Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 66

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣ 🔚
.......Tun haihuwarsu sukaso ɓoye mata suna, Ammah tace a kirata da sunanta bata son wannan ɓoye-ɓoyen. Dole ake kiranta da hakan, itace dai bata iya faɗa sai tace mata Ammah. Smart kuwa shine ya laƙa mata Hafcy gayu saboda ƴar gayence ta gaske. Duk da shekararsu ta shidda kenan itada Hassanarta Aysha iyayi a wajenta ba'a magana kamar wata babba can. Ko shi Smart ɗin yace mata Hassatuwa fushi takeyi kota sanya kuka. Hannunsa taja zuwa falon, inda sauran yaran suke kowa da hidimar gabansa. AA shi dama boss ne (like father like son), komai na ubansa bai bari ba. Baya son hayaniya bayi da yawan magana. Idan kaji bakinsa a gidan nan to al'amari yakai intaha, ga jarabar son ƙwallo da kallonta. Shekararsa takwas kenan da ƴan watanni. Sai ƴan biyu Aysha da Hafcy gayu. Bayan su ta ɗan huta kusan 3years kafin ALLAH ya kawo cikin auta dan tace daga shi fa Alhmdllh ta gama duk da dai Smart yace akwai sauran Ahmad bata gama ba. Shi auta sunan Uncle Yousuf yaci. Shikam akwai fitina, dan halinsa da Hafcy gayu iri ɗaya ne, itama Aysha bajin magana take ba, sai dai nata wani lokacin takan zama irin AA ba ko yaushe ta damu da shiga hayaniyar ba sai idan ita taso.

        “Wane ɗan jakar uba ne ya dakar min Babana?”.

   Lulu ta faɗa babu alamar wasa a fuskarta. Da sauri Aysha ta nuna Hafcy. “Wlhy itace Maah-maah. Yarinyar nan ta fitini kowa a gidan nan, dan ALLAH a maidata Nigeria wajen Ammah”.

     “Eh eh anji ɗin a maida nin, wake tsoron zuwa Najeriya ɗin ƴar iyayi kamar ma an kasa da ke”. Hafcy ce mai maganar cikin zaƙalƙalowa da tsiwa kamar su Lulu ana yarinya. Dan ita kam ko AA bata ragawa balle wata Aysha da suke kai ɗaya. A harzuƙe Ayshan ta miƙe tana huci itama da cewa, “Wai kaina zaki dawo halan. Kin san dai karanmu babu daɗi wlhy fasa miki baki zanyi bar ganin Papa mai goya miki baya yana gida ehe”.

     “To gwada idan zaki iya”. Cewar Hafcy.

    Tsaki mai ƙarfi AA da ke danna tab.. ɗinsa yana game na ball ya buga. Cikin jin haushi ya dubi Lulu da al'amarin yaran ya girmeta. “Maah-maah dan ALLAH kice ma ƴaƴanki su wuce ɗakinsu ALLAH sun isheni da hayaniya. Yaran nan suna bani ciwon kai ni gaskiya Nigeria zan koma. Gara naje wajen Daddy da Mamy”. (Ahmad da Maryam) dan kuwa ɗan gaban goshinsu ne. Ga kuma alƙawarin ALLAH ya cika sun haifa masa mata mai suna Rasheedah sunan mahaifiyarsa ana kiranta Nu'aimayah. 

     Cikin ɗoki auta da suke kira Uncle You ya ce, “Yaya nima zanje ka kaini wajen Mammah”. (Asma'u. Dan itama anyi bikinsu da Hussain yanzu haka tanada yaronta da yaci sunan Daddy). Fitowar Smart ya hana Lulu bama AA amsa. Gaba ɗayansu suka juya suna kallonsa saboda gyaran muryar da yayi. Aysha ce ta fara waro idanu waje. Yayinda Hafcy gayu ta dafe baki tana dariya. Duk rashin son hayaniyar AA sai gashi ya kwashe da dariya da faɗin, “Oh oh Papa waya maka kitso da kwalliya?”.

      Cikin mamaki Smart ya kai hannu ya shafo kansa da dama yake jin duk ya ɗaure masa. Ilai kuwa sai ga kitso. Da sauri ya kalli sashin da Lulu take tana faman kwasar dariya. Su Aysha na tayata. Babu shiri ai ya nufi mirror dake cikin falon....

     “Babbyyyy luvvvvvvv!!!” ya faɗa da ƙarfi ganin aika-aikar da tai masa. Mi yaran zasuyi in ba dariya ba kuwa. Yayinda Lulu ta arta da gudu zuwa bedroom shima ya take mata baya. Suko yara nata dariyar iyayen nasu dan ba yau suka saba gani ba, auta harda tsallensa duk da ba komai yake fahimta ba. Bedroom ɗin suka shiga zagayewa Lulu na dariya taƙi bari ya kamata. Cikin hakki da riƙe ƙugu ya ce, “ALLAH gara ki tsaya ma. Ni kikama wannan abun kamar wani ɗan daudu”.

