Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko 71

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣1️⃣


……..Tana fitowa ɗauke da dankali ya fuske kamar bashi ba ya cigaba da game ɗin yana satar kallonta ta gefen ido. Ganin ta fara firar dankalin ya sashi ajiye wayar tasa a table ɗin ya miƙe, gefenta ya tsaya kaɗan, ya ɗauka wuƙar data ajiye saman chopped board ya

fara yanka wanda ta fere, bata kulashi ba, ba kuma tayi magana ba ta cigaba da ferewa tana ajiye masa. Shima sai baiyi magana ba ya cigaba da yankawa, idan ya ɗan tara sai ya zuba a cikin ruwan data ajiye a bowl. A haka har suka kammala, kasancewar ta rigashi gamawa ita ta fara barin wajen ta ɗakko preyn fan ta dawo inda yaken ta zuba ruwan sabulu kaɗan ta wankesa da soso ta ɗaureye duk yana satar kallonta. Komawa tai gaban gas ta kunna ta ɗora sannan ta zuba man data ɗakko. Dai-dai nan ya kammala, sai ya wanke mata dankalin ya sake masa ruwa ya tace sannan ya juyo yana miƙa mata robar. Sai da ta hararesa ta amsa, shi dai ya gimtse dariyarsa da ƙyar ya juya yana ɗauraye wuƙa da sauran abinda sukai amfanin. Lulu kam koda albasanta ya soyu ta zuba dankalin sai ta nufi frizzier, kifi tai ƙoƙarin cira sai dai sanyin da ya ratsa mata hannu ya sata faɗin, “Ouchh!!”

Read More Here

Post a Comment for "Furar Danko 71"