Breaking News

Furar Danko 61

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

 


 

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

 

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

 

 

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣

 

 

……..Ƙarfe kusan tara Lulu ta tashi da ƙyar a dalilin kaɗawar alerm ɗin ƙaramin agogon da ke a side drawer ɗinta da ya gallabeta tun takwas. Amma nauyin da jikinta yay mata yasata kasa kasheshi ko ta tashi har zuwa yanzu da ya sake buga taran. Ƙaramin tsaki taja da ɗan kai hannu tana lalube, sai dai sam babu ma alamarsa kusa da itan. Tamkar wadda aka ƙwalama kira sai kuma ta miƙe zumbur, yau fa ya kamata ta shigar da case ɗin mijin matar can court, dama tai alƙawarin sai ya kwana bakwai a police station su Shu’aibu sunci mata ubansa gwargwadon iko sannan, yau kuma kwana bakwan cif. Wayoyinta ta shiga nema, sai kuma ta tuna sunafa hannun Uncle You nan kuma gidan da aka kawota jiya ne. Ƙaramin tsoki taja da dafe kanta da yay mata matuƙar nauyi, dole ta sakko a gadon cikin ɗan tangaɗi kaɗan sai dai bana mayen bane na nauyin jikine dan abinda tasha ɗin sun saketa sai abinda ba’a rasa ba. Bayi ta shiga ta tsaya ƙarƙashin shower batare data cire komai ba daga jikinta ruwa ya fara sauka mata a haka. Ajiyar zuciya ta dinga saki a jajjere, sai da ruwan yay mata sharkaf ta gamsu ta ƙara komawa garau da take buƙata sannan ta fara zame kayan jikin nata ta fara wanka. Tana kammalawa ta jefa kayan a injin wanki dan komai na ƴar gata an ajiye mata shi, sai da ta gamsu sun wankun sannan ta ciresu ta maida indai zai busar. Sai ga kaya ras ta fitar sannan ta fito. Tana buƙatar waya domin kiran Zainab sakatariyarta da kuma su Shu’aibu ɗan sanda, dan haka ta fito da ga bedroom ɗin nata daga ita sai rigar wanka da towel ɗin data naɗe gashinta da take son ruwan data jiƙashi da shi ya naɗe. Sautin muryarsa yana raira karatun Alkur’ani cikin suratul An’aam daya karaɗe corridor ɗin ya sata gane yana a ɗakin dake kusa da wanda take. Sai da ta sake gyara yanayinta dan karma ya kawo mata wani raini sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga kanta tsaye ba batun neman izini, sallama ma sai da ta gama shiga tayita ciki-ciki. Ƙamshin shower gal dana haɗin turarrukan wankan da masu gyara mata jiki suka shirya mata na musamman ne ya fargar da shi shigowar ta, dan cikin abinda baifi sakans ba ɗakin ya gauraye da masifaffen ƙamshinta. Kasancewar yazo inda ya kamata ya tsaya ya sashi rufe Alkur’ani ya ɗago ya kalleta. Kanta ta ɗauke daga kallon da take masa, shima sai ya janye nasa idanun yana ajiye Alkur’anin. Cikin izzar nan tata da gadara ta ce, “Ɗan bani aron phone ɗinka na kira Uncle You ya bada nawa a kawo min”.

“Kinyi salla?”.

Ya faɗa maimakon amsa mata abinda tazo nema. A yamutse tana balla masa harara ta ce, “Ina ruwanka. Ka bani aron waya idan zaka bani”.

“Idan kina buƙatar waya kije kiyi salla. Shin ke bakiji kunya ba a wannan shekarun naki ace sai an tuna miki abinda zai kusantaki da UBANGIJINKI, banbanci kafiri da musulmi shine sallah, duk wanda yabar salla baida maraba da kafiri, sannan duk wanda yabar salla zai iya aikata kowanne irin mummunan aiki, salla itace abinda za’a fara bincika mana a cikin ayyukanmu ranar sakamako, yin salla akan lokaci na ma masifu katanga da samunmu. Salla na ƙaramana kwarjini a idon al’umma da cikar kamala. Taya mai barinta zai samu waɗan can tagomashin dana lissafa wanda kaɗanne da ga cikin nasarorin da mai salla ke samu. Yinta zai baki damar yima mahaifiyarki addu’a da nemar mata rahamar UBANGIJI, sai ruhinta ya kasance cikin sallama tai alfahari da haihuwarki da jin bata bar bayan a banza ba. Mawaddat babu ruwan mutuwa da yanzu kika fara rayuwa, tana ɗaukar ɗan cikin ciki ma tabar uwa, alokacin da kike jin ke kin fara rayuwa wani ma a ranar aka samar da cikinsa. Ki dawo cikin hankalinki ki koyi darasi a duniya ba sai duniya ta shirya koya miki ba. Dan ita ɗayan biyu ce. Ko ka koya a yayin da take koyar da waninka, kota koyar da kai a lokacin da guri ya ƙure maka. Zaɓi ya rage naki”.

Da ga haka ya tura mata wayar ya miƙe yay wucewarsa toilet. Harara kawai ta bisa da shi ƙasa-ƙasa. Dan gaba ɗaya jitai kamar an danne mata baki a sanda yake maganar. Bakin ta taɓe da matsawa ta ɗauka wayar tasa ta fice abinta. Sai dai tana komawa ɗakin nata ta zauna a bakin gado da nufin kiran Uncle Yousuf hakan ya gagara. Maganganunsa ne suka shiga dawo mata, musamman akan yima mahaifiyarta addu’a kuma zatai farin ciki da ita daya faɗa, samun kanta tai da kiƙewa zumbur ta nufi toilet, babu jimawa sai gata ta fito da alamar alwalar tayi. Wardrobe ta buɗe ta ciro abaya ta saka tare da naɗa gyalenta a kanta ta kabbara sallar.. dai dai nan ya shigo ɗakin shima, dan haka kawai zuciyarsa ta kasa nutsuwa harya fara cire kaya zai yi wanka ya fasa ya biyota dan yaga zatayi sallar. Karo na farko zuciyarsa ta tsarga ganin yanda take salla babu wani bin ƙa’idojinta yanda ya kamata. (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa da ɗunbin takaici. Ashe dole abubuwa suke rikicema yarinyar nan dan babu nutsuwa ko nagarta a cikin al’amarin ibadarta. Tabbas rashin tsaida ibada tamkar wani dafin allura ce a jikin ɗan adam mai karya masa garkuwar nagarta da ɗaurasa akan laifuka. Ashe al’amarin nata ya gawurta da yawa har haka. Zafin rai da takaicin iyayenta ya sake mamaye masa zuciya, domin fa in har ɓera da sata to a bincika itama daddawa nada wari. Shin mi mahaifinta da matar babanta dama Uncle Yousuf keyi haka har balagaggiyar yarinya mai shekaru da yake da tabbacin sun haura ashiri amma bata iya salla ba? Amma a ilimin boko da anyi magana zata iya bugar ƙirji ta kira kanta mai ilimi. Oh ALLAH a wane irin zamani muka tsinta kammu da tarbiyya ke neman kufcewa iyaye saboda soyayyar ƴaƴansu?. Wannan al’amari ya tayar masa da hankali matuƙa, ya tuna lokacin suna yara, idan lokacin salla yay sukaƙi barin wasa suje suyi sai dai kaji saukar tazbahar Ammah a jikinka kawai. Idan ko bakayi ba ranar ko kulaka batayi sai tace ita bazatai magana da wanda yafi son shiga wuta ba. Amma yau sai ga shi wadda ke amsa sunan matarsa bata iya salla ba. A hankali ya jingina da ƙofar yana mai harɗe hannayensa a ƙirji da lumshe idanunsa abubuwa masu yawa na masa kaikawo a zuciya, lallai akwai aiki, dan yaƙine babba garesa akan yarinyar nan, shi duk ma sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi..

