Breaking News

Furar Danko Book 2 Page 37

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣

 

…….Cikin ɓacin rai abokin nasa ke kallonsa. Dan gaba ɗaya a watannin nan MM Atik ɗin ya sake birkicewa. Ɗan sauƙin da aka samu wani aiki da mahaifinsa ya haɗashi da shi ne zuwa Chaina shine dalilin ɓuyansa. Sai a watan jiya yake dawowa gida Nigeria. Abinda ya farayi shine neman Nadia. Sai dai ya taki rashin Sa’a wai tana kwance babu lafiya. Dan cikinta ya kumbura sosai tana fama da ciwon hanta da ƙoda sakamakon shaye-shaye. Ga ciki ta samu wanda taita faɗi tashin ganin ta zubar da shi amma ya gagara zuba, tayi ƙoƙarin ganin Alhaji Baita domin cikin tasan nasa ne, amma ta kasa samun kowacce irin dama. Daga ƙarshe mahaifinta ya korota da ga gidansa.
Yana gama jin abinda ke faruwa da ita a wajen yarinyar shagonta yaja tsaki da faɗin, “Mtsoww bata da wani amfani a gareni yanzu”. Da ga haka ya kaɗa kansa yay tafiyarsa. A sabon bincikensa ya gano Lulu na gida amma ta haihu, yaji baƙin ciki da jin ciwon jin kalmar haihuwar nan har ya nema susuta kansa. Dan giya ya dinga ɗorawa da cocaine yana sambatu. Da ƙyar su Asim abokinsa suka samu ya dawo dai-dai. Sai dai ya rantse yana akan bakansa sai ya mallaki Lulu koda ta ƙarfi ne dan sha’awarta zata iya kashesa. Saboda a ganin da yay mata ranar bikin ƙaddamar da ƙungiyarta sai yaji kamar ƙarya ake masa ta haihun. Dan tana nan fes da ita babu alamar wani koma baya ko tawayar haihuwa tattare da itan. Sai ma ƙyau na musamman da yaga ta ƙara masa da cikar kamala duk da yanzu dai bata shigar wando da riga ko matsatstsun kaya ta fita haka zuwai sai da abaya a sama. Wani lokacin ma da facemask, sai kuma wai yaron nan mai tashe da shi kansa yake matuƙar so wai shine drivern nan nata data aura. Wannan abu shima ya jijjigashi, ya jima yana mamaki a ransa. Amma dan ƙarfin hali har yanzu a hakan baya jin zai janye dan kullum kamar ana ƙara rura masa wutar buƙatar Lulu ne. Ko neman mata ya rage yi yanzu dan kowacce ta bar burgesa, sai ma idan ya ɗanga kina yanayi da Lulun ko idan yasha cocaine ɗinsa na faɗa masa banza wofi ya jajubeki, yana dawowa hayyacinsa kuma a ƙare da bala’i maybe ma ki samu tsabar duka…
Ko sau ɗaya bai kula Asim ɗin dake fece shi game da nacinsa akan Lulun ba. Sai ma miƙewa da yay yayi shigewarsa toilet ya bar Asim ɗin na cigaba da masa hayaniya….

__________★

Sosai abubuwa sukama Lulun yawan da har tace bazata bi Daddy ba ta fasa. Lallaɓata ya dinga yi har taso fara tsarguwa sannan ya taƙaita. Daga ƙarshe dai ta ce zataje ɗin kodan takardun nan da take son ɗakkowar. Taje gidan Uncle Yousuf suke maganar da aunty Saliha. Murmushi kawai aunty Saliha tayi dan tasan da tafiyar dama a bakin Uncle Yousuf da baya ƙasar. Wasu abubuwa ta haɗa ma Lulu wai na gyaran jiki. Bata kawo komai ba ta amsa dan yanzu ta dage da irin abubuwan gargajiyar nan ganin sun amshi fatarta da ƙyau. Ga kamshin da yanzu ya kama jijinta kuma duk dai irin haɗin su khumra data raina a da ne. Koda ta dawo gida batayi wasa da su ba, yayinda Mommy ma a kaikaice take ta bata nata sirrikan. Hatta da iya Tabawa ba’a barta a baya ba. Da ga ita sai AA zata wuce. Taso suje da Ummita amma Daddy yace ta bari sai da ga baya, idan ma harda iya Tabawa take so duk zai haɗo mata. Dariya tayi da faɗin, “Haba Daddy sai kace wadda zataje zama. Su bari kawai mu dawo danni ko Aliyu da zaku bari a gida zan barsa”.
“A’a bazai yiwu ba kije da shi shima ya huta. Tafiya babu abokina ai bazai mun daɗi ba”. Yay maganar yana lakace hancin AA dake tsale-tsalle a jikinsa. Murmushi kawai Lulu tayi daga haka suka cigaba da shirinsu musamman ma shi AA da komai sai an masa.

*_UK LONDON_*

Tafe yake a nutse kan ƙafafuwan sa. Da ka gansa kaga tsayayyen mutum mai cike da jatumta da lafiyar gaɓai. A komai nashi babu hayaniya babu ɗagawa duk da wasu kan fassara shiru-shirunsa da girman kai tun bai zama wani ba. A duk sanda yake da uzuri na fita ya kanfi buƙatar takawa da ƙafarsa in har wajen da yake son zuwan babu nisa. Kamar dai yau da ya fita zuwa shopping na ƴan abubuwan buƙatarsa. Ya riga da ya kai wani matsayi a yanzu da fuskarsa ta zama ba ɓoyayya ba musamman a cikin birnin London. Hakan yasa a duk sanda yake da buƙatar irin fitar nan yakan sakaya fuskarsa da abinda zai ɓadda masa kamanni. Kamar dai yau, ya saka facemask da glasses, ya kuma ɗaura p-cap duk dai cikin son kaucema idanun jama’a dan yaje ya dawo batare da kowa ya damesa ba. Alhmdllh har ko yaje ya dawo babu wanda ya ganesan, garama a cikin mall ɗin da yaje biyan kuɗi kasancewar dokace sai anga fuskarka da yaja nurse mask ɗin ƙasa mai cire kuɗin ɗin ta wani zaro ido bakinta a washe zata ambaci sunansa yay mata murmushi da mata alama zip abaki. Dole tai shiru amma murmushi da farin ciki yaƙi barin fuskarta, har da ɗan leƙensa da zai wuce, sai da ya fice gaba ɗaya take faɗama sauran ƴan uwanta da ke wajen harda masu cewa basu yarda ba. Wasu kuma suka biyo bayansa. Ya riga ya zargi za’a iya yin hakan dama sai yana fitowa ya canja hanya. Wannan yasa suka sake tabbatar mata basu yarda ba. Ba komai ya sasu jin basu yardan ba sai dan mall ɗin nasu ƙarami ne, a ganinsu Smart Mawashi yafi ƙarfin zuwa nan yin shopping. Irinsu ma sunfi son yin online shopping a manyan mall ai.
Ɗayan hannunsa da babu kaya ya fiddo da ga cikin aljihu wandonsa ya saka security ɗin ƙofar. Sai da computer ta ambaci sunansa sannan ƙofar ta buɗe kanta a hankali. Numfashi ya ɗan furzar yana tura kansa cikin gidan bakinsa da sallama duk da yasan shi kaɗansa ne a gidan nasa. Tuni ya samu canjin wajen zama. A inda yake nan gida ne shi kaɗai a ciki madaidaici mai ƙyau da tsarin birgewa, dan yana ɗauke da abubuwan more rayuwa da ɗan adam kan buƙata koda da sha’awa ne. Ya cire takalmansa a inda yake ajiyewa yasa slippers na zaman gida, tare da hanging rigar sanyinsa sannan ya ƙarasa shiga. Ya ɗan bi falon da kallo ganin fitila a kunne ga wani baƙon ƙamshi, sai dai bai kawo komai a ransa ba ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe bakinsa tunda yasan dai bayan Uncle Yousuf da yasan security ɗin gidan babu wanda zai iya shigo masa, sai ko Ahmad, maybe ya manta ne da zai fita bai kashe fitilan ba. Kayan shopping ɗin nasa ya kai duk inda ya dace sannan ya nufi bedroom ɗinsa hannunsa riƙe da jacket ɗinsa da ya zare ya ɗan sagalota a kafaɗa. Tafiya yake a hankali kamar cikin kasala da gajiya yana latsa waya da alama akwai abinda yake sonyi ko kira. Cikin rashin maida hankali ya tura ƙofar ɗakin da ƙafa ya shiga tare da sake turata da ƙafa ya rufe. Dai-dai nan take fitowa daga Bathroom sanye cikin rigar wanka pink da tazo da abinta. Sosai gabanta ya faɗi da ganin mutum ya shigo mata kai tsaye a inda batai tunanin ganin wani ba, duk da tun shigarta bathroom ɗin ta shiga halin tsarguwa amma ta dake. A bedroom komai need yake babu tarkace babu abinda aka bari a waje da zaisa ka zargin akwai mai amfani da ɗakin sai a toilet ɗin ne, sai dai wani tunani da yazo mata ya sata gamsuwa tai wankanta hankali a kwance.
“Who are you Man?!”.
Ta faɗa cikin faɗa da son dake razanar da tayi. Shi kansa gabansa ne ya faɗi, ya ɗago da sauri dan yasan bai bar kowa a gidansa ba shi dai, amma sai ga muryar mace a tsakkiyar kansa a cikin ɗakin barcinsa bama falo ba. A karo na biyu ƙirjinsa yay wata irin jijjiga ganin wadda bai zato ko tsammani ba, wayarsa da ke neman suɓuce masa a hannu yay saurin damƙewa, sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan gannin tayo kansa da masifa hannunta ɗauke da wani deco.. da ke ajiye a bedside drawer ɗinsa. Duk da yana a cikin yanayin ruɗani sai da ta so bashi dariya amma ya dake, yo abinda ta ɗakko ɗin ko buga masa tayi mizai ji duk da glass ne. Tana gab da zuwa ina yake ya ce, “Please Relax Ladyy”.
Cak taja ta tsaya zuciyarta na harbawa da masifar ƙarfi dan ko’a magagin barci wannan deep voice ɗin bazata layance mata ba. Cikin rawar lips da ta murya ta furta, “Aliyu!”.
Idanu kawai ya zuba mata ta cikin glasses ɗinsa na kusan sakanni talatin, kafin a hankali ya kai hannu yay ƙasa da mask ɗin fuskarsa tare da zare glasses ɗin. Idanun ya lumshe a hankali tare da sake buɗewa yana mai kamo gefen lips ɗinsa da haƙori. Kallon nasa da yanda gaba ɗaya ya canja fiye da ganin datai masa a lokacin haihuwar AA a Canada ya sata jin kamar jiri na neman kwasarta zuwa ƙasa ne ma. Shima yana jin fiye da abinda take ji ɗin, sai dai ƴan mazan a tsaye suke banda a ƙwayar idanunsa bata iya hango komai da zata iya bama fassara. Son tabbatar da ba aljana bace ko mafarkin da ya saba harta fara masa gizo ya sashi kauda idanunsa a kanta ya fara waige-waige. A saman gadonsa ya hango abinda yake neman a kwance yana barcinsa da alama ya gaji dan yayi wani baje-baje da ƴan kafafu da hannuwa yana zuƙar iskar sabuwar ƙasar Babansa da fesarwa cikin kwanciyar hankali. Karo na farko ya saki murmushi ganin wanda ya bari a jinjiri ya fara zama mutum, dan girman jikin AA yafi watanninsa yawa kasancewar ya ɗakko har tsawo irin na gida. Duk wanda ya kallesa yasan su ɗin jini ɗaya ne dan kamaninsa sun sake bayyana kansu matuƙa a tattare da yaron. Lulu da ke jin wani yamm-yamm kamar zata zube ƙasa a hankali ta furzar da iska mai nauyi tare da jan jikinta baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna cikin dafe kai. Wato ta fahimci Daddy da Uncle Yousuf wayo sukai mata kenan kawai. Shiyyasa taita fama da shi su fara zuwa U.S amma ya dage su fara zuwa UK yana da abinda zaiyi mai muhimmanci. Takun sawayensa ya sata kallonsa ta gefen ido, ganin kamar inda take yayo ya sata ɗagowa sosai tana masa kallo mai kama da harara. Sai kawai ya basar ya wuceta zuwa inda yaronsa yake………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments