Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 61

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣
......An cigaba da kame-kame a ƙasar mai ban tashin hankali. Inda harda sunan wani tsohon shugaban ƙasa, da wasu manyan ƴan siyasa a gwamnoni da ƴan majalisu ma dake ci a yanzu ya fito, sunayen manya-manyan ƴan kasuwar da ba'a taɓa zato da tsammani ba. Tare da manyan ma'aikatan gwamnati da tsabar yanda ake kallonsu iyayen ƙasa ake kiransu. Al'amari yakai intahar da mai gyarashi sai dai UBANGIJI. A cikin abinda baifi awanni a shirin da huɗu ba na cikar kwanakin Sulaiman a hannun hukuma sojoji suka sauke shugaban ƙasa tare da wasu gwamnoni. Hankalin mutane ya tashi matuƙa da tunanin ko juyin mulki ne, sai gashi bayan cikar wata a wa ashirin da huɗun an maye gurbin shuwagabannin da mataimakansu amma an maida shugaban ƙasar shima....


       _____★


  An wuce da Dada da Baba Garko zuwa ƙetare domin duba lafiyarsu. Hakan yasa Lulu shiryawa itama ta koma wajen mijinta bisa umarnin su Daddy. Taso ganin Ummah itama amma hakan bai faru ba saboda kai-kawon da tayi duk bata jin daɗin jikinta. Smart da kansa yaje tarbarta airport shi da ɗansa. Ta rungumesu su duka cikin ƙarfin hali da jin kewarsu duk da dudu kwananta tara ne kacal. Suna isa gida ta zube kwance a falo, hakan yasa kowa ya fahimci bata jin daɗin jikinta. Kiran Ammah da ya shigoma Smart da ke kallonta ne ya hanashi magana. Sai da ta katse ya kirata dan haka yake musu duk wanda ya kirashi koda a yaran gidansu ne. Bayan ya gaisheta da girmamawa take tambayar ƴan tafiya sun iso lafiya. Cikin ɗan damuwa yace, “Gata nan duk a galabaice muna shigowa ta zube a falo.”

        “Ya salam, ai kuma dai kunyi ganganci ne. Dan ma ALLAH ya bata ƙarfin hali ne kawai. Amma a halin da take ciki ai ba kowa zai iya ɗaukar wannan kai-kawon ba da hayaniyar da aka sha. Sai kuyi ƙoƙari ku tafi asibiti dan a tabbatar da lafiyar abinda ke jikin nata da ita kanta”.

     Cike da mamaki Smart da ke kallon Lulu ya ce, “Ammah abinda ke cikinta kuma? Wani abu tace miki yana damunta?”.

         Cikin murmushi mai sauti Ammah ta ce, “Aiba saita faɗamin ba Babana. Duk wanda ya kalli Mawaddat ai yasan akwai ciki a jikinta”.

       “Ciki fa Ammah?”.

    “A'a kaini tsaya, wai ku baku san da cikin ba ne ko mi?”.

  “Wlhy Ammah ni ban san tana da ciki ba. Itama kuma na tabbata bata san da shi ɗin ba”.

        “Kai nikam yau naga sakarkarun yara. Yanzu ita Bilkisun dake tare da ku ga wannan tsohuwar ace suma duk basu lura ba. Aiko wannan cikin in bai kai wata huɗu ba ma to gab yake da kaiwa. Dan da alama ma babu jimawa da zuwanta nan ALLAH ya bada shi. Sai kuyi ƙoƙari dai kuje asibiti to”.

      A sanyaye yace, “To Ammah insha ALLAHU”.

    Yana yanke wayar Lulu ta miƙe cikin ƙarfin hali zuwa bedroom. Dan wanka kawai take sonyi. Da kallo suka bita su duka. Iya Tabawa ce ta katsesu da ƴar dariyar ta. A tare duk suka juyo suna kallonta. Tace, “Ai tun watan daya gabata na fahimci uwar ɗakina nada shigar ciki. Nayi shiru ne dai kawai saboda dambarwar da naji anayi”.

       Dariya aunty Bilkisu tayi sosai tana kallon Smart daya rasa abin cewa. “Ka gani kunata faman fitina ashe ma ALLAH ya bada abinda ake ma rigimar. Nima sai gab da zata tafin nan na fahimta sai dai zuciyata bata tabbatar ba shiyyasa bance komai ba. Ashe Iya Tabawa ta mana na manya ne ma ita. ALLAH ya raba lafiya, ya bata lafiya ita kuma”.

      A hankali ya amsa da Amin yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya miƙe yabi bayanta zuwa bedroom ɗin. Ya samu tana wanka, dan haka ya zauna a bakin gado yana zaman jiran fitowarta. Babu jimawa ko sai gata ta fito tana faman dafe kai. Miƙewa yay ya riƙota ganin kamar tana tangaɗi. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Miya faru kuma?”.

    “Ina ganin jiri” ta bashi amsa a hankali. Kwantar da ita yay a saman gado ya rungumeta a jikinsa yana mai sauke tagwayen ajiyar zuciya. Idanunsa a lumshe yana shafa mata kai ya ce, “Dama kin san kina da ciki amma kika kasa sanar min?”.

         Kanta ta girgiza masa a hankali da faɗin, “Wlhy ban sani ba. Duk da ina jin canji a jikina ba a yanda na saba ba na ɗauka kawai yanayi ne dan lokacin cikin AA ma sai da ya kai wata kusan huɗun na sani bayan ma anyi yunƙurin zubar da shi”.

      Sake ƙanƙameta yay a jikinsa yana mai jin wani irin farin ciki mara misalin kwatance. Sosai yake son ƴaƴa a rayuwarsa. Kodan ta tashi cikin yawa ne a gidansu shiyyasa oho. A hankali ya shiga bata sumba yana mai sanya mata albarka. Ita dai riƙe kukanta kawai takeyi amma ita tasan mi take ji. Bawai bata farin ciki bane ba. Tana jin tsorone kawai dan ita kaɗai tasan irin wahalar da tasha a lokacin haihuwar AA da sanda cikinta ya tsufa. Sai dai a yanzu tana tsoron nunawa kuma ta takaloma kanta bala'insa. Haka ta cigaba da shanyewa da barma ranta kawai tunda dai mai afkuwa ta afku, sai dai tana mamakin ciki a jikin mace nayan tayi planing, gaskiya mutumin nan maye ne, itakam taga takanta kenan. Shi da kansa ya shiryata yana ta dai ƙoƙarin danne dariyarsa, dan daya tuna abinda tayi kuma ga cikin da take gudu sai yaji dariya na taso masa, haka dai ya daure ya kimtsata sannan ya fita ya kawo mata kunun gyaɗar da tace tana so yanata fan murmushi sai dai baice komai ba duk da bakinsa fal yake da zance. Kaɗan ta sha tace ta ƙoshi, daya matsa ma sai ta fara yunƙurin amai. Dole ya ƙyaleta suka wuce asibiti. An dubata tare da tabbatar musu baby na cikin ƙoshin lafiya. Gajiya ne kawai yay mata yawa, dan haka sukace taje ta samu hutu sosai a gida dan tana buƙatar bedrest. Sai magunguna da suka bata na ƙarin kuzari da ranakun da zata dinga zuwa ana duba lafiyarta suka kuma cire mata abinda ta sakama jikinta kamar yanda ta buƙata, dan bataga amfaninsa ba kuma. A haka suka kwaso suka dawo gida Smart na kwasar dariya dan a wannan gaɓar dai ya gagara daurewa. Itako sai kawai ta sakar masa kuka dan ta gane abinda yakema dariyar. (Mugu ɗan masa kenan😂😂)

      A ranar dai duk ƙwaɗayinsa dole ya haɗiyesa saboda kwana tai babu lafiya, sai amai da take faman yi ko ruwa ta sha. Washe gari dole suka sake komawa asibitin. Kwantar da su sukayi suma dole. Gashi washe gari yana da wasa mai zafin gaske dan gab suke da kaiwa ƙarshen primier link. Alhmdllh Dan yana taka rawar gani sosai ga kuma team ɗinsu na gaba da kaiwa zagayen ƙarshe. Babu yanda zai yi dole ya shirya ya koma ya barta da su aunty Bilkisu....


      ★Satin Lulu uku da dawowa aunty Bilkisu ta fara shirin komawa Nigeria. Alhmdllh taji sauƙi sosai sai fatan lafiya mai ɗorewa. Shatara ta arziƙi Lulu da Smart suka shirya mata. Haka ta wuce suna jin kewarta tana jin nasu dan Lulu harda hawayenta. Sai da Smart ya dinga lallashinta akan ta kwantar da hankalinta ba sun kusa tafiya bikin Maryam ba. Idan zasu dawo da Ammah zasu dawo in sha ALLAH. Hakan ya sakata jin farin ciki sosai.

       Lulu ta cigaba da rainon cikin ta cike da kulawar mijinta da Iya Tabawa da ta zame mata tamkar uwa. A haka su Aunty Saliha sukazo hutu UK, kuma anan London sukai masauki kamar yanda Lulu taita naci. Sosai ta kasance cikin farin ciki mara misali. Balle ga ɗan lelenta Deen kuma da ya ƙara girma. Cikin jikinta daya fito sosai bai hanata yin hidima da su ba, dan kusan a gidan suke yini ma. Sai dare su koma masaukinsu. Wani lokacin kuma ita taje can.

         Su Smart sun kai zagayen ƙarshe tare da ɗaukar kofi. Yayinda Smart ya taka rawar gani da sunansa keta sake zama abin ambato a zuciyar masoyansa. Ga ƴammata tako ina sun sakkoshi gaba. Sai dai shi ko kallo basu ishesa ba, dan yace ya rufe da ga Final Choice babu wata kuma. Kammala wasansu ya sashi fara musu shirin tafiya Nigeria dan ya samu hutu mai ɗan yawa. Ga kuma bikin Maryam da aketa shirye-shirye dan dama saboda shi aka ɗan ɗaga ƙafa....


         *_NIGERIA_*


   A Najeriyar ma abubuwa da yawa ne suka faffaru. Su Ammah sun koma gidansu da Smart ya gyara. An canja masa tsari mai birgewa da ɗaukar hankali. Yayinda Abba yace Ummah bazata dawo masa gida ba tunda ya saketa. Sai da aka taru a kansa anata bashi haƙuri akan tazo tai zaman ƴaƴanta. Cikin ƴan roƙo harda Smart. Da ga ƙarshe dai da ƙyar ya amince. Kasancewar itama da nata sashen ta dawo. Sai dai lokacin da zasu shigo gidan bata ma san ta ɓarke da wani irin kuka mai cin zuciya ba. Yanzu nan Aliyu ne ya gina musu wannan gidan. Duk faɗi tashinta dai ya tashi a banza a wofi an kai inda dai bata son kenan. Ranar kwana tayi tana kuka ita kaɗai a ɗaki. Wani tashin hankali kuma washe gari suka tashi da gobara a shagunan Salim. Komai ya ƙone ko tsinke ba'a fita da shi ba. Ana cikin wannan tashin hankalin ƴarta Hannatu ta dawo gida wai mijinta ya saketa. Gaba ɗaya Umma ta sake hargitsewa jiki ya koma ɗanye sharaf. Sai da aka kira Smart ana faɗa masa ne ya saka aka kaita asibiti. Satin ta ɗaya aka sallamonta. Gaba ɗaya Salim ya koma kamar zararre. Sai kuka yake yana jama Umma ALLAH ya isa akan itace ta ja masa. Ai dama nakan tudu ya faɗa duk bala'in data ƙulla akan Smart sai ya dawo kansu. Gashi nan kuwa. Ta cucesu ta zalunce su bazasu yafe ba. Ranar da matar Salim ta gudu da ƴaƴansa bayan ta saida gidan da shi ya kaɗai ya rage masa ai kaɗan ya rage a ɗaureshi a turu saboda tsabar zaucewa. Umma ta dinga kuka dan dama dai Salim ɗin ne abin tinƙahonta...........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 61"