Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 2

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣

 

……..Iyayensa ya kalla cikin nutsuwar data ratsashi a yanzu najin tabbacin ina matar tasa yake, cike da girmamawa ya ce, “Abba ku tashi muje gida kawai”. Abba da tausayin ɗan nasa ya ƙara mamaye masa zuciya ya ce, “Aliy ba tafiya gida ne masalaha ba, ka bari dai a sasanta muji miye dalilin aikata hakan”. “Abba bata da wani dalili face na son zuciya. Ina son cigaba da ganin girmanta a matsayinta na uwa kamar yanda kuka tarbiyantar dani girmama kowace irin furfura, tun farko ma ita ya kamata na zarga, amma banyi hakan ba saboda shi zargi bashi da amfani. Sai dai amsa ɗaya zan bada a yanzu har gaban Abada *_BAZAN SAKI MAWADDAT BA_*. Sai dai ayi ɗayan biyu. Ko na MUTU tamun TAKABA, ko ni na mata wanka na sallaceta zuwa kabarinta. Wannan dalilan guda biyu ne kawai zasu iya raba wannan auren da izinin ALLAH!!”. Ba su Dada ba hatta Abbah da Ammah sai da Smart ya girgizasu, dan magana yake a dake, a fusace, a kuma kausashe, hatta da Ahmad dake a matsayin aboki zai iya rantsewa bai taɓa sanin Smart ɗin yanada irin wannan zafin ba. Harara Dada ta watsa masa da faɗin, “Oh burinka kenan dama ta mutu kaci gadon dukiya. Sheɗani to ALLAH ya fika, sakin Mawaddat kuwa idan bakai ta arziƙi ba zakayi ta wuya dan bazamu taɓa haɗa zuria da jinin tsiya jinin talauci ba. dama koda ka aureta ai asiri kai ma iyayen nata matsiyaci”. Murmushi Smart ya saki da taɓe bakinsa cikin halin ko’in kula da zancen Dada. Sai ma ƙoƙarin barin falon da yake yi batare da ya bata amsa ba . Alh. Sulaiman da ya kai maƙura a kan Smart ɗinne ya miƙe a fusace yana nunashi da yatsa. Sai dai kafin ma yace wani abu Smart ya nunashi shima cikin gargaɗi, “Kai! Karka kuskura shiga ramin da zai bizne rayuwarka ta har abada ya barka da gangar jiki kawai da idanun kallo. Sunanka ƙanin uwa ne ba uba ko ƙanin uba ba. Ni da kake gani na nan Sulaiman na fika fiye da abinda ka iya wlhy. Idan kace zaka saka ƙafar wasa da ni sai na gigita rayuwarka ta yanda kai a karan kanka bazaka taɓa morarta ba balle waninka. Magana ake ta mutane ba irinku riɓɓaɓu ba okay…” da ga haka Smart ya sa kai yay ficewarsa kafin ma Alh. Sulaiman da jikinsa ke rawar ɓacin rai dana firgita ya iya furta komai, da gaskiyar Lulu idanun Smart sun cancanci kowane irin suna, musamman a yau da ransa ke a ɓace dan Alh Sulaiman idanun Smart na ɗaya da ga cikin abinda ya razana shi. Fitar Smart ɗin ta saka falon zama tsit, yayinda Alh. Sulaiman ke nuna ƙofa cikin rawar baki data hannu. Daddy ya sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya a karo na farko, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, dan tunda Smart ya fara magana yake kallonsa harya fice. Uncle Yousuf ne ya tashi yabi bayan Smart, haka ma Ammah da Abbah. A gate suka sami Smart yana waya da Coach, dan a gobe ya kamata ya wuce dama, sai dai da yayi aniyar haƙura dan bazai iya tafiya wata ƙasa batare da anga Lulu ba. Amma a yanzu ya gama yanke shawarar wucewa babu fashi. Uncle Yousuf da ke kallonsa da murmushi yay masa nuni ya shiga mota inda Abba da Ammah suke, bai musa ba ya shiga. Har gida Uncle Yousuf ya kaisu, inda ya samu zama na musamman da Abba da Ammah. Shi ya lallashesu akan su kwantar da hankalinsu dan ALLAH a zubama su Dada ido aga gudun ruwansu, dan ya tabbatar sun aikata haka ne dan Alhaji Garko baya nan. Sosai Abbah ya gamsu da bayanin Uncle Yousuf ɗari bisa ɗari tare da ganin shawarar itace dai-dai. Bayan wucewar Uncle Yousuf Abba da Ammah suka sake zaunar da Smart sukai masa nasihar ya cigaba da shirinsa na tafiya kawai kamar yanda Uncle Yousuf ya faɗa da masa faɗan abinda yay ma Alh. Sulaiman da Dada. Haƙuri ya basu da alƙawarin bazai sake ba. Wannan shine sanadin tattara al’amarin Lulu ya haɗa kayansa a washe gari shi da Uncle Yousuf da Coach suka nufo ƙasar UK a London. Inda yay signing da wani ƙaramin team Queen City. Su Uncle Yousuf sun sake masa nasiha akan ya kwantar da hankalinsa kan al’amarin da kanta zata bijirema su Dada. Shi dai cikin dauriya da dakiya yake amsa musu da to kawai. Amma a cikin ransa shi kaɗai yasan irin ƙunar da yake ji da matuƙar kewar matarsa. Sai dai ƴan mazan sun ɗauki aniyar da jarumtar a wannan karon na sai ya tabbatar ma family ɗin Lulu gaba ɗaya da ita kanta shi ɗan halak ne, sannan talauci ba hauka bane ba. Duk da dai yanayin yaso taɓa shi da son maidashi sanyi-sanyi a watanni ukun daya samu kansa, sannan sam yanzu baka ganin fara’a a fuskar Smart, ya sake zama shiru-shiru a yanzu ma harda miskilanci zamu iya cewa ya ƙaro. Dan bai shiga sabgar kowa, abinda ya kawosa kawai yake yi sai bautar ALLAH. Baya zuwa ko ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al’amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta….)

Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England.

Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci….

Wannan kenan.

____________________★

*_CANADA_*

Amai take sosai cikin galabaita da fitar hayyaci, a kallo ɗaya zaka fahimci yanda duk jikinta ya saki sai huttai take da ƙyar. Cikin tausayawa mai aikin da suka taho tare tun daga Nigeria ta ke jera mata sannu. Bayan ta gama aman ruwa ta sakarma kanta daga inda take zaune tana hawaye. Haka take tun can da ma bata da juriyar ciwo, a yanzu kuma da take jin ciwon tamkar ya bambanta da duk wanda ta sabayi ne ke sake galabaitar da ita da raunana mata zuciya, har tana jin anya bazata bijirema kakar tata ba ta bayyana kanta kota koma gida Nigeria. Tsahon watanni uku kenan da barowarta gida Nigeria bisa taimakon kakarta Dada. _(Dan a waccan ranar bayan fitar Smart da ga gidan ta fito toilet da taje yin fitsari, duk da tai masa kurarin barin gidan ba’a ranar tai niyyar hakan ba, sannan batai niyyar sanarma wani nata abinda yay matan ba kamar yanda aunty Khadijah ta bata shawara. Saman gado ta koma ta ɗauki book nata da take adana muhimman sirrikanta ta fara rubutu tana hawaye, bata kai ƙarshe ba ya cika dan haka ta buɗe sabo ta cigaba. Tana tsaka da rubutun ne taji sallamar Dada a bazata, kafin ma ta farga har ta shigo bedroom ɗin nata kai tsaye. Hawayen da Dada ta gani a fuskarta ya sata nuna tashin hankali da fara jera mata tambaya, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya ta sakarma Dadan kuka kawai. Komai Dada bata tsaya tambayarta ba ta hau haɗa mata kaya, bayan ta kammala drivern da ya kawota ya shigo har ciki ya dinga kwasar kayan, yana kammalawa ita kuma ta ce Lulu ta tashi suje, da farko Lulu taso tirjewa akan ta bari Aliyu ya dawo, amma Dada ta balbale ta da masifa. Dole badan taso ba tabi umarninta ta sako. Sai dai tanayin taku biyu uku Dada ta rabga uban salati da antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba’in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al’amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu)………✍️

Wannan kenan.

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 2"