Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 36

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣

 

……..A wajen Daddy ta karya kamar yanda ta faɗa. Sunata hirarsu cike da nishaɗi. A cikin hirar ne yake cemata yana son ya je ya ɗan huta kwana biyu da ga nan zaiga doctor ɗinsa da kuma wani business da zai yi a England. Batare da ta kawo komai a ranta ba dan harga ALLAH bata san a ina Smart yake ba yanzu, ta ce, Daddy badan ina akan gaɓar wani case ba ALLAH nima dana bika na ɗan huta kona 1week ne. Da ga nan ina son na shiga U.S ma duba wasu takarduna a gidan can”.
Da ƴar tsokana Daddy ya ce, “To ko na jiraki ne Sweetheart. Kin san fa na daɗe bamuyi tafiya tare ba ina jin kewar hakan”.
Dariya tayi da faɗin, “Daddy karka sa Naseer ya ɗauka na ƙwace masa fadarsa ta autanci fa.”
Shima darawar yay cike da nishaɗi yana faɗin, “Ai yace yanzu shi ba auta bane. AA ne Auta. Banda ƙarfin hali an taɓa ƙwace ɗan wani gida a bama wasu.”
Murmushi Lulu tai da cewa, “Nakune ai Daddy, wake da iko da shi sama da ku?”.
“A’a fa Mawaddat son kai da maida ɗan wani naka. Da haka ne ai da kema na haƙura na barma su Dada. Mahaifinsa na sane da abinsa kafin ya waiwayone kawai. Yanzu dai ki duba idan kinada dama zuwa hutun sai na jirakin, dan nima zan shiga U.S ɗin insha ALLAH. Nanny ɗinki ma ta kirani wai bata da lafiya sosai zata koma ƙasarsu Gambia tai jiyya. Amma nace ta ɗan jirani har naje sai ta wuce”
Sosai Lulu ta nuna tausayawa da mata addu’ar samun lafiya. Da ga haka suka cigaba da hira har lokacin fitarta yayi. Tare suka fito da Daddy ɗin har da Mommy data samesu itama. Ta samu Ummita na jiranta, dan haka bata ɓata lokaci ba ta ɗan tattaɓa AA da masa kiss tana jaddada ma su Amrah su ɗauki saƙon Ammah a ɗakinta idan zasu wuce kai AA ɗin yini can yau kasancewar juma’a ce duk sati can ake kaisa dama. Sun amsa mata da to ta shiga mota suka wuce….

________★

Kamar koda yaushe Ammah tayi farin cikin ganin jikan nata. Dama gashi juma’ar ƙarshen wata ce yaran gidan duk zasu zo. Shima cike da ɗokin ganinta ya maƙalƙaleta dan ya saba da kakarsa kasancewar ana kaisa. Da yaga Asma’u ma haka ya dinga zallo dan ɗan lelenta ne. Su Amrah basu jimaba suka wuce duk da ba haka Asma’u taso ba. Sai dai zasu wuce school ne dole babu yanda zasuyi. Itama yau bazataje bane saboda tun jiya tana kwance babu lafiya. Maryam kuwa tana gidan aunty Bilkisu saboda makaranta tafi mata kusa da ga can yasa tafi zama a can yanzu sai weekend ake ganinta anan gida tunda an zama ƴan jami’a bisa tsayawar Smart, da. Yaran Abba mata basa shiga jami’a sai a gidajen mazansu. Itama ganin an kawo kuɗi yasa Smart cin ƙarfin Abban da ƙyar dai ya amince ta fara. Shi kuma Smart yayi hakane saboda yasan dangin su Ahmad ƴan boko ne na gani kasheni, baya son ƴar uwarsa ta shiga cikinsu ta koma baya. Yanzu ko koba komai taci ƙarfin kusan shekara biyu kafin bikin tunda gashi yanzu tana da shekara kusan ɗaya. Bikin kuma shekara ɗaya aka saka.
Koko Amma ta fara bama AA sai ya ƙi sha ya fara bultso mata shi. Cikin dungure masa kai da faɗin, “Ɗan nema yau kuma kokon ne bazaka sha ba. Kaima dai tsurfa irin ta Babangida yana yaro duk ka iyata.”
Dariya Asma’u da ke kwance take musu. Ta ce, “Kai Ammah yayan ne yay tsurfa?”.
Ammah ta ce, “Tab har ma ana magana. Ai Hydar al’amarin sa daban ne dana kowa. Kinga tashi haɗa masa tea ko zai sha”.
“To Ammah. Amma ƙilafa baya jin yinwa ne.”
“Eh to da wannan kuma. Sai dai kum….” dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammah ɗin. Tashi Asma’u tai ta ɗakko cikin zumuɗi take faɗin, “Ammah Yaya Hydar ne”. Murmushi itama Ammah tayi, dan haka Asma’u ta ɗaga tana gaishesa cikin farin ciki da girmamawa. Da ga can ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta jama’ar gidan tace kowa lafiya yake. Ya tambayeta miyasa bataje makaranta ba ta sanar masa tun jiya bata da lafiya shiyyasa Ammah tace yau kar taje sai monday.”
“Okay” ya faɗa a taƙaice cikin rashin son hayaniyar nan tashi. Har zata miƙama Ammah wayar ya sake faɗin, “Kinje asibiti ne?”.
Amsa ta bashi da cewar, “A’a Aunty Mawaddat ta turomin Doctor ya dubani da dare”.
Da mamaki ya ce, “Gidan tazo?”.
“A’a Yaya ai bata iya zuwa har yanzu, ta kira Ammah ne suka gaisa shine taji Ammah namun faɗan shan magani. Tace mata ta barni bari doctor yazo ya dubani sai yay min allura idan ban son maganin ne”.
“Yayi”.
Ya faɗa a taƙaice. Da ga haka yay shiru. Ita kuma sai ta miƙama Ammah wayar. Ya gaida Ammah cike da girmamawa. Ta amsa masa da kulawa. Dariyar wasan da Asma’u kema AA ya jiyo. Ya ce, “Wake dariya haka?”.
Ammah ta ce, “Babana ne Asma’u kema wasa.
“Yau kuma anan ya kwana kenan?”.
Da ƴar dariya Ammah tace, “Banda abinka Hydar ina mai shan no-no zai kwana wani waje bada uwarsa ba. Yanzu su ƴan biyu suka kawoshi dai. Sai kuma dare sai Mubarak ko Abdull su maida shi. Sai dai nasan yanda baida da rigima kwana nan ma zai iya yi batare da ya damu ba, badai a taɓa gwadawa bane. Da har haƙurinka ya biyo bai bar komai ba shikam”.
Ɗan murmushi kawai Smart yay da ga can da faɗin, “Hummm”.
Sanin halinsa na rashin amsa komai dalla-dalla yasa Ammah fahimtar abin cewar kenan. Dan haka ta ɗora da faɗin, “Hydar baka ganin ya kamata kayi magana su taho haka nan ko ALLAH zai sa a dace komai ya daidaita, duk da dai bata iya shigowa gidan nan har yanzu kuma tana son hakan. Ko tazo sai dai ta tsaya waje shima da ƙyar ake sha dan sai ta tafi da ciwon kai. Amma ƴar albarka kullum bata gajiya sai ta kirani safe da yamma taji lafiyata. Kayan shayi da su sabulu zuwa kayan buƙata irinsu-irinsu sai dai na bama wani. Ai duk wanda yay wannan shiga tsakani na kai da iyalinka bazan yafe masa ba a wannan karon” hawaye suka cika mata ido.
Cikin rauni da sanyi Smart yay murmushin ƙarfin hali da faɗin, “Ammah dan ALLAH ni bana son kina damuwa. Komai lokaci ne ai, ALLAH dai ya bamu ikon cinye jarabawa. Wlhy ni kuma ina jin nauyin su Daddy ban san taya zan taresu da maganar nan ba. Ina ga kawai mu cigaba da zubama sarautar ALLAH ido komai zai wuce. Yanzu ya batun ganin naki likitan ne? Kodai nan zaki taho. Dan ina son itama aunty Bilkisu tazo nan ɗin saboda matsalarta, akwai wata ƙwararriyar likita anan da nake fatan insha ALLAH ta ganta za’a dace”.
“Hydar kai dai na kula baka jin kisan kuɗi sam. Wannan ƙoƙarin naka yayi akan ƴar uwarka. Amma ni dai ka barni anan ai akwai likitoci ƙwararru in sha ALLAH zasu dubani. Dan ma ka damune kawai amma ai ƙafar ba wani tanayi sosai bane yanzu tunda ka aiko min maganin nan”.
“Ammah ai lokacin abu a yisa. Da banyiba ai da bani da shi. Yanzu kuma Alhmdllh. So nake ma muyi magana da Abba dan ina son gyara gidan nan tunda naga baya son barin anguwar”.
“Tab kaima kasan mai raba Abbanku da anguwar nan ai sai dai mutuwa. Gyaran dai shi yafi kam”.
Cike da gamsuwa ya ce, “In sha ALLAHU hakan za’ayi kawai”. Da ga haka suka cigaba da hirarsu tsawon lokaci kamar yanda yakanyi duk sanda ya kira. Har sai da aka kaima su Umma suma su gaisa. Kamar ko yaushe sai da Umman ta bugi cikinsa akan komawar matarsa. Shi dai yay murmushi kawai kamar yanda yakanyi a duk sanda tai masa tambayar saboda nuna kunya. Sai dai hakan na ƙona mata zuciya da jin ƙarin tsanarsa. Cikin rashin daɗin rai ta miƙama Asma’u wayar batare da ko sallama sunyi ba. Mama ma ankai mata sun gaisa da aunty Amarya. Lokacin da ta maida ma Ammah wayar take sanar mata “Yau ma Ummah sai da ta tambayi Yaya wai yaushe zai zo ya maida Aunty Mawaddat ne? Ko baturiya zai kawo musu wannan karon?”.
Murmushi kawai Ammah tai da girgiza kai tana mai mamakin halin irin na Ummah. Tana rakata ne kawai zuwa gaɓar da take buƙatar bata amsa. Shiyyasa a yanzu take cigaba da shanye komai, dan ta gama ji a ranta da hannun Ummah a al’amarin su Smart ɗin……

