Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 27

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 


🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣

 

…….“Humm akwai wahala sosai da bata da misali. Na ƙara jin ƙaunar mahaifiyata da jinjina mata wahalar da tai dani a dalilin wannan cikin. Ko abinci bana iya ci, da naci sai amai, ko wani abu na sha sai nayi amai. Gashi nan ko yanzu dana haihu magani ma ya gagareni sai dai allurai ake min dan in naga magani amai nake ji. Kunun gyaɗa ne kawai ya zama abincina kwana da yini. Gaba ɗaya dai abin babu sauƙi kawai dan ba’a iya misaltashi ma Aliyu. Balle naƙuda Hummm……”
Duk da a dunƙule ta bashi labarin ya fahimci dai ciki ya hanata shaye-shaye, sai kunun gyaɗa daya zamar mata abinci kawai. Cikin ƙara sanyaya murya da jin tausayinta da farin ciki ya ce, “Addu’ata dare da rana UBANGIJI ya tasirantar da itane atare da gudan jinina, ya ƙarasa min aikin dana fara kenan, sannan a kowane awa bayan awa yana tuna miki Abbiensa ne ta hanyar shan abinda yafi so fiye da komai.” yanda ya ƙare maganar da ƴar dariyar tsokana ya sata ɗan harararsa da taɓe baki, sai dai batasan hararar tata ba ta juye ne zuwa wani sassanyan kallon dake neman hargitsama Smart lissafi da hankali.
“Ita hararar nan tana son tada zaune tsaye ne fa. Zakuma ta iya takalo yaƙin ƙasa da ƙasa a taƙaice rigakafi yafi magani”. Ya faɗa a wani irin kasalance yana ƙasa-ƙasa da idanu. Ba fahimtar zancensa tai ba, amma salon da yay maganar da yanda yake wani narke idanu da murya ya sata janye jikinta a nasa cikin basarwa duk da saƙon nasa ya isa ga manyan mata fiye da yanda yay tsammani. Shima kawai sai ya basar cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Yanzu miye shirinki akan suna gobe idan ALLAH ya kaimu?”.
Cikin mamaki ta ce, “Suna kuma? Da suwa za’ayi sunan to? Bayan naga idan za’ai suna a gida Nigeria taruwa dangi sukeyi da matan anguwa, in dai ban manta ba haka na gani a sunan Deen ɗin mu fa anyi, anan kuma mu yanzu wa garemu da zai zo?”.
“Mu mana, iya mu ɗin nan ma ai mun wadatar muyi suna bawai wajibi bane sai antarun kamar yanda kika gani a sunan Deen, in sha ALLAHU kuma za’a yanka masa rago kamar yanda ake yankama kowa. Ƙyautar da ban san da itaba ce ba fa a hannuna, taya bazan nuna godiyar ALLAH ba nikam. Sannan ni so nake daga nan mu wuce kawai basai kin koma Nigeria ba”.
“Hanyoyin nuna godiyar ALLAH ai suna da yawa ba sai ta hanyar yin taron suna ba. Sannan idan ban koma Nigeria ba ina kake son naje banda neman magana irin taka. Kuma ni nama faɗa maka na shirya cigaba da zama da kai ne? Auren contract akayi kuma ya ƙare it’s ok”.
“Hakane kam, Alhamdullah suma waɗan can godiyar UBANGIJI ɗin duk na kamanta su, amma duk da haka dai ina son muyi shagalin suna. Kinga koda ƙannensa sun zo nan gaba suma shi bazaiga an musu ba’ai masa ba”. Ya ƙare maganar batare daya amsa maganartata ta ƙarshe ba.
Hakan ya bata haushi, dan haka a tunzire ta ce, “Miye wani ƙanne? Malam ka san abinda kake faɗa fa! Na gaya maka ni na gama auren nan”.
Dariya ta bashi ganin yanda tai maganar a gatsire, amma sai ya danne da ƙyar yay murmushi kawai da faɗin, “Naki tsarin kenan wannan ai”.
