Breaking News

Inda Rai 12-13

 *INDA RAI*....🥰🥰*By*          *MARYAM ABDULLAHI*
    (💔💋Oum Shaheed💔💋)      *MIKIYA WRITRE'S ASSOCIATION*✊🏼💋
*12 - 13*Tunda Samha ta sanar da Maryama dawowar su Sudais ta kasa zama waje ɗaya, sai kai kawo ta ke yi tsakanin ɗakinsu dana Samha, farinciki ya kasa barinta, yau kenan mijinta abun sonta zai dawo gareta, mai ya kamata ta yi, lumshe ido ta yi tana tuna moment ɗinsu a daran farkonsu, daran da ya tsaya mata a rai, sam ta kasa manta wannan moment ɗin, hannu ta kai saitin jajajen lallanta tana shafawa, sake sakin murmushi ta yi a karo na babu adadi, sannan daga bisani ta sake tashi ta shige toilet ta sa ke wankewa ta saka turare ta jawo ƙofar, sannan ta gyara ɗakin sosai namma ta saka turare kala kala, masu daɗin ƙamshi, ta kalli ko ina taga ya mata

yadda ta ke so sannan ta fi ce zuwa gurinsu Mommy inda suke ta hada hadar  haɗa musu abinci da abun sha masu ƙayatarwa.


"Ta na zuwa zata saka musu hannu a aikin Sahla ta dagatar da ita da wata irin tsawa har sai da Maryama ta gigice, saboda babu abun da ta tsana irin tsawa, har garama a dake ta akan a mata tsawa, Samha da ke aikin haɗa juice ce ta kalli Sahla ta ce, "haba Aunty, mai yasa ki ke hakane kan? ni banga abun da Aunty Maryam ta miki ba.


Kallon ta Sahla ta yi ta taɓe baki sannan ta juya ta ci gaba da aikinta ƙasa ƙasa ta yi magana kasan cewar Mommy na gurin, amma ko ci kanku ba ta ce musu ba, sa ke juyawa  ta yi ta kalli Maryama ta ce, "sai ki wuce ki gyara mana ɗaki canne ya da ce da ke ba nan ba, jan hanunta Samha ta yi suka fice daga kichine ɗin a hankali yadda Sahla ce kawai za ta ji ta ce, "duk dai yadda zakiyi matarsa ce, kuma da alama har isun san juna a gado. Wani juyi Sahla ta yi ta wanke fuskar Samha da mari, ba Maryam ba har Mommy sai da ta girgiza da wannan ƙarfin hali na Sahla, lalle za ta yi maganin a bun soon, Samha ta kalli Mommy idonta fal hawaye, amma sai gani ta yi ta ɗauke kai daga gare ta ciga ba da aikinta, mai hakan ya ke nufi,? ta tambayi kanta, duk yadda Mommy ke sonta amma ta rasa gane maiyasa Mommy ba ta iya dogon motsi a gaban Ammi da yaranta.


A fusace ta ja hannun Maryan suka bar kichine ɗin.  Haƙuri sosai ta bawa Auntyn nata ta na shaida mata ba haka Mommy ta ke ba, tana da tsauri akan kowa amma ban da ahlin Ammi.


Murmushi mai ciwo Maryam ta yi domin ita duk wannan bai dame ta ba kamar yadda ta lura yarinyar na mugun son mijinta, ba ta da ja akan son da ta kewa mijinta amma tasan bata da halin ta kawa Sahla burki, saboda Mommy ma kamar tsoron ta ta ke ji, zata barwa Allah komi har sanda komi zai zama dai dai, domin nanɗin shine gatan ta, inama tasan in da dangin mahaifiyarta suke,? da sauri ta miƙe ta hau wargaza kanyanta ta na ne man wani da Innarta ta ba ta amma ba ta gani ba, da fe kanta da yasara mata ta yi tunawa da ta yi ta barshi a ruga, wanda kuma shine zai taimaka mata wajan gano in da dangin Innarta su ke.


Wajejen ƙarfe biyu na ranar yau zasu ƙariso, amma har yanzu ƙarfe 1:30 ta kasa tashi ta yi wanka, kowa ya shirya amma ita ta kasa tashi, ganin halin da ta shiga ya sa Samha ta shi ta nufi hanyar ɗakinsu ta na ce wa, Aunty ki zo ki ta ya ni gyara ɗakimmu kafun su ƙariso.


A can ta umarci Maryam da ta je ta yi wanka aiko da sauri sauri ta ke yin komi dan dama a ƙage ta ke kawai dan ta rasa yadda zata yi ne, ta na fi to wa ta samu Samha ta fi to mata da wata haɗaɗɗiyar dogowar riga ƙirar tukiy, rigar kalar sky blue sai duwatsun jikinta mai ruwan gold, sosai ta yi kyau ba kaɗan ba domin Samha ta tsara mata kwalliya da kanta, ɗakin Mmmy ta je ta ɗakko turarurruka irinna matan sudan ta bata ta ce ta ahafa a ko ina na jikinta, ko wanne da in da za'a shafa shi, sosai ɗakin ya rikiɗe da wani mayataccen ƙamshi, sak Maryama ta fi to a amarya, sai zaman jiran ango.        RUGAR
A ƙofar gidan Malam Bukar wasu haɗaɗɗun motoci suka hau jerin ganon parka wa ɗaya bayan ɗaya, sai ka rantse da Allah gasar motocin zamani a ke yi a gurin.
Wani mutumi ne ya fi to daga motar da ta fi ko wacce kyau, kai tsaye ya nufi cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ba yi da burin da ya wuce ya yi tozali da ƙanwarsa ɗaya tilo a duniya, Haulat!! Haulat!!! Haulat; kina ina!!!!!! ya sake kwalla mata kira a karo na uku, amma shiru bai gan ta ba, sai wani ya ƙunannan mutum da ya fi to a hargitse jin kira kamar daga sama, kuma da alama sunan marigayiyar matarsa ake kira.


"Bawan Allah lafiya kuwa?  Malam Bukar ya tambayi mutumin da ke tsaye ya juya masa baya, da sauri Alhaji  Aminu shugaban wake ya juya zuwa in da ya ji maganar, a kiɗime Malam Bukar ya ke nuna mutumin da ke tsaye a gabansa da hannu, Aminu!!! dama kana raye,? "ina ƴar uwata ta ke"? Aminu ya tambayi baffah, ta ke cikin Baffah ya ɗori ruwa, tabbas yau kwanasa ya ƙare, amma maiyasa tunda yabar masa amanar ƙanwarsa Haulatu bai kuma dawowa ba sai yanzu da su ke neman shekaru ashirin da rabuwa.?Da sauri Alhaji Aminu ya ƙarisa ya rumgume abokinnasa ya na zubar da hawaye ya ce ina amanata,? ina ƴar uwata ta ke,? ka kiramin ita na gan ta na nemi ya fiyar ta, na bar ta tsawon lokaci, sai dai nima ba'ason raina hakan ta faruba, labari ne mai tsawo, amma kafun komi ina amanataa,? ya sake tambaya a karo na babu adadi.


Babu abun da zuciyar Malam Bukar ta ke yi sai bugawa, saura

ƙiris ya samu bugawar zuciya, da kyar kamar wanda ya ke ciwon baki ya buɗe a hankali ya ce ka zo musamu waje mu zauna tukunna.


A razane Alhaji Aminu ya miƙe jin cewar ƴar uwarsa ɗaya tilo a duniya ta rasu, innalillahiwa'inna'ilahirraji'un, hasbunallahu'wanihmal'wakil, shine abun da Malam Aminu ya ke ta maimaitawa hankalinsa amatuƙar tashe, kuka ya yi sosai kafun daga bisani  ya ɗauko ƙuɗi masu yawa ya a jiye masa, ya miƙe da rauni sosai a tattare dashi ya ce, "zan koma,yanzu ina zaune da iyalina a garin gombe, zan dawo maka da duk wani alƙwarin dana maka na riƙe mini ƴar'uwata bisa amana da ka yi, jiki na rawa Malam Bukar ya sa hannu ya karɓi kuɗin ya na washe baki, sallama sukayi har zai fi ta sai kuma ya yi wani tunani ya ja ya tsaya, juyowa ya yi ya kalli Bukar ya ce masa, " ba ta bar yara bane ko guda ɗaya,?Maryam na zaune a ɗakin Samha ita kaɗai domin duk sun fi ce ɗauko su daga airpot, ta shi ta yi ta koma ɗakinsu ta kwanta akan godo sai juyi ta ke yi cikin farin ciki, moment ɗinsu a wanna gadon ya ƙi bari kwakwalwarta sai tunawa ta ke yi ta na jin wani filling na shigarta a ta ke duk wata gaba ta jikinta ta hau sanyi tsikar jikinta suka hau miƙewa, saurin tashi ta yi jin ƙarar shigowar motoci habar adana motoci na gidan, da hanzari ta ƙarisa ta ɗaga labulen windon ɗakin, can ta hango heart ɗinnata sai wani guy a gefensa wanda bata iya ganin face ɗinsa, wani abu ta ji ya daki zuciyarta sakamakon ganin Sahla da ta yi ta rumgume Sudais kamar wani muharraminta ko kunya ba taji, sake labuken ɗakin ta yi ta koma bakin gadon ta zauna jin kanta na na neman tarwatsewa, dafe kanta ta yi ta na addau'ah har ta ji ranta ya fara sanyi, jin sun shigo cikin palon gidan har ta miƙe zata fi ta sai kuma ta koma ta zauna.Tunda suka shigo harabar gidan zuciyar Sudais ta ke bugawa da ƙarfi, duk yadda ya so ya bar tunaninta da moment ɗinsu ya kasa hakan, zuciyarsa ta ƙi basa damar hakan, kuma ya zama dole ya ɗau mataki akan gudirinsa, ƙarisa shiga cikin parlon sukayi kowa ya nemi guri ya zauna ban da Imran, dan shi ba'ason ransa ma ya zo gidannasu ba, burinsa ya wuce gidansa ya yi abun da ke gabansa, amma Mmmy ta ƙi hakan, Daddy ne ya basu umanin suje su yi wanka be for su ci abinci, har Imran ya nufi part ɗin Sudais sai Daddy ya umarce sa da wu ce nasa part ɗin, wanda rabon da ya yi using dashi har ya manta, tare sukeyin komi a ɗakin ɗan uwansa, jiki a mace ya sai kai yanufi bangaransa,

