Breaking News

Furar Danko 64

 

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

 

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

 

 

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣

 

 

 

……..Ƙarshen kuma firgita Lulu ta gama kaiwa, sai dai kafin tai wani yunƙuri a matuƙar bazata taji saukar lips ɗinsa masu sanyi akan tausasan nata masu sheƙi da ƙamshin lipgloss ɗin data ɗan saka, cin abinci ma yasa duk ta shanye rabi. Iyakar rikicewa da firgici Lulu ta shiga, gashi ya mata ritsawar da ko iya motsa kanta ta gagara yi balle tace zata iya ƙwacewa. Shi kansa da yayi ne domin kawai tabbatar mata ba drama ɗin data ambata ɗin bane jiyay gaba ɗaya jininsa na yamutsawa, dan karo na farko kenan a rayuwarsa da haka ta faru tsakaninsa da mace. Da ƙyar ya iya juriyar shafe minti guda sannan ya sake mata lips amma bai matsa da ga jikin nata ba, sai ma magana da ya fara cikin kunnenta muryarsa a wani irin sarƙe duk da jarumtar son hana hakan bayyana da yake nunawa. “Waya gaya miki baƙo na kwana gidan sabbin aure ne? Ai sai ya jiyoma kansa abinda zai hanashi barci, bar yarinyar mutane ta tafi gidansu girmanta bai kai ba. Sannan ki rage ɗaukar kanki sama can ƙololuwa, dan a wannan fadar Aliyu Hydar shine ZAKIN KI. Fassara SARKIN KI Mawaddatan’warahmah Isma’il Ibrahim Jiƙamshi”. Ya ƙare maganar da ɗanja baya yana wani kashe mata ido ɗaya ya bar wajen gaba ɗaya.. Suɓul numfashin Lulu ya nema barin jikinta. Takaici ne, baƙin ciki ne. Mamaki ne bata sani ba. Abinda kawai ta sani wannan itace rana mafi abin takaici da koma baya da tazo mata a tarihinta. Bakin illiterate driver ɗinta ne cikin nata, ya zuba mata yawunsa ta sha fa a cikin cikinta. Wayyo ALLAH shike nan tata ta gama ƙarewa….

Kamar Smart ya san mi take tunani, dai-dai yana hawa gadon ya wani lashi lips ɗinsa da faɗin, “1-0 kenan, amma fa yawunki akwai daɗi Madam. Ina fatan nawa ma akwai ɗanɗano na musamman irin wanda iyali zasu so. Dama na faɗa miki jahilin baƙauyen nan fa ɗan takife ne, ki guji masa gatsali dan bajin magana yake ba. kije ki sallami yarinyar mutane inba haka ba na tashi na ganta a gidan nan ita ranta zai ɓaci, ke kuma zakisha yawun baƙauyenki”.

Harara ta watso masa da faɗin, “Shash….” bata ƙarasa ba ya yunƙura zai tashi. Da gudu ta fice kuwa tana nunashi da yatsa da faɗin, “Wlhy sai na koya maka hankali. Maye!”.

Komawa yay ya kwanta yana mai lumshe idanunsa da sakin ƙaramar dariya. A hankali ya furta, “Na samu promotion da ga illiterate velleger zuwa MAYE kenan”. Sai kuma ya kai hannunsa saman lips ɗin nasa ya shafa yana jin wani abu na masa yawo a cikin jini har yanzu. “Ko mima ya kai ni, ni Aliyu Madam ce fa”. Ya sake faɗa yana wani ɓata fuska kamar gaske, sai kuma yaja filo ya ɗaura a saman face ɗin sa da sake faɗin, “ALLAH ya shiryeka Aliyu wannan abun kunyar da ka tafka fa wa ogarka”.

 

(😂😂Ɗan manni, amma ka kwana da sanin idan muka tashi ramawa sai ka raina kan ka malam🥱 Tom😏🚴).

 

 

_________★

 

 

A hankali Mommy ta jinjina kanta tare da sakin ajiyar zuciya na ɗunbin mamakin Daddy a karo na babu adadi. Kallonta ta sake maida wa garesa har yanzu yana a yanda yake zaune da tagumi hannu bibbiyu. Abincin data ajiye masa kusan tsawon awa guda har ya ƙandare shayin ko ya koma kamar ruwan sanyi. A tsakanin shekaranjiya zuwa yinin jiya yanayinsa na nuna kewar barin Lulu gidan ne kamar yanda suma duk sunji hakan a ransu, amma da ga daren jiya zuwa safiyar yau yanayin nasa sai ya ninka ko barcin kirki bata tunanin yayi, da farko tayi tunanin ko baya jin daɗin jikinsa ne. Amma koda ta tambayesa amsar da ya bata sai taji ta girmi kunnenta. Tun cikin daren take tunanin anya kuwa mijin nata kuma ɗan uwanta lafiya lau yake? Dan al’amarin nasa kuma ya fara wuce makaɗi da rawa. Ita bama ta fatan ko Yousuf yaji wannan taɓargazar tasa a wannan gaɓar dan abin kunya ne na gaske. Ajiyar zuciyar ta sake saukewa, sai kuma ta miƙe a nutsenta ta koma gefensa ta zauna. Karo na farko akan al’amurin Lulu ta fuskancesa da son tausasawa da nuna masa goyon baya ɗari bisa ɗari. Hannunsa ta kamo cikin nata tana ɗan murmushi da faɗin, “Yaya kayi haƙuri kaci abincin, ka kuma kwantar da hankalinka bari na shirya sai naje gidan na duba mana Mawaddat ɗin, duk da dai inaji a jikina yaron nan bazaiyi abinda zamuce ALLAH wadarai ba. Amma nima zuwa yanzu zuciyata tafi gamsuwa da naje na dubatan tunda babu waya a hannunta balle mu kira, tura yara kuma bazai bamu abinda muke so ba.”

A karo na farko shima Daddy ya dubi Mommy ɗin da tausasawa a akan lamarin Lulun. Murya a sanyaye ya ce, “Kina ganin baza’ace munyi ba daidai ba Kareema, kin san fa masifar Yousuf akan yaron nan daban ce, na rasa wane irin so yake masa da bai son ace yayi ba dai-dai ba. Ni kuma wlhy ina tsoron ya illatamin yarinya a banza tunda dai ba taɓa auren nan yay ba balle muce zai kamanta dattako”.

Shike maganar amma Mommy ita kejin kunyar, amma sai ta danne ta biye masa cikin sake kwantar da murya. “Na fahimceka Yaya, dan samarin nan na yanzu kam rawar kai ya musu yawa, duk da shi dai a fuska kamar nutsatstse amma ba’a yabon ɗan kuturu. Yanzu dai kaci abincin bara na canjo maka sai naje na gano ɗin ko yaya kace?”.

“Shike nan, in dai kina ganin babu matsalar kije ɗin, dan nima dai hakan zai fi sama min kwanciyar hankali. Sannan dan ALLAH ki lallaɓa Yousuf ya bata wayoyinta dan mu dinga jinta akai-akai”.

“Karka damu idan yazo anjima zan masa magana. Bari na kawo maka abincin kaci namaje na dawo da wuri kafin yazo gidan”.

Kai ya gyaɗa mata, ita kuma ta tashi ta fice idanunta na cika da ƙwallar tausayinsa. Yayinda zuciyarta ke faman kai kawon anya kuwa mijin nata yana lafiya? Dan ita dai gaskiya a wannan gaɓar ta fara jin al’amarin nasa da girma, wanan wace irin makauniyar soyayya ce? Haka fa idonsa yay masifar rufewa akan mahaifiyar yarinyar nan a lokacin tamkar wanda baya a hayyacinsa. Anya kuwa basuyi kuskuren nutsuwar fahimtar al’amarin nan ba a bai-bai tun a shekarun baya? Kuɗi kam na iya canja mutum fiye da abinda Daddy yayi a kan Mawaddat, sai dai akan ƴarsa Mawaddat kuma fa? Idan ance soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta gaba ɗaya ai abin nasa na neman wuce makaɗi da rawa kuma, sannan ko sanda ya auri Mawaddat yanada abin hannunsa, bayan auren nata ne dai ya sake bunƙasa za’ace, gaskiya tana buƙatar yin dogon nazari a wannan karon fiye da wanda sukeyi a baya game da shi. Koda ta kawo masa abincin ma lallaɓashi tai tayi sai gashi yaci, ta sake lallaɓashi yay wanka ya kwanta dan yau kam babu alamar zaije office ma. Ita kuma ta shirya ta fice a gidan kamar gaske gidan Lulun zataje. Yo ita zata biye masa ne su zama ɗaya miya ja mata wannan abin kunyar. Gidan Uncle Yousuf tai tafiyarta, tai sa’ar samun shima yau ɗin bai fita office ba wai zai ɗan huta a gida…….