A ɓangaren Lulu tunda ta idar idanunta ya sauka akan Smart kamar wani mayan ƙarfe. Sai da taji gabanta ya faɗi musamman da abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata a rai, amma sai ta basar tama miƙe tana naɗe abin sallar. Sam Smart shi bai san da ta idar ba. Dan idanunsa a lumshe suke ya afka duniyar tunani. Samun kanta tai da tsura masa idanu, yayinda kalaman Nadiya na waccan ranar na dawo mata a zuciya. Kamar wadda aka tsawatarwa sai kuma ta ɗauke idanunta cikin yamutsa fuska tana jan tsaki. Duk da bai san mi take jama tsakin ba saukarsa a tsakkiyar kansa ya sashi ɗagowa cikin nutsuwar nan tasa ya buɗe idanunsa a kanta.

“Gadin na miye?”.

Ta faɗa cikin ƙarfin hali dan ba ƙaramin tasiri idanunsa keyi a duk sassan jikinta ba. Maimakon bata amsa ɗauke kansa yay, hakan kuma sai ya tunzura mata zuciya. Ta buɗe baki zata fara masifar tata yay gyaran murya kaɗan, kamar zata share sai kuma dai ta jiyo ta ɗan kallesa cikin harara tana ƙoƙarin warware gashinta. Ido suka haɗa ta mirrorn ta balla masa harara ta ɗauke nata. Shima ɗauke nasan yay ya maida kan gashinta mai tsaho da alamun samun gyara ya sashi yin wani ƙyau na musamman da sheƙi duk da a jiƙe yake a yanzu. Knocking gate da ake da ɗan ƙarfi ya sashi haɗiye maganar da yay yinƙurin yi. Agogon dake a ɗakin ya kalla sai kuma ya buɗe ƙofar ya fita. Ƙaramin tsaki yaja lokacin da ya fito harabar gidan sosai yaji bugun ƙofar babu ƙaƙƙautawa, sai da yasa key ya buɗe sannan ya zare sakatan. Da sauri Huwaila taja baya tana sissine kanta. Sai da ya gama kallonta ita da kwandon hannunta sannan ya matsa mata fuskarsa na ƙara tsukewa, dai-dai nan napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin, dakatawa yay da ga yunƙurin rufewar da yake saboda hango Asma’u na fitowa a Napep ɗin. Fuskarta da murmushi ta ƙaraso garesa tana faɗin, “Yaya ina kwana”.

“Lafiya Lau” ya amsa mata idonsa akan kayan hannunta, itama kallon hannun tayi har sannan fuskarta da murmushi ta ce, “Yaya abincinku n…..” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda hango Huwaila da tai a ƙofar shiga falon ɗauke da kayan abinci itama, da sauri ta kalli Yayan nata kamar zatai magana dan ita bata san da zuwan Huwaila ba. Ganin yay gaba abinsa ya sata bin bayansa batare data faɗi abinda ke bakin nata ba. Kallon juna sukai ita da Huwaila da ke hararta ta ƙasan ido, Asma’u ta ɗan girgiza kanta cikin basarwa ta ce, “Adda ai ban san nan zakizo ba da mun taho tare”.

“Zaku shigo ne ko zaku tsaya surutu”. Smart dake kaiwa zaune cikin kujera ya faɗa. Shiga sukai da sauri, kowa ya ajiye kayan hannunsa suka gaishesa. Amsa musu yay da kulawa, sai kuma Asma’u cikin zumuɗi ta ɗora da faɗin, “Yaya ina auntyn?”. Ɗan jimm yay sai kuma ya nuna mata hanyar bedroom ɗin da Lulu ke ciki.

“Yaya dan ALLAH barci takeyi?”.

Kansa ya sake girgiza mata nan ma. Miƙewa tai, kafin ma yace wani abu harta kusa zuwa ɗakin, ƙoƙarin dakatar da ita yay dan shi dai yasan wacece matar tasa, kuma baya buƙatar ƴan uwansa su fara sanin wacece itan su tun a yanzun, sallamar da Asma’u tai da ɗan knocking ƙofar ya katse masa tunani.

“Asma’u!”.

Ya kira sunanta kamar a kasalance, amsawa tai da “Na’am Yaya”. Tana jiyowa………✍️

 

 

(😂Lulu karki bamu kunya dan ALLAH)

 

 

 

 

 

 

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

 

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

 

FURAR DANKO

Billyn Abdul

 

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

 

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

 

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

 

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

 

Pay at👇

 

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇

 

09032345899

 

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070

 

 

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

 

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

 

Zafafa🫶🔥

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments