Breaking News

Furar Danko Book 2 Page 35

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣

 

……..Wannan roƙo nasu Smart da Daddy da Uncle Yousuf harma da Abba da shima yazo masa murnar ƙara aure akasha hira da barkwanci na tsoffin abokai bayan sati biyu Dada ta dawo. Dawowar data zame mata matsanancin jin zafi. Gashi ba abun tace bazata dawo ɗin ba ta rasa sauran damarta. Ga muzantatan da surukanta keyi na sake ɗaga mata hankali. Ta samu gida fa komai ya sauya. Hatta masu aiki kowa dai Aunty Amarya dai aunty amarya dai. Dan yarinya ta kwantar da kai tana cin garar arziƙi abinta. Ta kuma kame kowa na gidan da ƙyautatawa bayan uban gayyar Baba Garko da taima ram da zuciya yake jinsa kamar wani ɗan shekara talatin, dan more tsufansa yake hankali kwance ya manta da batun wata aba Dada… Ganin cikin amarya da Dada kejin wai-wai a bakin mutane ya sake ɗaga mata hankali ta ɓarke da kuka. Wai itace yau tsofai-tsofai da kishiya, kishiyar ma sa’ar jikokinta kai jama’a wane irin cin zarafine wannan Alhaji Sufi yay mata ne ita kam a duniya, duk wahalar da tai a ƙuruciya na hana wata shigowa gidanta sai a wannan gaɓar za’ace wai ga ɗan uba a cikin zuri’arta. Ga shi Baba Garko yaƙi ko saurarenta tunda ta dawo, duk ranar girkinta fa zai yi kamar suna tare amaryarsa bata zuwa inda yake, amma kuma bai barin itama Dadar tazo. Ko kuma ma ya ƙirƙiri tafiya. Bayan wata ɗaya da dawowar Dada yasa aka saki Alh. Sulaiman shima…..

______★

A ɓangaren uban gayya kam al’amura sai dai Alhmdllh. Dan komai yana tafiya fiye da yanda akai fatansa. Ya zama cikakken ɗan wasan Arsenal da yanzu duniya ke kallo ta faɗa da kiransa *_GWARZON ZAKI_* Sunan Smart Mawashi sake dilmiya yake a duniyar ƙwallon ƙafa. Dan a yanzu haka ya fara taka sabuwar rawa a sabon team ɗin nashi na Arsenal. Duk da kuwa wasanni uku kenan suka buga kacal. Sai dai aduka wasan babu wanda bai saka musu ƙwallo ba. Wannan ya sake jawo hankalin al’umma kansa tako ina a duniya. Ya zama ɗaya daga cikin matasan yara masu tashe a duniyar ƙwallon da ake faɗa ake ma kan faɗa a kowane yini. Al’amarin matarsa bawai baya damunsa bane, ya miƙama UBANGIJI al’amarinsa ne kawai da fatan cinye waɗan nan jarabawoyi kashi-kashi. Shi kaɗai yasan abubuwan da yake jurewa a irin wannan tsukun. Amma yana matuƙar begen matarsa a kusa da shi har ma da gudan jininsa takwaransa…..

____________★

Yau ma a gajiye ta dawo gidan kamar kullum Ummita biye da ita da tarkacenta. Tunda aka kammala bikin buɗe ƙungiyar nan tata bata huta ba. Ga aikin kungiya gana office ga karatun islamiyya ga shago. Dan rainon AA dai bazatace komai ba kusan Mommy da su Afrah ne keyi da Iya Tabawa. Tsakaninta da shi kawai ta shayar da shi. Kasancewar ma yana shan tea da koko hankali kwance bai cika damuwa ba. Shiyyasa ma bata fita da shi ko’ina. Ba kuma ya kuka dan shi ɗin mai iyayene da yawa. Itada kanta ma wani lokacin har tausayi yake bata da rashin samunta yanda ya kamata. Amma yaya zatayi.
Tunda sukai sallama AA da ke a bayan Suhaib na masa doki ya fara zillo. Saukesa yay suna masa dariya. Ya rarrafo da saurinsa zuwa gareta. Kamar yanda suke dariyar itama dariyar takeyi. Daukarsa tai ta jefa sama ta cafe tare da rungumesa tai masa kiss. Shima yay mata a kumatunta biyu. Lakace masa hanci tayi cike da farin ciki da jinjina wayonsa. A kullum kamar ana ƙara masa wayo ne. Baya magana dai sannan tafiya bata nuna ba, amma idan ka gansa bazakace watansa tara ba. AA akwai zafin nama da ɗankaren wayon tsiya. Shiyyasa ɓarna babu kama hannun yaro. Idan aka kaisa hira wajen Daddy har korosa yake saboda ɓuruntu. Hakama Mommy sunta faɗa kenan.
Cikin zubewa a kujera Lulu ke faɗin, “Wayyo ALLAH ku bani ruwa kafin na shiɗe Please”. Amrah na dariya ta miƙo mata ruwa da kofi, kofin ta ture ta ɓalle murfi goran ta kafa kai kawai. Neman ƙwacewa AA yake tana buge masa hannu, bata kulashi ba sai da ta kusan shanyewa ta bar masa ɗan kaɗan sannan ta bashi.
“Wai lallai aunty Lu.. kinji ƙishi fa”.
Cewar Mubeen dake ƙoƙarin ɗaukar AA da ke miƙa masa hannu. Dan shigowarsa kenan shima da ga makaranta. Tace, “Ka bari kawai broth wlhy yau munsha wahala ne. Ai bazan iya driving-driving ɗin nan ba a nema min driver please. Sai dai mai hankali dan ALLAH ban son mai surutu da ƙazanta”.
Dariya Amrah da Afrah da Mubeen suka sanya. Mubeen ke cewa baki son irin su Dallatu yake ko wa ma mai shegen ƙaryar nan ga yalalen haƙora”.
Itama dariyar tayi, dan ta tuna da wanda suke maganar, shine ta kora aka kawo Smart. Akwai shegen surutu da son fafa amma ba tsafta. Aiko yasha marukanta babu adadi. Haka kawai sai Smart ya zo mata a rai. Taɗan lumshe idanu da jan ajiyar zuciya, gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Tsam ta miƙe tabar falon suna cigaba da hirarsu bama su farga ba. Dan Ummita suka shiga bama labarin direbobin Lulun da akasha kala-kala a gidan. Tana shiga ɗakin nata da ke tsaf-tsaf yana ƙamshi mai daɗin gaske dan yana nan a yanda kowa ya sanshi da tsafta, iya Tabawa bata wasa da gyaransa saboda Lulu sam bata son ƙazanta. Abayar jikinta ta saɓule, wando da rigar data saka a ciki suka bayyana. Suma zaresu tai ta shiga wanka. Tana fitowa ta gabatar da sallar magrib da aketa yi. Alkur’ani ta ɗauka tai karatu gwargwadon abinda ya sawwaƙa kamar yanda ta saba a yanzu, kafin ta ɗora da azkar na yamma da bata samun damar nutsuwar yi sai irin iyanzu ɗin. Koda Ummita ta shigo mata da takardun ta da Laptop bata katse abinda take ba, sai ga Iya Tabawa ma da tea da Lulun kesha duk dare AA goye a bayanta. Tea ɗin ta fara ajiyewa a inda Lulun ke zama yin ayyukanta sannan ta matsa gaban gado ta sauke AA ta kwantar a hankali. An masa wankansa an masa shirin barci sai ƙamshi yake yi kamar ba dare ba. Fita sukai gaba ɗayansu suka ja mata ƙofar, dan babu kuma mai sake shigo mata kenan, itama da wahala ta sake fita in ba Daddy ne bai shigo gidan da wuri ba taje su gaisa. Kamar dai yau da suka samu baya a gida bai dawo ba.
Bayan kammala addu’ointa tsam ta miƙe ta maida komai a inda yake tare da zare abayar sallarta ta maidata a inda take ajiyewa. Doguwar riga mara nauyi da bata kai mata har ƙasa ba ta saka mara hannu. Ta ɗan rage gudun acn ɗakin saboda AA mai saurin ɗaukar mura sannan ta nufi gadon nata. Zama tai a hankali gefen da yaron yake da ga can ɗan tsakkiya tana sauke ajiyar zuciya da ɗaukar wayoyinta. Ɗan dudduba massages tayi da miss calls da akai mata ɗazun bata samu amsawa ba. Ta kira wanda zata iya ta share sauran. Sakwanin ma amsa wanda suke da muhimmanci tayi sauran ta barsu. Tana ƙoƙarin ajiye wayar kira ya shigo. Number nan ce dai da ko ta ɗaga ba’a magana tayi masifar har ta gaji, har blocking tayi amma tarasa yanda ake cigaba da kiran nata. Har ta tsinke bata daga ba, aka kuma sake kira. Tasan idan bata ɗaga ɗin ba dai ba dainawa za’ai ba koda za’a jera mata kira hamsin ne, dan haka ma take ɗagawar ta samawa kanta lafiya tunda bata san wane aljani ne ba kuma. Kamar kullum shiru anƙi ace komai, sai dai tana iya jiyo saukar numfashi da fitarsa a hankali. Itama yau sai taƙi yin magana. Haka sukai shiru kusan na mintuna uku kamar ba kuɗi ake ci ba.
“Hummm koma waye dai ALLAH ya shiryesa”. Ta faɗa cikin jin haushi da yanke kiran tana jan ƙaramin tsaki. Wayar ta jefar gefe tare da kai hannu ta gyara ma AA kwanciya, sai ta samun kanta da zubama yaron ido kamar yau ne ta saba ganinsa. Ta ja tsahon mintuna biyar tana ma yaron kallon ƙurillah tare da cakuɗa abubuwa da yawa da ke cimata zuciya. Ganin zata zurfafa tunaninta yay yawa ta sumbaci goshin yaron da sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta masa addu’a ta gyarashi. Miƙewa tai zuwa inda take zaman aikinta ta zauna, sai da ta haɗa shayi sannan ta kunna laptop tare da rage hasken ɗakin, bakajin komai sai motsin keyboard da na ac. Ta kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ta tashi tana faman miƙar gajiya, toilet ta shiga tai uzirirrikanta ta fito tai shirin barci ta haye gado kusa da gudan jininta ta kwanta…..

Washe gari kamar yanda ta saba da wuri tai shirin fita. Dan ma tana ta fama da AA da ya maƙale mata yau shagwaɓa yake ji, sai da Ummita ta shigo ne ta ansar mata shi ta samu ta ƙarasa gyarawa tana faɗin, “Yaro zaka gane kuranka yayeka zanyi ai a cikin watannan”.
Cikin waro idanu waje Ummita ta ce, “Kai aunty wasa kike amma dan ALLAH?”.
“Oh wasa ko zakuga wasa”.
“Kai aunty wata tara fa, baima cika cif-cif ba. Banda ma yanada kirinki da zafin nama ai bai kai a fita a barsa ba”.
“Uhm Ummita kanku fa akeji, wlhy jira kawai nake ya taka na yayesa. Tunda yana cin abincinsa ba wani ya damu da nonon bane sosai ai gara na hutar da kaina ko.”
“Mudai aunty kiyi haƙuri to ko shekara ɗaya mu cika dan ALLAH mun tuba”.
“Ummita kenan, wai baki tausayina ne ma dai ko. Da wanne zan ji?”.
“Aunty damu mana, ai mune farko kafin komai. Dan kulawar mu da ta Abbienmu itace farko”.
Shiru Lulu tai bata sake cewa komai ba. Dan a duk sanda Ummita zata ambaci Abbien AA ɗin takanji zuciyarta na mata nauyi, shiyyasa bata sakewa hirar tai nisa a kansa take basarwa. Ficewa tai a ɗakin tana faɗin, “Bari na duba Daddy zanyi breakfast a wajensa ki yi maza ki shirya kin san munada aiki yau”.
Cikin girmawa Ummitan ta amsa mata da to tare da Binta da kallo tausayi. Sosai ma’aurata ke matuƙar bata tausayi, bata taɓa ji ko labarin irin aurensun nan ba. Auren kusan shekara ɗaya da fin rabi kaɗan babu a biyu amma zaman wata ɗaya cikakken ba’a samu ba, dan ma UBANGIJI mai hikima da ya saƙa zare mai girma na azurtasu da ɗa. Tana ma kanta addu’a, amma gaskiya Lulu na ɗaya daga cikin manyan addu’ointa a kowacce rana. Fatanta ALLAH ya kawo iyakar komai ta koma wajen mijinta da ayanzu duniya ke faɗa da saurara a fanin ƙwallon ƙafa. Ita tasan duk da Lulun bata nunawa tanada damuwa sosai. Dan tasha kamata tana kallon AA kallo mai harshen damo kasancewar sa tamkar photo copy na mahaifinsa. Sannan shi kansa yaron soyayyar da take nuna masa mai kallo yasan ba tashi bace shi kaɗai harda ta Abbien nasa……..✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments