Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 58

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣8️⃣

.........Kiran Smart ya saka Lulu tashi ta koma gefe. Kafin ma tace wani abu ya furta, “Akwai matsala fa Baby luv. Dan Kawunki ya baza yaransa sosai nemanki. Fitarki a asibin nan ma inaga sai da jami'an tsaro”.

        Murmushi Lulu tai har yana iya jiyo sautinsa. Ta wawwaiga gefenta, tabbatar da babu kowa a kusa da ita cikin sake ƙasa da murya ta ce, “Karka damu zan tafi yanzu. Ka turo min address na wajen kawai kai dai”.

    “Kin san mi kike faɗa kuwa. Taya zaki fita a gaɓar da wannan mara imanin ke nemanki ruwa a jallo. Ayanzu haka asibitin yake shirin tahowa dan ya samu tabbacin kina a ciki. Ga Uncle Yousuf nan zuwa shi da Daddy ma”.

             “Ka kwantar da hankalinka zamu wuce plan E ne yanzu a kansa”.

      “What! Plan E fa?. No no no Mawaddat. Bakya ganin halin da tsohuwar nan take ciki. Mu rushe plan E ma kwata-kwata bashi da amfani”.

      “Shiko keda amfani musamman a wannan gaɓar Mr A. Dan babu abinda ya rage mana kuwa sai plan E ɗin. Dada ta riga taga video, shine ma dalilin kasancewar ta a wannan halin. A yanzu haka Grandpa da Uncles suna zaman meeting kuma nasan duk a kansa ne. So kaga abinda ya rage kawai mu ƙarasa sauran aikin. Dan haka yanzu zan saki....”

       Da sauri ya ce, “Maw....” kafin ya ma ƙarasa sunan nata ta yanke wayar. Dan zuciyarta gaba ɗaya ta riga da ta gama kaiwa bango. Duk kiran da yake mata bata ɗaga ba. Cikin abinda baifi mintuna biyar ba ta gama sakin videon a ɓoyayyun shafukan data ɗauki tsawon lokaci tana raino da tara followers. Shafi ne da dama yake taka rawar gani akan harkar fyaɗe da shaye-shaye. Ta ginashi tun lokacin da su Dada suka saceta. Zuwa yanzu shafukan nada ɗunbin mabiya saboda abubuwan da ake posting a cikinsu. Sunasa kuma guda ɗaya ne a instegram, twitter, facebook, TikTok, da website. Sunan wanda ta saka, da abinda ta rubuta a saman video ɗin yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya samu makallata masu ɗunbin yawa, kafin kace mi an fara shearing ɗinsa.  

     Yaron Alh. Sulaiman da suka kafa suka tsare a bakin asibiti na jiran fitowar Lulu ne ya fara cin karo da video ɗin, shima wani abokinsa ne ya tura masa yana tambayar ya duba wannan ba ogansa bane. Wani ihun tashin hankali ya fasa batare da ya farga ba. Har takai wanda ke ɗan wuwwucewa ta wajen suna kallonsa. Jiki na rawa ya shige mota. Kira ya dannama Alh. Sulaiman dake tsaka da yin online meeting shima a mota dan yana hanyarsa ta tahowa asibitin ya samu kira da ga Lagos. Sun buƙaci ya ajiye koma mi yake yi zasuyi online meeting na gaggawa. Hakan ya sashi samu waje yay parking hankali a tashe. Suna tsaka da tattaunawar akan batun kayansu ne dai kiran malami ya shigo masa. Bai yi niyar ɗagawa ba sai da yaga kira na biyar na sake shigo masa kuma duk da ga malamin ne. Yasan baya masa irin wannan kiran mafarautan, dan haka zuciyarsa ta bashi lallai akwai matsala. Dole yay excusing kansa ya ɗaga kiran.

       “Oga ka duba na tura maka saƙo ta WhatsApp. Wlhy akwai matsala. Babbar matsala ma kuwa”.