“Kamar ya nawa tsarin kenan?. Amma kasan dai ba haka akai da kai ba ko?”.
“Humm” yace kawai. Baice komai ba akan maganar tata yanzun ma, sai ma ya nuna mata ledojin da suka shigo da shi. “Kuyi haƙuri da waɗan nan babu yawa, sauran abinda ya dace duk na damƙashi a hannun Usman. Munyi magana da Daddy akan suna son a turaki Saudiya ki zauna a can na wani lokaci saboda Kawunki Sulaiman, dan bazai taɓa ƙyaleki ba zai cigaba da bibiyar al’amarin ku. Ke yaya kika gani?”.
“Ni babu inda zani, shi ɗin banza da zan cigaba da masa wasan ɓuya. Ko wannan ɗin ma da yaga yaci nasara saboda Dada ne wlhy, sannan ina kan sani na cigaba da biye masa bayan nasan manufarsa. Nayi hakkanne kawai domin sake tabbatar da shi ɗin waye. Amma har miye wani Sulaiman can”.
Murmushi yayi kaɗan, a zuciyarsa yana ayyana (ashe a wajen Daddy kika gado wannan taurin ran naki da kafiya) a zahiri kam sai ya nisa cikin ɗan cije lips ɗinsa ya ce, “Zamu iya tunanin shi ba abin tsoro bane ba, sai dai idan muka shagala da hakan zai mana illa a ƙanƙanin lokaci cikin salon duka ta inda bazamu taɓa iya sosawa ba balle mu rama. Mawaddat Kawunki ya wuce duk yanda kike tunani a kansa. Domin ya jima biye da rayuwarki tun kina ƙarama. Bana raba ɗayan biyu shine ya koya miki shaye-shaye. Kuma shine ya taɓa harar rayuwarki ta hanyar keta miki haddinki har kike firgita kika tsani maza….”
Da wani irin sauri ta kallesa, sai kuma jikinta ya fara tsuma. Dan danan annurin fuskarta ya ɓace gaba ɗaya. Cikin yanayin faɗa-faɗa ta ce, “Aliyu rayuwata ta baya ta zamar maka abar bibiyane ko mi?”.
“No ko ɗaya, mizai sa na bibiya bayan na gama fahimtar komai. Sannan Mawaddat nake so ba halayenta ba. Ruwana ne na maidata a irin halayyar da nafi buƙata kona barta da wanda na ganta a ciki. Mawaddat ki sani shure-shure baya hana mutuwa, duk yanda kike jin zaki iya ɓoye abinda ya faru a baya wataran zuciyarki bazata iya ɗauka ba. Kiyi haƙuri ba ina tilasta miki bane sai kin sanar min, kidai sani cigaba da riƙewar zai iya sake nakasaki akan shaye-shayen nan. Doctor ya jima da tabbatar da idan kika cigaba zaki cutu, sannan a yanzu ke ɗin Uwa ce Mawaddat, taya kike tunanin idan yaron mu ya taso yaji wannan ɗibi’ar koda a labari ne zaiyi farin ciki. Mahaifiyarki mutuniyar kirkice data shinfiɗama rayuwarta alkairai da dama da a yanzu sune ke bibiyarta da ke kanki har maƙiyanki da nata suka gagara cin galaba a kanki. Taya kike tunanin naki ɗiyan zasu samu irin wannan kariyar idan har baki zama uwa ta ƙwarai ba Mawaddat. Please ina so ki canja, canjawar taki kuma zata tabbatane kawai ta hanyar fidda abinda ke zuciyarki, dan shine yay miki nauyin da har kike jin abinda kike sha zai iya danne miki shi. Taya za’a gyara ɓarna da ɓarna banda wautarki……”
Wani irin kuka mai tsuma zuciyar da ta saki ne ya saka shi yin shiru, a hankali ya furzar da iska tare da miƙewa ya koma daf da ita, matsota yay ya saka a jikinsa ya rungume. Sai kawai ta sake sakin masa kuka da iya dukkan ƙarfinta da baƙin cikin dake cinkushe da zuciyarta da ƙwaƙwalwa. Bai sake mata magana ba ya barta tai kukan mai isarta dan haka zai rage mata nauyin zuciyar. Tako yi kukan sosai dan sun kai kusan awa guda tana abu ɗaya har sai da taji kanta na sara mata sannan tai shiru ta koma shashsheka. Cikin son kauda yanayin ya ce, “Uhm nace ba! Yau dai anan zan kwana ko? Naga ai gadon zai ishemu”.