 

____________★

 

Duk yanda Lulu taso lallaɓa Asma’u ta zauna hakan bai yiwu ba, dan ita dai Asma’u tasan wanene yayan nasu. Haƙuri tai ta bama Lulu akan ai zataje ta dawo kawo musu abincin rana. Amma yanzu idan bataji maganarsa ta tafi ba ya fito zai iya zane ta. Mamakin Lulu sai ya sake ninkuwa, irin wannan tsoronsa da suke ai abin yayi yawa. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Sai tayi duk yanda zatai Asma’u ta dawo gidan nan da zama kafin cikar sati ukun da zatatai a cikinsa kodan ta tabbatar masa itama ɗin ba kanwar lasa bace. Da ga haka tabarta ta wuce. Kasancewar gidan shiru ita kuma bata son kaɗaici yana tayar mata da hankali ya sata miƙewa ta ɗan zazzagaya, duk da kasancewar gidan ƙarami sosai, dan ko sashen masu aikinsu ya fisa girma bai hana gidan birgeta ba. Balle ma an sake ƙawatashi da kayan da aka zuba mata, wanda har mamakin sakasu tayi ita da zatai zaman sati uku. Sai dai batace komai ba akan hakan. Ta ɗan jima a waje tana shan iska sai kuma ta koma ciki, bedroom ɗin ta, a ranta tana raya gara ta ɗan sha abubuwanta ta kwanta itama tai barci, sai dai me koda ta duba babu ledar maganin ma gaba ɗaya. Shiru tai alamar tunanin ko ta ajiyesu a wani waje ne, kai ina a bedside drawer ta barsu. Da sauri ta buɗe drawer ɗinsa amma babu alamar su, maganganunsa na ɗazun bayan zuwan su Asma’u ne suka shiga dawo mata, to ko ya fahimci abinda tai jiyan. “Wayyo ni” ta faɗa tana dafe kanta. Dama fa tayi matuƙar mamakin jin ya ɗakko topic ɗin nan, sai dai kafin tai masa tambayar da tai niyya ya fita ya barta. “Mutum nan maye ne, ya akai yay saurin ganoni” ta sake faɗa tana faɗawa saman gadon da jan tsaki. Bataso haka ba gaskiya, dan tana ganin ta samu hanya mai sauƙi da zata dinga samun abinda take so cikin sauƙi tana wasa da hankalinsa. “Mugun kai fal gadara da ƙauyanci sai shegen wayo kamar ɗan dila” ta sake faɗa cikin nuna takaici. Da ga haka tai shiru lamo abinda ya farun yanzu babu jimawa a tsakaninsu na sake dawo mata. Tsaki taja mai ƙarfin masifa ta sake juya kwanciyarta dan sam bata son tunawa, dan duk ƙaƙarin aman data dinga yi bayan barowarta ɗakin nasa batai ba, sai ɓigewa tai da yin brush kusan sau huɗu amma hakan bai hanata cigaba da jin saukar lips ɗin nasa a nata ba har yanzu. Tsaki taja tana tunzura bakin gaba. Da ga haka ALLAH ya taimakata barci ya kwasheta mai ƙarfi. Dan koba komai akwai gajiya da ƙarancin barcin na kwana biyu a tattare da ita………✍️

 

 

 

 

 

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

 

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

 

FURAR DANKO

Billyn Abdul

 

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

 

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

 

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

 

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

 

Pay at👇

 

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇

 

09032345899

 

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070

 

 

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

 

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

 

Zafafa🫶🔥

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments