Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Inda Rai 20-21

 *INDA RAI...*🥰🥰🥰



*MARYAM ABDULLAHI*




 (💔💋Ouma Shaheed💔💋)


    *Daga ƙungiyar, ko da kuɗinka.....*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*✊🏼✊🏼💋💋💋


*Page  20 - 21*



Farin ciki sosai ya kama Daddy bayan gama jin wannan yarjeje niyar, da wannan damar zai yi amfani, zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, sauƙi ya zo masa har in da ya ke.


Haka aka shirya cirewa Raheem zuciya ba tare da sanin Mimi ba, an gama komi cikin nasara aka sakawa Imran, sai fatan ganin farkawarsa.


A ɓan garan Sudais ma sai sam barka, domin lokacin da likita ya ɗi ba masa na cika ya farka, sai  dai an masa allurar bacci dan sake samun nutsuwar zuciyar tasa, sosai Daddy ya ke farin ciki da wannan nasara da ya samu ta ko wane bangare. Alhaji Aminu ya yi farin ciki shima jin cewar an samu nasara, suna zaune da Mimi ta ke tambayar sa, "ƙalbi: ina son naga yaron nan kafun a gama duk wani ciku cikun da za'ayi, a gigice Abee ya ke kallon ta, ta ya zai bari ta ga ɗan ta a halin da ake ciki,? yasan ba zata ta ɓa fahimtarsa ba, tashi ya yi ya fi ce ya ce mata yana zuwa, da kallo ta bisa kawai, domin ta fahimci akwai abun da mijin nata ke ɓoye mata, amma ta na addu'ar Allah yasa koma miye ne to ya zama musu alheri, tashi ta yi ta nufi ɗakin da Amrish ta ke ciki, a kwance ta same ta tana waya, kuma da'alama da wannan guy ɗin da ta basu labari ne, wanda suka haɗu a jirgi, zama Mimi ta yi har sai da ta ƙare wayar, Amrish ta kalli mahaifiyar ta'ta ta ce, "Mimi Humait zai shigo kano zuwa biyu, na so ya bari mu kuma gida amma ya ƙi, "ki barshi ya zo ɗin kawai, in ya so sai mu wu ce tare, "to shikenan Mimi, yau she zamu wu ce,? sai na faɗa masa, ajiyar zuciya Mimi ta sauƙe, ta. ce ni kaina ban san cike ciken da Abee ya ce min ana yi na miye ba , amma bana tunanin zamu kwana. Allah ya jiƙan ya'ya na abun sona, Allah ya masa rahma, sharrr sai hawaye, haka suka ta kuka su kaɗai babu mai lallashin wani, a haka har Abee ya shigo ya tadda su, dakyar ya samu su ka yi shiru sannan ya hau musu nasiha akan yadda da ƙaddara.



Maryama ta ga duniya a wannan ranar, ta yi kuka har ta gaji, wuni kas ta kasa saka komi a cikinta, batama sha'ar cin, ko a wani hali mijinta ya ke ciki shida ɗan uwan nasa,? tashi ta yi ta nemi ruwa tasha ko zataji sauƙi a ranta, aiko tana gama shansa ya dawo ko motsawa daga in da ta ke ba ta yi ba, amai ta ke mai matuƙar wahala kasan cewar babu komi a cikinta, da kyar ta samu ta gyara wajan ta shige toilet ta watsa ruwa, tana fi to wa zazzaɓi ya sake rufeta ruf, babu abun da ta ke buƙata a wannan lokacin irin kasan cewa da mijinta, ji ta ke har wani tsuma ta ke yi, runtse ido ta yi tunawa da ta yibya can kwance babu lafiya, har wani ɗa ci ta ke ji a ranta idan ta tuna furicinsa na ya tsaneta.



Tun da Sudais ya farka kalama ɗaya kawainya furta, jin ce war an samu nasara Imran ɗinsa zai warke bai sake ko uhm ba, babu yadda Mommy ba fa yi ba akan ya ci abinci amma fir ya ƙi, Mommy na zaune kusa dashi idanunsa a lumshe kamar mai bacci, ya yi hakanne dan gujewa takurar da ta masa akan sai ya ci wani abun, kira ne ya shigo wayar Mommy, tana ganin mai kiran ta leƙa fuskarsa domin tabbatar da ya yi bacci, ɗaga wayar ta yi ganin yana bacci, "hello, "ina jinki, inji Mommy ta ba ce wa me kiran, "Aunty ya ake ciki ne, "kekan kar ki damu, ni na miki alƙawari ai, mun gama magana da likitan da ke kula dashi, sannan ki dai na kirana, saboda gudun zargi, "to Aunty, Allah ya bamu nasara, kit Mommy ta katse kiran ganin kamar ya na motsi, tun da ta fara wayar yasan dawa ta ke, Allah sarki Uwa, yanzu haka akan jinyar Imran ko tasa suke magana, amma maiyasa ta ce kar ta sake kiranta gudun zargi,? shifa Barrister ne, ya fahimci akwai lauje cikin naɗi. 



Humait ya ƙariso kamar yadda ya faɗawa Amrish, haka suka haɗu suka gama duk wani cike cike aka basu gawa suka wu ce Gombe a daran, tun da Abee yaga Humait da yadda Amrish ta ƙarɓesa hankalinsa ya ke tashe, yasan halin ƴarsa akan abun da ta ke so, amma yasan ta in da zai bullowa al'amarin.



A yau ne aka sallami Sudais daga nashi jinyar, a ido ya warƙe ras, amma a ransa gymbo ne mai girma, yasan abun da ya ke shirin aikatawa babban laifine, amma ya zama dole ya yi hakan, sosai zuciyarsa ta ke masa ciwo, Mommy ta yi farincikin warkewar ɗanta ɗaya tilo, hakama Daddy ya yi farin ciki sosai.



Alhamdulillah, Imran ya farka cikin nasara, sai ɗan abun da baza'a rasaba, Daddy ya fi kowa fadinciki, haka a ka haɗu ƴan uwa da abokan arziƙi anata ta ya juna murna, sai da yasa ke kwana biyar sannan aka sallemesu suka wu ce gida, maa shaa Allah, shine abun da Daddy ya ke ta ambata.


A part ɗinsa a ka mai masauƙi, ya yin da Sudais maga ya tare a can, sosai zuciyarsa ta ke azabtuwa da rashinta, cikin dare ya saci jiki ya wu ce part ɗin nasu, a kwance ya same ta tana  baccin wahala, ya daɗe a tsaye a kanta ba tare da sanin taba, daga bisani ya buɗe sif ya ɗauki biro da takadda ya yi rubutu mai tsayi ajiki, kafun ya gama hawaye ya jiƙe takaddar sharkaf, ya linke ya ajiye mata dai dai inda zata gani, cikin sauri ya haɗa duk wani abun da zai buƙata yabar gidan.


Duk wannan bidiri da ake Maryam ba ta saniba, tana idar da sallar asuba wanda ta yi ta da kyar ta sake komawa gado, tana bacci har ƙarfe goma na safe, cikin bacci ta ji a nna buga ƙofad ɗakin, jan jiki ta yi a hankali taje ta buɗe, Mommy ta gani a tsaye a gabanta, ras taji ƙirjinta ya buga, kafun ta kainga buɗe baki ta gaidata taji ta ce mat, "ki shige ki kirami shi, da mamaki ta ke kallon Mommyn, shiwa,? ta tambayi kanta, ganin kallon da take yasa Mommy ce mata, "ina shi Sudais ɗin,? "ai  yana asibiti bai dawo ba, Maryam ta bata amsa kanta a ƙasa, "kina nufin bai shigo ba tun da muka dawo,?  "bamma san kun dawo ba, da sauri Mommy ta juya ya nufi part ɗin Imran, abun da ya faɗa maya ɗazu ya sake mai maita mata, "tin cikin dare yaga fitar shi, kuma ya bisa a baya yaga part ɗinsa ya nufa, abu kamar wasa babu Sudais a kaf gidan, har bedroom da toilet ɗinsu an duba amma babu shi, ita Maryam kamma gaba ɗaya ta kiɗime, tama rasa mai suke nufi, ɓata ya yi komi? kamar ance ta duba bayanta, ɗaukar takardar ta yi tana karan tawa ganin tabbas rubutun Sudais ne a jiki,,  ai tun kafin ta kai ƙarshe ta zumfuma ihun da ya sake gigita alhlin gidan, a ɗari 360 suka nufo ɗakin, gani sukayi Maryam ta durƙushe a ƙasa sai sanbatu ta ke, faɗi ta ke, kar kamin haka, wlh ina sonka. bazan jureba, kaine kaɗai bangona a yanzu, ka taimaka ka cemin wasa ka ke min, ina zan saka raina naji sanyi, karka gujeni bayan ka sabawa zuciyata da sonka,,,, ganin yadda ta ke abu akamar mai shirin ta da iska yasa Mommy karɓar takaddar da ke ƙumshe a hannunta, ta rige gam gam, jiri ne kwashi Mommy Samha ta yi saurin riƙota ta faɗa jikinta, Daddy da shigowarsa part ɗin kenan ya ƙarɓi takaddar ya fara karantawa kamar haka....


*Assalamu alaikum*


*Iyayena da ku zan fara, kusani ina matuƙar sonku kamar raina, kummin aure ba bisa son raina ba, na so na muku biyayya amma na kasa yin hakan, kuyi haƙuri ku yafemin.*


 *Na saki matata Maryam saki ɗaya, idan kuna ƙaunata ku taimaka ku aurawa ɗan uwana  Imran ita.*


*Daga ɗanku mai ƙaunarku, SUDAIS*


Murmushi Daddy ya yi a ransa,tabbas Allah na sonshi tunda ya ke kawo masa komi cikin sauƙi, dashi dama Maryama ta da ce matar manya ce dama bata yara ba.



KUMIN AFUWA JIKIN SAI A HANKALI, DA KYR NAYI WANNAN ƊIN MA WLH🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🫂🫂

Post a Comment for "Inda Rai 20-21"