Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 39

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣

 

…….Sai dai yana waigawa ta rufe idanun ita a dole barci take. Nasa idanun ya rufe da sakin guntun murmushi ya ƙarasa shiryawa ya miƙe. Wando yasa 3quater da ƴar riga armless yasa turare. Baice da ita komai ba ya fita domin duba mima zai bata taci ne duk da yasan halinta bawai ta damu da abinci bane. Ganin babu wani abinda zata iya so sai kawai yay mata order na gasashen kifi da abinda yasan zata iya so. Cikin abinda baifi mintuna ashirin da biyar ba aka danna bell ɗin gidan. Tashi yay zuwa ƙofar dan yasan abinda yay order ne aka kawo. Shi ɗinne kuwa. Mai kawo saƙo ɗin na ganin shine ya wani washe baki, cike da zumuɗi da farin ciki ya ce, “Smart Mawashi”.
Murmushi Smart yay masa. Shi kuma ya zaro wayarsa yace Please ya bashi dama suyi hoto ɗaya. Kai ya jinjina masa alamar babu damuwa. Ya gyara sukayi sai farin ciki yake yi. Shi kuma ya amsa kayan ya koma ciki. A falon ya ajiyesu ya nufi bedroom ɗin…..

*_NIGERIA_*

Kamar yanda ta saba a ƙarshen kowane wata take sake ƙulla silin zare ɗaya a jikin battar da malamin ya bata game da asirin da taima Smart da Lulu. Yau ma cikin nishaɗinta ta jawo battar hannunta riƙe da farin zaren kirtani tana ɗan raira waƙarta ta barmani coge alamar dai tana a cikin nishaɗi. Dan bayan Aunty Amarya da Ammah ta sanar mawa babu wanda yasan yau Lulu ta koma wajen mijinta a gidan.. Wani irin kwance-kwance ƙirjinta yay ya yanka lokacin da take jawo battar idanunta ƙyar akan zararrikan data ɗaura zube ƙasa a warware. Battar ta tukunyar ƙasa ƴar ƙarama ta wani tsage daga sama har ƙasa. Tana ɗagata ta rabe biyu tsokokin nama biyu da suka wani tsotse a waje guda tsire da allurai suka zube a ƙasa. Ƙara ta daddage ta fasa na tsananin fita hayyaci da tashin hankali batare data farga da ɓaranɓaramar da take neman yi ba. Su Huwaila dake falo suna kallone farkon shiga a ɗakin nata a gigice. Ganinta kwance wanwar a ƙasa babu numfashi ga wata ƴar tukunya-tukunyar tsafi zube a ƙasa harda allurai a jikin tsokar nama ya sasu suma fasa ƙararar data ankarar da su Ammah. Kusan a tare suka afko ɗakin tare da gayyar yaran gidan. Babu wanda idonsa bai gane masa wannan tarkacen tukunya ba idan ya shigo, har Abba da ya shigo a ƙarshe dalilin kiran da Salis yaje yay masa akan tarkacen ya fara sauke ido kafin Ummah dake kwance wanwar ana sheƙa mata ruwa amma babu alamar numfashi tattare da ita.
Wani irin harbawa ƙirjinsa yayi tare da jin kansa ya sara. Yana sake maida idonsa akan Ummah ya ga ta koma masa wata irin mummunar hallita. Da sauri ya kauda kansa yana mai ambaton sunan ALLAH. Yanda yay baya zai faɗi sai da Ammah ta tarosa tana faɗin, “Ya Salam Abbansu yi ahankali”.
Hannun Ammahn ya riƙe yana jujjuya mata kai, muryarsa na rawa ya ce, “Hafsat fiddani a ɗakin nan kaina zai fashe”.
Furucin Abba yasa gaba ɗaya hankalin sauran yaran da su Aunty Amarya dawowa kansa. Sai kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin halin da Abba ke a ciki. Amma mi abin mamaki yana fitowa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya da sakin kan. Kallonsa Ammah tai da faɗin, “Yaya dai Abbansu?”.
Kamar bashi ya gama cewa kansa kamar zai fashe ba ya ce, “Wlhy Hafsat kinji kuma ya saki kamar ba’ayi komai ba.” Sosai abin ya ɗaure kanta. Bata gama fita a mamaki ba kuma sai ga yaran na fitowa da ɗaɗɗaya hannayensu dafe da kansu. Wasu ma a guje suke faɗin, “Dodo! Dodo!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya gama rikicewa. Kowa ya fito a ɗakin Ummah, da kuma sun fito sai su jisu sakawai kamar an zare musu komai. Umma da hayaniyarsu ta sakata farfaɗowa cikin tashin hankali tabisu da kallo ganin yanda suke fita a guje. Ganin babu kowa sai taga damace ta sameta ta tattare kayan nan. Da sauri ta tattarasu jikinta na mazari ta ɗaure a ɗan kwali ta tura ƙarƙashin gadonta. Sannan ta fito cikin ƙarfin hali. Tana sakko ƙafarta waje yaran suka shiga yanka ihu suna kwasa da gudu zuwa ɗakunan iyayensu da faɗin, “Wayyo Umma ta zama dodo! Ummah ta zama dodo!”. Ba yaran kawai ba sai ga su Aunty Amarya suma duk sun rufta ɗakunansu. Abba ma har tuntuɓe yake na barin wajen sai Ammah ce ke kallonta da ambaton addu’oi a bakinta. Dan itama kam yanzu a wata irin mummunar siffa mara ƙyan gani tane kallon Ummahn.  A nutse ta nufi nata ɗakin itama aka bar Umma ita ɗaya a tsakar gida cikin tashin hankali da mamaki. Sai kallon jikinta take taga minene sukema gudu amma bataga komai ba. A take jikin nata ya kama rawa. Ɗakinta ta koma ta jajibi waya tai kiran Hajiya Naqiba….

*_★UK★_*

Cikin mamaki Smart ke kallon Lulu da ta buɗe gasashen kifin ta maida ta rufe da sauri fuskarta a ɗan yamutse. Dan shi dai a sanin da yay mata tana son kifi sosai. Shi kam baya so, dan ko a yanzu haka dauriyar shaƙar ƙamshinsa kawai yake yi. Da farko yayi tunanin halin nata ne ya motsa, sai ya so ɗauke kansa. Amma ganin yanda ta tura baki da faɗin, “Nifa bana cin kifi yanzu” ya sakashi zuba mata idanunsan nan.
Cike da shagwaɓa ta ce, “Ni ka daina kallona da wannan idanun”. Ƙaramin murmushi yayi da janye idanun nasa, da kulawa ya furta, “Yaushe kika daina cin kifi kuma Madam?”.
Harararsa tai saboda Madam ɗin da ya kirata da shi, sai ya riƙe kunnuwansa alamar sorry. Mikewa tai tana ƙara tura bakin. Hannunta ya riƙo da sauri dan yasan kaɗan daga aikinta tace zata koma bedroom ɗin da da ƙyar ya samu ta fito. Saman cinyarsa ya zaunar da ita, cikin lallashi kamar wata ƴar yarinya ya ce, “Faɗa min yaushe kika daina cin kifi?”.
A ɗan tunzure ta ce, “Da cikin ɗanka”.
“Woow really?!”.
Kanta kawai ta jinjina masa da yunƙurin tashi ya hanata damar hakan yana dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Oh oh like father like son. Babie luv anya akwai wanda ya kaini sa’ar nasara a ƴakin ƙasa da ƙasa kuwa?”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa tana kallonsa a karo na farko. Gira ya ɗage mata tare da kwantar da kasa a kirjinta ya ce, “Aliyu ɗan Aliyu a suna. Aliyu ɗan Aliyu a kamanni. Aliyu ɗan Aliyu a hallaya. Ya kamata ki bani Award na gwarzon shekara ALLAH kuwa.”
Ƙoƙarin ture masa kai take ya riƙe hannun, cikin mamaki ta ce, “Wai dan ALLAH yaushe ka lalace haka Aliyu? Ko abinda zama cikin turawan ya koya maka kenan kai?”.
Idanunta da suka canja launi ya ɗago yana mata wani irin narkakken kallon da ya sanya jininta da tsigar jikinta yamutsawa a lokaci guda. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kece kika lalatani fa Mawaddatan’warahmah.”
Da sauri ta waro manyan idanunta a cikin narkakkun nashi. “Ta yaya?”.
Bakinsa ya kai dai-dai kunnenta ya raɗa mata maganar data sakata jin inama kasa ta tsage ta shige kawai. Dan a take ta wani daburce ta shiga kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen ya shiga ƙoƙarin riƙewa yana dariya. Har sai da ta kai shi da kaiwa kwance a kujerar, bata barshi ba ta bisa tana a saman jikinsa ta cigaba da mintsininsa shi kuma yana tarewa da faɗin, “Wayyo fatana da zafi fa ban san mugunta baby luv”. Yanda taga yana ɓata fuska alamar zafin dai yake ji da gaske duk da bada wani ƙarfi take masa ba ya sata fara dariyar itama. Abu mai wahala ga Lulu kenan, kaga tana dariya haka tab ɗin, ai ko murmushi sai a inda taso ga kuma wanda taso. Gaba ɗaya ma sai ya shagala ma shi yana kallonta tamkar ya samu television.
Dariyar ta daina yi ganin yanda ya zuba mata mayatattun idanun nasa da gaba ɗaya suka canja launi da ƙanƙancewa, sai dai murmushi bai bar fuskarta ba, ta ɗan lakace masa hanci da ɗage gira ta ce, “Kallon fa?!”
Idanun ya lumshe a hankali da sake buɗesu a kanta, “Dariya na miki matukar ƙyau my heartbeat”. Ya faɗa cikin wata irin murya mai laushi da sanyi. Samun kanta tai da lumshe nata idanun itama tana ɗan kauda fuskarta gefe da ƙoƙarin sauka a jikin nasa. Hannunta ya riƙo ya dawo da ita ta kwanto jikinsa fiye da farko, fuskarsu gab-gab da juna suna musayar numfashi. A hankali ya sake faɗin, “Kada ki sake barina dan ALLAH. Ina azabtuwa matuƙa Mawaddatan’warahmah. Wlhy kece farin cikin Aliyu, kece bugun zuciyarsa, kece sanyin idaniyarsa, bayan mahaifiyata bana jin na taɓa jin wata mace a cikin jinin jikina da komai na sama da ke. Ki bani dama koda ƴar karama ce domin tabbatar miki da hakan Pleassseee!”.
Wani irin luuuu tayi da idanunta ta lumshesu, sai kuma ta sake buɗesu a kansa. Cike da basarwa ta kai yatsanta saman lips ɗinsa ta fara zagayawa. “Dama kai ɗan ƙwallo ne?”. Ta faɗa cikin basar da zantukansa. Idanunsa da ke rufe ya buɗe a kanta. Jan ajinta na sake rikita masa lissafin rayuwa, ya ce, “Humm!”.
Gira ta ɗaga masa kaɗan tana wani cije lips da jan hancinsa. “Miye wani Hummm amsa nake so da baki?”.
Kauda fuskar tashi ya ɗan yi gefe yana murmushi, kafin ya sake maido idanunsa a kanta da ɗan juyasu alamar tunani. Sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe baki kaɗan ya furta, “Tun ina yaro ma”.
“Uhhyim! Shine ka zama kuma driver?”.
“Ƙaddarata ce wannan”.
“Bani labari to”.
Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Ba yau ba amma?”.
“Miyasa?.”
“Saboda ina da abinda yafi labarin muhimmanci. Ango fa nake ki tausayawa min? Niba ɗan jarida ba na ƙare da bada labari haba ai ace min ma shakatafi”.
Kalmar shakatafin ta bata dariya, dan haka ta murmusa har haƙoranta na bayyana. Ta ce, “Miye shakatafin? Ni Bama gane manya-manyan hausar nan naka suna yin girma da yawa”.
“Oh kefa na manta rabi da rabi ce baki cika bahaus”.
“Kai ka rabani ɗin ko?”.
“Inba ni ɗin ba waya isa kaiwa ga wannan aikin”. Ya faɗa cikin fassara maganar tata da wata siga daban.
“Kai kana da matsala ba’a hirar arziƙi da kai. Sakeni naci abinci na fara jin yunwa”.
“Sorry na daina ayi hirar arziƙin. Abinci kam nan kawai ya isheki ƙoshi yau ai”. Ya ƙare maganar da nuna lips ɗinsa.
“Lips ɗinne kuma ya zama abinci?”.
“Sosai kuwa, kona gwada miki”.
“A’a na yafe girmana bai kai can ba”. Ta faɗa tana ƙoƙarin sauka a jikinsa………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 39"