Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 24

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣

 

…….Shiru ɗakin yay bakajin komai sai ɗan ƙarar room hitter kasancewar sanyin da ake zubawa. Zaune yake cikin kujerar nan cike da ƙasaita ɗansa rungume a jikinsa ya zuba masa idanu kawai tamkar mai son gama haddace halittar jikinsa gaba ɗaya. Yayinda ita kuma take zaune a gadon jiyyarta ta miƙe ƙafafunta dake cikin blanket hannunta riƙe da sabuwar tab da Usman ya siya mata jiya. A zahiri wayar take kallo da sarrafawa, sai dai a ƙasan zuciyarta mamakin irin canjawar da Smart ɗin yayi take har yanzu, tamkar fa ba drivern nan nata ba, ya wani goge ga tsadaddun kaya wanka iya wanka, koda yake tun ma yana a drivern sa ita shaida ce ya san sirrin saka kaya, sai dai na yau ɗin dabanne, dan ko faratansa ka kalla kasan ya samu canjin rayuwa. Dama can bamai hayaniya bane shi, amma yanayin nasa na yanzu ya sake sakashi a wani matsayin zafafan maza masu aji da jan ajin. Kai itafa ALLAH da’ace a hanya taga mutumin nan maybe bazata iya shaida shi ɗin bane ba duk da kamaninsa na nan a tare da shi, sai ƙyawu da kwarjininsa mai bayyana cikar kamala da haiba da ya sake bayyana. Numfashi taja a hankali ta fesar, sai kuma taja ƙaramin tsoki da ya sakashi ɗagowa a hankali da ga kallon babyn nasa da yake yi ya sauke mata firgitattun idanun nasa da take kira na macizai. Duk da bashi take kallo ba sai da tsigar jikinta ta tashi ta kuma ji kaifinsu a cikin jininta. Sai kawai ta sake ɗaure fuska.
Cikin son ta kallesa da deep voice ɗin nan tasa acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Ashe haka kika ɗauki darasin nan nawa da gaggawa ɗaliba ta? Ai ban san ke ɗin zaki kasance duka ɗauka ba haka, ga result na first class na gani kam”.
Sosai ta danne zuciyarta wajen nuna masa tamkar bama ta jisa ba balle ta fahimce shi. Amma duk da haka sai da ta ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Wani murmushin ƙasaita ya saki tare da miƙewa ɗauke da babyn ya isa zuwa gareta, kafin tayi wani yunƙuri ya kai zaune a bakin gadon har jikinsu na gogar juna. Babu wanda baiji shock a jikinsa ba amma kowanne ya basar. Kaifafan idanun nasa ya zuba mata yana mai kai hannunsa ya ɗago haɓarta ta yanda zai kalla fuskarta sosai da ƙyau. Suna haɗa ido sai kawai ta lumshe idanun nata da ture hannunsa zuciyarta na wani irin harbawa, ita kaɗai tasan mi take ji game da shi, amma bata so tayi giving up, not now. Ƙoƙarin sake riƙo fuskar tata yake yi ta buge masa hannu a karo na biyu.
Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗin, “Baki son gani na ne?”.
Ba tare data sake iya kallonsa ba a tunzire ta ja tsaki da faɗin,, “Aliyu bana son damuwa, wannan rayuwa ta ce, ka fita kamar yanda na buƙata tun farko please. In ma saboda wannan ɗan kazo kasa a ranka baka da alaƙa da shi, koma kana da ita to yafi ƙarfinka danni da ga yau da ga yanzu na datse alaƙar taku har abada.”
Wani irin murmushi ya saki mai ƙayatarwa tare da tsurama babyn ido, sai kuma ya ɗago yana kallonta cikin lumshe idanunsa da buɗesu duk a lokaci guda. Cikin murya mai taushi ya ce, “Mawaddatan’warahmah! Kin taɓa ganin inda aka raba jijiya da ƙashin baya aka cigaba da rayuwa akan ƙafafu? Duk wanda ya kalla wannan ajiyar ALLAHn yasan zufan Aliyu Hydar Mika’il Idris Mawashi ne ai. Shi ɗin jinin jikina ne, ke da kika haifa min shi kuwa jijiyar ƙashin bayana ce, taya kike tunanin zan rayu a lokacin da babu jini a jikina babu lakar ƙashin baya? Please ki kalla cikin ƙwayar idanuna ko sau ɗaya ne, maybe ki karanci abinda ke a cikin zuciyar Aliyu Hydar ɗin ki. So ɗaya yake miki tak da in sha ALLAHU wata mace bazata sake samun kwatankwacinsa ba. Ko so kike sai na kai ƙasa gaba ɗaya zaki yarda da ni?…”
Harga ALLAH kalamansa sukarta suke. Sannan yamutsa mata illahirin jinin jikinta sukeyi. Duk wani ƙwarin gwiwar ta a garesa neman suɓucewa takeyi. Cikin sanyin jiki da rauni ta ɗago idanunta cike da ƙwalla, sai dai bata iya kallon cikin nasa idanun ɗin ba kamar yanda ya buƙata ta maida su ta duƙar.
“pleaseee!”.
Ya faɗa a hankali cikin wani irin salon jan “e” ɗin ƙarshe data saka tsigar jikinta mimmiƙewa gaba ɗaya. Sai kawai ta samu kanta da sakar masa kuka da faɗin, “I say live me alone please Aliyu. Kace ka sakeni bayan ka keta min haddi akan abinda na bada tsahon shekarun rayuwata na hankali ina karewa, mi kuma ya rage da kake buƙata a gareni yanzu? Ko ɗan numfashin da ya sauramin kuma shima so kake sai ka rabani da shi zaka huta? Ka barni dan ALLAH, ka cigaba da zama a nesa da ni ni yafi min I beg you” ta ƙare faɗa cikin haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo🙏.
A hankali ya kwantar da yaron gefe ɗaya, tare da matsawa kusa da ita. Jikinta ta janye baya tana sake fashe masa da kuka. Ƙoƙarin riƙota yake tana buge masa hannu. Bai damu ba ya riƙota ya saka a jikinsa ya rungume tsam. Tana ƙoƙarin masa magana cikin kuka da fisge-fisge ya hanata kowacce irin dama ta hanyar manne lips nashi cikin nata. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya saki yayinda ita kuma ta sake sake masa kuka da san ƙwatar kanta. Sai da ya tabbatar ya saka jikinta yin laushin da ta daina ƙoƙarin raba jikinta da shi sannan ya saketa dan jikinsa ya fara karɓar al’amarin. Da sauri taja jikinta gefe ta dunƙule waje guda tana faɗin, “Mugu ALLAH sai ya sakamin”.
Murmushi yay da lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. A nutse cikin firzar da huci ya ce, “Muguntar mi nayi ni da halalina kuma. Mawaddat believe me duk wanda ya faɗa miki na sake ki ƙarya yay miki, har abada Aliyu bazai taɓa rabuwa da Mawaddat ba koda ana min azaba da bulalai ina tuɓe a tsakkiyar sanyin ƙanƙara. Har abada Aliyu zai cigaba da kasancewa matsayin mijin Mawaddat ne koda bazata cigaba da rayuwa da shi ba.”
“Aiko dole ka rabu dani, dan inada kalar mijin da nake so in ma auren zanyi amma ba irin ka ba”.
“Ohh just keep your mouth up Mawaddat! Idan ma mafarki kike to ki farka wlhy, kuma duk sanda kika sake ambatar min kalmar wani namiji na rantse miki sai na darje waɗan nan silly lips ɗin naki ta yanda bazasu sake buɗuwa da sunan magana ba”. Ya faɗa cikin hasala da birkice mata tamkar wani bajimin bahagon matashin zaki. Har Babyn da ke a gefensu yana barcinsa na ɗan zabura shima dan tsorata. Da sauri ya ɗaukesa ya mannasa da jikinsa yana mai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jazur a ƙankanin lokaci. Duk tsaurin ido irin na Lulu ita kanta sai da ta firgita. Dan tsantsar tartsatsin wutar bala’in kishi ta hango a cikin birkitattun idanun nasa. Ta gefen ido ta saci kallonsa, dan ya miƙe yana jijjiga yaron saboda mutsu-mutsun da ya cigaba da yi. Ganin ya fara ƙushin-ƙushin ɗin kuka ya dawo gabanta cikin takun ƙasaita da hasala. Saman cinyarta ya ajiyesa babu alamar wasa a tattare da shi cike da bada umarni ya ce, “Shayar min da yaro abincin sa”.
Ɗago idanunta data ƙanƙance tai cikin hasala da mamakin ƙarfin halinsa. Sai dai hararar da ya wurga mata cikin tashi hasalar ya tabbatar mata wannan fa ba Aliyun baya bane data saba yima yanda taso. Sai ma duk taji tana neman daburcewa. Shiko ganin bata da niyar bama yaro abinda yace kawai ya kai zaune gab da ita kansa tsaye ya tura hannunsa a rigarta ya fiddo, zaro idanunta tai a wani irin razane, sai dai shi ko’a jikinsa dan kallo ma bata ishesa ba hidimar gyara yaron yake da ƙyau ya saka masa a baki. Shiko ɗan albarka ya cafke abinsa da sauri har sai da tai ƴar ƙaran jin zafi. Sai dai ta gagara ture uban da ɗan dan duk ya kanainayeta ga numfashinsa da ke sauka a jikinta wani irin harmutsa mata lissafi yake neman yi gaba ɗaya.  Da ƙyar ta iya fisgo kalmar, “Aliyu wai miye haka bana son wulaƙanci f…..”.
Fuskarsa ya matsar gab da tata ta yanda ta kasa ƙarasa abinda ta faro faɗar, ya wani busa mata iska a fuska da wata irin murya acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Naga dai namu ne ai ni da shi. Dan haka bama son hayaniya karmu ƙware”.
“Takaici, haushi, kunya, duk suka kanainaye Lulu a lokaci guda. Ga wani irin neman rikita mata lissafi da kusancin nasu ke neman yi. Shima kansa a wahalen yake da kusancin nasu, dan da ƙyar yake danne zalamarsa da haɗiyeta….. Lips ɗinta da ke rawa-rawa ta buɗe zatayi magana sallamar Ummita ta katse ta, Ummita da ta shafa’a da kasancewar sa a ɗakin bata jira an amsa mata ba ta shigo, hakan ya sashi jan jikinsa baya da gyara mata yaron cike da basarwa. Ita ma Ummitan sai tai saurin juyawa zata koma cikin ruɗewa tana faɗi, “Ya ilahi dan ALLAH kuyi haƙuri, wlhy na shafa’a”.
Smart ne cikin ɗan furzar da iska mai nauyi ya furta, “Karki damu dawo abinki”. Badan Ummita taso ba ta dawo, sai dai kanta a ƙasa ta ajiye bowl ɗin data shigo da shi mai ɗauke da gasashen nama da yaji kayan haɗi da Mamy ke haɗama Lulun duk bayan kwana biyu. Zata juya Lulu dake hararar baby da babansa ta dakatar da ita da faɗin, “Ummita anko samo zam-zam ɗin?”.
Kanta a ƙasa ta ce, “Eh Yaya Usman ya sayo tun ɗazun ai, harma da zumar”.
“Yauwa dan ALLAH haɗo a fidarsa kin sanshi ba ƙoshi yake ba ya gado ci irin na ub….”
Sai kuma ta kasa ƙara sawa ta murguɗa baki kawai. Murmushi Smart ya saki, a hankali ya furta, “Ai dama ƙyawun ɗa ya gaji Ubansa. Baki ji har sunan bai bari ba ya gado. Ashe haka kike son sunan nan amma baki taɓa faɗa min ba?”.
Harararsa tai cikin takaici tana jin kamar ta shaƙurosa. Sai dai batai magana ba dan sai ma yanzu take jin haushin kanta da tace a saka mata sunan. Baki Smart ya taɓe kaɗan shima da ɗaukar bowl ɗin naman ya buɗe, guda ya cira da ɗan tsinken da aka sako a ciki ya kai baki yana lumshe ido. Hakan ya saka Lulu zuba masa nata idanun batare da ta lura da abinda take yin ba har ya buɗe nasa da suka wani ɗan shanye tare da yin luww kamar mai jin barci. (He looks so handsome) zuciyarta ta ayyana mata. A fili kam sai tai saurin fara janye nata tana wani taɓe baki. A kasalance shima ya janye nasan yana jan ajiyar zuciya………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 24"