Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 57

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣7️⃣

.......Uncle Yousuf da kansa yaje ɗaukar Lulu airport. Da ga airport ɗin kuma asibiti suka wuce kai tsaye. Ba ƙaramin girgiza zuciyarta tayi da ganin kowa da kowa na asibitin ba. Ashe ƴan Saudiyya ma har sun ƙaraso. Kasa haƙuri tai sai da ta leƙa Dada ta window. Dan an hana kowa shiga wajenta Baba Garko ne kawai ya shiga bayan likitoci sun sami kanta da ga aman jinin da take yi. Kuka sosai Lulu keyi da ya sake ɗaga hankalin duk wanda ke a wajen. Uncle Taheer Auta ne ya kama hannunta suka bar wajen, da ga gefe ya zaunar da ita yana lallashinta akan ta daina kuka addu'a Dada ke buƙata a yanzu. A hakama an samu kanta ba kamar da safe ba. Wannan ɗan lalashin da autan Dadan ya mata ne ya ɗan saka mata nutsuwa kaɗan ta rage kukan da take yi. Lokacin da zasu wuce gida tace ita a barta anan zata kwana. Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ce tai ƙarfin halin cemata, “A'a Mawaddat kema kulawar kike buƙata ai a wannan halin da kike ciki. Ga tafiya mai nisa kinyo”. Da yawan ahalin wannan family sun san ALLAH ya bama Hajiya Turai baiwar gane ciki koda ƙarami ne, dan haka kowa ya fahimci abinda take nufi akan Lulu ballema duk mai lura yaga Lulu yasan tana da ciki saboda illahirin halittun jikinta sun nuna hakan duk da kuwa akwai jin daɗi da samun kwanciyar hankali. Abinda bata sani ba hatta Iya Tabawa ta jima da fahimtar tana da ciki, tayi gum da bakinta ne kawai har ya bayyana kansa. Ita kanta aunty Bilkisu cikin kokwanto take magana ce kawai batayi ba. Amma har so tai ta tseguntama Ammah da ga baya kuma dai tai shiru dai. Lulu dai ba fahimtar Hajiya Turai tayi ba, sai dai babu yanda zatai ta yarda ta bisu. Kasancewar motar Hajiya Turai ɗin ta shiga sai kawai ta wuce da ita can gidansu (Gidan Alh Sulaiman kenan).


        Alh. Sulaiman da tun wayarsa da Tajuddeen ransa ke'a ɓace yana zaune labarin zuwan Lulu Nigeria ya sameshi. Baida niyyar zuwa asibitin duk da baƙaƙen maganganun da ɗan cikin nasa ya faɗa masa sun kartar masa zuciya amma jin abar farautarsa a kusa da shi ya sashi niyyar zuwa. Sai dai bai baro Companyn nashi ba sai dare sosai saboda bada ƙafa. Sun riga sun gama shirya yanda zasu sace Lulu shida yaransa. Dan haka kai tsaye asibitin ya nufo. Sai dai ya samu kowa ya tafi sai ƙanwar Baba Garko kaɗai da ke tare da Dada. Inna Sadiya nada labarin komai na tsakanin Sulaiman da iyayen nasa, dan haka ta kallesa sheƙeƙe ta watsar, gaisuwar tasa ma sama-sama ta amsa masa. Duk yanda yaso jin wani abu daga gareta bata kulashi ba. Dole ya kama gabansa yana jan tagwayen ƙwafa da jin kamar ya make banza ya wuce. Yana fitowa yay kiran yaronsa Malami. Ya sanar masa su rabu zuwa gidan Daddy da Uncle Yousuf dan Lulu bata asibitin. Sun amsa masa da girmamawa, duk da sun san tsaron dake zagaye da gidajen daya faɗa ɗin, daga haka ya wuce gidansa shima. Koda ya iso bai nema matarsa ba kamar yanda itama ba shiga sabgarsa takeba a yanzun, dan tace zaman ƴaƴanta kawai takeyi ita kam dan ya gama fita mata a rai kasancewar amaryarsa ta sanar mata komai. Dan bayan dawowarta ƴaƴanta mata yayun Tajuddeen da ita sunje gidan su amaryar tasa domin lallashinta itama ta dawo ta nuna musu ai itakam tabar gidan nan har abada. Da suka matsa ne taja Hajiya Turai gefe ta sanar mata komai tare da nuna mata video ɗin nan. Hankalinta ya tashi matuƙa, dan itace ma ta bata shawarar ta kaima su Baba Garko videon inba haka ba mijin nasu zaibi duk wata hanya ya kwacesa a hanunta. Ba ƙaramin ruɗani Hajiya Turai ta shiga ba a week ɗin da ya gabata, da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ko yaranta bata sanarmawa ba har yanzu.

        Zuwa cikin dare jikin Lulu ya ɗume da zazzaɓi, kasancewar kwana biyun nan haka take fama sai bata damu ba. Ta dai sha magani ta kwanta duk da tana jin kewar mijinta ta taushi zuciyarta, sai gabannin asuba zazzaɓin ya saketa. Tana idar da salla kasa haƙuri tayi ta ɗora layinta na Nigeria akan waya. Smart ta fara kira. Bugu ɗaya ya ɗaga mata. A tare suka sauke nannauyan numfashi. Kafin a hankali ya fara furta, “Kin san ko yanda kika bar zuciyata cikin barazana da tashin hankali Baby luv. Tunda kika sauka nake jiran kiranki amma shiru har na fara jin nauyin yawan kiran da nakema Daddy da Uncle Yousuf.”

        “Kayi haƙuri”.

  Ta furta a hankali. Ajiyar zuciya ya sake saukewa da faɗin, “Ya zanyi, na haƙura. Ina dai fatan babu wata matsala ko? Dan wlhy gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk da nasan wawan baiyi zaton kina gidansa ba”.

    Murmushi Lulu tayi har yana iya jiyo sautinsa. Cikin ƙara tausasa harshe ta ce, “Bayan ka bashi ƙafa taya zai iya gano ka. Dolene na bama wanda ya saka maka suna Smart ƙyauta gaskiya. Mutum yana nemana ruwa a jallo amma ka turoni gidansa na kwana kuma. Sannan kada ka manta kawuna ne kake cema wawa”.

         Ƙaramar dariya yayi shima. Ya ce, “ALLAH sarki masu kawu yi sorry. Sannan banda wata mafita sai hakan ai. Dan nasan bazai taɓa kawoma ransa zaki zo gidansa ki kwana ba. Yanzu dai sai kiyi taka tsan-tsan kuma.”

     “In sha ALLAHU mijina. Jiya gaba ɗaya kewarka ta hanani isashen barci”.

               “Uhm kamar da gaske. Ni ban san daɗin baki. Ina Aliyu yaga wannan matsayin. Ke dai kawai kice tsoro ya hanaki barci kina a gidan dodoki”.

          “Oh hakama zakace ko? Shikenan ai zan rama. Bazan ma dawo ba sai bayan wata tara kama kanka”.

     Dariya sosai yakeyi da faɗin, “Haba Baby luv ki tausayamin mana. Ni kaina kin ganni nan yanzu haka nama kasa kwanciyar sai lissafi nake da kallon hotunanki kawai. Na gayyato Baban Ammah ya tayani kwana ya addabeni da ɓuruntu.”

          Cikin dariya ta ce, “Kai miya kaika wannan gangancin siyen gida a sama.”

      “To yana iya kewar Mamansa ta isheni ne. Ni da ƙyar ma idan zan iya haƙuri ban taho Nigeria ɗin nan ba”.

   Idanu ta waro sosai kamar tana gabansa. Ta ce, “Are you serious zaka iya barin wannan kwallon ka taho Nigeria?”.

        “Humm yarinyar nan kina wasa da Aliyu ko? Zan baki mamaki”.

    “A'a A'a nagode basai ka bani ba. Ai nasan zaka aika wlhy yi zamanka na yafe. Nima ba jimawa zanyiba ai. Yanzu dai ina son naje naga Ammah yaya za'ayi?”.

    “Kefa rigimarki yawa gareta Mrs Mawashi. Keda ake ɓoyonki ina kuma zaki je yawo?”.

            “Zuwa wajen uwata ne yawo. To nidai kasan yanda zakai dani gaskiya”. Ta faɗa cikin shagwaɓa har yana iya jiyo sautin yanda take buga ƙafa ƙasa.

       “Kirufamin asiri Baby luv nayi barcina lafiya, kinga dai na sakama raina haƙuri tunda kika taho ko kuka banyi ba”.

    Sosai Lulu take dariya. Ta ce, “Kuka fa?”.

      “Eh mana, na dai zama kalar tausayine kawai ko wanka yau ma bazanyiba. To in nayi wazan mawa baƙya kusa”. 

     Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi. Smart ɗinta kenan Zuma ga zaƙi ga harbi. Duk wanda kake buƙata za'a sayar maka akan farashin da ya dace. Sun jima suna hirarsu kafin ta tashi tayi shirin zuwa asibiti. Dan bazata iya sake komawa barci ba....


      ★Yaran Alh. Sulaiman nacan sun kasa sun tsare a tituna jiran fitowar Lulu da ga gidansu ko gidan Uncle Yousuf. Anan ko su har sun fice gidan Alh. Sulaiman sai fitar motar matarsa ya jiyo. Ƙwafa yayi dan yayi alwashin koya mata hankali itama dan yasan ita ke zuga masa yara suna mai rashin mutunci. Ranar matan sun masa akan dawowarta gidan. Jiya kuma Tajuddeen ya masa akan Dada. Bai damu da fitar tata ba dan yasan asibiti ta wuce. A asibiti sun samu jikin Dada yau dai Alhmdllh, da sauƙi irin na malam bahaushe da ake faɗi. Amma dai har yanzu bata gane komai, sai ambaton sunan Sulaiman da take a hankali hawaye na ziraro mata. Duk wanda ya shiga dubata sai ya fito da mamakin yanda ta damu da al'amarin yayan nasu Sulaiman haka, bayan rashin mutuncin da yake zuba musu salo-salo. Sai da ta koma barci ne Baba Garko ya ce iyayen su sameshi gaba ɗaya a gida. Ganin haka sai itama Lulu tai kiran Smart kawai akan zuwa wajen Ammah. Sai da yay ɗan jimmm sannan ya amsa mata da “Naga dai kin matsa da ganin Ammahn nan, ɗan bani 10minut haka”.

       Baki ta murguɗa masa tamkar tana gabansa....      *_GARKO HOUSE_*


     Ƴaƴansa ne gaba ɗaya. Alh. Sulaiman da wanda suka rasu biyu mahaifiyar Lulu da Sultana ne kawai babu. Sunyi kusan zaman mintuna huɗu kafin ya fito. Bayan yakai zaune suka sake gaishe da mahaifin nasu. Da kai ya amsa musu yana gyara zama dan zuciyarsa sam babu daɗi. Sai da ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya kafin yay gyaran muryar da ta sakasu sake maida hankalinsu garesa. 

       “Na taraku anan ne a dalilin abinda yay sanadin kwanciyar mahaifiyarku asibiti duk da ni har yanzu ban san minene ba shiyyasa na buƙaci ganinku mu gani tare dan zata iya yiwuwa nima na tsinta kaina a yanayin da yafi nata ma...” cikin tashin hankali da ruɗani duk suke kallonsa. Bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan wasunku sun san rikicin dake tsakanin ɗan uwanku da matansa wasu basu sani ba. A watannin da suka gabata rikicin da bamu san tushensa ba ya ɓarke a tsakanin Sulaiman da matansa su dukansu har suka wuce gida. Sai daga baya uwar ƴaƴansa ta dawo amaryar da al'amarin yafi tsamari a kanta taƙi ta koma. Na barsu ne naga iya inda abin nasu zai kai sai kuma gashi jiya ta samemu anan gida. Flash drive ta kawo mana ta tace shine sanadin rikicin nasu. Da ga haka batai mana wani ƙarin bayani ba ta tafi. Bayan wucewartan ne mahaifiyarku tazo ta ɗauki Flash ɗin ta wuce da shi sai mai aikinta ta isarmin da saƙon gata can ta faɗi babu rai. Duk abinda zai saka mahaifiyarku a wannan mummunan yanayin bazai kasance mai sauƙi ba. Shiyyasa tun jiya na kasa dubawa ni kaɗai na zaɓi mu duba tare da ku”. Ya ƙare maganar yana jawo tab ɗin Dada da har yanzu flash ɗin ke a jiki. kusa da shi duk yay musu nunin su dawo. Haka suka zauna wasu kusa da shi a ƙasa wasu a kujera. Babu wanda zuciyarsa bata kaɗa ba a lokacin da fuskar marigayiya Mawaddat ta bayyana. Kafin sukai karshen videon babu wanda jikinsa baya rawa a cikinsu, ga hawaye duk ya cika musu idanu. Auta da yafi kowa shaƙuwa da Sultana a gidan baima san sanda ya fashe da kuka ba tamkar ƙaramin yaro. Kasa jurewa Baba Garko yayi ya miƙe jikinsa na karkarwa. Sai dai dole sukai saurin riƙosa saboda hajijiya dake neman zubar da shi a ƙasa, shima sai kawai ya fashe da kuka. Kukan mahaifin nasu ya sake tayar musu da hankali. Suma duk suka fara sharar hawaye..........✍️_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 57"