Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 13

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣

 

……..Cikin rufewar ido da nuna ɓacin rai Abba ya tsawatar musu. Ganin Umma na gunguni ya ce, “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ta bar min gida a wannan daren. Kuna son maidani wani shasha ne? Kuje an ɓoye muku tafiyar Aliyun kuyi duk abinda kuke jin zaku iya yi dan ALLAH marasa mutunci kawai”. Da ga haka ya koma ciki fuuu ya barsu da harare-harare. Duk abinda akeyi Ammah na jiyosu amma ko leƙowa batai ba, ta kuma hana har su Asma’u leƙowa wajen. A haka aka kwana cikin ɓacin rai wannan dare. Tun kuma a daren su Umma suka bazama sauran ƴaƴansu bayani ta waya cikin nuna hassada. Haka ma ƴan anguwa da rikicin ya ɗan shiga kunnuwansu musamman maƙwafta aka fara riƙe bakin mamakin jin Aliyu ashe baya Nigeria, duk ƙaryar da su Umma keta bazawa matan anguwa cewar ya gudu Lagos saboda dangin matarsa sun ce sai ya saketa ashe ƙarya ce. A wannan dare Umma bata koma ta kwana ɗakin Abba ba, washe gari sai ga yaran gidan na ma’auri nata zuwa musamman mazan tunda safe a cikin tashin hankali. Salim babban ɗan Umma da take ji dashi da fariyyar yafi kowa kuɗi a gidan shine tsageran tunkarar Abbah da maganganun rashin kunya wai yana nuna musu banbanci akan Aliyu. Sai da Abba ya gama saurarensa tsaf sannan ya zageshi ciki da bai da faɗi masa ashe sai yau ne suka san matsayin Aliyu da mahaifiyarsa a wajensa. To bari ya ƙara tabbatar musu da cewar Ammah ta daban ce a zuciyarsa, dan itace first love ɗin sa. Ta auresa a sanda baida komai, yayinda mahaifinta ya tallafi rayuwarsa batare da ƙyama ba a matsayinsa na almajiri, da ya nuna yana son ƴarsa ko sau ɗaya bai nuna ta fisa ba ya aura masa. Tun suna zama a gidan haya ɗaki ɗaya har ALLAH ya horo masa gidan kansa. Ammah tasha rufama rayuwarsa asiri da danginsa da abunta bata taɓa nuna masa isgili da hakan ba koda a cikin wasa. Tayi haƙuri da shi ita da iyayenta akan rashin haihuwa, har sai da uwarsa ta shigo da ƙarfin tuwo ta haifesa shi da ƙaninsa Sadiq kafin ALLAH ya bata cikin Bilkisu. Amma bata taɓa nuna baƙin cikinta ko hassada akan wata tazo a bayanta ta haihu ba. Uwar tasu da suke gani matsayin ƴar uwarsa shi bai taɓa jin sonta ba, da biye-biyen dangi ta kama ƙafa aka tilastashi aurenta… Wannan magana ta Abba taima Umma zafi matuƙa, har ta kaita da fashewa da kukan wai Abba naci mata mutunci a gaban kishiyoyi. Duk da Mama da ita aka fara fitinar sai gashi ta koma yima Umma dariyar ƙeta. Dan ba ƙaramin wankin babban bargo Abba yay mata ba a ranar. Har sai da ta kaita da kuka da hawaye. Da ga ƙarshe ta shige ɗaki ita da ɗiyanta suna zagin Ammah da jawa Smart mugayen addu’oin rashin nasara badan ya musu laifin komai ba sai hassada da uwarsu ta cusa musu kawai a ransu matsayinsa da ɗan uba garesu. Ɓacin rai ya saka Ammah tattara kowa a gidan ta watsar, inda cikin hikima ta nusar da aunty Amarya akan kada ta sake biyema su Ummar dan ALLAH. Tako ji maganarta dan itama ta kame kanta dana ƴaƴanta waje guda kamar yanda Ammah tayi.