     Dariya ta sake kwashewa da shi da masa gwalo. Tuni ya sake yin kanta ta haye saman gado. Tsalle ɗaya ya cafkota suka faɗa saman gadon gaba ɗaya. Kanta ya haye yana mintsininsa. “Wayyo zaka fasamin ciki na banu na, nauyi fa gareka kamar Shari'a wlhy.”

         “Sai dai ya fashe kuwa yau ba dai ni kikama kitso da kwalliya ba”.

     “To bagaka nan ka fito a binka shar ba kamar wani ƴar budurwa. ALLAH da kai mace ne da su aunty Bilkisu sunci kuɗin samari”.

    Cikin ɗage gira ya ce, “Sai kuma akai sa'a a namiji nazo ko. ALLAH kin gama da ni. Kigafa yanda yaran nan suke dariya. Yanzu wannan autan naki mai bakin surutu zai je yana bazani”. Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa.

          Dariya Lulu ta sake kwashewa da shi harda hawaye. Yayinda shi kuma ya zuba mata ido yana sake ƙwaɓe fuska. Kan nasa ta rungumo a jikinta cikin son sassauta dariyar tata take faɗin, “Sorry Babyna bazan sake ba. Ammafa ALLAH kayi ƙyau. Dan ALLAH ka yarda kullum na dinga maka kwalliya, kitson nan kuma ka barshi ai ba haramun bane ba dai tunda MANZON ALLAH ma kai ka faɗa min yanayi, mu dan ba al'adarmu bace ba dai shiyyasa idan mukayi lissafin baya dai-dai”.

      “Anƙi ɗin” ya faɗa yana ture mata hannu da sauka a jikinta ya koma gefe yana faman kumbura fuska shi a dole yayi fushi. Dariyar ta sake kwashewa da shi ta tashi ta koma kusa da shi ta rungumesa ta baya. Da ƙyar ta iya haɗiye dariyar ta ce, “Sorry Babyn Baby luv ɗinsa.”

         “Ban yarda ba, har zuciyarki ne?”.

    “Eh mana, ai kasan ni da kai bata ɓaci”. Ta faɗa tana kai masa kisses. A hankali ya lumshe idanunsa da kamota ya juyota ta dawo saman cinyarsa. Cikin wani irin narkakken kallo da sauke murya ya ce, “I love you so much FURAR DANƘO na”.

         “I love you too babyn baby luv. Amma kai ne FURAR DANƘO ba Mawaddat ba. Su Umma sun shekara sunan damawa har suka bar duniya baka zame musu farau-farau ba”.

     “Ina ban yarda ba Baby luv. Ke da Daddy kune FURAR DANƘO har su Sulaiman suka faɗi baku zame musu farau-farau ba. Amma ni Ummah ai sanadin alkairi tamun, dan maybe da bata min abinda tai ba da ban zama driver na haɗu da Mawaddatan'warahmah Isma'il Ibrahim Jiƙamshi ba. Ke dai i love you irin mara ƙarewa ɗin nan har a cikin aljanna”. Ya ƙare faɗa yana wani ƙanƙameta a jikinsa ƙwalla na ciko masa ido na farin ciki da jin tamkar ya haɗiyeta. Itama ƙanƙamesan tayi tana hawaye. Kara rungumeta yay ajikinsa yana murmushi ya ce, “Kinsan abinda yabani mamaki kamar yanda su *NAWAFF* suka samu rashin jituwa atsakaninsu karshe ya rikiɗe ya koma soyayya sai gashi muma hakan ce ta kasance agaremu *RASHIN SANI* yasa muka zurfafama junanmu ƙiyayya amma ni nayi tunanin *WUTSIYAR RAKUMI* ce tayi nesa da kasa ne, ban taba tunanin zan sameki ba, na ɗauka aneman aure ma ana nuna *SIYASA KO KABILANCI*”.

       Ƙara gyara zamanta tai ajikinshi tana murmushi ta ce, “Ni kaina bantaba tunanin akwai yuwuwar aure atsakaninmu ba ganin irin *TAKUN SAKAR* Daya dinga shiga tsakaninmu, sai dai da yake ance *RAINA KAMA* kaga gayya, niba abinda zance sai dai in kara godema ALLAH daya mallaka min kai amatsayin miji kamar yanda *ABDUL MALEEK* (bobo) yayi, kuma ina kara godewa ALLAH daya baroni daga rayuwar *BAKAR INUWA* wacce gwanda rana da ita, kuma gwanda ni tawa rayuwar da irin rayuwar da zaka kasa tantance *KANWAR UWACE KOH KISHIYAR UWA*”.

        Kallanta yay ya ce, “Wannan ai ba *SABON AL'AMARI* bane in kikai duba da irin yadda mutanan yanzu suka kware da *SARAN BOYE*, sai dai sun mance shi *CIKI DA GASKIYA* wuƙa bata huda shi, kuma gwanda irin rayuwar da kikayi da wacce mutane suke jefa kansu *A SANADIN BIKIN SALLA*”.

       kallan shi tai itama cike da shauƙi ta ce, “Toh ai kasan su mutane basu *GUDU DA WAIWAYE*, sun manta cewa *MAKAUNIYAR KADDARA* duk inda kai tana tare da kai kamar yanda *NIDA AMINIYATA** aka haɗa baki da ita don amin fyade sai dai ta manta shi *KWAI CIKIN KAYA* wahalar fita gareshi, kuma shi *KUKAN KURCIYA* jawabine me hankali kadai ke iya ganeshi”.

       Murmushi yay yana shafa kanta ya ce, “Kamar yanda nima aure na dake nake  masa kallan *AURAN KADDARA KO BIYAYYA* a lokacin nayita tunanin naƙi amincewa saina tuna da irin wahalar da star din littafin *BAN SAKETA BA* yasha, shi ahakanma bai saketanba saboda rabuwa da abinda kake so balai ne wanda yafi *KARAYAR ARZIKI* zafi kidaina tuna abinda ya wuce domin duk wata *DAUDAR GORA* ciki ka shata”.

      Ƙara faɗaɗa fuskar ta tai da wani murmushin tace harkasa na tuna da irin soyayyar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul majeed Shahan-Shan na daular ruman yake nuna ma Fareedah Iffah, duk da alokacin suna cikin fuskantar tashin hankali da matsaloli, sai dai *MUTUM DA DUNIYARSA* ya dace ya gyara kansa.”

      Murmushi ya sake saki mai sanyi wanda ya kara fidda ainahin kyan fuskarshi yace duk da irin tarin kaunar da yake mata bata kai kwatan kwacin wacce nake miki ba domin kedin *FURAR DANKO* ce ashekara ana damu ba farau farau”.

     “Tabbas na yarda da irin son da kake min domin da *BABU SO* ba abinda zai kawo kishi Babyn Baby luv” ta ƙare maganar da manna masa kisses shi kuma yana lumshe ido da sake ƙan ƙameta.  A haka yaran dake laɓe suna leƙensu da saurarensu suka shigo da gudu suma suna faɗin “Maah-maah!! Papa!! I love you so much.”✍️
      *_Kai to nimafa I love you ɗin nan irin trillions wujiga-wujiga manya-manya nan masoyan amana🤣😂👏_*


*_ALHAMDULLAHI YA RABBI👏😭_*


      _ALLAH na gode maka daka kawoni wannan rana ta Friday/10/2023. Abinda nai kuskuren rubutawa ALLAH ka gafarta mini kuma da kuka karanta ya gafarta muku. Sannunku-sannunku da ƙoƙarin haƙuri kuma. ALLAH ya saka muku da alkairinsa ya bar zumunci. Yanda kuka so ni domin ALLAH ina fatan kuma UBANGIJI ya soku haka ku da zuri'arku baki ɗaya. ALLAH ya karemu ya tsaremu baki ɗaya. Ya sanya albarka da tarin alkairi a garemu. ALLAH ka gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama. Marasa lafiyarmu ALLAH ka basu lafiya. Masu ciki ALLAH ya saukesu lafiya. Ƴammata da zawarawa ALLAH ya baku mazaje na ƙwarai da sukafi mazan novels ƙayatarwa da nagarta. Mu da muke gidajen auren namu ALLAH ka cigaba da bamu zaman lafiya. Masu neman haihuwa ALLAH ka basu idan alkairine, idan ba alkairi bane ALLAH ka musanya musu da abinda ya fita alkauri. ALLAH ka shirya mana yaranmu, wanda suke shaye-shaye ALLAH ka yaye musu. Masu tasowa da basayi UBANGIJI ka cigaba da kare mana su. Ya rabbi ka kawo ma musulmanmu dake cikin wani hali a ƙasashensu mafita, ALLAH ka karya azzaluman kafirannan. Ya rabbi ka kawo ma bayinka ɗauki na halin da suke ciki.😭😭👏_


   *Duk wanda naima kuskure a yayin rubuta littafin nan ya yafe min dan ALLAH. Dan zata iya yiwuwa wannan shine littafin Bilyn Abdull na ƙarshe a duniya. Zaku iya jin saƙon mutuwata akoda yaushe. Idan hakan ta kasance kumin addu'a da neman gafarar UBANGIJINA dan ALLAH 😭😭🙏*.


Ta ku ce dai har kullum.
Bilkisu Ibrahim Musa (Bilyn Abdull ce😘🤳)


    
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 66"