Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Aunty Book 1 Page 9

Free page 9 🦋

********
Suna zaune tun safe basu fito ba, oumma ta dafa musu ragowar taliyar jiya sukaji ana faman buga kofar da karfi kamar za a karya,” maryam bazaku fito bane kuna ji ina magana”, tsaya wa duk sukai daga cin


abincin da suke jin muryar kaka tabawa, cikin damuwa oumma ta fito bayan ta yiwa su tahee kashedin karsu fito, a tsats tsaye tagansu ko wannan su , kaka ta bawa sai faman zaginsu take , “inna ina kwana”, bata bari ta karasa ba kaka ta bawa ta katseta“ban kwana ba , nace miki ban kwana ba , wallahi maryam kiji tsoran Allah , yanxu daman bakin cikin nace zan aurawa waccan yar taki me kama da aljanu tanimu shine zaku bi dare keda ban ka daddun ‘ya’yan ki ku fasa mun randa, kunsan tsawan shekarun randa ta da zaku tashi ku fasa mun” bata bari oumma tayi magana ba ta dora “ toh wallahi bari kiji,ko kina so ko ba kyaso aure kamar ya d’aurune dan ba fashi, itama munafukan da suka ‘ki futowa dani suke magana, ku fito ka aiki can kutashi kuyi, uban me ya hanaku yin aiki ma yau” sun kuyar da Kai oumma tayi kafun ta fara bata hakuri”kiyi hakuri inna, bamusan Wanda ya fasa miki randa ba” bata karasa ba Dije da bakin ta ya kun bura cikin haushi ta fara”toh karya za ai muku , in baku ba uwan wane ze fasa mata randa, yan bakinciki , shiyasa nace muku zuwan mutanen nan ba alkairi bane “ta kara sa da juyawa tana kallan mutanan gidan. “Hindu ce ta kalli inna ta bawa “ inna shiyasa ai jiya nace kawai kisa tanimu ya turo ba sai an jira bintalo ba, dan wannan bakin halin nasu ma waya sani ko sunbi wajan boka “ ta karasa tana hararar oumma da ta sun kuyar da Kai har ynxu fuskarta tana a yadda take.

A daki kuwa jin yadda suke zagin oumman nasu yasa tahee fashe wa da kuka , sosai take kukan bakin ciki akan abunda suke musu, ita ba Auran ne ya dameta ba suje su aura mata duk Wanda suka ga dama amma bazata kuma lamunta da cin mutuncin da suke wa oumma ba, sosai shima taheer ransa ya baci. Kara fashewa da kuka tahee tayi jin kaka tabawa nacewa auwalu ya kirawo mata tanimu asa musu rana , sosai sukai musu tatas ko hakurin da oumma take bayarwa basu saurara ba suka bar wajan , Dije sai faman d’ingishi take dan tayi alwashin sai ta ruguza farin cikin su , dan tasan bokan da oumma ta ke bine yasa ayi mata haka (nace uhmmmmm Dije jikin ki be gaya miki ba kenan🤭).

Farin macijin dake la’be tun dasu ya kurawa tahee ido ganin yadda take kuka shima sai launin idanuwansa suka canza daga baki zuwa ja ,sai ya silale ya fita baki d’aya daga dakin ganin oumma na kokarin shigowa.

➰➰➰➰➰➰➰➰
DADA
zaune take cikin wasu lallausan kujera jikinta sanye da wasu fararan cotton din kaya , sosai kayan sukaiwa jikin tsufanta kyau,a center din gabanta wani dan madaidaicin glass jug ne cike da fura, sai faman tashi kamshin furar da yaji damu yake, kallan Aunty dake gefe a zauna tayi tare da gyara zamanta , inajinki Amina , cikin inda inda Hajiya Amina ta soma magana “ wai dada naga yan matan gidan duk sun tasa ne , shiyasa nake ganin me zai hana ayi Auran dangi, ko King ne a aura amsa amrah, naga kamar suna kyaunar junansu”, sosai dada ta zuba mata idanuwa kafun ta soma magana “amma dai haroon kike magana akai ko, ke yanxu Amina bazaki dena wannan halin naki ba , shi sadaukin Yaushe kike ganinsa har yace miki suna Kaunar juna”, kin kina ta soma tama kasa magana “ saurin da katar da ita dada tayi”bana san irin haka , inda shi sadaukin ne yace yanasan yar taki da babu abunda zai Hana Aki aura masa , amma tunda be fada ba kar nasake Jin wannan batu, zaki iya tafiya”, sosai ran hajiya Amina ya baci da magan maganun dada , dan tabbas tasan da hajiya kilishi ce ko uwar king din da babu abunda zai hana tayi naam da zancen, daman ta dad’e da sanin cewa dada ba kaunarsu take ba , amma fili sai ta saki murmushin nan nata “tuba nake dada , ban fada da wata manufa ba, na barki lapiya”, itama dadan jinjina mata kai tayi “akiyaye “,itama aunty mikewa tayi tana fadin “insha Allahu”, tare da kama hanyar fita daga falon, bin bayanta da kallo dada tayi kafun ta girgiza kanta tacigaba da sabgar gabanta.

Kamshin da batayi tsammani bane ya cika mata hanci ,juyowa dada tayi domin tabbatarwa, shidin ne tsaye , fuskarsa kwata kwata ba annuri akai ,kallo daya dada tayi masa ta dauke kanta ,cikin kasan makoshi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya bude bakinsa “Assalamu alaikum” dabadan hankalin ta na kansa ba da babu abunda zaisa taji sallamar tasa” Wa’alaykumussalm “ tabashi amsa itama ,ta kowa yayi ahankali tare da karaso wa inda take, a maimakon ya zauna a kujerar kusa da ita sai ya zauna akan kujerar da take , “barka da yamma dada”, ta bile baki dada tayi “sai yanxu ka bayyana kenan, Kai yanxu saraki da ban nemekaba da bazakazo ba kenan,kadai ji tsoran Allah “,amai makon ya bata amsa sai ya kwantar da kasan a kafadunta tare da dan kwa’be fuskarsa kadan,ture kafadarsa dada tayi tare da mikewa , cikin masifa ta soma magana “ kabari in kayi aure sai kawi wa matar ka haka , bani ba salan zawaran da sukeso su aureni su gudu sabida karyayyan kashi”,dan murmushi leben baki ya saki da ko dada dake kusa da shi bazata gane hakan ba, sosai yayi musamman da pink lips dinsa ya kara turuwa,harara dada ta sakar masa tare da ta’be baki “kajirani” tana gama fada ta mike da nufar kitchen dinta, bata dade ba ta fito dauke da wani dan karamun tray, cikin yanayinsa na rashin garaje ya mike tare da amsar dan karamin tray din da ta fito dashi, inda suke zaune suka koma sai a sannan dada ta karbi tray din, lafiyayyar tuwo ne da miyar kubewa d’anya da taji nama da Ganda , sai kifin da aka sa masa, sosai kamshin abincin yayi masa dadi amma sai ya dan kawar da kansa gefe, dungure masa kai dada tayi” toh d’an neman magana ni na yi da kaina”, sai a sannan ya jiyo fuska a sake amma kwata kwata babu murmushi akai,karban abinci yayi tare da fara ci bayan yayi Bismillah, sosai yaci tuwan dan ya dade beci abinci da yawa ba,tunda ya fara cin abincin dada take binsa da kallo, Itade tanasan jikan nan nata, maganar hajiya Amina ce ta fado mata arai, kamar zatai masa magana sai kuma ta fasa, tasan halinsa yanxu ze iya tsanar yarinyar ko yaje ya ‘bab’bala yar mutane. Ganin yadda take kallansa ne yasashi dage mata gira , waro idanuwanta dada tayi “yanxu ni sadauki kake dage wa gira daya , sai kace yar iska, toh maza maza tashi ka bar part dinnan, ga furar ka nan ma, ka ‘bacemun da gani” sallamar zoya ce ya katse dada , da sauri zoya ta karaso wajan king “akhi “,lumshe mata ido yayi tare da budewa”na’am ukhti”, dariya sosai ta saki jin ya kira ta da ukhti “akhii duk yau ban gankaba fa” ta fada tana marairaice fuska,kamar bashi ba , shima ya dan kwaikwayi muryarta “Nima duk yau ban ganki ba ukhti”, binsu da kallo kawai dada tayi tana tabe baki” da yake kin ga ubanki shine kika manta inda kikazo, toh ku tattara kubar min daki”marairaice fuska zoya tayi “Haba dadar mu”yanxun ma harararsu tayi “Oho dai “, king ne ce mata komai ba sai mikewa da sukai tare da daukan furarsu “sai mun kara dawowa dada”,ka tsesu dada tayi “bana bukata”, shima king din tabe baki kawai yayi suka bar part din, da kallo dada ta bisu tana sakin murmushi” kaidai ba me iya maka , zanga macen da zata iya hakuri da wannan baud’ad’d’an halin naka “.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
BUNKURE

Kai tsaye macijin bai tsaya a ko ina ba sai cikin ban dakin gidan, Daidai kaka tabawa tana kama ruwa jitai kamar abu ya hau kanta, sai ta taba Wajan taji ba komai , sharewa tayi tare da cigaba da abunda take, dan karamin abu takumaji kamar yana yawo a jikinta, a  sukwane tayi mike tana karka da jikinta, abun be dena yawo a jikinta ba sai ma kara yawa da yayi, ihu dada ta saki da nufar hanyar fita daga bayin, dan karamun halittar da ta ganin a kofar bayin yasata komawa ciki da sauri tana zare ido”nashiga uku” jitai wasu murya yan kanana suma suna cewa “na shiga uku”, amaimakon tayi salati sai ta fara “laha’ila, ni tabawa na shiga uku me nake gani” ta karasa maganar tana fashewa da kuka duk ta hada uban gumi, wata muryar daban sa’banin ta dazu itama” laha’ila ni tabawa na shiga uku ne nake gani” aka karasa maganar da fashewa da dariya, wani kukan kaka ta bawa tasaki ganin yadda halittar ta nufota Gadan gadan yasa kaka ta bawa sumewa take a wajan .macijin nanne ya bayyana tare da karasa wa inda take Daidai bakinta ya buga mata jelarsa, take a wajan bakin kaka tabawa ya kunbura, batt ya bace shima da barin ban dakin.

Su tahee duk sun fito suna aikin su, yau kwata kwata ba annuri akan fuskokinsu, ruwa suka fara d’ebowa kafaun su fara aikin gidan , tana cikin aikin taji zuciyarta ta fara washewa daga cunkushewar da tayi a kirjinta, shima taheer hakan yaji, lokaci d’aya suka sake tare da cigaba da ayyukansu yadda suka saba, ganin haka yasa itama oumma zuciyarta yin sanyi ganin duk sun saki ransu, kusan  awa daya suna aiki a tsakar gidan duk mutanan gidan sunshige ciki sabida ranar da ake me zafin gaske, ganin yadda ake kokarin bude bandaki yasa duk zubawa kofar ido, da kyar kaka ta bawa ta bude kofar sabida yadda bakinta ya kunbura sai faman din gishi take, binsu tayi da kallo ganin yadda suka tsare da idanuwa, bakin da ya kara kunbura ta bude daniyar zaginsu, zugin da taji ne yasa ra hadiye maganar tana matsar kwalla da bin gefensu ta wuce. Sosai dariya take so ta kwace musu ganin yadda ta wuce tana tsamin kashi, tana shigewa daki kuwa suka fara dariyarsu, TAHEER harda faduwa sabida dariya, itama oumman murmushi ta saki ganin yadda kaka ta bawa ta dawo kamar tsohuwar mahaukaciya, sosai suke dariyarsu, sai da suka gama dan kamsu sannan suka cigaba da aikinsu.

**DIJE
zaune take cikin dakinta da ya cika da uban shirgi ,sai faman tashin wari yake da d’oyi , ko ina na dakin yayi kaca kaca dashi ita kadai ce a dakin sai karamar nokia dinta dake hannunta , ta dad’e tana waya da kawarta jimmala kafun ta kashe tana dariyar mugunta, kamar jira ake kuwa tana kashe wayan aka tsinka mata mari, take a wajan tayi filinki sabida azabar marin da taji, bata dawo hayyacinta ba ta kara jin saukar wani marin a fuskar ta, kuka ta fashe da shi, sai faman waige waige take, ganin ba kowa a dakin yasa kudawa zuwan mata take a wajan, sosai ta kuma rud’ewa jin abu na yawo a jikinta,duk inda takai da tabawa sai taji ba awajan abun yake ba, sosai Dije ta rude sai faman marin kanta da take , tana marin tana kuka, ga majinan da ya cika fuskarta , sai faman tashin tsamin wari take…

Comment and share

💖 THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA💖
👇
💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖

         💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖

            💖JINI DAYA ( MRS bbk )💖

💖YA FITA ZAKKA(maman sayyid)💖

💖SARKI SAMEER (xeenat love)💖

          Mss LEE💖✍️

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( A heart touching love story)

Story &written
By
Mss Lee💖

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

MAISAN AYI MASA TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

Post a Comment for "Gidan Aunty Book 1 Page 9"