Tun a ranar Umma tai kiran Hajiya Naqiba ta sanar mata komai cikin ɓacin rai. Ran aminiyar cin mushen nata ya ɓaci itama. Inda ta balbale Umma da faɗan miyasa ta kasa riƙe kanta ne ta fito tai magana haka har miji na mata tonon silili a tsakiyar ƴaƴa da kishiyoyi maƙwafta na saurare. Cikin damuwa da hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Rainane ya ɓaci wlhy Hajiya Naqiba. Kiga wahala da kashe kuɗin da nai akan yaron nan amma sai da ya tafi wannan shegiyar tamaular da na dutse ya tabbatar min itace silar arziƙinsa da bama gidanmu ba hatta ƴan anguwa nan sai ya riƙe da dukiyarsa. Wane irin koma baya ne ya sameni da har haka zata kasance. Wai yaushe ma ƙullin malam Na-zuru ya kwance akan yaron nan?. Haka fa zancen aurensa sai ji kawai mukayi, yanzu dan cin amana da makircin wannan shegiyar matar dake wani sim-sim kamar ta ALLAH za’ace wai yana Turai……”
Ƙaramar dariyar data katse Umma Hajiya Naqiba tayi, sai kuma tai saurin faɗin, “Yi haƙuri wlhy kece kika ban dariya da kikace sim-sim. Bayan kinsan Hafsatu ba sim-sim bace ba kawai dai tana kwasar ƙurarku ne ta watsar. Amma matar da in ta tashi muku wankin babban bargo sai kun kasa sukuni kike jinginawa da sim-sim, kawai dai shegen girman kai ne da ita kamar yanda ɗan nata ya gado saboda taga ta fiku komai. Ubanta mai arziƙi, tanada ƙyau, gata da ilimi kamar zai kasheta duk da ma bata son nunawa…..”
“To wai ni ban gane ba, yabonta kike ko minene?”.
“A’a rufamin asiri, wane yabo zanma kishiya nikuwa. Kinga mubar zancen tunda kin gagara fahimtata. Yanzu dai bamuga ta zamaba kenan. Dan na fahimci makircin da muka ƙullo a gidan Garko ba dukane yay tasiri ba ko kuwa yaya miya faru?”.
“Dan tasiri fa yayi tasiri, tunda gashi har sun ƙwace ɗiyarsu daga hannunsa. Abinda dai zamuyi shine shima fa makircin sai an haɗa mishi da ƙulli….”
“Ƙulli wane iri? bayan wanda mukayi”. Ummah ta katseta da sauri. Ɗan jimmm Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai kuma fa haka ne, to kodai tsohuwar nan bata bama yarinyar nan rubutun nan ba ne? To aiko da sakel, dan dolene kiyi duk yanda zakiyi a satin nan mu shiga wajen Malam Na-zuru. Dan ba’a bori da sanyin jiki, dolene mu sake tashi tsaye akan wannan ɗan iskan yaron kuwa.”
“A yanzu kam da ya hau sama bana jin zai bar wata fita a gidan, sai dai ki taimaka min kije zan kirashi ta waya mu fara magana kafin kije”.
“Shike nan hakan ma yayi kuma dabara ce. Dan ko wani abu ya biyo baya ma baza’a zargeki ba kamar wancan sai dai suyita tunani cikin abokan tamaular tashi ne”.
Haka suka cigaba da tattauna mugayen ƙudirinsu akan Smart da Ammah iri-iri kamar basa tuna mutuwa mai gaggawa da kan iya ziyartar bawa a kowane lokaci a kowane irin yanayi mala’ikan mutuwa shi mai cika umarnin UBANGIJI ne…….

(ALLAH ka gafarta mana ka tsarkake mana zukatanmu, ka hanamu damar saɓa maka balle ta kaimu ga shirka ko cutar da wani mun akan abinda bazamu taɓa iya sakawa ko hanawa ba.😭🙏)

*_CANADA_*

Dada ta iso ƙasar Canada kamar yanda taima Dr Olivia alƙawari, sai dai a ranar babu damar ganinta dan bata duty kamar yanda ta sanar mata. Kai tsaye gida ta nufa inda ta samu tarba a wajen Lulu ta musamman. Zuciyarta ta mata sanyi ganin yanda jikar tata ta saki jikinta a yau ba kamar yanda suka rabu ba. Sai dai duk motsin Lulun idonta na’a kan cikinta ne, amma batace komai ba dan Alh. Sulaiman yace mata kartace ma Lulun komai har sai ya iso. Tsaf Lulu na lure da ita amma ta basar sai ma tambayoyi data shiga jero mata akan yaya jikin Baba Garko. Dada ta amsa mata da cewar, “Ai jiki yayi sauƙi dan yanzu haka ma an sallamemu muna gida, har shi yana ma batun komawa Nigeria dan ya gaji da zaman turan”. Murmushi Lulu tayi cikin tsokana ta ce, “Dada kawai dai yana son ya gudu ne saboda tsoron kar sanyi ya ƙarasa rugurguza miki shi.” Ranƙwashi Dada ta sakai mata amma sai ta kauce da sauri tana dariya. Haka sukai hirarsu yau cikin nishaɗi har Tajuddeen ya iso. Anan ɗin ma Lulun ta basu mamaki dan bata tashi ba kamar yanda takeyi a duk sanda ya shigo gidan. Koda ya gaisheta ma sai ta amsa masa harda cewa “ykk?”. Duk da ataƙaice ta tambayi lafiyar tasa wani irin sanyi da shauƙi ne suka riskesa a lokaci guda. Ya saki wani irin lallausan murmushi da sauke ajiyar zuciya. Ƴar sakewar Lulun ya sashi kwana a gidan yau, washe gari sun wayi gari da zuwan Alh. Sulaiman tamkar a ƙasar ya kwana. Shima Lulu ta gaishesa sama-sama yana binta da wannan shegen kallon nasa ƙasa-ƙasa. Yayinda shima Tajuddeen ke ɗan binta da kallon mamaki musamman cikinta da yaga ya turo. Dukansu Lulu a hankalce take dasu, dan cikin ma ta saka rigar da zata bayyanashi ne garesu su gani da ƙyau saboda neman magana. Sai kuma wani salon yamutse-yamutse takeyi na ƙularwa ita a dole mai ciki (😂Lulu problems kenan🤣👏).

Abinda Lulun keyi ya matuƙar sosa zuciyar Alh. Sulaiman, dan kasancewarsa gogaggen mutum mai huɗɗa da jama’a a fannoni da dama ciki harda matan banza. Ya fahimci da wani manufa yarinyar ke nuna musu ciki su tabbatar yana nan. Ya cije lips ɗinsa a hankali tare da miƙewa yana kallon Dada. “Zan ɗan je na wani waje na dawo Dada. Kai Tajuddeen ka jirani dan zamuyi magana”.
A tare suka amsa masa da adawo lafiya, yayinda Lulu da ke shan kunun nata na fama ta ɗan laɓe baki hankalinta a television kamar bata san mi suke ciki ba. Har ya fice bata tanka ba kuma, sai a zuciyarta take ayyana (Kuyi duk ku gama ƙulla makircin naku ina biye daku har a gaba danan dan inaji a jikina za’a samu canjin wajen zama in har akwai abinda kuke shirin)…
Alh. Sulaiman na fita asibiti ya nufa wajen Dr Olivia, kusan a tare suka iso da ita cikin asibitin. Koda suka ƙarasa cikin Office cikin tsatstsareta da idanu ya ce, “Ya akai cikin yarinyar can bai fita ba? Bayan na baki duk abinda kika buƙata da ga gareni?”.
Ɗan murmushi baturiyar likitar tayi mai cike da ma’ananoni. Kafin ta ɗago tana kallonsa cikin ido. “Ciki kam na zubar da shi, kuma na saka amata wankin ciki da gwaji domin tabbatar da fitarsa. Sai dai in wani ta sake samu kum…..”
“You are vary stupid Olivia. Kalleni da ƙyau na miki kama da bakar fatar da zaki rainama hankali ko ki kalla wawa?. Niba likita bane, kuma banda ilimin likitanci, dan haka yaya akayi?!! Ciki bai fita ba!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace da buga tebirin ya sata ɗan zabura kaɗan. Sai kuma ta watsa masa harara ta koma cikin kujerarta ta lafe. Sosai ransa ya sake ɓaci matuƙa, zuciyarsa sai zallo take da tuƙuƙi a cikin ƙirjinsa. Ya nunata da yatsa da faɗin,……..✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

  1. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 13"