Gidan Aunty Book 1 Page 71-72
BOOK 1
Not edited
Page 71-72
🔚
Tunanin abunda ta gani cikin pillow ne ya fi komai d’aga mata hankali, yanxu gabaki d’aya hankalinta ya karkata kanshi, so take tasan ko yana lapiya , wayarta ta soma
dubawa ganin batanan ne yasa tayi saurin barin d’akin har zata hau sama sai ta fasa ta sakko kasa , Wanda ta gani akasanne ya bata mamaki bata yadda da hakan ba shiyasa ta ‘kara matsowa dan tabbatarwa kanta ,tabbas ,”shine” ta kara nanawata, da Sauri ta karasa inda yake , a hankali ta kai hannunta kan goshinsa , sanyi goshinsa yayi hankali a tashe ta soma jijjigashi, kuka ta fara ganin abun kamar a mafarki gashi ko motsi ya kasa yi , gabaki d’aya ta rasa abunyi, ruwan da ta gani tayi saurin ‘balle murfin tare da yayya famasa ruwan amma gabaki d’aya kamar ba mutum take yayyafawa ba , rud’ewa ta karayi ga wani irin murd’awa dataji cikinta ya soma yi mata , salati kawai ta soma hannunta d’aya dafe da mararta yayin da d’aya hannun nata yake kan fuskarsa, kuka kawai Tahee take da iya ‘karfinta ganin ko motsi bayayi,rubutun da dada ta batane ya fado ranta da Sauri ta mi’ke duk da tsananin murd’awa da cikinta yake mata , fridge d’inta na sama ta hau cikin Sauri sauri gudu gudu , tana bud’ewa Kuwa ta ganshi, da Sauri ta dauko ko kallan gabanta bata yi, Daidai inda yake ta nufa , cikin Sauri ta ‘balle murfin robar ta soma yayyafa masa kafun ta bud’e bakinsa ta saka masa ruwan kad’an, tari ya fara sosai wani ba’kin ruwa ya fara fitowa daga bakinsa, adduar da oumma ta koya mata ta soma kafun ta fara tofamasa, gabaki d’aya fuskarsa tayi zufa duk da sanyin Ac dake ratsa ko ina na falon, ruwan adduar ta kara saka masa ,yanxu ma tarine ya sarkesa jijiyoyin kansa gabaki d’aya sun fito waje, ta d’au kusan 20 minutes tana masa addua kafin ya soma ajiyar zuciya , gyara masa kwanciya tayi yanda zai ji dadin sakewa . Tsawan lokaci Tahee ta d’auka tana bin kyakkyawar fuskarsa da kallo, a zuciyarta kuwa addua take faman yi masa , dabarace ta fad’o mata, babbar plasma Tvn ta ta kunna tayi connecting, suratul Bakara ta kunna ta saka volume dadda zata dunga ji daka kitchen, kafun ta kulle kofar shigowa part d’in gabaki d’aya , cikin d’auri ta shiga kitchen dan ta Sama musu abunda zasu ci, chips tayi masa tare da pepper chicken , sai omelette din da ta kara yi masa , amaimakon ta had’a coffee yau hakanan zuciyarta bata yadda da kayan coffe din ba shiyasa ta d’ona ruwan tea me cike da kayan kamshi,Lokacin data duba a gogo almost 10:30 tayi , a dinning ta jera musu breakfast d’in kafun ta dawo inda yake , fuskarsa ta soma shafawa a hankali, kusan tsawan 2 minutes kafun ya d’an saki a jiyar zuciya, idanuwansa da sukai masa nauyi ya bud’e a hankali bakinsa d’auke da addua, zuba mata narkakkun eyes d’insa yayi itama shidin ta ke kallo, temaka masa yayi ya zauna kafun ya kalli inda yake da mamaki, kokarin tuna abunda ya faru yake amma ya kasa ,” me yasa na ke kwance anan” ya furta cikin sanyin murya , kallansa Tahee tayi na ‘yan sakanni kafun ta furta “ ka gajine shiyasa bacci ya d’auke ka , ynxu ka tashi kayi Wanka sai muci breakfast “, a gogon hannunsa ya kalla ganin lokaci yayi saurin mikewa tsaye tare da ita a jikinsa, dining din ya nufa dakansa yayi serving abincin a plate, jinsa yake kamar an cire masa abu me nauyi a kirjinsa ga bakinsa kwata kwata ba appetite din abinci,batare da yace mata komai nan ya soma bata abincin abaki har saida ya tabbatar ya isheta, zata bashi yayi saurin kawar da kansa gefe , “ I lost my appetite, and inaso nayi wanka “, kamar zatayi kuka ta kallesa “ ko na dafa maka wani abunne “ murmushi ya sakar mata sosai da ya dad’e beyi kamar saba “ don’t worry bari na fara wanka , okay ?”, a sanyaye ta furta “okay”, wayarsa ya mika mata kafun ya furta “ used it “, tana kar’ba ya juya ya nufi upstairs,kallan wayar tayi na ‘yan seconds hakanan yau take dan taga abun cikin wayar, da pin ajiki abun mamaki tana saka hannunta pin d’in ya bud’e take a wajan hotan ta ya bayyana lokacin da take part d’in Ammey, da Sauri ta shiga photos gabaki d’aya babu hotunansa a ciki sai hotunanta da ita kanta bata san lokacin da aka d’auke ta ba, wasu hotunan bacci take aka d’auketa , hatta lokacin da ta Samu matsalar kai, da ta fara shigowa part d’insa akwai hotunan a ciki, hawaye ne ya fara tarar mata a ido tayi saurin sharesu, soyayyar mijinta na kara shiga cikin zuciyarta , a hankali ta cigaba da kallan hotunan ita kadai tana murmushi.
********
*********** A cikin part d’in Ammey kuwa a zuciye ta fasa wani babban glass d’in jug, gabaki d’aya idanuwanta sun canza Sabida bala’in da yake cinta , sai faman zagaye inda aka kawatashi kamar wajan iska take ko tsoran a ganta bata yi, daga gefe d’aya wannan mutumin da yake yawan zuwa d’akin amrah shima zaune, dukda ba a ganin fuskarsa a yadda idanuwansa sukai ja mutum zai gane yana cikin tsan tsan tashin hankali da bacin rai, a fusace Ammey ta jiyo kan mutumin, “kace mun kasaka kwalbar ban inda ya dace Garin ya akai komai zai lalace lokacin da burinmu yake gab da cika, bazan d’auki a sara ba , bazan d’auka ba , na dad’e da tsara rayuwata , babu Wanda ya isa yace zai lalatamin,zan kashe sa , sannan na kashe duk Wanda yayi run’kurin ruguzamun shiri, kamar ydda nayi rantsuwa da dodo , bazan sa’ba ba dole burina ya cika ,yau ba sai gobe ba zan fara aikina dole na basa babbar kyauta da zai ‘kara ruguza farincikin sa har abadah”, ta karasa zancanta tana sakin wani d’an iskan dariya , taso wa mutuminnan yayi daga zaunan da yake , inda Ammey take ya nufa tare da kamo hannunta d’aya yana shin shinar wuyanta, tsaki Ammey taja tana turesa , a zuciya ta furta “ wannan ba lokacin da ya dace bane , raina a bace yake karka kara batamin, kaje wajan waccan karuwar yarinyar tukunna me zubin arha banza da kasaba latsawa, komai ina sane dashi”, da karfi ya matse hannunta guda d’aya , cikin wata kausash shiyar murya ya furta “ ke baki isa ki hanani jikin kiba sabida ked’in mallakina ne , dole na kashe mijinki dan naga alama yana kokarin shigar mun hanci da kudun duni, yanxu zan barki sabida raina a ‘bace yake , akan duk da haka yau zan kawar da aikina akan d’an talikin can, sannan karki manta dole ki fara aikin boka yanxu, bazan taba yadda jinin da ke cikin waccen shed’aniyar ya fito duniya ba , zuwan shi duniya kamar ruguzama shirin da muka dad’e munayi ne ,inaso a salwantar Dashi cikin ‘kan’kanin lokaci, dan wannan karan bana bu’katar kuskure , kafun na koma kan yan iskan yarancan da suka dawo, suma rayuwar su tana cikin gangara “, ‘karar fad’uwar glass sukaji da Sauri suka juya dan ganin ko wanene, babu kowa a wajan da Sauri Ammey ta nufi inda glass d’in ya fashe , nan ma babu kowa a wajan sai glass d’in sai kuma labulen da aka d’an bud’e da alamun mutum ya tsaya a wajan, cikin tashin hankali Ammey ta ‘kara dubawa babu wa kowa a wajan gabaki d’aya , a’bangaran mutumin kuma yana jin fashewar abu ya d’auki wani Jan zobe ya saka a hannunsa tare da soma karanta wasu abubuwa marada a dad’in ji take a Wajan ya ‘bace gabaki d’aya. Da Sauri Ammey ta shiga cikin falon ta nan ma ba kowa a jan, cikin bacin rai ta d’auki wani d’an karamin aban kifi fari tas Dashi ta buga a kasa tare da caka masa ‘karamin wu’ka ko tsaran azo Atarar da ita bata yi, a kausashe ta soma magana “ inaso a kasheta , sannan aka she mun abunda ke cikinta , sanadin hakan inaso zuciyar mujinta ya buga” sai kuma ta fara ‘kyal’kyalewa da dariya tare da nufar d’akin ta na sa azuciyarta tana ayyana duk Wanda yayi gangancin saurarar magan maganinsu na d’azu to ya kawo kansa Halaka dan sai ta kashe koma wanene “.
✨✨✨✨✨✨
Apart d’in Tahee kuwa har yanxu karatun Alkuranin da ta saka bata kashe ba sai ma ‘kara volume da tayi da Zata hau sama , Hakanan take jin ranta babu dad’i lokaci zuwa lokaci sai ta ta’ba cikinta ,intatuna halin da mijinta yake ciki sai kuma taji zuciyarta na bugawa haka kurum, dakin da yake ta shiga lokacin harya shirya cikin shigar’kananan kaya da kullum yake futo da ‘kyansa da kwarjininsa, ‘kura masa ido Tahee tayi hakanan take ji bata so ta dena kallansa , har ya ‘karaso inda take bata sani ba sai daddad’ar iskar bakinsa me ‘kanshin mint da ya hura mata a fuska,nunfashi ta sauke tare da ajiyar zuciya “ wannan kallan fa ,kamar kina missing d’ina”, bata san lokacin da hawaye suka fara sakko mata a ido ba da ita kanta bata san na Menene ba , cikin tashin hankali ya ri’keta a rud’e ya soma tanbayarta “ me ya faru?, me kikosa?, baki da lapiya ? Cikin ki? Baby…..”, bai ‘karasa ba ta had’e bakinsu waje d’aya , sosai take kissing dinsa kamar me jinyunwar haka , kokarin raba bakinsu yake ta kara had’e lips dinta cikin nashi yau da kanta take basa hot kisses d’in da yake neman zautar dashi,be hanata ba sai ma ‘kara gyara mata tsayuwar ta yayi, tana sakin bakinsa ta soma sunbatar face d’insa ta ko ina, kafun ta rungumeshi tana sakin wani saban kukan,” ya ilahiiiiiiii, please banasan kukan nan yana ta’bamun zuciya please kiyi shiru karki d’agan hankali”, gyada masa kai tayi kafun ta soma share hawayen , kallanta yayi sosai kafun ya furta “ me yasa ki kuka “ ajiyar zuciya Tahee ta sauke , kafun ta bud’e bakinta da yayi mata nauyi “ Nima ban sani ba , kawai banaso ka fita ne yau” murmushi ya saki me d’au sauki yana jan hancinta,” am sorry kinji akwai operation d’in da zanyi wa wani a zuciya , but zan i promise insha Allah zan dawo dawuri,okay ?”, kamar zatayi kuka ta d’aga masa kai ,”oya smile “ ya fad’a yana kara sakar mata wani murmushin, a hankali ta murmusa dukda har zuciyar batajin dad’i sam, “please kaci abinci kafun ka fita “,d’an risina mata yayi kafun ya furta “ duk yadda madam tace “, bata san lokacin da murmushi ya su’buce mata ba sai da ta murmusa, har sukaje wajan dinning hannunsu na sar’ke da na juna , da kanta tayi feeding d’insa a baki har lokaci kuma bata dena binsa da kallo ba , wayarshi da ya bata d’azu ta mika masa , kiss yayi mata a kumatu ka fun ya d’auki main wayarsa dake kan dinning d’in , ko a bakin kofar fita daga falon nasu ‘kin sakinsa tayi har hakan yaso bashi dariya da Alama yau rigima takeji, da ya juya zai fita sai ta ri’kosa ko tace “ zawj amma babu Wanda zaiyi operation din sai kai “, hannunta biyu ya kama kafun ya mayar da ita cikin falon ya dur’kusawa, “ zan dawo ba da dad’ewa ba , yau naga alama rigima kikejii, take care of you and my baby, I love you “, a sanyaye ta furta “ I love you too, kafun ta soma masa adduar data saba yi masa idan zai fita “ har zuciyarsa yaji dad’in adduar da tayi masa haka kurum yaji kamar ya fasa fitar shima sabida kewarsa da yaji ya soma yi lokaci guda Amma ba damar hakan sabida operation d’in da zaiyi.
A kan kujerar da ya zaunar da ita anan ta kwanta, ita kad’ai ta dungajin kad’aici na damunta , Addu’ar neman tsari ta soma yi a cikin zuciyarta tare da yiwa mijin ta adduar dawowa gida lapiya,tana zaune akan kujerar wani wahalallan bacci mara dad’i ya d’auke ta .
✨✨✨✨
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
ABUJA
A ‘bangaran zarah da khaleed wata irin soyayya suke wa oumma , duk Wanda ya gansu tare da oumma babu me cewa ba Itace ta haifesu ba , sosai Hutu da kwanciyar hankali ya bayyana a jikin oumma ta zama babbar hamsha’kiyar mace , a yanxu Dady ya bud’e mata babban super market da ya zama mallakinta komai na ciki a ‘kasar waje ake kawo mata musamman da dady ya had’a ta da wata matar abokinsa da take zaune a London ita da yaranta, a tsakaninsu sosai Amin ta ya shiga tsakaninsu har ya zam to sun zama ‘kawaye sosai duk da har yanxu hajiya madina bata taba zuwa nigeria sun had’u ba saida ko kaya za a kawo akwai Wanda take sawa ya kawowa oumma da ynxu ake wa la’kabi da Hajiya maryam.
A yanxu ma shirye shiryen tafiya BUNKURE suke da dady yace zasu kai wa ziyara kafun su wuce saudiya, da farko oumma ta so ‘kin zuwa amma dady ya zaunar da ita tare da yi mata nasiha akan tawakkali da hakuri, duk da yasan macece me hakuri da juriya dan ko shi saida ne. Gabaki d’aya gidan tare zasuje hatta hajiya da itama tace da ita za ‘ayi tafiyar , A kano zasu fara sauka ta jirgi kafun su bi ta mota zuwa BUNKURE .
Sanye zahra take cikin shigar doguwar Abaya pink colour tare da small fashion bag d’inta fara da shoe din ‘kafarta me d’an tsini shima white colour , tayi rolling da mayafin abayar da ya kasance shima pink colour , babbar wayar ‘kirar iPhone 13 promo max d’inta ita bayn kwabar pink colour ne me d’antan barin barbie, sosai kayan sukai mata kyau, dukda ba wani makeup ne a fuskartaba amma sosai tayi kyau, d’ayan hannunta kuma janye yake cikin medium size trolley bag d’inta. Khaleed ne ya fito shima cikin shigar ‘kananan Kaya d’aya hannunsa shima janye da trolleys guda biyu bayansa hajiya ce itama taci uban adonta na tsofaffi har da ba’kin glass a idanunta. Oumma da dady ne suka fito suma sosai shigarsu ta ‘kayatar, dady sanye yake cikin wani Boyel d’in manyan kaya blue colour da suka ‘karawa fuskarsa dattako da annuri, oumma kuma sanye take cikin wani tsadajjen material pink colour sai adansa flowers me blue da yake jiki, ta kalmin kafarta da Jakarta sai ya kasance blue colour yayin da mayafinta ya kasan ce pink colour , ita kadai sai walwali take , duk inda ta motsa sarkar wuyanta da stone Suma sai sun ‘kada,kallan juna zahra da khaleed sukai , kafin zahra ta karasa wajansa tana masa rad’a a kunne, shima khaleed kamar ‘karamin yaro yayi mata rad’a a kunne suka ‘kyal’kyale da dariya, cikin had’a baki suka furta “ Oumma Wlh kunyi matching sosai 100%”, sun kuyar da Kai oumma tayi cikin jin kunya ganin hajiya a falon tarasa Yaushe zarah zata dena ‘barin bakin nan nata , itama hajiya da ta fuskanci oumma taji kunyar maganar zarah sai tayi shiru batare da tace komai ba , Dady kuwa kanshi kawai ya girgiza aranshi yana tunanin lokacin da zahra zatayi hankali. Basu ‘bata lokaci ba suka d’au hanyar NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT, cikin sa’a da suka je Airport d’in ma basu zauna ba jirginsu ya tashi zuwa Garin Kano Ta dabo.
Hour 1 d’aya da mintuna 10 ne ya kawo su Garin Kano , kai tsaye manyan motocin da suke jiran su a Airport d’in aminu Kano Suka shiga , Dadyn da zahra sai khaleed motar su d’aya , oumma kuma ta zauna tare da hajiya, a maimakon su nufi Gidan su na G.R.A kai tsaye hanyar da zata kaisu Bunkure suka nufa , gabaki d’aya oumma sai ta kasa sakewa tuna abubuwan da sukai mata,fahimtar hakan yasa hajiya cikin dattako ta rike mata hannu” karki damu babu abunda zai faru sai Alkairi”, gyada mata kai oumma tayi, mamakin yanda suke bin hanyar tayi wani wajan duk angyarashi ba kamar daba , lokacin da aka shigo layinsu saida gabanta ya fad’i ga Taheer d’inta da ya fad’o mata arai, tun daga layin shiga unguwarsu aka soma bin motocin su da kallo, wasu rayan na bin motar har aka zo bakin kofar gidan su , labari har ya kai cikin gidan cewa ga mutanan Birni sunzo da manyan Mota.mazan cikine kawai suka fito dan sosai rayuwa ta canza musu, suma su kawu sule shida rabi’u kowa yayi jugum jugum Suna jiran abinda zai faru, Dan duk atunaninsu anzo kama d’aya daga cikin sune, su Dady ne suka fara fitowa , tsakanin Rabi’u da kawu sule har yar rigen du’kawa sukai wajan gaishe da Dady, da fara’a a fuskarsa ya amsa musu, su oumma ne suka fito daga mota suma , gabaki d’aya babu Wanda ya gane oumma a cikinsu , kamar yanda suka gaishe da Dady haka suka gaishe da su oumma kafin cike da fargaba kawu sule ya furta “ Allah yasa ba kamamu kukazo yi ba Dan girman Allah kuyi hakuri”, kallan mamaki oumma ta bishi dashi, abunda bata ta’ba gani ba kenan wai magana cikin salama , cikin sakin fuska dady ya furta “ ko zamu iya shiga daga ciki”, d’an shiru sukayi kafun Rabi’u ya furta “ bari na yiwa yan gidan magana “, tun kafin dady ya amsa masa har yashiga gida , cikin ‘kan’kanin lokaci kuma ya dawo” Bismillanku “, su oumma ne suka soma yin gaba kafun su khaleed suka bi bayansu, suna shiga suka tarar da anshin fid’a musu doguwar tabarmar da gaba d’aya ta fita a hayyacinta duk ta zare , bin gidan oumma tayi da kallo gabaki d’aya ya canza mata yanxu babu wannan ‘kazantar, batare da wani ‘kyan ‘kyami ba suka zauna nan tabarmar, ragowar yan gidan kuwa gabaki d’ayansu cun kushewa sukai waje guda a ‘kasa kowa ka gani abun tausayi ba kamar suba, da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai suka soma gaishe da su oumma har lokacin kuma babu Wanda ya gane ta a cikinsu, kaka ta bawa ce ta fito cikin d’akinta sai faman d’ingisa ‘kafa take, kallan Oumma ta tsaya yi kamar zatayi Magana kuma ta fasa itama zata tsugunna Oumma tai saurin ru’kota, a hankali oumma ta furta “ kaka tabawa”, itama kaka tabawa cikin dafe ‘kirji tayi saurin furta “Maryama”, gabaki d’aya ‘yan gidan kallan kallo suka fara a tsakaninsu suna tunanin wace maryama ake nufi,murmushi me ciwo oumma ta saki kafun ta furta “Na’am “, ai ba shiri kaka tabawa ta fashe da kuka tana neman yafi yar oumma , abinda bata ta’ba tsammani ba , ‘ko’karin dur‘kusawa take duk da ciwon da ‘kafarta take mata amma oumma ta hanata hakan batare da ‘kyan’kyamiba oumma ta rungumeta a cikinta, suma ‘yan gidan sai alokacin suka gane wacece, gabaki d’ayansu ko wannensu neman yafi yar oumma yake ita dai babu abunda take yai sai murmushi, ta lura Dije da Bintalo basa cikinsu amma bata ce komai ba , saida komai ya lafa kaka tabawa ta soma basu ha’kuri akan basu da abunda zasu basu, sukuwa sai murmushi kawai suke sakarmusu, ‘kara neman yafi yar oumma kaka tabawa tayi kafun ta soma labarta mata irin neman ta da suka dungayi da neman Taheer da har yanxu basu ganshi ba, sannan da irin cin zalin da Dije take gana musu, cikin kuka taka tabawa ta ‘karasa da “ maryama nasan Alhakin kine yake bibiyar mu, na ro’ke’ke da Girman Allah, ki yafe mana , mun gane kuskuren mu”, itama oumma cikin kuka take furta “ Na yafe muku gabaki d’ayanku ,” itama a ta ‘kaice ta basu labarin barowarta gida da Auran ta, abunda yafi baba oumma mamaki yanda suka nuna tsananin farincikinsu babu Hassada, nasiha sosai dady yayi musu da jan hakali cikin hikima da dattako, koda ya kammala hajiya itama sai data ‘kara yi musu nasihar su so junansu da hakuri da juna”, Tashi khaleed yayi, ba dad’ewa aka soma shigo da manyan kayan Aminci tun daga kan shinkafa, makaroni da mai da manja har dasu Dankali da doya da kwai sai da aka ajjemusu, sosai akai musu siyayya hatta oumma siyayyar taso bata tsoro, cikin kuka kaka tabawa ta soma yi musu Godiya da addua , daman tun safe babu abinda suka ci, Dije ta tattara komai na anfanin gidan ta siyar Dashi, hatta gidan tayi ‘ka’karin siyarwa Allah be bata sa’a ba , ta ibi wasu kayanta a cewar ta zata shiga yawan samo kud’i, har lokacin kuwa Bintalo ba a ‘kara ganin ta acikin unguwar ba.
Gabaki d’ayansu saida Dady yabi ya rarraba musu kud’i akan su ja jari, wasu dubu hamsin wasu talatin, kaka tabawa kuwa dubu d’ari ya bata cif cif . Babu Wanda baiyi nadamar abunda yayi wa oumma ba gashi a sanadinta, mijinta ya temaka musu, itama oumma tsarabar da tayi niyar basu tasa aka rabasu, Atampopi mazan kuma shadda, hatta hajiya kaka sai data bawa kaka tabawa tsarabar kujerar makka , so kaga farin ciki wajan mutanan gidan kamar su akai wa albishir, itama oumma sosai taji dad’in canzawarsu ko ba komai an zama ‘yan uwa yanxu, ko da zasu tafi har bakin ‘kofa suka rakosu suna yi musu addua , ba ‘karamin dad’i oumma taji ba harda hawayenta da zasu rabu, aranta kuma tana Adduar Allah yasa shima Taheer yana cikin ‘Koshin lapiya a duk inda yake, basu d’au dogon lokaci ba suka kama hanyar komawa Kano dan gobe da sassafe jirgin su zai tashi zuwa ‘kasa me tsarki.
✨✨✨✨✨✨✨
1:29pm Tahee ta farka a firgice sabida mummunan mafarkin da tayi, da Sauri ta janyo wayarta tare da dialing number d’insa amma abun mamaki switched up ake ce Mata abun da bai ta’ba faruwa ba , ‘kara dialing number tasa tayi the same abinda ake ce mata kenan, ajiyar zuciya ta sauke data Tuna cewa zai may be ko yana cikin theatre har yanxu, ganin lokacin sallah na tafiya ne yasata mi’kewa ta nufi d’akinta.
Tana idar da sallah wanka tayi cikin material d’in me rawa black colour , ganin babu Wanda ya shigo part d’in harsu ihsan yasa ta saka wayarta kawai a aljihun kayanta , tare da rolling d’in mayafinta da niyyar zuwa part d’in Dada.
Lokaci d’aya gabanta ya yanke ya fad’i, ga wata irin iska data soma ratsa mata zuciya kamar ana cire mata wani sassa na jiki, hannunta dafe da zuciyarta ,gabaki d’aya yau ta rasa me ke damunta lokaci zuwa lokaci Babynta na fado mata arai ganin haryanxu be kira taba .
A ‘bangaran king kuwa a hanyar dawowansa
Gida ,lokacin da yake driving dan yau shikad’ai yafita dan dakansa yake driving yau, hatta zaki yau be fita dashi ba ,Daidai Lokacin da ya yanki kwanar Area d’in babban titin da zata sadashi da banana Island wata babbar trolley data ‘bullo tayo kansa gadan gadan, ‘ko’karin Jan burki yayi amma sai burkin ya kwace take a Wajan babbar trolley d’in tayi sama da motar da King yake ciki tare da fad’owa duk ta rugurguje. Driver ciki na ganin hakan yayi saurin d’aga wayar sa dake ringing kafun ya furta “Angama sir “ sai kuma yayi saurin Jan trolley d’in da gudu ganin a ‘ko’karin tsayar dashi.
Wasu matasa biyu da akai abun kan idan su ne sukayi saurin ‘karasowa inda motar king take kafun su kira jami’an ‘yan sanda ,ganin yadda motar ta lotse , wani card da d’aya daga cikin samarin ya ganine ya d’auka kafin yayi dialing number , Daidai lokacin dasu Abeey suke zaune a falon dada kiran matashin ya shigo wayarsa , haka kawai zuciyarsa ta tsinke kamar ba zai d’aga ba sai kuma ya d’auka , tun kafin yayi magana Matashin saurayin ya sanar dashi Accident d’in king duk da be tabbatar da alakarsu ba , “ babu abunda Abeey ya ke furtawa face Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, cikin gaggawa ya bada umarnin akaishi NAHYAN hospital ko sauraran su dada dake tanbayar me ya faru be yi ba , cikin tashin hankali suka nufi asibitin lokacin har manyan likitocin asibitin sun shiga da shi Emergency Room, tsaro sosai Abeey ya sa a saka a cikin asibitin gabaki d’aya , dai dai lokacin da uncle musaddiq da uncle saleem suka karaso cikin tashin hankali suma , sun fi 2 hours tsaye a bakin emergency room har lokacin kuma likitocin da suka shiga basu fito ba sai abubuwan da nurse ke ta faman d’akkowa. Umarni ya bama uncle saleem da yaje ya d’akko su Dada amma kar a fada musu condition d’in da king yake ciki sai sunzo. Hakan kuwa akayi yana zuwa ya tarar dasu ashirye hakanan komai ummey asanyaye take yinsa , ga wata iska da take ratsata kamar lokacin data rasa Moha d’inta ,ga baki d’aya da mutanan gidan aka tafi ban da tafi dake fama da fad’uwan gaba lokacin.
Suna shiga asibitin saura kadan jiri ya kwashe ummey, Ammey kuwa sai faman murmushi take saki a fakaice da mutum ya kalleta kuma zaiga Tsantsan tashin hankali akan fuskarta . Lokacin da suka samu labarin accident gabaki d’aya mutuwar tsaye sukai, ummey kam yau ta kasa daurewa tazo zata fad’i Abbey yayi saurin ri’ke ta hakan kuwa ba karamin bacin rai ya saka Ammey, gabaki d’aya ita sai ta nuna tafi shiga zamuwa Dan har faduwa kasa saidatayi gabaki d’aya kowa hankalinsa ya tashi, ganin babu Tahee a cikinsune Dada ta bata umarnin Mamy Matar uncle musaddiq suje su d’akkota, Aunty kam yau itama ta shiga damuwa ko ba komai ba shi ta tsana ba Tahee ta tsana, yan matan gidan ma kowa sai faman kuka take a cikinsu .
****A ‘bangaran Tahee jitayi gabaki d’aya zaman gidan ya isheta babu abunda takeso kamar tajita a waje ,da Sauri ta zabura cikin Sauri ta nufi hanyar fita daga part d’inta , babu inda take kalla sai hanya duk da duhu ya farayi, abun mamaki har tazo gate d’in farko babu security Sabida lokacin sallah yayi, a gate na biyu ne yake da tsaro amma duk cikin su babu Wanda ya hanata fita harta fice daga gidan mutane biyu ne sukayi run’kurin tsayar da ita amma babu Wanda ta kula a ciki, tana ganin ta Fita daga gidan kuma lokaci guda ta saka gudu , gudu kawai take abunta ita kanta batasan hanyar da take biba. Su mamy na zuwa suka samu wannan mummunar labari, gabaki d’aya an duba gidan bata ciki, har layin gidan kwata kwata babu Tahee babu alamarta , Gabaki d’aya bincike aka soma , lokacin da d’aya daga cikin masu tsaran ya fad’awa zaki abunda sukayi take a Wajan ya dakatar dasu daga aiki gabaki d’ayansu mutane kusan goma sannan yasaka wasu tsaran da suka fi wanda ya bari, sosai a ka shiga binciki.
Su mamy na barin hospital d’in wani doctor Armeen ya fito daga cikin ER sai faman had’a gumi yake , ba Wanda be san Abeey ba shiyasa dakansa yayi wa abeey jagora zuwa office d’insu, cikin girmamawa ya soma bawa Abeey hakuri kafun ya sanar dashi King ya shiga COMA, alokacin kuma Mamy take sanar dashi neman Tahee da akai aka rasa, gabaki d’aya kuma sai kowa ya ‘kara har gitsewa musamman ummey da Ammey da suka yanke jiki suka fad’i lokaci guda, dada ma kuka kawai ta saka babu abunda take cewa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, cikin gaggawa Abeey yasa a binciki duk inda take anemota kafun ya sanar wa da commissioner da kansa akan abincika masa duk inda take anemo ta cikin gaggawa , shima gabaki d’aya ya shiga damuwa , yana tsoran halin da King zaishiga idan yasamu labarin ‘bacewar matarsa
******
SHIN KING YANA TASHI DAGA COMA?
GA TAHEE DA TAKE DA CIKI TABAR GIDA KO INA ZATAJE?
SHIN ZASU KARA GANINTA ?
INA TAHEER ?
INA DIJE DA BINTALO?
WANENE MUTUMIN DA YAKE MAGANA DA AMMEY?
WANENE YAJI ZANCANSU LOKACIN DA SUKE TATTAUNAWA?
SHIN SU OUMMA ZASU KARA HADUWA KUWA ?
INA YAYAN OUMMA DA AKACE YA BAR GIDA?
Alhamdulillah anan na kawo karshen littafin GIDAN AUNTY BOOK 1 .
Ina rokan Allah kamar ydda na fara littafin nan a sa’a ya bani ikon kammala shi.
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH…
Post a Comment for "Gidan Aunty Book 1 Page 71-72"