta ta take, tana zaune dai har yanzu sai dai yanzu da waya a hannunta, dan tunda ta turama Uncle Yousuf text take tsammanin shigowar kiransa amma shiru kake ji.

“Ko zamu samu Hijjab?”.

Firgigit ta dawo a hayyacinta dan jin saukar deep voice ɗin sa a bazata cikin kunnen ta. Sake maimaita mata yay ganin kamar bata jisa ba. Kanta ta gyaɗa masa da sauri tana nufar inda ta jiye hijjab ɗin sallarta ta ɗakko masa. Amsa yay kawai ya koma ciki. Yana ɗan sauke ajiyar zuciya, yanzun ma bai yarda ya kalletan ba ya warware hijjab ɗin tare da kaiwa duƙe gabanta. Karan farko na rayuwarsa ya ambaci “Mawaddat!” cikin ɗacin murya da tausasawa, sai dai acan ƙasan makoshinsa zaka iya fahimtar jin zafinta. Ƙarfin muryarsa da yanda yay kiran nata ya saka shigar sautin cikin kunnenta a bazata. Kamar wadda aka farkar a cikin barci ta juyo idanunta da suka sake girma da ɗan juyewa kansa. “What!” ta faɗa a zabure tana tashi zaune sosai. Sai kuma ta kalla sama da ɗaga hanunta. “Mammah ki jirani dan ALLAH”.

Kallonta yay jin abinda ta sake faɗa, hakan sai yay dai-dai da yanda ta zuba masa juyayyun idanunta fuska a yatsine tana wani ƙwaɓeta ta ce, “Who are you? Miya kawo ka nan?”.

Tsaki ya saki tare da ɗauke idanunsa ya yafa mata hijjab ɗin a jiki. Hannun da takai cikin yar kokawar ture hijjab ɗin ya buge. Da sauri ta janye tare da faɗin “ouch!” saboda zafin da taji. Baibi takanta ba ya ƙarasa saka mata hijjab ɗin batare da ya yarda ya taɓa mata jiki ba. Wata muguwar harara ta watsa masa ta ƙara kai hannu zata cire hijjab ɗin ya daka mata tsawa.

“Idan kika cireshi na rantse sai na canja ma fuskarki kammani da mari!!”

Sosai tsawar tasa ta ratsata. Gaba ɗaya sai ya sake juye mata a cikin idanu kamar wani bahagon zaki. Kuka ta saki da duban p.o.p ɗin ta ce, “Mammah kinga yana min ihu ko. Bana son shi yanada girman kai”.

Bakinsa kawai ya taɓe da cigaba da tattare kayayyakinta data barbaza a office ɗin waje guda, a zuciyarsa yana faɗin (aike naki kan ƙarami ne). A dai-dai nan aka turo ƙofar aka shigo. Juyowa yay da ɗan sauri dan a tunaninsa sakatariyarta ce, amma sai ya ga Uncle Yousuf ne. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan gaskiya yaji daɗin zuwan nasa. Dama sai faman ƙullawa da kwancewar ta yanda zai fita da ita a office ɗin yake. “Barka da yamma Alhaji”.

Murmushin ƙarfin hali Uncle Yousuf ya saki yana jinjina kasa, sai kuma ya maida dubansa ga Lulu da har yanzu ke sambatunta irin na rashin kasancewa a hayyaci. Idanu ya ƙura mata da kamar wanda ya zurfafa kansa a tunani, maganar Smart ta sakashi yin firgigit. Cikin ƙoƙarin shanye abu mai ƙona zuciya ya sake dubansa da murmushi. “Aliyu ya jikin naka? Kai da nace yau karkazo aiki shine kuma ka fito?”.

“Naji sauƙi ai Alhaji. Kasan zaman gidan isar mutum yake yi shiyyasa na fito. Nafito ɗin kuma na rasa ina zan nufa shine kawai nace Bara na duba ko bata tashi aiki ba sai na maidata..”

Uncle Yousuf da ke jin zuciyarsa babu daɗi ya kai zaune yana mai tallafo haɓarsa. Kusa da shi ya nunama Smart da ke kallonsa. Babu musu ya zauna sai dai a kujerar gefensa. Ya fahimci irin damuwar da Uncle Yousuf ɗin ya shiga, dan haka sai shi ya ɗan sassauta tasa cikin furzar da ƙaramin huci. “Alhaji damuwa bata zama maganin matsala ba, sai dai ta zama sanadin ƙirƙirar sabuwar matsala wa rayuwa…..”

“Hakane Aliyu. Amma ka duba fa kenan har a wajen aikinta ma tana sha? Hakan kuma na nufin duniya ta jima da sanin halin da Mawaddat ke a ciki amma mu bamu sani ba”.

“Banajin hakan gaskiya Alhaji”.

Idanu kawai Uncle Yousuf ya tsira masa, dan haka office ɗin yay shiru sai surutan Lulu kawai ke tashi cikin sambatun maye. Kiran da ya shigo a wayar Uncle Yousuf ɗin ce ta katse shirun nasu. Kamar zai share sai kuma dai ya cirota a aljihu. Daddy ne, yasan jiransa ya keyi dan sun zauna zasuyi magana ne Zainab ta tura masa saƙo shine ya taho hankali tashe. Wayar ya ɗaga tare da kaiwa kunnensa. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Yaya!”.

Daddy da tun fitowar ƙanin nasa ya kasa zaune ya kasa tsaye ya ce, “Yousef miya faru da ita?”.

“Babu komai yaya ka kwantar da hankalinka dan ALLAH. Dan nama tadda Aliyu har yazo ma shi….”

“Waye Aliyu? Ko drivern ta?”.

“Eh yaya.”

“Ka faɗa min gaskiya Yousuf abubuwan tasha ko?”.

“Yaya dan ALLAH k…”

“Yousef please”.

Daddy ya faɗa cikin tare numfashin Uncle Yousuf ɗin. Cikin sakin ajiyar zuciya ya ce, “Hakane. Amma dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, gamu nan tahowa gidan ma”. Daga haka ya yanke wayar. Shi ya ɗauki Lulu kamar ranar, Smart kuma ya fita da kayayyakinta a hannu. Zainab da gaba ɗaya hankalinta ya tashi da ganin yanda aka fiddo auntyn tata ya kalla. “Ki rufe office ɗin ki sameni waje a maidaki gida”. Daga haka yay ficewarsa.

Kamar yanda ya bata umarni hakan tayi, lokacin data fito har Uncle Yousuf da ya saka Mawaddat a motarsa yana ƙoƙarin ficewa a gidan. Yayinda smart ke tsaye yana jiranta. Batare da yi mata magana ba ya shiga motar, itama sai ta buɗe ta shiga kusa da shi. Har gida ya kaita abisa kwatancen da tai masa, godiya taita masa cikin girmamawa, karan farko yay mata guntun murmushi cikin jinjina kai ya ja motar ya wuce……..✍️

 

 

 

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

 

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

 

FURAR DANKO

Billyn Abdul

 

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

 

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

 

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

 

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

 

Pay at👇

 

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇

 

09032345899

 

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070

 

 

VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

 

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

 

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

 

Zafafa🫶🔥

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments