Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 62

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣2️⃣
.......A ɓangaren Garko family ma dai ALLAH ya bama Dada da Baba Garko lafiya har sun dawo gida Nigeria. Sai dai Dada ƙarfin hali kawai take. Gaba ɗaya ta zama wata shiru-shiru. Sai da kaga ta tasa hoton Maman Mawaddat da na Sultana gaba tana kuka. A yanzu Baba Garko kan zauna ya lallasheta da mata nasiha. Hakama amaryarta takan ƙyautata mata duk dan dai ta kwantar da hankalinta, haka ma ƴaƴanta basa gajiyawa wajen tattalinta saboda an tabbatar musu zuciyarta idan har ta buga shike nan kuma. Dan haka kowa baya wasa da al'amarinta. Lulu kanta ba'a barta a baya ba wajen lallashin Dadan. Dan tana kallonta tamkar Mawaddat ɗin ta ne data rasa. Akoda yaushe cikin yin video call suke da ita....


       __________★


   Shirye-shiryen bikin Maryam ya kankama sosai, dan takowane ɓangare shiri kawai akeyi. Ana saura sati guda ɗaurin aure Smart da iyalinsa suka iso gida Nigeria. Ƙasar da yay kewa. Tarba ya samu maiban mamaki da ga al'ummar ƙasar tasa da ƴan uwa da abokan arziƙi. Dan da ƙyar suka iya baro airport sai da taimakon jami'an tsaro. Yayinda ya samu rakkiyar masoya har gida. Anan ma ya samu yaran anguwa da iyaye suna jiransa. Sai ga Smart na hawaye dan farin ciki. Ya tabbatar da mutane rahama ne. Duk wanda yace maka yana sonka da ƙaunarka ya gama maka komai a rayuwa. (Ya ALLAH ka barmu da masoyanmu. Duk wanda ya somu dominka ya rabbi shima ka soshi shi da zuri'arsa baki ɗaya. ❤️❤️❤️😘 wannan nakune masoyan alkairi 🙏).

     Anan ɗin ma dai da ƙyar ya samu suka shiga gida saboda yanayin Lulu. Dan cikinta yayi girma sosai wannan karon fiye dana AA. Ga kuma kullum cikin laulayi take dan tunda ya fara tsufa bata da wani ishashen lafiya. Duk da dama dai haka taketa fama tun da cikin ya shiga watanni biyar. Babu kunya yau kam Smart ya rungume Ammah da Abbah a gaban jama'ar gidansu. Ya kuma rungume ƙannensa su Mubarak da yasan suna matuƙar kaunarsa. Kannensa mata nata kawo masa gaisuwar girmamawa harma da wanda suka girmesa kamar wani sarki. Tunda Ummah ta leƙo sau ɗaya ta gansa bata sake maimaitawa ba, ɗaki ta shige tana sakin wani irin kuka mai ƙona zuciya. Smart ya koma kamar wani baƙin bature. Ko makaho ya laluba yasan kuɗi da jin daɗin rayuwa da ɗaukaka sun zauna sai dai fatan gamawa da rayuwa lafiya.

    Shiko sanin bata da isashiyar lafiya har ɗaki yaje ya gaisheta tare da duk sauran matan Abba har aunty Amarya. Ita kanta Mama a ruɗe take,  kawai dai tana ƙoƙarin dannewa ne kar ai mata irin kallon da akema Umma. Dan ƙamshin Smart kawai rikita zuciya yake. Saboda kowa ya gama sanin hankalin Ummah fa a tashe yake. Wasu a cikin yaranta har abun nata na basu kunya.