________★

Tunda ya fito a prison da mahaifinsa ya sa aka kaisa jiyya ya kwanta kusan ta wata guda saboda wahalar da yaci a wajen. Da ga ƙarshe ya ɗauki amaryarsa suka wuce Mexico. Watanninsa biyu kenan sai yau ne ya dawo Nigeria. Ya murje abinsa tamkar komai bai faru ba. Sai ƙiba da ya ƙara abinsa mammokaɗewar da yay duk ta ɓace. Tafe yake cikin izzar nan tashi da ƙasaita yana faman hura hanci. Abokan cin mushen nasa ne su Hon. Nakowa sukaje tarbarsu. Sai Tajuddeen da shima baifi kwanaki uku da dawowa ƙasar ba. Shima dai ya murje abinsa kasancewar hankalinsa kwance yake akan zaman Lulu a gida. Gani yake auren ya mutu suna ɓoyewa ne. Acewarsa ta gama ɓoye-ɓoyen ya fito a ɗaura musu aure. Shiyyasa ya ajiye makaman yaƙinsa da mahaifinsa ya ɗorasa tsakaninsa da kakanninsa ya je suka dai-daita da Baba Garko. Dan ya bashi haƙuri sosai da tabbatar masa shi baya tare da mahaifin nasa, sannan bai san manufarsa akan Lulu ba. Baba Garko yaso korasa amaryarsa ta lallashesa da tausashi akan ya jawo Tajuddeen ɗin a jikinsa, hakan zai sa ya canja masa ra’ayi akan dagiyar soyayyar Lulu harma ya haƙura. Ya fahimci manufarta, dan hakan da zai yi ne kawai zai barranta halin jikan nasa da ubansa kar shima su rasashi.
A kallo ɗaya zaka ɗauka babu komai a tattare da Alh. Sulaiman ɗin sai farin ciki, nan ko zuciyar tsatstsage take da mugayen nufi musamman akan abubuwa da dama. Dan wannan karon kam ya dawo da shirinsa shiyyasa ya bada ƙafar ja baya. Acewarsa ja baya ga rago ba tsoro bane shirin faɗa ne………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 36"