Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 30

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣

……..A hankali suka cigaba da shiga jikina da nuna kulawa har takai na amshi maganin da suke yawan kwaɗaitamun na sha wai zai min maganin damuwata, wannan shine sanadin komai, domin kuwa a randa na sha na farkon sai na fahimci na samu sassaucin damuwata, har takai bana iya tuna komai na wani ɗan lokaci, da ga haka aka fara, a hankali, a hankali al’amarin ya fara tasiri har aka farga damu. Malamai sun tsawata mana, saboda shekarunmu sunyi ƙaranci da shaye-shaye, sai dai babu alamar zamujisu, daga ƙarshe suka nema iyayenmu. Nanny na ce taje, amma koda muka dawo gida na tabbatar mata idan ta bari Daddy na ko Uncle You suka sani a bakin aikinta. Tasan zan iya, kuma Daddy na jin maganata, ga shi kuma ina nuna bana sonta dama. Dan haka taja bakinta tai shiru. Ni kuma sai na ɗauki matakin daina shan komai sai da dare, kafin safiya ya sakeni. Sai a week end ne nake sha da rana, wataran a gidan su Luna wataran gidan su Alice anan gidan dai bana taɓa yarda suzo ma balle musha wani ya gane, sai takai har week end ina zuwa gidajen su Alice da Luna. Sai da Daddy ya farga ne hankalinsa ya tashi, yayma Nanny na tas da tabbatar mata in fa har bata kula da aikinta ba zai sallameta. Ni kuma ya rufe ido yamun tas da faɗa dan ya fahimci na fara wasa da karatu, ya kuma haɗani da Uncle You shima yay nashi. Har lokacin babu ruwana da ko mazan ajinmu, ƙawayena biyun nan dai sune Luna da Alice. Faɗan da su Daddy sukai min ne ya dawo dani hankalina akan karatu sosai, sai kuma burin dake raina shima na ƙaramin himmar hakan matuƙa har muka kammala karatun. Mun samu damar shiga jami’a ni su Alice kamar yanda muka tsara, hakan ya sake bamu lasisin cigaba da shaye-shayen mu da yawon clubs. Sai dai inata taka tsantsan ta yanda babu wanda ke fahimtata har lokacin. Kula maza da su Luna suka fara ne ya fara sakamu fara samun matsala, sunyi-sunyi suja ra’ayina akan hakan amma ya gagara, sai ma saɓani da muka fara samu da su. Akwai wani yaro a depertment namu da ya takura min, duk da bashi kaɗai bane sauran dana karta musu rashin mutunci sukan kama kansu. Shiko naci yaƙi ya barni na samu sakat, har takai ya fara shiga jikin su Luna domin su shawo masa kaina. Amma hakan ya gagara. Ganin bazai samu nasara ba suka haɗa baki da shi aka bugar da ni, matsalar da aka samu ni ba komai ke sani buguwa irin ta galabaita ba, mukan sha abu tare da su su fita a hayyacinsu sosai amma ni ina normal sai dai ɗan yanayi, wannan yasa na fahimci manufarsu a kaina. Wannan shine sanadin daya sa na karta musu rashin mutunci irin wanda basu san zan iya ba, na kuma rabu da su dan su basu san nai mugun tsanar maza irin haka ba. Bayan rabuwa da su nasa Daddy ya canja min makaranta, naso barin shaye-shaye a lokacin sai dai hakan ya gagara dan ya shiga jikina matuƙa, sai dai ina kiyaye duk wani yanayin da wani zai iya fahimtar halin da nake a ciki, zuwa lokacin bani da Nanny, sai masu aiki, sai kuma wata yarinya da aka kawo da ga Ghana wai ɗiyar abokin Daddy ce tazo karatu. Babu ruwana da ita dan ko harakar ta bana shiga, sai mu kwashe sati biyu ban mata magana ba, koda tamun ma sai ma gadama nake amsawa. Duk ina mata wannan abunne saboda tsanar ƙawaye da nayi, bama na son ta shiga jikina da har zamuyi shaƙuwar da zata kaimu ga wani matakin kuma, sannan bana son ta san ina shaye-shaye. A haka na gama karatu da ƙyar, dan a wasu lokutan sai nayi kamar zan ɓaras saboda yanayin da nake ciki sai kuma dai na dawo hankalina da ƙyar na maida hankali. Alhamdullah na samu result mai ƙyau saboda inada kaifin basira, kuma na saka zuciyata ga abin. Na yi wasu courses da ban da ban da suka shafi karatuna har na tsawon shekara ɗaya da wasu watanni, da kaina na ce zan dawo Nigeria nayi service, dan haka kawai nake jin kewar asalina, na dawo Nigeria a tsagerata, dan bana iya ragama kowa sai Daddy Uncle Yousuf, Mommy ma rashin ɗaukar halina yasa nake shakkarta, Aunty Saliha da Aunty Naja’atu kuwa soyayyar da suka nuna min da kulawa tasani jin ƙaunarsu a lokaci guda. Dan naje Abuja ne gidan Uncle Khamil nai hidimar ƙasa ta, sai kakata Dada dake nuna min soyayya irin ta uwa, tana mun gata sosai da yimin duk abinda nake so. Case ɗin wata yarinya akan fyaɗe ne ya zama sanadin fara aikinna a Nigeria, raina ya ɓaci da abinda ya faru, har takai Aunty Naja’atu na sanar min ai wannan ba komai bane da ga cikin tarin cases na fyaɗe a Nigeria. Musamman ma a yankinmu dan gwara nan Abuja akwai wayewar kan da iyaye basa bari. Amma tacan wajen gida akan rufe zancen wai dan kada yarinya ta rasa miji ko ahalinta su tozarta sai dai iyayen baƙin ciki ya kashesu, itako ta ƙare rayuwarta a cikin ƙunci da baƙin ciki. Wannan al’amari ya tayar min da hankali sosai, sai ko na ɗauki ɗammarar zama kan ƙafafuna domin hana samuwar irin waɗan nan mata tasiri, da kuma kai duk wani shegen daya ce shi mace ce abar wulaƙantawarsa ta hanyar fyaɗe prison ya ƙare rayuwarsa acan ko ƙuruciyarsa.. Wannan shine jiyan na Aliyu. Banda baƙin ciki da takaici mi kaji a cikinsa? Babu wani abun birgewa ko ƙayatarwa”
Smart ya kasa magana, sai kukan zuci kawai, a ransa yana auna tsakanin Lulu da mahaifinta waye yafi wani zama a ƙalubale?. Sai dai duk da haka tabbas Daddy yayi sakaci da al’amarin ta, dolene a faɗi hakan, amma tunda har ya amsa laifinsa da tabbatar da kuskurensa shikenan. Lallai a yau ya koya darasin rayuwa a labarin Daddy da Mawaddat, bai taɓa tunanin ko hasashen za’a iya samun wanɗan nan al’amuran ba masu gogayya da juna. Sai dai shi fa har yanzu zuciyarsa na bashi dole akwai hannun Sulaiman akan al’amarin Lulu. Daddy bai farga bane a wannan gaɓar saboda yarda da kansa da yayi na ganin tako ina, ta kowanne motsi yana dabaibaye da al’amarin Sulaiman ɗin, ko kuma dama ya riga ya gama shirya hakan kafin shi Daddyn ya fara nashi shirin. Ya kuma haɗa da wannan itace ƙaddararta babu wata dabara ko tsaro da zai hana hakan. Duk da kuɓutar da itan da Daddy yayi hakan bai hanata fuskantar ƙaddararta da yake gudan mata a inda aka haife ta ba. UBANGIJI kenan, gagara misalin masu misali. Shi kaɗaine masanin gaibu a zahiri da baɗinin rayuwa…. Sai da ya firzar da nannauyar iskar bakinsa a kusan karo uku sannan ya ɗago Lulu da ke hawaye har yanzu a jikinsa a hankali. Sosai idanunta sun kumbura abin tausayi. Nasa juyayyun idanun ya zuba mata, tare da riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa duk ya fara goge mata hawayenta da babban yatsun sa da faɗin, “Kalleni” cikin sarƙewar muryarsa da ke nuna tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki.
A hankali ta ɗago nata Lulu idanun ta saka cikin nashi, a take gabanta yay wata irin masifar faɗuwa. Kanta ya sara. Yanayin da take jin kanta da jikinta tun a jiya ya shiga sake zafafa gudanar jinin jikinta da motsin numfashinta. Shi kam Murmushi mai sanyi ya sakar mata batare da ya fahimci halin da take ciki ba. Cikin ƙanƙanin lokaci kamaninsa suka juye mata zuwa wani abu daban kamar a mafarki. Baya taja jikinta daya fara ƴar rawa-rawa da sauri. Cikin mamaki Smart ke kallonta, kafin ya iya cewa wani abu a bazata kawai ta fasa wata iriyar gigitacciyar ƙara da ta saka su Daddy dake ƙofa na saurarensu shi da Uncle Yousuf shigowa a firgice. Hatta Abbah da Ammah da Mamy ma a ruɗe suka iso ɗakin. Riƙetan da Smart yayi sai take neman sume masa ma. Al’amarin ya bama kowa mamaki, Ummita na kuka tai kiran Usman, ya ce mata gasu nan shi da Dr Lameer ma a kusa. Ammah ce hankalinta ya kai da yanda numfashin Lulu keyi da yanda take son raba jikinta da na Smart ɗin. Da sauri ta ƙaraso garesu, hakan yasa Smart sakarma Ammah ita dan a rikice yake shima. A kuma dai-dai nan su Usman ke shigowa ɗakin. Zabura Lulu ta shiga yi a jikin Ammah da nuna Smart tana faɗin ya fita, bata son ganinsa ya fita. Yanda ta fita a hayyacinta cikin ƙanƙanin lokaci ga ciwo a jikinta yasa Abba jan hannun Smart ɗin suka fita, abin mamaki da al’ajab kamar ƙyaftawar ido sai ta koma laƙwas tana sauke numfashi. Cirko-cirko kowa yayi da mamaki, Dr Lameer ne yasa a maidata saman gado, yay ƴan dube-dubensa ya ce musu lafiya ƙalau take, dan jikinta ma Alhamdullah kaɗan ya rage. Wannan al’amari ya saka kowa mamaki, sai kallon Lulu dake sauke ajiyar zuciya sukeyi. Ganin an samu komai ya daidaita Abba da Smart suka sake shigowa. Zabura ɗaya Lulu tayi ta dire ƙasa tana neman kwasa a guje da ihun “Aliyu ka fita! Ka fita bana son ganinka, na tsaneka ka fita!”. Nanma sai da aka rirriƙeta, yayinda Smart yama kasa koda motsi. Ganin zata jima kanta ciwo akace Smart ya fitan. Yana fita abin mamaki sai ta sake komawa laƙwas. Ran Daddy ne ya ɓaci dan shi zuciyarsa bata kawo masa komai ba sai ganin da gangan Lulu keyi. Sai dai Abba ya riko hannunsa yana girgiza masa kai da faɗin, “A’a Alhaji Isma’il wannan ba abin faɗa bane abin dubawa ne. Sai dai idan shine yay mata wani abun tunda tun ɗazun suna tare a cikin ɗakin ko”.
Da sauri Daddy yace, “Babu abinda yay mata, dan duk abinda suke tattaunawa muna jiyosu ni da Yousuf. Baka san halin Mawaddat bane ba Malam Mika’il”.
Cikin damuwa Mamy ta ce, “Mawaddat wani abu yay miki ne?”.
Kai Lulu da hawaye ke silalomawa ta shiga girgizawa a hankali. Sai kuma a hankali tace, “Mamy yana koma min wani irin siffa ne mara ƙyan gani daban tsoro. Dan ALLAH kuce kada ya sake shigowa bana son ganinsa”.
Babu wanda hankalinsa bai tashi ba da wannan furuci na Lulu. Ga kuka da AA kayi duk ya sake gigitasu. Dama kuma tun jiya da dare yake kukan sai da Ammah ta dinga masa addu’oi sannan suka samu yay barci gabannin asuba. Shiyyasa ma yake ta ramuwar barcin da safen nan ko wanka ana masa yana barci. Uncle Yousuf da gaba ɗaya ya gama ruɗewa ya ce, “Ko aljanune, dan gurin nan da suke ai baya rasa aljanu ba”.
Ammah da tun ɗazun tai shiru tana nazari ta ce, “Dama Mawaddat nada aljanu ne?”………✍️

*_Lulu da Smart dole a kiraku da FURAR DANƘO kam….🥲 Sai dai in sha ALLAH maƙiya SU SHEKARA SUNA DAMU BAKU ZAME MUSU FARAU-FARAU 🤦😏🚶._*
 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 30"