       Bayan yaci ya sha daga girkin mahaifiyarsa data musu girki da kanta dan Lulu bata iya cin komai sai kunun gyaɗa. Shi kaɗai taima sha na hauka dan motsi kaɗan taji yunwa yanzu. AA na hannun iyayensa wannan ya ɗauka ya ba wancan haka aketayi. Yaron birgesu yake gashi fes kamar ka lashe, komai na ubansa bai bari ba. Zuwa yanzu ya ɗan fara magana sai dai ba gane abinda yake nufi akeyiba ma sosai. Kwanciya Lulu tayi danta hutama ranta. Yayinda su Ammah da Smart suka buɗe shafin hira dan Gwaggo Sa'adah na gidan da su aunty Bilkisu da Hawwah. Daga baya sai ga Abba shima ya shigo duk da su Smart ɗin sun je sun gaishesa...


     Washe gari aka kawo lefen Maryam daga gidan su Ahamd. Lefe ne na nunama tsara dan an nuna dukiya kam babu ƙarya. Ƙwaƙwalwar Umman neman zautuwa takeyi. Dan kasa jurewa tai yau ma sai kulle kanta tai a ɗaki. Ga dangin Ammah dana Abba nata zuba mata habaici batare da sun duba cewa ƴar uwarsu bace ba. Anyi komai cike da girmama juna da mutuntawa dan suma sun bada tukuyci mai tsoka. Bayan wucewar ƴan kawo lefe Smart ya ɗauki Lulu da AA da Asma'u suka nufi gidan su Lulun. Daddy da su Amrah sunyi farin cikin ganinta, duk da kuwa jiya harda su a ƴan tarbarsu. Basu koma gida ba sai dare. Mommy ma taji daɗin ganinsu. Tana ta tsokanar AA. Hira sosai Smart suka sha da Daddy, dan anan suka yini sai bayan sallar azhar suka nufi gidan Uncle Yousuf. Anan ɗin ma dai hirar aka sha, samun su twins da sukai can yasa Smart da Lulu fahimtar akwai wani abu tsakanin Hussain da Asma'u. Hakan yama Lulu daɗi sosai ita da Smart. Basu bar nan ba sai bayan la'asar. Sun nufi gidan Baba garko inda suka ƙarasa yinin. Itama dai Dada harda kukanta dan ta fahimci dai waɗan nan ma'aurata kainuwa ne dashen ALLAH. Sannan FURAR DANƘO ne damasu ace za'asha farau-farau abune mai wahalar gaske. Jiki luɓus suka koma gida dan Lulu tayi laushi. Ammah taita ma Smart faɗan miyasa bai barta acan ba yaketa yawo da ita haka. Shi dai murmushi kawai yayi yana kallon Lulu dake masa gwalo ƙasa-ƙasa. Washe gari yana tare da Ahmad da Coach, acan ya yini sukasha hirarsu da ubangidansa. Bai dawo gidan ba sai dare dan har Malam na Yakasai yaje ya gaidar bai manta alkairi ba nan ma....


       Al'amarin biki ya kankama sosai, Smart ya haɗama amarya gidan mijinta da kaya na kece raini da nunawa tsara. Yayinda aka fara events da aka shirya wanda ya kafa ya tsare ya hana Lulu zuwa ko ɗaya saboda yanayinta. Daga ƙarshe ma da yaga hayaniyar gidan na mata yawa sai ya dinga janyeta zuwa masaukinsa. Acan suke kwana sai da safe ya dawo da ita nan ta yini cikin danginsa. Lulu ta amsa suna matar babban Yaya. Dan komi aka buƙata bata jin ko ɗar zata fidda a jakarta ta bada batare da tabi takan mijinta ba. Sai wasu a ƴan uwa suka fara tsogumin ai ta kankane komai sai abinda taso take badawa. Tun anayin ƙus-ƙus har zancen ya fito fili yakai kunnen su Ammah. A take Ammah ta nuna ɓacin ranta akan hakan, yayinda Smart da shima ransa ya ɓaci ya basu amsa da ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Shi kansa a ƙarƙashin say ɗin Lulun yake bama dukiyarsa ba. Ballema ko sisi bai bata ba duk abinda suka nema ta basun kuɗinta ne. Wannan zantukan nasa yasa jikunansu yin sanyi, dama dai cikin dangin Abba ne da ƴaƴan Mama da wasu ana Ummah masu gulmar. Sai aka koma ƴar sinne kawunan jin kunya.

    Ana gobe ɗaurin aure akai dinner. Ita kaɗai Smart ya bari Lulu ta halarta. Shima kuma yaje. Dan tare sukaje tana gefensa riƙe da hannunta AA daya maƙale masa da ga hannun su Abdull ɗauke a kafaɗarsa. Sun isa a lokacin da kusan kowa ya gama zuwa. Dan har biki ya fara. Dan haka gaba ɗaya attention na mutane ya dawo kansu musamman yanda mc ke kwarzanta wanene Smart ɗin da matsayinsa a wajen ango Ahmad da ma Amarya Maryam. Nan fa dangin Ahmad ɗin masu ɗan jijji da kai irin na dangin miji suka shiga hankalinsu. Dan sun fahimci abinda sukeji basu yarda ba ashe gaskiya ne. Dan kamanin Smart da Maryam a bayyane suke. Nan fa ƴammata suka ruɗe da ganin matashin ɗan ƙwallon da duniya ke yayi mai ji da kuɗi. Sai dai Lulu dake fama da cikinta tana nane da abunta. Duk yarinyar data kama tana kallar mata miji kuwa zatasha harara. Shiko Smart nata ƙunshe dariya dan yana sane da matar tasa. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji, yayinda bakin Ahmad yaƙi rufuwa. Liƙi sosai daya ruɗa hall ɗin Lulu da Smart suka dinga zuba musu harda AA da Ahmad ya ɗaga sama yana sumbatarsa da faɗama mc cewar a sanar kowa ya sani wannan surukinsa ne. In sha ALLAH yanda suka taru anan bikin aurensu haka wataran zasu taru bikin auren AA da matar da zasu haifa masa. Wannan zance na Ahmad yasa kowa dariya a wajen tare da addu'ar ALLAH ya tabbatar da hakan. Ba'a tashi ba Smart ya ɗauki matarsa suka gudu dan taje ta huta saboda bata jimirin hayaniya yanzu....


      Washe gari aka ɗaura auren Ahmad Rabi'u Ƙoƙi, da amaryarsa Maryam Mika'il Mawashi akan sadaki naira dubu ɗari biyat bayan sakkowa da ga massalacin juma'a. Ɗauri aure ne daya samu halartar manyan mutane a dalilin gidajen biyu. Tare da ɗunbin masoyan Smart da ga jihohi daban-daban. Anyi walima da yamma. Zuwa bayan isha'i aka shirya kai amarya ɗakinta. Yayinda kaf yayunta harda su Sadiq ƙanana suka taru a falon Abba domin mata nasiha. Tasha kuka sosai har muryarta na dishewa. Dan yayun nata sun mata nasiha mai ratsa zuciya. Bayan an kammala Smart da Salim da Zubair da Kamal suka sakata a danƙarereiyar motar da Smart ya siya mata suka kaita gidan mijinta da rakkiyar mata iyaye guda biyar kawai. Da zasu taho ne ta rungume Smart tana kuka da jera masa godiya. Murmushi yayi a hankali yana mai lumshe idanunsa kafin ya ɗagota a jikinsa. Fuskarta ya riƙe cikin hannayesa yana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Daga haka ya shiga gaya mata daɗaɗan kalaman da saida ta saki murmushi. Sannan ya kamo hannun Ahmad ya saka masa nata a ciki ya ɗan bubbuga kafaɗarsa ya fice yana maida hawayen da suka cika masa ido shima. Smart na matuƙar so da ƙaunar ƴan uwansa matuƙa a rayuwa. Akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da bawani sakewa yake da su ba. Dama sauran duk sun fita harma sun shiga mota. Yana zuwa shima ya shiga kawai suka wuce........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 62"