Breaking News

Furar Danko Book 2 Page 48

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣8️⃣

…….“In dai muna son kama mutumin nan ya zama mai ƙarfin da bashi da mafita dolene sai mun haɗa hannu da Baba Garko, inba hakaba ko yazo hannu zai zama a banza ne, kai koda an kaisa kotu ne zai iya kuɓuta ma fa, idan ma an tsallake nan alƙali ya yanke masa hukunci to abokan huɗɗarsa zasu iya cireshi saboda yana huɗɗa ne da manya-manyan shegu na duniya bawai na Nigeria kawai ba. Duk da dai abu ɗaya dana sani ga manyan dilas na waɗan nan kayan a duk sanda sukaga zata kwaɓe musu ko zaka ci amanarsu zasu iya kashe juna. Ma’ana kamar yanda sukeyi akan duk wanda ya so bijire musu, shima ya koyo wannan ɗabi’ar ne a hannun turawan nan. Dan haka dolene zamuyi amfani da matakai uku na salon yaƙin kuma duk masu kamanceceniya da juna. Matakin farko shine Baba Garko, sai kuma kama duk wanda suke zagaye da Sulaiman ɗaya bayan ɗaya, hakan zaisa mu ruɗa masa hanjin ciki da jigata masa rayuwa mu sabautashi a tsaye. Hikimar saka Baba Garko anan itace yanada ƙarfi, sannan a fannin safarar miyagun kwayoyi shi maƙiyinsu ne, zai iya yin komai akan duk wanda hukuma ta cafke ta yanda bazasu taɓa kuɓuta ba. Mataki na biyu zamu ƙullama Sulaiman talala tsakaninsa da abokan huɗɗarsa musamman turawan nan na ƙasar Mexico. Kunsan duk wani shege akan harkar waɗan nan kayan yana ƙasar Mexico, saboda wannan matsalar na zagaye da rayuwarsu fiye da kowa a duniya, kuma nanne Sulaiman yafi safarar kayansa. Na uku dolene mu ɓoye kammu mu duka ta yanda idan muka kunnamasa wuta Daddy zai fara hara har zuwa wani mataki, saboda shi kaɗai yasan yana da camara ɗin nan, mu kuma zamuyi amfani da wannan fusatar tashi ne muyita fidda laifinsa waje ta yanda wasan zai zame masa gaba kura baya sayaki…”
        Su duka babu wanda murmushi bai bayyana a kan fuskarsa ba, domin gamsuwa da shawaranta ɗari bisa ɗari. Albarka Daddy ya dinga saka mata, yayinda Uncle Yousuf ke tayashi. Smart dai na murmushi da binta da kallo ƙasa-ƙasa. Dan ya sake tabbatar da lallai matar tasa ƙwaruwace a lauyanci ashe tasan mutakeyi. Daddy ne yace, “Ni yanzu gaskiya bawani sanin kowa da kowa na cikin kasuwancin nayi ba, inma komai zai mana wahala sai dai wannan”.
      “Shima bazai mana wahala ba Daddy, karka manta lungu da saƙo na sani, nasan manya da yara masu wannan business ɗin, kuma duk da haka zan nemo Nadiya itama, duk da bana jin zata bamu haɗin kai ta ciki sauƙi saboda abinda nai maita a last rabuwarmu, amma zan ƙoƙarta naga na ta dawo gareni saboda nasanta zata iya komai akan kuɗi, dan wannan ita ido ce a garemu tamkar google. A yanzu haka zan iya bada list na wanda wasan zai fara a kansu”.
         Anan ma duk sun gamsu da zancenta, a take kuma ta zana musu sunaye da adireshin wajajen da take sayen kayayyakin, tun daga hannun ƙananan ƙwari har zuwa manya-manyan dila data sani a dalilin abokan huɗɗar nata. Ba kuma wai a wajen Kano kawai suke ba, a faɗin Nigeria gaba ɗaya harma da kasashen ƙetare dake maƙwaftaka da Najeriyar. Sosai Daddy yasha mamakin ganin waɗanda ta zano ɗin, har ma da Uncle Yousuf. Shi dai Smart ba kowa ya sani ba sai ɗaidaiku irin su Hon Nakowa suma dan sun kasance sanannun ƴan siyasa ne. Sai dai ganin sunan MM Atik Kumo ya sashi kallonta. Ta fahimci mi yake nufi, dan haka ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Shima Dila ne ai, ko’a ranar daka ɗakkoni a gidan nan tare da tsoffin nan gidansa ne, sannan shine ya sayar mana da kayan”.
       “Shi wannan ɗin da nake gani simi-simi?”.
     Lulu ta ce, “Humm bakaga komaiba ma, wasu ma dan ban san yanda zan misaltasu bane ku gane saboda sunan banza na sansu da shi, wasu kuma haɗuwar club ne kawai”.
   Babu wanda ya sake iya magana dan sun san a zancen Lulun kam babu tantama…

       A ranar su Daddy suka koma Manchester, dan washe gari suke son tafiya Nigeria su duka biyun, a Abuja kuma zasu sauka domin wucewa da su Twins, dan har Daddy ya nema musu transper zuwa Kano, duk da dai sun so bijirewa ya nuna musu basu isa ba. Har Mommy sai da ta kirashi akan hakan ya nuna mata babu ruwanta, ƴaƴansa ne, yanda yaso haka zai tafi da rayuwarsu. Dama dai da amincewarsa suke aiki a Abujar yanzu kuma yace su dawo gida suyi a gabansa. Jin ya buɗe mata wuta dole ta kama kanta, dan Daddy nada haƙuri, idan aka ƙuresa kuma akwai hayaƙi.
     Tunda su Daddy suka wuce Lulu ta maida Camara ɗin nan abar kallo, sai da Smart ya ga kukan nata yayi yawa ya kwace ya ɓoye, duk roƙon datai masa akan ya bata ƙi yayi. Da ga ƙarshe ma ya ɗauketa suka fita. Wannan ɗan yawon da sukayi ne ya rage mata raɗaɗi da damuwar da take a ciki sosai. Dan basu dawo gidan ba sai da dare ya tsala kasancewar su daren da rana duk babu ruwansu bai hanasu hidimar gabansu. Washe gari ya kwasheta suka sake fita, sune har wajen gyaran jiki da wajen wasan yara aka kai AA duk da shi ba fahimtar komai yake ba. Wannan ɗan busy ɗin ya saka mata nutsuwa ta cire komai a ranta, sai sake duƙufa yima mahaifiyarki addu’a kuma.
      Ahmad yay kiran Smart akan pharmacy da jami’an tsaro dana hukumar NDLEA sukaima dirar mikiya. Inda babu wani shan wahala aka gano na mahaifin aunty Khadijah ne dai, ta kai ma har an kamashi shi da yaran pharmacy ɗin gaba ɗaya. Duk da wasu sun rantse su basu san ana wannan baƙin kasuwancin ba. Sai dai ba’a sauraresu ba an ce sai abinda bincike ya tabbatar… Sosai Smart da Lulu suka tausayama Aunty Khadijah, dan Ahmad yace ana faɗa mata yanke jiki tai ta faɗi a asibiti, yanzu hakama tana can, bama ita kawai ba, zuri’ar gidansu gaba ɗaya suna cikin tashin hankalin al’amarin, dan abunne da babu wanda ya taɓa kawowa a ransa…..

*_NIGERIA_*

   Tako ina komai a hargitse yake. Musamman ma a fanin iyalan Alhaji Sadi Dikkon da aka wayi gari da labaran kamashi, tare da yima babban pharmacy ɗin da sai yau mutane da yawa suka san nashi ne tsirara. Inda aka dinga nuna miyagun kwayoyin dake danƙare a cikin pharmacy ɗin da yanda ake kasuwancinsu a tsawon lokaci batare da hukumomi sun fargaba balle jama’ar gari da basu taɓa kawoma ransu ba. Gaba ɗaya Kano a rikice take da kace nace, saboda Alhaji Sadi babban mutum ne da ke a cikin jerin ƴan kasuwar da ake ji da su a Kanon dama ƙasar ta wani fannin. Sannan sam a fuska bazaka taɓa kawoma kanka zai iya aikata irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.
         
        Alh. Sulaiman na kwance a gidansa hankali kwance, yana ma tsaka da jin daɗin duniyarsa shi da amaryarsa kira ya shigo masa a waya kusan ƙarfe biyun dare. Rai a ɓace ya ɗaga duk da yaga Hon Nakowa ne a kan layi. Sai dai yana ɗagawar furucin Hon. Nakowa ya sashi zabura yana ture matar tasa gefe da lailayo wata gawurtacciyar ashariya mai kawuna goma sha biyu ya dire. Har neman taune halshensa yake wajen faɗin, “Tayaya hakan ya faru? Shi wane sakaci ne ya kaishi ga haka?”.
         “Babu fa wanda yasan yanda akayi, Garko kaima kasan Alhaji Dikko na cikin mutane masu taka tsantsan matuƙa. Kawai dai akwai abinda ya kamata musani, sannan muna buƙatar zaman meeting na gaggawa dan nasan zuwa safiya zasu iya cewa zasu kamashi”.
      “Wane zaman jira zai tsayayi ayi meeting da shi, a daren nan ya sayi ticket ya bar ƙasar nan kawai, idan kuma ya bari suka kamashi to tabbas zai mutu, dan mutuwarsa tafi rayuwarsa muhimmanci a garemu yanzu. Sauran aikin zamu ƙarasa a rufe zance. Dan haka kai kiran su Baita yanzun nan mu haɗu, dan muna buƙatar ganin shugaban NDLEA da IG ma kansa”.
      Cikin gamsuwa Hon. Nakowa yace “Hakan yayi”.
         Alh. Sulaiman na yanke waya idonsa ya sauka akan amaryarsa data zuba masa ido. Wani irin dafe kai yayi da faɗin, “Oh shiitt” dan harga ALLAH ruɗewa tasa ya manta bashi kaɗai bane a ɗakin ya zauna yana sakin zance har haka. A wani irin fusace ya nufeta, babu zato taji ya mata wata irin tsawa da nunata da yatsa. Har sai da ta zabura.
     “Me kika ji?!!”.
Ya faɗa a gigice. Kanta ta shiga girgiza masa jikinta na rawa. “Banji komai ba wlhy Alhaji. Kwata-kwata banji komai ba”.
           “Idan ma kin jin ki ɗauka baki ji ba, idan kuma kikace zaki nuna kinji kiyi kuka da kanki”. Da ga haka ya wuce fuuu zuwa toilet domin tsarkake jikinsa. Tashin hankali na haƙiƙa ta shiga, dan jikinta har rawa yake yi, zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Gaba ɗaya kalaman mijin nata sun ɗimautata, so take tabar ɗakin ko zata samu iska, sai dai babu dama, dan fitar tata zai iya sawa ya zargi wani zataje ta faɗawa. Bata taɓa sanin atsabibancin mijin nasu ya kai haka ba, karo na farko a rayuwarta da taji ashe garama da ALLAH bai bata haihuwa a gidan nan ba..
      Tana a kwancen ya fito, jikinsa duk laima bai damu ba ya saka jallabiya tare da zarar wayarsa da key ɗin mota ya fice. Da kallo kawai ta bishi kamar matacciya, dan ko dogon numfashi bata iyayi saboda tsabar tashin hankalin da take ciki..

        ★A lokacin da su Alh. Sulaiman ke nufar inda zasu haɗu meeting a lokacin jami’an tsaro sukai dirar mikiya gidan Alhaji Dikko dake ƙoƙarin sulalewa ya bar gidan batare da sanin ko iyalinsa ba. Aiko a take sukai ram da shi. Jiniyar motocin jami’an tsaron ne ya fargar da iyalinsa dama ƴan anguwa. Hankalin kowa a tashe, yaran sai kuka suke suna kiran yayunsu a wayoyi, ta hakane Aunty Khadijah da batasan mike faruwa ba tun safe da aka fara tone-tone a pharmacy ɗin mahaifin nata da ita kanta bata taɓa sanin nasa ɗin bane labari ya risketa daga bakin ƙaninta. A wajen ta yanke jiki ta faɗi tana tsaka da duba mara lafiya. Tun a daren Coach da Ahmad suka nufi asibitin cikin tashin hankali. Shine ma ya samu damar kiran Smart suka tattauna bayan aunty Khadijah ta farfaɗo an mata allurar barci mai ƙarfi. Zuwa safiya labari ya ƙara karaɗe ko’ina da ina, yayinda shugaban NDLEA na Kano dama na ƙasa gaba ɗaya suka ƙi ɗaga kiran su Alh. Sulaiman. Hakama IG da CP basu ɗaga musu kira ba. Abinda basu sani ba shine akwai wata ƙullaliya tsakanin gwamna da Alhaji Dikko, yana samun labarin abinda ke faruwa yay kiran CP da shugaban NDLEA na jiha yay musu gargaɗi. Tare da tabbatar musu in suka bari Alhaji Dikko ya ƙuɓuce musu a bakin aikinsu. Sannan Baba Garko ogan Gwamna ne na amana, dan haka yay kiranshi shima akan su IG da shugaban NDLEA na ƙasa. Shi baba Garko dama abune daya tsana a rayuwarsa, yake kuma yaƙi da masu alaƙa da shi, amma sam bai san akwai alaƙa tsakanin ɗansa Sulaiman da Alhaji Sadi Dikko ba sam…
     Matuƙar tashin hankali sun shiga jin an cafke Alhaji Dikko, a take meeting ɗin su ya canja akala zuwa shirya yanda zasu kashe Alhaji Dikkon kawai. Dan sunci alwashin bazasu taɓa barinsa ya tona musu asiri ba. Sai dai dolene suyi komai ta ƙarƙashin ƙasa saboda gujema idon mutane a kansu. Sun nema amintattunsu dake cikin jami’an tsaron, kai tsaye suka basu umarnin kashe Alhaji Dikko ta hanyar guba. Kasancewar suma abokan cin mushen nasu ne sukai na’am da hakan. Dan in dai aiki ya buɗe suma nasu ya buɗe ai……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments