Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 41

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣

…….Al’amarin Umma kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba. Dan ita kanta tun tana ɗaukar abun matsayin ba komai ba sai gata ta fara hawaye cikin tashin hankali. Dan kuwa dai ƙawarta Hajiya Naqiba tazo, amma tana shiga ɗakin nata itama da gudu ta dawo tana ihu mai firgitarwa da yafi na jama’ar gidan. Hankali tashe Umma ta biyota tana faɗin, “Na shiga Uku ni Yaha, Aminiya kema ɗin abinda suke min zaki min? Wai mina muku ne haka kuke irin wannan firgita da ni? Dan ALLAH ki faɗamin Aminiya kar ki min yanda suke min kema”.
     Ina Hajiya Naqiba ba sauraren Umma take ba. Ihu kawai take kwarawa da iya ƙarfinta har maƙwafta da mutanen waje na iya ji, daga ƙarshe ma ta yanke jiki ta faɗi a sume dan Ummah taƙi daina binta. Cikin tashin hankali Umma ta isa gareta ta na jijjigata, a dai-dai nan mutane suka fara shigowa gidan da ga waje hankali a tashe. Ai sai ga maza na dafe huluna suna juyawa a guje. Duk wanda ya shigo yana tozali da Umma rungume da Hajiya Naqiba sai ya afa da gudu ya juya. Ba matan ba ba mazan ba ba yaran ba. Cikin ƙanƙanin lokaci zance ya zagaye anguwa. Masu ƙarfin hali na cigaba da shigowa domin tabbatar wa. Sai dai fa babu fashi duk wanda ya shigo zai juya a gujensa yana ihu da faɗin “Wayyo Dodo!! Wayyo dodo!!.”
       Umma da ke zubama hajiya Naqiba ruwa tana kuka dan ganin abin da bana lafiya bane ta zabura jin aminiyar tata ta sake fasa gigitacciyar ƙara. Dan tana farfaɗowa taci karo da ita a kanta. Yin ƙurin da zatai domin ceton ranta ƙafa ta gurɗe jikake ɓass kamar an ɓalla katako ba ƙashi ba. Sai ta sake zubewa a ƙasa cikin wata irin wahalalliyar ƙarar azaba ta sake sumeya. Duk da abinda ke faruwa kaf ƴan gidan na maƙale ta windows suna kallo har ƴaƴanta da suka rarrabu. Wasu a ɗakin Ammah wasu na Mama. Ita dama aunty amarya da yaranta ɗakin Ammah suka afka suma. Ammah da al’amarin ya jijjiga ma zuciya na zaune a kujera tana cuɗawa da kwancewa. Dan in har lissafinta yayi dai-dai ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya fa a wannan karon. Tukunyar da suka gani tarwatse a tsakar ɗakin Ummah itace asirin da taima su Aliyu matarsa ke ganinsa da mummunan siffa irin wadda suke ganin Umma da ita a yanzun. Abba ne yay hikimar kiran yaranta na ma’auri da su Salim yace suzo babu lafiya. Dan shikam yama rasa ina zai kama a wannan lamari. A yau dai ya sake tabbatarwa Umma na bin bokayen tsubbu, kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya mai kamanceceniya da juna akan al’amarin Aliyu da matarsa da wanda Umma ke’a ciki yanzu. Yau matar Aliyu ta koma wajen mijinta, hakan na nufin komai ya daidaita tsakaninsu asirin ya dawo inda aka aikashi. Dama ai sharri ɗan aike ne, idan ya isar da saƙonka sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Har zai kira Smart sai kuma ya fasa cikin girgiza kai dan a yanzu ya tabbatar dare ne a UK.
      Yaran nata ma koda suka iso duk wanda yay tozali da Umma sai gudun ceton rai. Umma ta fashe da kuka da tun ɗazun take irinsa har muryarta ta dishe. Ga aminiyarta kwance ƙafa sai kumbura take kowa ya kasa zuwa a taimaka mata saboda Umma da ke a wajen. Al’amarin dai sam babu daɗi, Umma na cikin tashin hankali fiye da wanda al’umma ke ciki akan ganinta a mummunar halittar da kowa ke ganinta. Ita kuma lafiya Lau take kallon kanta, dan har ɗaki ta nufa ganin kanta a madubi babu wata damuwa ko tawaya tattare da halittar ta sai fuskarta datai kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka ɗauke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi masifar kumbura damm abin zattashin hankali……

           *_UK_*

    
      Wahala iya wahala Lulu tasha a wannan dare hannun Smart. Dan zata iya rantsewa ita kam bata ga banbancin sa da daren farkonsu ba, kodan ta saka ma ranta tsoron al’amarin ne oho. Amma tabbas ko a yarda da ita ko kar a yarda Smart namijin gaske ne da ko’a cikin mazan ma zai iya amsa sunan mazaje ne. Sai dai bata sani ba ko ragwantakarta yasa take masa irin wannan kallon ko kuma dan shi ta sani bata san sirrin sauran mazan ba.
         Shi kansa sai da ya koma tausayinta, dan magana ta gaskiya fa bai raga mata ba, wahalarsa ta kusan shera ɗaya da wasu watanni sai da ya fanshe abinsa tsaff. Sai dai kuma shi a karan kansa bashi da zaɓin da ya wuce hakan. Bai sani ba ko tsananin begenta da yake a cikine ya sashi jin yau ɗin babu bambanci da wancan daren da ya kasa goguwa a zuciyarsa, amma ako ina kam zaiyi alfahari da baiwa irin ta matar tasa. Dan a wancan dare shima sabo yake, yau kam ya banbance tsakanin aya da tsakkuwa. Ya kuma zaɓi yimata mai gana ɗaya ne dan cire mata tsoron nan da ya lura yay mata tasiri. (Humm gyaran su iya Tabawa bai faɗi a banza ba kenan🥱🤣🚴).
        Langyare iya langyare, raki iya raki yasha shi. Kuka kam muryarta har bata fita. Tun ana bashi haƙuri da roko da magiya har dai aka koma kiransa mugu. Yaƙushi da cizo duk ya samu rabonsa kafin duk wani ƙarfinta na neman ceton kai ya ƙare ta koma zallar hawaye da jiran mala’ikan mutuwa (acewarta🥱😜😂).
       Shi ya fara farkawa lokacin da alerm ɗin da ke tadashi sallar asuba ya kaɗa. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da ke jingim da barci dan basu wani jima da kwanciyar ba. Hannu ya kai ya kashe alerm ɗin gudun kar AA ya tashi shima. Tunda ALLAH ya taimakesa dai har ya gama bidirinsa na daren jiyan yaron bai farka ba. Idannunsa ya zubama fuskar Lulu dake barci kamar a wahale, shi sai ma ta bashi dariya, dan haka ya ɗan murmusa da kai hannu ya shafa fuskar tata. Baki fal tsiwa da rashin ragiya amma sai tosoro da ragwantaka uwa farar kura. Ɗumin da yaji a fuskarta ya sashi jan bargon kaɗan yasa hannunsa a wunyanta. Zazzaɓine sosai a jikin nata kam kamar yanda yaji. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe da sumbatar goshinta yana sake matseta a jikin nasa cike da tausayawa.
      “I’m so sorry Final Choice. Aliyu bazai sake baki wahala ba da ga yau kinji”. Ya sake kai mata sumba a saman hanci yana mai sake jinta sama can ƙololuwa a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya samu ta tashi sai faman langyare take masa da kukan shagwaɓa. Shi dai biye mata yake yana binta da lallashi. Dan ko a wancan karo na farko ba’ai masa wannan langwai ɗin ba. Koda yake wancan ana bori yaushe ma ya samu kanta. Dan haka yau kam ya ƙudiri aniyar rama mata dukkan tattalin da bata bashi damar yimata a waccan ranar ba. Yanzun ma taimaka mata yay ta sake ɗan gaggasa jikinta, duk da dai yasan taimakon da yay mata jiya kawai ya wadatar, yasan kam harda raki da ragwantaka dai koma yace shagwaɓa. Shine ya jasu salla yanzu ma, suna idarwa ya miƙe ya fita, bai jima ba ya dawo ɗauke da kofin tea da soyayyen ƙwai. Da ƙyar ya samu ta sha tea ɗin, kwan ko bata ko kallesa ba balle ta ci, sai maidashi yayi. box ɗin magungunan sa ya ɗauko ya bata na zazzaɓi tasha da rage raɗaɗi. Sai da ya ga ta sake komawa barci ya sauke ajiyar zuciya. Yasan koyaushe AA zai iya tashi shima, dan haka ya haƙura da fita ko’ina motsa jiki ya ɗan yi a gida. Ilai ko bai jima da farawar ba AA ya farka. Rarrafawa yay kan Lulu yana kuka. Hakan ya sakata farkawa. Harararsa tayi, itama kamar zata saki kukan ta ce, “Ni bazaku kasheni ba kai da ubanka wlhy. Kai tayi idan ya jika yazo ku ƙarata”.
       Kaf a kunnen Smart dake shigowa, dan haka ya saki murmushi yana ƙarasowa ciki. Tana jin motsinsa ta maida idonta ta rufe kamar barci take. Nanma murmushi yayi kawai da ɗaukar AA dake neman yimasa ƙiwa kamar jiya. Tsaff yama yaron wanka duk da dai da ƙyar akasha, dan sau kusan biyu yana neman suɓuce masa ALLAH dai ya kiyaye baisha ƙasa ba. Ganin kamar yunwa yaron keji yay zaman fara bashi tea da dama ya haɗo ya ajiye tun ɗazun kafin ya shiryashi yana nishi da ƙyar dan bai iyaba. Pampa’s ma da ƙyar aka iya sawa sai da ya duba a net.. yaga yanda akeyi. Duk kuma abinda sukeyi Lulu na kallonsu dariya kamar ta kasheta amma ta zaɓi yin likimo wai ya ɗanɗana yaji shima idan da daɗi. Shiko a zatonsa barci takeyi, sai da ta kasa riƙe dariyarta dai tayi sannan ya farga idanunta biyu. Cikin kalar tausayi yake kallonta da faɗin, “Yanzu nan idonki biyu aketa wannan dambarwar amma babu ko taimako Baby luv?”.
         “Ku ƙarata nima ta kaina nake”. Ta faɗa tana masa gwalo da jan bargo ta rufe har kanta. “Haka kikace ko? Ba komai zamu rama ne ai”. Bata sake magana ba tai luf a bargo abinta tana dariya har suka kammala ya hawo gadon da yaron yana sauke numfashi ɗaɗɗaya. Sauka da ga jikinsa AA yay zai haye kan Lulu ya riƙoshi yana faɗin, “A’a Sweet heart abar Momy ta huta kaga Papa ya koya mata karatu duk ta jikata”.
       “Yaushe ka koyamin karatun?”. Lulu da bata fahimci inda ya dosa ba ta faɗa tana buɗe kanta da sauri harara idonta kamar zai faɗo. Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya ya ce, “Yanzu ma malamin a shirye yake in har za’a barsa ya ƙara ɗora sabon darasi”. Yanzu ne ta farga da inda zancensa yaya dosa. Bargon taja ta sake rufe kanta da faɗin, “ALLAH dai ya shiryeka Aliyu. Ni kutashi ku fita barci nake son yi kun daman”.
       “Amin ya rabbi tunda addu’a aka min. Amma fa babu inda zamuje muna nan tare da ke”.
     “To ku koma ƙasan carpet kun ishan ALLAH”.
             “Anƙi ɗin”.
        Harararsa tai shi da ɗan nasa ta matsa can ƙarshen gado ta sake jan bargo dan da gaske jikinta ciwo yake mata sosai, ga zazzaɓi. Murmushi yayi da binta da kallo, dan yasan da gaske bata da lafiyar, yana mata hakane danta saki jikinta dai ne kawai. Wasa ya cigaba da yima AA dake son shi kawai a saukesa yayi ɓarna, sai da ya tabbatar tayi barci ya ɗan janye mata bargon da ga kan fuska danta samu iska. Goshinta ya taɓa yaji da ɗan sauƙin zafin, sai kuma ya maida kan wuyanta. Shima dai alhmdllh ya fara sauka. Sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciya……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 41"