 shima Sudais zai bisa

 Daddy ya ce ya wu ce shima nasa part ɗin, haka shima ya wuce jiki a mace a ransa yana addu'ar Allah yasa bata can ɗin.Rai a dagule Alhaji Aminu ya shigo cikin gidan nasa, da sauri Hajiya Balkisu ta ƙariso ta shige jikinsa ta na masa sannu da zuwa, jin bai amsa mata ba kuma bai mata yadda ta saba ba sai ma janyeta da ya yi ya wu ce bangaransa, bin bayansa ta yi bayan ta ɗauko masa ruwa mai sanyi, zama ta yi kusa dashi ta miƙa masa ruwan dai dai bakinsa, babu gardama ya buɗe ya hau shan ruwan, dan ji ya ke yi zuciyarsa da maƙoshinsa sun bushe sosai, sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa sannan ta mai da cup ɗin ruwan gefe ta zauna ta cite masa takalama da safar sannan ta dawo kan kayan jikinsa, ta cire babbar rigar ta kai ta ajjiye, toilet ta wuce ta haɗa masa ruwan wanka ta zo ta kama hannunsa ta kai sa har toilet ɗin, ganin yanayin sa yasa da kanta ta masa wankan har ta gama bai ce mata komi ba, da kanta ta shiryasa ta basa abinci amma ya kasa cin ko kaɗan, ajiye spoon ɗin ta yi ta tura baki kamar ƙaramar yarinya ta juya masa baya, ganin abun da ta yi yasa yakamu hannayenta ya jiyo da ita suka ƙurawa juna ido, "bazan iya ci yanzu ba, amma na miki alƙawarin anjima zanci kinji ƴar aljanna, ya ƙarisa maganar da sigar zolaya ya kwaikwayi muryarta ya sake cewa, "Balkisu gimbiyar mata" zolayarta ya dinga yi har sai da yaga murmushi akan kyakykawar fuskasta sannan ya haƙura, ganin ya ɗan dawo dai dai sai ta manna kanta akan ƙirjinsa ta na yambayarsa mai ya ke faruwa dashi,? faɗa mata komi ya yi da rasuwar ƙanwar tasa, sosai ta ji tausayinsa saboda tunda ya dawo hayyacinsa ya ɗaga musu hankali akan ya na da ƴar uwar da ya bawa abokinsa amana a garin kano, Allah sarki ashema bata duniya, "to yara fa,? ta jefa masa tambayar, "ta haifi yarinya ɗaya sai dai itama Allah ya yi mata rasuwa ana saura kwana biyar da auranta.


Sosai Hajiya Balkisu ta tausaya masa, domin ta fahimci ba ɗaramin so ya ke wa ƴar uwar tasa ba, tunani ta ke yi mai zai sanyaya masa zuciya,? murmushi ta saki sannan cikin salon jan magana ta ce yau dai Amrish ta kira waya, kuma abun farin cikin a ƙarshen watannan zata dawo gida, ai da wani sauri ya juyo ya kalli balkiss ɗin tasa ya saka hannu ya ɗaga ta sama ya na juyi da ita, cewa ya ke yi lalle kin cancanci kyauta mai girma, my gaughter ta yadda zata dawo NIGERIA a bisa raɗin kanta,? lalle Allah shine abun godiya, ganin ta yi nasarar cire masa damuwar da ke ransa ta sake ce wa,"yarona ma zai sauƙa a Nigeria  gobe jin cewar ka samu masa goggonsa.
*Kuyi haƙuri da wannan yau ɗin bana jin ɗadi*🙏🏻🙏🏻🙏🏻


*Ta kuce Oum Shaheed*


*Ina sonku masoya na*🥰🥰🥰✊🏼

No comments