    Ba ƙaramin faɗuwa gaban Alh. Sulaiman yayi ba. Babu shiri ya shiga WhatsApp ɗinsa. Ai kawai sai ga mutumin waya na neman suɓuce masa. Duk da shi ya ga video ɗin amma tashin hankalinsa anan a ina malami ya samesa shi kuma? Ko amaryarsa da flash ɗin ke'a wajensa ce ta tura masa? Kai ina. Rashin samun gamsashiyar amsa ya sashi kiran malami. Muryarsa har harɗewa take wajen tambayarsa a ina ya samu video ɗin. Malami da gaba ɗaya yake a ruɗe ya ce, “Oga bama ni ba, a kowace waya zaka iya samunsa a yanzu. Dan an sake shi ne a wasu shafukan sada zumunta da ke a manyan apps da mutanenmu suka bama amanna. A yanzu haka wani abokina ne ya tura min wannan bayan na turo maka nima na shiga bincike wlhy tako ina videos ɗin trending sukeyi. Acikin abinda baifi minti arba'in ba miliyoyin mutane sun kalla”.

     Karo na farko jikin Alh. Sulaiman ya shiga kakkarwa ta haƙiƙa. Bai gama dai-daita da wannan bala'in ba wani kiran ya shigo masa. Mai kula da ɓoyayyen Companyn sa ne na magunguna. Ruɗanin da yake ciki ya sashi ɗagawa batare da ya farga ba. Bai gama dai-daita wayar a kunnensa ba furucin Babban mai haɗa magunguna ɗin Companyn nasa ya daki kunnensa.

           “Mun shiga uku Alhaji jami'an tsaro ne zagaye da dajin nan da Companyn nan. Gasu nan sun gama shiryawa da bindigu suna bamu umarnin mu miƙa kammu ta sauƙi kosu cinnama Company ɗin wuta. Yaya akayi haka Alhaji? Taya suka san da wannan wajen duk taka tsantsan ɗin da mukeyi na tsawon shekaru. Shike nan na mutu Alhaji kofa aure banyi ba balle na bar mai mun addu'a” ya ɓarke da wani irin kuka da ya nema fasa kwanyar Alhaji Sulaiman da gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa. Ƙitt ya yanke kiran tare da tada mota a haukace. Wani kiran yaga yana shigowa, baida buƙatar duba wanene ma balle ya ɗaga. Kai tsaye gidansa ya nufa cikin wani irin mahaukacin gudu. Kaɗan ya rage ya take maigadinsa da ya gigita da horn. Baiyi parking na kirki ba ya fita cikin gudu-gudu daya firgita ma'aikatan gidan. Dan babu abinda babbar rigarsa keyi sai tashi sama bulummm-blummm-blummm. Yana gab da shiga falonsa ya nema yin wani uban tuntuɓe sai gashi ƙasa wanwar. Fuskarsa ta wani irin dunguruwa da ƙasa. Duk da azabar datake ratsa masa lips da goshe da kan hanci bai damu ba ya miƙe cikin ƙarfin hali. Sai ga jini na ɗiga yararara. Falon ya afka a ɗari uku da sittin, yana ajiye ƙafarsa ciki wayar da abokan huɗɗarsa ne kawai a ciki ta cigaba da ruri. Kamar zai fasa ihu ya ɗaga....

       “Alhaji Sulaiman kayi takanka. Aiki ya buɗe wlhy yanzu haka an kame su Olu.....”

     Wani irin kuka Alh. Sulaiman ya ɓarke da shi kawai tare da yakice babbar rigarsa da hular ya watsar. Sai kuma ya kwasa a guje zuwa cikin bedroom ɗinsa. (Gaskiya ka zare😂🤣😂🤣😂🤣😂🤣) Passport ɗin sa ya ɗakko, da gudu ya sake fitowa yana kai waya kunnensa. Malami yake kira yana ɗagawa ya ce masa ya siya musu ticket yanzun nan ta online nama kowacce ƙasane. Jirgin da zai tashi yanzu-yanzu dai yake buƙata. Yayi maza kuma su haɗu a airport.

          Hankalin ma'aikatan gidan nashi ya tashi ganin gaba ɗaya kamar ya zare. A take sukai kiran Hajiya Turai suka sanar mata gida da babu lafiya. Dan sun gagara gane kan Alhaji gashi nan ya shigo a haukace, ya kuma fito ya shiga mota da alama sake fita zaiyi”. Kafin sukai ƙarshen wayar ma shi ya fice a gidan a haukace......


         *_★UK★_*


    Tun Smart da ke ganin komai na halin da Alh. Sulaiman ke ciki ta direct camara ɗin su yana dariya har al'amarin ya fara tada masa hankali. Jin da yay Alh. Sulaiman na shirya guduwa ya sashi saurin kiran Uncle Yousuf ya ce suyi report Immigrations office. Dan tabbas suka bari ya tsallake ƙasar yasha kenan. Dan a ƙasashen ƙetare yanada wanda zasu bashi kariya tunda bada kayan aka kamashi a hannu dumu-dumu ba. Cikin sauri Daddy ya aiwatar da hakan kuwa. Lokacin da Alh. Sulaiman da malami ke isowa airport har an fara shelar masu tafiya a jirgin Dubai su shirya. Sunyi farin ciki da samun hakan, dan Malami har ya siya musu ticket ɗin ta hanyar cuwa-cuwa ta hanyar wasu ruɓɓaɓun ma'aikatan da ke da alhakin hakan ta online. Restroom Alh. Sulaiman ya nufa domin canja kaya, yana fitowa har tuntuɓe ya nemayi wajen saurin nufar jirgin da har mutane sun fara shiga. Yana taɓa ƙofar ainahin inda hanyar zuwa wajen jirgin yake aka dakatar da shi duk da ya rufe fuska da facemask da glasses ga p-cap. Cikin masifa yake tambayar ba'asi. Kai tsaye ma'aikacin ya bashi amsa da yanzu-yanzu an tabbatar musu da karɓe lasisin fitarsa wata ƙasa. Sun samu saƙone kuma da ga immigrations office. Jiyay tamkar ya saki zawo a wando. Amma abinka da ɗan cocaine sai ya nema birkice musu har yana ƙoƙarin ture jami'in shi a dole zai wuce. Dai-dai nan aka sauke masa bindiga a saman kai tare da nuna masa handcuffs a kan fuska. A dake aka furta. 

      “You are under arrest Mr Garko..”

   A wani irin hargitse ya juyo kunnensa na bada wani irin sautin tsuuuu!!! Kamar an doka masa guduma a kansa. Ido biyu yay da jami'an tsaro na ƴan sandan farin kaya wato DSS da na ainahin ƴan Sanda, dana immigrations sai na filin jirgin zagaye da shi kusan su hamsin. Kuma kowanne riƙe da bindiga. Gaba ɗaya airport ɗin tayi tsitttt baka ganin komai sai hansken wayoyin mutane dana ƴan jarida. Masu video nayi, masu hoto nayi, masu kallo nayi. Harda masu nunawa live a social media. Sai kawai ya rimtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sun yi bala'in mimmiƙewa ruɗu-ruɗu. Bashi da zaɓin da ya wuce yin surrender kawai. Amma saboda ƙarfin hali da taurin zuciya irin na Tsule sai gashi da fakar ido ya hamɓari na gefensa bindigar hannunsa tai tsalle sama ya tare hannu ya cafe tare da ɗaurata saman kanta. A cikin abinda bai wuce sakan biyu ba hakan ta faru, shi adole sai ya tabbatar musu shi ɗin ƙwararren maharbi ne. Bindigar a saman kansa yana dariyar da tafi kuka ciwo da nunasu da hannu ɗaya ya ce, “Lusarai kawai. Da na miƙa kaina gareku wlhy Gara na kashe kaina. In ce dai shine ƙarshen abinda za'a iya min a duniya ko....”

        “Karka aikata haka Mr Garko. Yin hakan kuskure ne ka miƙa kanka ga hukuma salin alin zaifi maka sauƙi”.

    Shugaban NDLEA ne dake ƙarasowa yanzu ya faɗa daga inda yake tsaye. Wani banzan kallo Alhaji Sulaiman yay masa. Sai kuma ya kwashe da dariya yana ƙoƙarin ɗan kunamar bindigar. Tauuuuuu!!!! Kakejin sautin ya karaɗe airport ɗin da ya saka mutane fara kwasa a guje cikin ruɗewa da rikicewa.....


       _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 58"