Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 47

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣

…….A gidan Alhaji Garko kam ALLAH ya sauki amarya lafiya, ta silloɓo ƴan biyunta duk maza har guda biyu masu kama da Baba Garko da ƴan uwansu. Farin ciki a wajen Baba Garko da ma’aikatan gidansa ba’a magana. Babu ko ɗar balle jin kunya ya ɗaga waya yay kiran Dada a farko. Rabon da ya kirata a waya harta manta a rayuwarta, duk da halin da take ciki jikinta har rawa yake wajen ɗauka. Dan addu’a take a ranta ALLAH yasa baƙar dagar ce ta mutu ita da cikin. Sai dai me tana kaiwa kunne kalma ta farko da ga bakin mijin nata, abin sonta da sukai ƙuruciya ga su a tsufa tare itace, “Alhamdullahi ALLAH ya sake azurtani da yara biyu MAZA masu kama da ni kamar sauran ƴan uwansu. Sai ki shirya kayan tarbar sabbin ƴaƴa Hajarah”. Da ga haka ya yanke kiran kamar dama da gayya yayi, hakan yay dai-dai da tsayawar numfashin Dada da tunda ya fara maganar yake fita dama a fisge. Yaraf ta sulale a wajen ta zube babu numfashi…..

(🥱DADA team sai ku kai ɗauki🚴).
       _________★

    Kamar kullum pharmacy ɗin cikin hada-hada da kai-kawon mutane yake. Dan babban pharmacy ne da duk kalar maganin da kake nema ko kayan anfani da ya shafi lafiya zaka sameshi. Ga shi akan babban titin da mutane ke yawaita kai-kawo sosai kuma. Ba sayen ɗai-ɗai kawai suke ba har sari suna badawa wa ƙananun camix ma. Banda ɓoyayyun masu amsar miyagun kayansu da ko yaran shagon ba kowa yasan ana harƙallar ba sai amintattun ciki da masu lura, sai dai kosun luran babu damar magana dan anfi ƙarfinsu.
          Duk da safiyace akwai mutane sosai musamman masu sari. Basu wani damu da jin dirar motocin ƴan sanda ba a ƙofar pharmacy ɗin kowa ya cigaba da abinda yake yi. Sai dai me motocin ƴan sandan na gama dira ta NDLEA suka dira suma har mota uku. Sai a lokacin hankalin mutane ya fara dawowa jikinsu, sai dai kafin yin wani yunƙuri jami’an gaba ɗaya sun rufe ƙofar pharmacy ɗin. Sauran kuma sun afka ciki. Gaba ɗaya mutanen ciki an tattaresu zuwa mota, hakama ma’aikatan an tisa ƙeyarsu cikin store ɗin wajen wasu kuma cikin pharmacy ɗin. Duk tambayar da suke akan su mi sukayi babu wanda ya basu amsa. Jikin Manager ɗin wajen har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran layin oga kwata-kwata ya sanar masa.
     Duk da hankali Alhaji Sadi Dikko Baduku ya tashi da jin wai NDLEA a pharmacy ɗin nasa sai cikin rashin damuwa da gadarar masu arziƙi ya buƙaci yaron nashi ya bama ogansu waya. Cikin jin ƙwarin gwiwa Manager ya nufi wanda yake ƙyautata zaton ogan nasu ne ya kai masa wayar. Kallon sama da ƙasa mutumin yay masa tare da daka masa tsawar da sai da ya zabura. Ba Manager ba hatta shi kansa Alhaji Sadi Dikkon sai da ya zabura. Mamaki da al’ajabin wane ɗan iska ne wannan ya sashi yanke kiran, da sauri ya shiga neman shugaban hukumar NDLEA na Kano baki ɗaya, sai dai har wayar ta gama ring ba’a ɗauka ba. Sake kira yay aka danna masa busy alamar an yankesa. Anan ne fa hankalinsa ya fara tashi, da sauri ya shiga neman number Hon. Nakowa…..

         *_UK_*

    Kasancewar yau bashi da wasa suna nane a gida suna zubama juna taɓara. A yanzu haka zaune Lulu take gaban Mirror Smart tsaye a bayanta wai yana mata gyaran gashi. Yayinda AA yay busy a ƙasa da kayan wasansa cikin kuzari da lafiyar da ALLAH ya bashi. Dan yanzu haka Alhmdllh yana miƙewa har ai taku ɗaya zuwa biyu musamman idan idanun iyayen basa kanshi. Idan ma sun gansa sai ya koma ya zauna kamar dai yanda akasan yara masu koyan tafiya kanyi na rashin son a musu ihu yayinda suka miƙe. A hankali Lulu da ke kallon hotunan Smart a waya ta ɗago idanunta jin kamar ya daina motsa hannun nasa a saman kan nata. Cikin mamaki ta ɗan waro idanunta da faɗin, “Lafiya kuwa? Tunanin mi kakeyi haka?”.
    Shiru babu alamar Smart ya jita, dan sosai yayi zurfi a tunanin nasa. Wayar ta ajiye tare da juyowa tana fuskantarsa, sai da ta riƙo hannunsa cikin nata ne ya sauke ajiyar zuciya. Hannun nasa taja zuwa wajen gado, babu musu ya bita. A bakin gadon ya kai zaune, ita kuma ta tsugunna a tsakanin ƙafafunsa hannayenta dafe a cinyoyinsa suka zubama juna idanu. “Mike damunka haka kake irin wannan tunanin Mr A?”.
      Murmushi yayi a karo na farko, dan ya fahimci a kwana biyun nan bata iya kiransa da Aliyu kamar yanda take yi, ya ɗa furzar da iska kaɗan da kai hannu ya gyara mata gashin da ya sakko mata a gefen ido. A hankali ya furta, “Ba komai fa tunaninki kawai nake yi”.
           Hararsa ta ɗan yi cikin girgiza kai, sai kuma ta marairaice fuska kamar zatai kuka. “Ina kusa da kai ne zakai tunani na. Ni ban kai na san matsalarka ba ko?”.
      “Ke kikafi kowa cancantar sanin matsalata ai Baby luv”.
   “Ban yarda ba tunda gashi ka kasa gaya min. Ni kuma duk sirrina babu wanda baka sani ba”.
       Murmushi ya sake sakin mata da ɗan lakace hancinta. “Nima ai duk kin sani. Dan babu wanda ya kaiki sanin Aliyu a yanzu ciki da bai ɗinsa.”
            “Ni ban yarda ba”.
       “To mi kike son ji?”.
   “Damuwarka”.
Hannunta ya kama tare da ɗagota ya zaunar a saman cinyarsa. Sai ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya. Kusan minti ɗaya suna a haka sannan ya sassauta mata yana kwantar da kansa a kafaɗarta. “Baby luv abubuwane suna neman yin yawa a tsakanin nan. Na fahimci sam gidanmu babu kwanciyar hankali ga kowa musamman ma Abba da Ammah. Suna ɓoyemin ne kawai amma lamarin Ummah na damunsu. Nima da nake anan ɗin yana damuna, shiyyasa nake jin da inada dama zanje Nigeria a tsakanin nan gaskiya. Ga batun mutumin nan, nasan hatsabibine bana wasa ba, zai iya bin hanyoyi da yawa dan ganin ya cuta mana.”
         Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, sai kuma ta saki murmushi da shafa fuskarsa, wasa ta cigaba da yi da gashin ƙasunbarsa a hankali. “Humm ni dai ka kwantar da hankalinka. Na farko dai batun wata Umma ma ka ajiyesa gefe ita ta jama kanta damuwa da ita baida wani amfani. Na biyu mune ya kamata mu kwantarma da Abba hankali shi da Ammah dan suna damuwa ne saboda abinda duk ya faru a kammu akayisa. Sulaiman kuwa shi ba komai bane a yanzu takansa ma yakeyi. Amma kamar yanda ka faɗa kam zai iya yin komai da ga sanda ya farga ruwa ya ƙare masa. Dan haka komai yana buƙatar ayisa cikin gaggawa a yanzu gaskiya”.
        “Kema kinzo da shawara kam. Sai dai kin san kamashi a yanzu kai tsaye bazai yiwu ba duk da muna da hujjoji”.
     “Eh hakane, muna buƙatar gaɓa. Ma’ana a kamashi cikin wani laifi dumu-dumu irin wanda baida mafitar nan. Wannan shine zai sa a cigaba da zaƙulo laifukansa na ɓoye. Shiyyasa ka daure ka barni na koma Nigeria. Aikin nan yana buƙatar fuska da fuska ne fa”.
            A take fuskarsa ta tsuke, babu alamar zai ce komai. Kansa ta ɗaga da ga kafaɗarta tana mai zuba masa idanu. “Wai kai ance maka zan gudu ne. Ina fa gama abinda nakeyi zan dawo ALLAH kuwa. In dai gudu ne kasa a ranka ka ƙaremin nawa yanzu babu sauran wajen ɓuya. Idan ma nace zan barka ai Uncle Yousuf da Daddy sai sunyi farfesuna koma su tauneni ɗanya. Kasan irin matsayin da kake da shi kuwa yanzu a gidan mu. Ai ko Ummita dana sani a baya-bayan nan defender ɗinka ce ta gani kasheni.”
        Kallonta kawai yake shi dai, kafin ya samu damar cewa wani abu kira ya shigo masa waya. Ita ta miƙe zuwa mirror ta ɗakko. Gannin Daddynta ne ta ɗaga tana kaiwa kunne.
    “My Son!”.
Daddy ya faɗa daga can. Cikin ɓata fuska tamkar tana gabansa ta ce, “ALLAH ya soni nima ina da Ammah da Uncle You da Abba da Mommy, ga Baba Garko”.
        Sosai Daddy ke dariya. Ya ce, “Oh oh irin wannan gori haka Mawaddat. To ai ALLAH yasa ma Baba Garkon nawa ne ɗan sammiki nayi. Kinga sai ki ƙarata da iyayenki nima ki barmin nawa da kuma yaro na”.
     Dariya tayi itama da faɗin, “Ai nafa bar maka Daddy ku ƙarata.”
   “To shike nan ƴar albarka. Ki faɗawa mijin naki gamu nan tafe in sha ALLAH. Ina fatan dai yana gidan?”.
         “Lah Daddy wai nan zaku zo? Dama kana London”. Ta ƙare maganar cikin shagwaɓa. Murmushi Daddy yayi da ga can har tana iya jin sautinsa. “A’a yau dai zamu shigo, ina Manchester.”
     “To Daddy ALLAH ya kawoku lafiya, mizan dafa muku?”.
      “Basai kin dafa komai ba ƴar Daddynta. Muda bazamu jimaba ma. Bye bye sai munzo”. Ya yanke wayar kafin tace wani abu. Bata damu ba ta zauna kusa da Smart da ke kallonta tana murmushi. “Mr A dama Daddy zasu zo shine baka sanar min ba?”.
          Murmushi kawai yay mata baice komai ba. Itama sai ta dungure masa kai tana miƙewa. Fita tai a ɗakin zuwa kitchen ta barsa shi da ɗansa…..

      ★Tarba ta mutuntawa Daddy da Uncle Yousuf suka samu, shi Daddy wannan shine zuwansa na farko, Uncle Yousuf kam ɗan gida ne. Sun ci abinci a tare cikin farin ciki. AA na nane da Daddy dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu. Kasancewar ba wani jimawa akai da rabuwa ba bai manta kakan nasa ba. Bayan sunci sun sha sukai zaman abinda ya tarasu. Tsakanin Lulu da Daddy sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya faru tsakaninsa da Sulaiman da Mahaifiyarta. Yanzun ma sai da tai hawaye. Ashe babban kuka na gaba, dan lokacin da suka fara kallon abinda ke cikin camara ba Lulu ba hatta Smart da Uncle Yousuf sai da sukai hawaye. Daddy kam ƙasa kawai yay da kansa yana mai jin kewar matar tasa. Kuka sosai Lulu keyi na fitar hankali da ganin mahaifiyarta. Smart na son lallashinta yarasa yanda zai yi ga surukai. Dole ya hakura ya zuba mata ido sai tissue da yake faman miƙa mata na share hawaye, sai Daddy ne ya sakata a jikinsa ta gefe yana lallashinta. Yau jinta take kamar gata ga mahaifiyarta. Ashe dai haka suke tsananin kama, dan duk wanda ya ganta yasan mamanta yasan itace ta haifi abinta. Suna kama matuƙa tamkar tayi kaki ta ajiye ne. Ƙuruciya kawai Lulun zata fita. Ganin waɗan nan tsiyataku na Alh. Sulaiman ya sa Lulu cewa tanada shawara. Su duka idanu suka zuba mata alamar saurare. Zamanta ta gyara cikin dasashiyyar muryarta da kuka ya ɗasar ta ce,………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 47"