Da sauri ta ɗago tare zuba masa harara da kumburarrun idanunta da suka sha kuka. Murmushi yayi da marairaice face yana shafa kai. “Nifa bance wani abu ba Madam. A wajen kwanciyar ma na yarda sai ayi kai da ƙafa AA a tsakkiyar mu. Kinga dai ai babu batun kawo harima balle ace da wata manufa nazo”.
Filo ta ɗauka ta maka masa. Ya shiga karewa shi kuma yana ƙyalkyala dariya. Dai-dai nan Usman yay sallama. Hararar ƙofar Smart yayi cikin dafe kai. Hakan ya saka Lulu dariya ta amsa da cema Usman bismillah shigo. Babu kunya yana shigowa Smart ya hararesa da faɗin, “Kai wai miyasa baka iya zaɓar lokacin zuwa bane ɗakin mutane?”.
“Oh ba’ai farin ciki da zuwana ba kenan na koma?”.
“Eh gaskiya koma anjima sai ka dawo, wannan ai shiga tsakanin masoya ne”.
Ita Lulu abin harya bata kunya tana kallon Smart ɗin a daburce, sai taji Usman ɗin cikin dariya yana faɗin, “To kama jama kanka yanzu ma anan ɗakin zan koma yini”.
“Uhm saboda ka sake tabbatarma da duniya kai ɗan Sa ido ne kenan?. To aiko addu’ar tsole ido zan fara da tsiyaye ido, ba sai naga da idon da zakai sa ido ba”.
Cikin mamakin yanda suka saki jiki da juna a ƙanƙanin lokaci bayan tasan Smart da shegen ɗaukar kai wa mutane ta ce, “Wai dama kun san juna ne kafin jiya kenan ko me?”.
Dariya Usman yayi, yayinda Smart ke murmushi yana harararsa. Cikin marairaice murya ya ce, “Inafa ya sanni Baby luv. Jiya fa daya rabani da ke a ɗakin nan ya tafi dani can ya dinga isa ta da surutu kamar rediyo. Har sai da ya nema sakamin ciwon kai”.
“Kinga laifina ne Momyn AA. Ni ban iya kurumta ba, naga ana neman maidani kurman ƙarfi da yaji bayan ga ɗan ƙasata na gani. Ni mamaki ma nake yanda yake miki hira ke ko mu ya raina kenan dai yake mana shiru-shiru”.
Murmushi Lulu tai da kallon Smart ɗin, dan tasan zaman Usman a ɗakin nan da saka musu baki da take dauriya kawai yake yi. Ita bata taɓa ganin mutum mai kishin tsiya irinsa ba kodan bata rayu a Nigeria ɗin bane oho. Ilai kuwa kafin ta gama tunanin nata ya miƙe tare da jan hannun Usman ɗin ya na faɗin, “Muje tunda dai ka rantse sai ka rabamu sa’ido master”. Da ga haka yaja hannun Usman suka bar ɗakin.

Ajiyar zuciya Lulu ta sauke da maida kallonta kan AA bayan ficewarsu da ganin Hararar da Smart yay mata sanda yake ficewa. A dai-dai nan Ummita ta shigo ɗakin da sallama. Harara Lulu ta sakar mata cikin wasa da faɗin, “Sai yanzu ake ganinki? Ɗan naki ma yayi fushi ai shima”.
“Oh oh karki haɗamu faɗa Aunty, my sweetheart, I’m sorry sorry naga kana tare da Daddy ai yau ko shiyyasa ban zo ba” Ummita tai maganar tana ɗaukar AA da manna masa kiss a goshi. Har zuciyarta take jin ƙaunar yaron, dan ya shigar mata rai sosai. Murmushi Lulu keyi, sai kuma takai kwance da faɗin, “Su Ammah barci sukeyi ne?”..
“A’a suna hira abinsu tun ɗazun. Amma gasu can tare da su Daddyn AA yanzu suna magana. Ashe gobe idan ALLAH ya kaimu shagalin sunan Yarona zamu sha?”.
“Ku kuma ƴan son bidi’a dama haka kuke so ko?”
Dariya Ummita tayi ranta fes……✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 27"