Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 51

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣1️⃣
........ “Gaskiya Umma kin cucemu, haka kawai kin saka mutane zuwa wannan azababben wajen”. Babu dai wanda ya tanka masa a cikinsu. Wani yabiɗaɗɗen tsoho suka samu a saman dutsen jikin bukkarsa. Surutai yake tayi kamar wani zararre, yana ganinsu ya kwashe da dariya. Turus sukai duk suna kallonsa, sai ƙanwar Hajiya Naqiba da tasan haka yake ne ta zube tana masa kirarin da suke masa. Hakan ya sashi yin shiru yana saurarenta, sai da ta kammala ya sake kwashewa da dariya yana ma kansa kirari shima. Sai kuma ya tsuke fuska yana kallon su Abba kamar bashi yay dariyar ba, “To asararru, ku bazaku zube ku kwashi gaisuwar bane wajen waliyyin ALLAH?”.

       “Waliyyin shaiɗan dai. Ubanka ne zai gaisheka matsiyaci haihuwar asara” Salim da hanunsa ke masa azaba ya faɗa a fusace. Kaɗan ya rage Kawu Idi yay dariya ya dai daure. Kawu Jibirin ne ya ɗan girgiza kansa da fuskantar boka na kan dutse. Babu wasa a tattare da shi ya ce, “Muba neman wani abu mukazo wajenka ba. Hasalima baka da wata daraja a idanunmu face kasancewa a gafalalle abin ƙyama”. Ya zaro wayarsa yana nuna masa hoton Ummah, wannan matar tazo wajenka kayi mata aiki akan wasu mata da miji, tare da tabbatar mata asirin idan baici ɗaya a cikin ma'auratan ba zai iya komawa kanta anyi haka?”.

      Dariya nakan tufu ya kwashe da shi harda ƙyakykyewa. Sai da yay mai isarsa kafin ya tsagaita da faɗin, “Shegiyar kaya ai wannan tasan takan mugunta. Dan koni uban gayyar da kaɗan na ɗarata. Sai dai a yanzu haka tana can cikin bala'i hhhhh. Dama mun faɗa mata ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya bata yarda ba hhhhh. Asirin bai kama mijin ba matar kawai ya kama, itama kuma ya saketa hhhh. Dan haka ya dawo kanta kuma bazata taɓa warkewa ba hegiya ta shiga kamun ɗan ƙallau.”

      “Kaima yau zaka shiga kamun ALLAH ai matsiyaci. Ka tsufa har an yayyafa maka gishirin mutuwa a saman kai amma baka san Annabi ya faku ba” Salim ya faɗa yana ɗaukesa da mari. Kafin kace mi ya rufesa da duka. Da ƙyar su Kawu Idi suka riƙesa, zafin dutsen dana ranar yasa suka yayibosa zuwa ƙasa bayan Kawu Idi da Salim sun ɗaureshi. Abba dai ko sau ɗaya baice tak ba. Haka suka jefashi a mota duk da warin jikinsa ma ya ishesu suka ɗauki hanyar Kano. Da yamma liss suka iso, sun sami gida jigum-jigum baka jin komai sai nishin Ummah. Ganin boka na saman tudu ya firgita mutane da yawa. Duk da shi a cewarsa ba boka bane malami ne, dan hatta shigarsa dai ta malam ce sai dai dauɗa da warin rana ba'a magana. Ga Salim ya tunɓuke rawanin tun a can sai ƙwalelen kansa da yasha ƙwal a kwabo.....


          __________★


   A bisa umarnin Lulu Ummita ta shiga binciken gidan su Nadiya ta hanyar yaranta na shagon saloon da yanzu ƙanwarta ke riƙe da shi. Da farko yaran nata sunji tsoro sunƙi faɗa saboda gargaɗin da akai musu. Sai da Ummita ta dinga musu magiya sannan suka faɗa mata gaskiyar a inda Nadiya take yanzu haka. Acan cikin wata tsohuwar makaranta ce da rufunta ya kwaye a ruwan bana. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa da ganin Nadiya duk da bata santa ba kafin yanzu, sai hotonta data gani a wajen Lulu. Tayi baƙi ta lalace sai uban ciki haihuwa yau ko gobe. Wasu ƴan shaye-shaye dake zama wajen ke bata abinci da kayan shaye-shayen. Hankali tashe Ummita ta kira Lulu a video call. Da farko Lulu cewa tai bata yarda Nadia bace, sai da ta fashe mata da kuka cikin ƙarfin hali ta rantse mata cewa itace. Gaba ɗaya sai Lulu ta sake birkicewa da tashi hankali, itama ta fashe da kuka. Da ƙyar ta iya cewa Ummita sukai Nadia asibiti, amma ta kira Uncle Yousuf a waya. Koda Ummita tai kiran Uncle Yousuf ta sanar masa babu ɓata lokaci ya iso wajen shi da ƴan sanda da ambulance. An ɗauki Nadiya zuwa SHIRA'S HOSPITAL. Babu ɓata lokaci likitoci suka rufu a kanta, kamar jira cikin nata keyi dama sai naƙuda ta tashi. Doctors sun tabbatar bazata iya haihuwa da kanta ba, dole akai mata cs. Ana shiga da ita ɗakin theatre Uncle Yousuf ya nema gidan iyayenta. Sai dai koda yaje babu wanda ya sauraresa duk da ya sanar musu tana can a asibiti an shiga da ita theatre basu saurarensa ba. Haka ya baro gidan ransa a ɓace, sai bayan tahowarsa ƙanwarta ta biyosa asibitin a sace bisa umarnin mahaifiyarsu...... (ALLAH sarki Uwa kenan😭🙏).


        *_★UK★_*


       Fuskarsa ɗauke da murmushin zancen Iya Tabawa ya tura ƙofar bedroom ɗin a hankali ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, zuciyarsa cike da ɗokin san ganin sahibar ruhin nasa.. Cak kalaman bakinsa suka tsaya sakamakon tozali da ita zaune fuska share-share da hawaye ta zubama waya idanu...

      “Mawaddatan-warahmah!”.

  Ya kirayi sunanta cikin wani irin salon taushin murya mai amo da ratsa zuciyar mai saurare. A bazata ta ji saukar muryar tasa duk da a tsumayen isowar tasa suke. Dan hatta kwalliyar da taci yau a cikin skert da riga na atamfa da sukai mata ƙyau tayine da shi. Harda kwalliyar da hawayen tausayin Nadiya suka gama batawa. A hankali ta ɗago idanunta da suka kaɗa harda ɗan kumburowa. Sai ya samu kansa da lumshe nasa da sake buɗe su a kanta ya ware mata hannayensa alamar tazo garesa. Babu musu ta taso da ɗan gudu-gudu ta shige jikin nasa ya maida hannayensa ya naɗe a nata jikin. Wani kukan da ya sakashi runtse idanu da ƙarfi ta sake saki tare da ƙara ƙanƙamesa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata tayi kukan ba har tsawon mintina biyu. Sai da ya tabbatar tayi ya wadaceta sannan ya ɗagata cak zuwa saman gado. Kwantar da ita yayi tare da kishingiɗa a gefenta ya tokare hannunsa da tallafo kansa ta yanda zai iya mata runfa. Ɗayan hannun kuma ya tallafo fuskarta ya zuba mata ido. Itama kallonsa take tana jan ajiyar zuciya. Karo na farko ya sakar mata murmushi mai sanyi da saka babban yatsansa ya ɗauke mata hawayen.

       “Waya taɓa Final Choice ɗin Aliyu Mawashi? Maman Aliyu Mawashi? Kin san kuwa yanda nake jin ƙunar zuciya a duk sanda naga hawaye na sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskar nan taki. A gaɓa ɗaya kawai nake son naga waɗan nan hawayen da rakinki, amma ba'a banza haka ba okay”.

      Hawayen ne suka sake ciko mata idanu, a hankali ya shiga girgiza mata kansa alamar kar tayi. Haɗiyesu ta shiga ƙoƙarin yi, sai kuma ta juya ta sake rungumeshi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a goshinta da hancinta ya sakko saman lips ɗinta. “In sha?”. Ya faɗa cikin raɗa yana nuna mata lips ɗinta da yatsa. Murmushi ta sakar masa a karo na farko da hawaye. Shima sai ya murmusa da kai nasa lips ɗin saman nata. A hankali suka lumshe idanu a tare kowanne na sauke ajiyar zuciya, daga haka tsarin ya canja zuwa wani fage daban...


        Yana zaune a bakin gado yana goge jikinsa da ƙaramin towel ta fito itama sanye cikin bathrobe. Idanu ya zuba mata cike da jin ƙarin ƙaunarta da tausayi, suna haɗa ido ta ɗauke nata cikin jin nauyi. Wucesa tai niyyar yi ya riƙo mata hannu. Batare data juyo ba ta furta, “Zan shirya ne fa na haɗa maka abinci”. Murmushi yayi da jawota baya ya zaunar a saman jikinsa. Cikin kunneta ya raɗa mata maganar da ta sakata jin rikicewa dan kunya, shiko ya shiga darawa abinsa. Tashi tai zumbur a jikinsa ta gudu zuwa gaban mirror tana murmushi da faɗin, “Ni dai babu ruwana wlhy”.

        “Daga baya kenan yarinya”. Ya bata amsa yana tasowa zuwa gaban mirror ɗin shima. Da jikin mirror ɗin ya jingina, hakan ya basu damar facing juna. “Miya sakaki kuka?” ya jeho mata tambaya dai-dai tana ƙoƙarin warware gashinta data naɗe a cikin ƙaramin towel. Numfashi ta ɗan firzar a hankali idanun nata na sake cikowa da hawaye, murya a raunane ta ce, “Nadiya ce”.

    “Nadiya kuma? Who is she?”.

“Ƙawata ce, sai dai bama tare yanzun”.

“Ya akai banji sunanta a labarinki ba?”.

      “A Nigeria na santa ai, kaima kuma ka santa ma. Dan ka taɓa kai ni shagonta saloon”.

           Cikin ɗan yin jimm na alamar tunani ya ce, “Okay na gane, ba itace kikace zata taimakemu ba?”.

    “Yes ita”.

“Uhmum miya faru da ita?”.

Wayarta ta ɗauka ta miƙa masa. Amsa yay ya duba. Recording ne na video call da sukayi ita da Nadiya. Shi kansa da farko bai ganeta ba. Al'amarin ya girgiza shi da bashi tsoro. Jiki a sanyaye ya miƙa mata wayar batare da ya iya furta komai ba. A bazata Lulu data sake fashewa da kuka ta ce, “Aliyu nagode da ƙoƙarin ka a kaina, bani da abinda zan iya biyanka da shi a duniyar nan face na dawwama ina maka addu'a har ƙarshen numfashi na kai da Uncle Yousuf. Yanzu nima da ALLAH bai taimakeni, kun tallafi rayuwata kun cireni da ga wannan mummunar ƙazamar rayuwar ba da hakance zata kasance da ni. Abinda nake sha ko rabinsa Nadiya bata iya sha fa. Amma kaga yanda rayuwarta ta koma, bata da maraba da mahaukatan kan layi masu wucewa yara na musu atire. Iyayenta sun korota a makaranta data lalace take kwana tsakkiyar kazaman ƴan shaye-shaye. Na shiga uku Hydar wace irin rayuwa ce muke jefa kammu ne haka?....”

       Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yanda take kuka na fitar hayyaci. Ɗagota yay ya rungumeta a jikinsa, tare da fara jera mata kalaman lallashi da nasiha. Sun jima a wajen tsaye ya karasa busar mata da kan nata ya ɗaure mata shi. Cikin son kauda mata yanayin ɓacin ran nata ya ce, “Ina auntyn taki wai, naga da Iya Tabawa kawai muka gaisa tana goye da AA”.

       Murmushi ta ɗan saki kaɗan, sai kuma ta kallesa tana ɗan lullumshe ido cike da salon dake narkar da mutumin nata tace, “Tana asibiti ai, tun randa suka zo”.

   Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce, “Asibiti kuma Madam”.

      Sai da ta ɗan hararesa saboda kiranta Madam sannan ta bashi amsa. “Eh ai abinda ya kamata ayi kenan, mizai sa na riƙeta a gida har sai ka dawo kuma. Yanzu kam kaga har sun bamu ranar da zasu mata aikin ma. Sai ka ƙarasa shiryawa muje ka ganta dama Doctor ɗin ta buƙaci ganin mijinta, sai dai nace mata baya kusa sai ƙaninta dai.”

           Rasama mizaice mata yayi shi kam, sai kawai ya zuba mata idanu yana kallonta, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya huta ma kawai. “Kallon fa?”. Ta faɗa tana wani tura masa baki da kashe masa ido ɗaya. Hannu ya kai zai cafkota ta zille tana dariya. Shima sai ya murmusa yana dimtse gefen lip ɗinsa da haƙori. Kayanta ta maida dan bata son Iya Tabawa ta zargi komai tunda ta ganta da su. Ta dawo gaban mirror ɗin ta maida ɗaurin ɗan kwalinta kamar yanda yake ɗazun da yin ƴar kwalliya. 

         Shima sai ya nufi closed ɗinsa ya saka kaya. Tsaff suka fito suna zuba ƙamshi da annuri, ita sai yanzu ma ta san ashe tare yake da Ahmad. Amma yake komansa hankali kwance a ciki kamar bai bar kowa na jiransa ba, shiyyasa da zata fito ya sakata sanya abaya ashe. Sun gaisa da Ahmad yana faman tsokanarta kamar yanda ya saba. Ita dai nata murmushi ne musamman daya kasance boss ɗin nata ya watso mata kallon gargaɗi. Abincin da suka sha wahalar yi ita da Iya Tabawa ta gabatar musu. Sosai Smart yaji daɗin ganin tuwo, dan zai iya cewa tunda ya baro Nigeria bai sake ci ba. Kasa haƙuri yayi ya tambayi inda suka samo garin tuwo haka. Lulu ta bashi amsa da cewar su Aunty Bilkisu ne sukazo musu da shi. Bayan sunci sun ƙoshi kaɗan suka huta Lulu ta takura musu dole suka fice zuwa asibiti duba aunty Bilkisu, zuwa lokacin AA ya tashi yana hannun Babansa da yay kewa.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 51"