Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Furar Danko Book 2 Page 7

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗


 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣

 

……..Kwanan Dada goma sha ɗaya ta fara shirin komawa wajen mijinta. Lulu ko ta maƙale tace ƙafarta ƙafarta dan bazata sake zama ita kaɗai anan Canada ba ciwo ya halakata. Cikin lallashi Dada ta nuna mata bazai yiwu ba, ta kwantar da hankalinta ai Tajuddeen na dawowa nan ɗin duk da ba’a gidan zai zauna ba. Tsaf ta tubure cewar ai ita ko ƙasa ɗaya ma bazata zauna da shi ba. Tunfa Dada na lallashinta harta birkice mata da masifa cikin ɓacin rai. Amma hakan baisa Lulu ta yarda zata cigaba da zama a Canada ba. Sai ma cewa tai ita gida Nigeria zata koma to. Tofa babbar magana, hankalin Dada ya tashi, dan tasan taurin kai irin na Lulu sarai. Alh. Sulaiman tai kira ta sanar masa. Washe gari sai gashi ya sake dawowa Canadan. Shima balbale Lulu yay da bala’i tare da zageta tas ita da Daddy sannan ya saka Dada tattaro masa passport ɗin Lulun da komai da zai iya taimaka mata fita a ƙasar ya wuce da su harda na Ummita ma. Wannan abu ya tada hankalin Lulu, hakama Dada sai al’amarin ɗan nata ya fara bata mamaki kuma. Dan sai take ganin ya zafafa da yawa, miye na ɗauke passport kamar wasu masu son kidnapping yarinya?. Amma ta kasa iya masa magana dan harga ALLAH tana shakkar ɗan nata kasancewarsa ba kanwar lasa bane ba.

*_NIGERIA_*

Alh. Sulaiman ya koma Nigeria bisa matsawar Tajuddeen dole yakai kotu akan alƙali ya saki Lulu, amma sai ya bashi amsa da cewar sai ma’aurata duka sun gurfana a gabansa zai iya aikata hakan. Zancen ya matuƙar bashi haushi ya yayyaɓama alƙalin magana duk da kuwa suna mutunci. Shiko yay biris da shi dan yace bazai aikata abinda ya saɓaba, taya zai kama kashe aure ma babu masu alaƙa da auren kamar a garin da babu shari’a, to yace yamawa hukunci kenan. Kusan alƙalai biyu ya sake tunkara bayan na farko amma amsar duk iri ɗaya ce suma since sai ma’auratan sunzo, dan koda aka aika sammaci gidan su Smart sai akace ma nai kai takardar ai Smart bama ya ƙasar, bakuma asan randa zai dawo ba ma. Alƙalin ƙarshe ne ya bukaci ganin iyayen Smart. Koda Abba yaje sai ya nunama Alh. Sulaiman yafisa sanin takan duniya, dan cayayma alƙali ai yaron da matarsa suna tare acan turai, shi Alh. Sulaiman shirmensa kawai yake yi, yasa a kira masa Smart a waya, akayi kuwa sa’ar samunsa, sun tattauna sosai da alƙalin akayi sa’a kuma shima Smart ɗin yace yana tare da matarsa Alh. Sulaiman yana shirmensa ne kawai saboda yana son raba auren dan taƙi ɗansa. Alƙali kuwa ya samu Alh. Sulaiman yay masa tas tare da gagaɗin yabar wannan shirmen da zubda mutunci yara su rayu da juna tunda sunce suna tare, ɗanshi kuma yaje ya nema wata. Wannan makirci ya matuƙar ƙona masa zuciya, dan haka ya ƙullaci Abba a ransa da fara shiri na musamman….

Taƙaddamar Daddy da Alh. Sulaiman ta matuƙar sake ɗaukar zafi a wani yanayi shi da abokan haɗin kansa su Hon. Nakowa. Duk da dai Alh. Sulaiman ɗin bawai ya fito ya faɗa musu komai da komai bane a tsakaninsa da Daddy bayan wanda ya shafesu su duka ba, dan shi yana nuna musu TAKUN SAƘARSA da Daddyn dai iya tasu ce data shafesu. Bai kawo ɓoyayyen al’amarin dake a tsakanin su sam. Sun ƙara shirya sabon plan akan Daddy, tare da shiga kogin tunani da binciken ta yanda yake bibiyar al’amarin su. Musamman ma shi Alh. Sulaiman da yaji har poisoning ɗin mahaifinsa da yasa akayi wai Daddy ya sani. Wannan zance ya matuƙar tada masa hankali, dan daga ALLAH sai shi sai yaronsa Malami suka san wannan sirrin. Duk da dama gubar da suka bashin bata kisa bace, wadda zata kwantar da shi jiyyace kawai na tsawon watanni harya samu kammala shigo da abubuwansa wanda ya tabbatar da in har mahaifin nashi na tsaye akan ƙafafunsa za’a iya samun matsala a wannan karon. To Alhmdllh burin nasa ya cika, dan kayayyakinsa da suka taso daga ƙasar Mexico sun iso lafiya, inda cikin nasara yay hada-hadar rabawa customers ɗinsa shi da abokan Business ɗinsa da ayanzu sukafi ƙarfi a kudancin Nigeria. Bawai baya huɗa da hausawa ƴan arewa bane akan harkar, akwai su jefi-jefi a cikinsu, sai dai sunada tsoro matuƙa ba kamar ƴan kudancin ba, sunfi yarda su zama dilolin cikin gida bawai masu ɗakkowa daga wajen ƙasar ba. Sannan wasun su basa fito musu da kurwarsu a fili sai dai kawai ace business ne na kaya ko wani abu idan an haɗa sai a sakko kayan da suke shigowar da shi. Akan samu matsala idan mutum ya farga da wuri, dan mafi yawan hausawan da ake riftawa a ciki da zaran sun gane sukan zare hannunsu, sai ƙalilanne da ga ciki masu busashiyar zuciya da son dukiya ke afkawa a cigaba da harka kawai. Wasu kuma tsoro, dan daya zamana ka gane ka fidda kanka to lallai sai su Alh. Sulaiman sun kashe ka ta inda babu wanda zai gane su suka aikata. Hakan shine ya faru Da Daddy, dan kuwa dai Alh. Sulaiman yaja Daddy a jikinsa lokacin daya fahimci shine babban yaron mahaifinsu na gaban goshinsu da yake tsindum akan harkar shigar kuɗi da fitarsu, saboda duk wani babban business na ƙasashen ƙetare na Alhaji Sufi Garko Daddy shine tsaye akai. A lokacin Alh. Sulaiman yana buƙatar kuɗi masu yawa domin shigo da kayansa, sai dai kuma yana tsoron tunkarar mahaifinsa da batun dan bazai bashi ba kai tsaye sai ya bisa da tambayar ƙwanƙwanto. A hankali yayta hillatar Daddy da sunan abota har suka zama aminai ma sosai, kamar wasa ma sai shaƙuwa ta gaske ta fara shiga tsakaninsu ba kamar yanda Alh. Sulaiman ɗin ya tsara ba da farko. Tafiya tai zurfi sosai tsakaninsu har Alh. Sulaiman ya fara jan ra’ayin Daddy suka ƙulla alaƙar business na kawo motoci, sai dai kafin hakan sai da ya fara kafa masa tarko na musamman akan dukiyar mahaifin nasa, inda wasu manyan kuɗi suka dulmiye Daddy ya rasa yanda akayi, hankalinsa ya tashi matuƙa a lokacin, amma sai Alh. Sulaiman ya kwantar masa da hankali tare da maye gurbin kuɗaɗen da aka rasa ɗin yace Daddy ya dinga biyansa a hankali, wannan yasa Daddy sake sakin jikinsa da shi saboda rufa masa asirin da yake gani yayi akan abinda bai taɓa faruwa ba dan shi mutum ne mai takatsantsan da gaskiya shiyyasa Alhaji Garko ya yarda da shi matuƙa, shi kuma tsoron rasa wannan yardar daga mutumin kirki irin Baba Garkon ya sashi shiga a tashin hankali lokacin da kuɗin suka salwanta, iya bincike kuma bai iya gane komai ba. Sun fara business na safarar motoci daga waje zuwa gida Nigeria. Wannan shine silar buɗe *_JIƘAMSHI MOTO’S_* Kamar abin arziƙi Business ya fara tafiya yanda ya kamata, alhkairai suka ƙara buɗe hanyar shigoma Daddy tako ina. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake ɗagawa dukiya ta sake zama a hannunsa ya kuma biya Alh. Sulaiman kuɗinsa. Hakan ya saka Alhaji Garko a farin ciki, dan shi irin mutanen nan ne marasa baƙin ciki wana ƙasa da su. Maƙudan kuɗi ya sake bama Daddy akan ya ƙara a business ɗin, duk da kuwa dama can bawai ya barsa haka bane ba, yana masa alkairin tare da fidda masa hakkinsa na albashi mai tsoka. Amma sai wannan karon ya kasance na musamman, ba komai yaja ra’ayinsa dayin haka ba kuwa sai ganin yanda Daddy shima ya fara sanin ciwon kansa. Alh. Sulaiman da Daddy da sabbin abokan daya sani a dalilin Daddy su Alh. Misau sun cigaba da juya taro yana komawa sisi batare da Daddy yasan ainahin sirrin kasuwancin nasu ba bayan abinda aka sanar masa, dan ta ƴan bariki kawai ake masa da sunan shigo da motoci da babura, da wasu nau’o’in kayayyakin daban-daban. Sai da shekaru suka ka kusan huɗu a tsakani sannan ya farga a dalilin wani lokaci yaga cocaine da ga cikin kayan nasu da aka killace a store batare da su Alh. Sulaiman sun san yaya akai basu cireta ba sanda suke cire sauran.  Hankalin Daddy yay masifar tashi a wannan ranar, dan ya horu da ƙyamatar harkar shaye-shaye ma gaba ɗayanta a dalilin yanda ubangidansa Alhaji Sufi Ado Garko ya tsanesa matuƙar tsanar da sai da ya shiga ya fita da dukiyarsa cikin gwamnati aka kafa babbar hukuma da in ta kamaka da irin wannan kayan sunanka sorry kawai. Daddy baida yawan faɗa sam, sai dai mutum ne mai zuciya idan ka kaisa maƙura. Dan haka a wannan ranar ma ya tunkari Alh. Sulaiman cikin tashin hankali. Shima Alh. Sulaiman ɗin ya girgiza matuƙa shi da abokan huɗɗarsa, saboda suna kiyaye duk wani abinda zai iya kai idon Daddyn, amma sai gashi aiki ya buɗe a gaɓar da suke cin moriyar al’amarin fiye da baya. Da gaggawa sukai zaman meeting na musamman akan dolene fa a kawar da Daddy a duniya kamar yanda akema duk wanda ya nema bijirewa. Sai dai mi Alh. Sulaiman yay saurin ƙwaɓarsu akan karma su fara wannan taɓargazar, dan duk wani motsin Daddy a idon mahaifinsa Alhaji Sufi Garko yake, saboda yanda yake ƙaunarsa. Ya tabbatar musu idan suka taɓa Isma’il Jiƙamshi cikin ƙanƙanin lokaci komai zai buɗe musu, sudai jinkirta suyi tunani. Wannan furuci na Alh. Sulaiman shine ya kawo rabuwar kai, dan wasu na ganin ai yayi hakanne saboda Daddy abokinsa ne kawai, sannan yaron mahaifinsa. Amma inba hakaba su sauran da suka kawar ai akwai na jikinsu suma. Duk yanda Alh. Sulaiman yaso su fahimceshi hakan bata faru ba akai baran-baran. Wannan shine dalilin rabuwar Alh. Sulaiman da su Hon. Nakowa. Sannan yay amfani da wannan damar ya nunama Daddy goyon baya tare da tsarashi kan cewar shima bai san komai ba yaudararsa akeyi kamar yanda shima Daddyn akai masa, amma ya fita da ga wannan gaɓar. Hakan ya bama Daddy nutsuwa, inda ya yarda da Alh. Sulaiman ɗari bisa ɗari suka cigaba da amintakarsu tare da cigaba da business ɗin motocinsu kamar yanda suka fara. Sai dai fa a yanzu Daddy a ankare yake ƙwarai da gaske. Wannan ya saka Alh. Sulaiman canja taku. Shekara biyu da faruwar haka Mawaddat mahaifiyar Lulu ta dawo Nigeria daga karatu. Akwai shaƙuwa matuƙa tsakanin Mawaddat da Alh. Sulaiman yayanta, dan suna ɗasawa matuƙa duk da dai ita kowa a gidansu na sonta da ji da ita kasancewar itace mace sai autarsu, sai ƴaƴan ƴan uwa da Dada ta riƙa mata. Ƴar cikinsu dai su biyun ne kawai mata ita da auta Sultana. Akwana a tashi da dawowar Mawaddat Nigeria ALLAH bai haɗata da Isma’il Jiƙamshi da take yawan ji a bakin mahaifinta da ƴaƴanta ba sai a randa yazo gidansu game da kawo takardun matarsa da Alhaji Sufi yace a kawo. Wannan kuma shine karo na farko da ya shiga gidan shima dan duk iyakar huɗaɗarsu da Alhaji Garko da Alh. Sulaiman iyakarsu office ne da ma’aikatu, sai kuma gidan Alh. Sulaiman ɗin wannan Daddy yasha zuwa. So ne farat ɗaya ya shiga zuciyar Lulu, sai dai ta fahimci bazata taɓa samun kulawar wannan haɗaɗɗen guy ɗin ba (Sannan su Daddy anaji da ƙarfin samartaka ba’a ruɓe ba😂🙏). Ta nema shawaran Yayanta Sulaiman dan babu wani kunya ko shakku ta sanar masa. A lokacin dariya Alh. Sulaiman ɗin yayi da faɗin, “Anya kuwa zaki iya Kandala? Dan yanada mata da yara biyu twins sannan shi ba ɗan kowa bane face wanda Baba ya ɗaga darajarsa ta hanyar ɗaurasa akan dukiyarsa”. (Dan sukan kirata da sunan Kande ne saboda bayan haihuwarta ita ɗaya tilo a cikinsu mace Dada ta sake jimawa bata haifi mace ba sai a haihuwarta ta ƙarshe ta haifi autarsu mace mai suna Sultana, sai dai Sultana sikila ce ko isashen lafiya bata da shi yarinyar. Gata da wayon tsiya da shiga rai)………✍️

_Ayi haƙuri mu cigaba a next page muji sauran._

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Post a Comment for "Furar Danko Book 2 Page 7"