Inda Rai 7
*INDA RAI*....🥰🥰
*By*
*MARYAM ABDULLAHI*
( 💔💋Oum Shaheed💔💋)
https://chat.whatsapp.com/FI2ovuaHMbz0GBDNr2JeZXFI2ovuaHMbz0GBDNr2JeZX
*MIKIYI WRITER'S ASSOCIATION*
Page 07
Bismilla'hirrahma'nirrahim
Durƙushewa yayi agun yana kuka mai cin rai, yanzu dama duk wannan halin da ɗan uwan nasa ya shiga saboda ita ce,? yanzu ya zaiyi da ransa, tabbas yana sonta sosai, amma duk son da ya kemata bai kai ko rabin na ɗan uwansa kuma rabin jikinsa ba, sake jan jiki yayi ya janyo pic ɗin yana mai ƙare masa kallo, tabbas dai ita ɗin ce, sharrr yaji sauƙar hawaye masu matuƙar zafi, sakamakon tunawa da yayi da daransu na jiya, shafa fuskarta yayi ya hau magana shi kadai, "to ya a kayi tafi kyau anan,? komi nata ya banbanta dana wancar, fari, tsayi, gashi, wayewa, sannan kuma shekaru, daga dukkan alamu wannan tafi wancar komi da komi, to ko dai saboda zanene,? yasake tambayar kansa a karo na babu adadi, "a ina suka haɗu,? tunda yasan ɗan uwansa sai yayi shekaru baije rugar ba, ya Allah, wannan wacce irin chakwakiyace,? son mace ɗaya tsakaninsa da rabin ransa, kuma wanda babu abun da zai naima ya kasa masa, koda zai naimi rayuwar sane, to zai sadaukar masa, balle kuma mace, baƙin cikinsa ɗaya, yadda komi ya faru a daran jiya, inama hakan bata faru ba, yanzu da wanne ido zai kalli ɗan uwan nasa? sosai yayi kuka ya ƙoshi babu mai ban haƙuri, bai an kara ba sai gani yayi lokaci ya tafi sosai, jiki a saɓule ya miƙe ya maida komi inda ya samu sannan ya karanta komi ya fice daga ɗakin domin komawa asibitij SANJE VANI.
Da ƙyar Maryama ta miƙe bayan ta tabbar da bacci ya ɗaukesa, tasan idan bata gudu ba to tabbas kasheta zai yi, dan taga alamar bayida imani barai tausayi, jan jiki tayi ta fice a ɗakin, tana saka ƙafarta a parlon sukayi kiciɓis da Mommy, wanda ita kuma ta fi to haɗawa Daddy coffee, sosai ta rikece tana son kumawa ɗakin dan tsoron Mommyn takeyi sosai, garin sauri ta fame ciwon dake tsakanin cinyoyin nata, occhhh tayi ɗan ƙara kaɗan,ta zauna agun, "kallon ta kawai Mommy tayi tace mata," maiya fito dake a darannan,?,"sai kawai tasaka mata kuka, yi takeyi kamar an aikota, dan dama Maryama ba dai rakiba, "kijirani ina zuwa yanzu, tasa kai ɗakin Daddy, bayan tabar wajan Maryam ta so ta gudu amma ta kasa saboda zuwa lokacin jikinta yayi tsami sosai, tana zaune tana tunani har Mommy ta fito ta kamata har zuwa bedroom ɗinta, umarni ta mata data zauna a bakin gadon, ita kuma ta wuce toilet ta haɗa mata ruwa mai cike dasu haɗin tazargade da ƙwaro da kananfari, su komi da komi dai, wannan haɗin ba ƙaramin gyara mace ya keyi ba, sannan ta kuma ta kira ta, cike da kunya ta na ɗingisa ƙafa, Mommy ta umarceta data shiga ruwan, da sauri Maryam ta ɗaga ido tana kallon Mommyn, tsare gida sosai Mommy tayi tace, "kina ɓata mini lokaci, nabar nawa mijin yana jirana, oya zoki shiga, cike da kunya ta ƙarisa ta shiga ruwan, wanda batasan lokacin da ta zuba ƙara kuma ta miƙe da sauri, ai kan a wannan dare Maryama ta gane kuranta a hannun wannan ahali, dan saida Mommy ta sanja mata ruwa kusan sau biyar, kuma ko wani haɗin ruwa da kalar abubuwan da take zubawa, tun tanajin zafi har tafara jin daɗin jikinta, daga ƙarshe Mommy ta haɗa mata ruwan wanka ta bata sabon soso tace tayi wanka tsarki dana sabulu ta fito tana jiranta a ɗaki, kafun ta gama ta fito ta samu har Mommy ta fitar mata da wata sabowar dogowar riga, wanda azahiri Samha ta sayawa amma kuma bata bata ba, sosai rigar ta zauna ɗas ajikinta ta mata kyau ras da ita, "jawo ferfesun naman zabo Mommy tayi tace mata ta cinye tas ta bata plate ɗin, "karɓa tayi tana kai lomar farko taji wani kala a bakinta, kai yau itakan ta shiga ɗari bama uku ba, dakyar taci rabi ta ajjiye sauran, amma duk da haka bata tsiraba, sai gani tayi ta sake miƙo mata wani ferfesun na zallar kifi, shima dai haɗinne a ciki, shikan tas Mommy tasa ta cinye ta shanye romon, daga ƙarshe ta miƙa mata cup cike da tea mai kauri sosai, shima dai abunne a ciki, magani ta bata sha tace ta kwanta a ɗakin, kada ta sake ta fito.
ASIBITIN SANJE VANI
Zaune Sudais yake akan kujera kusa da gadon Imran, wanda har yanzu bai farka ba, an kira doctor Anjali bata kai ga ƙarisowa ba, sai da ya shafe kusan awa biyu a zaune yana jiran ta sannan a kace ya fice doctor ta ƙariso, ya so ya ganta amma babu hali, haka ya haƙura, acan ɗakin tearter an ci nasarar masa aiki cikin nasara domin hakanan Anjali taji tana son ceto rayuwar wannan majinyacin, ɗaki na musamman tasa aka kaisa sannan ta bada umarnin kada wanda aka bari ya gansa har sai in ita ta bada umarnin hakan.
Jin abun da likita tace da kuma shawarar su Anwar yasa badan yaso ba ya koma can gidan É—an uwan nasa domin ya yi wanka da sallah.
Yana komawa gida bayan ya gama duk wani abun da zaiyi harya kwanta domin kansa ba ƙaramin ciwo ya keyi masa ba, damuwa ta masa yawa a ransa, kawai daurewa ya keyi, ƙirrrrr ƙarar shigowar wayarsa ya dawo dashi duniyar daya tafi, ɗaga wayar yayi ganin Daddynsu ne akan layi, "hello, cewar Daddy, daga ɗaya bangaran yaji muryar Mommy tana cewa ya bata wayar, gaidasu ya yi sannan suka hau masa faɗa kamar zasu ari baki, musamman Mommy, "cewa takeyi, " wato saboda ka ci moriyar ganga zaka yada ƙoranta ko,? "tunda ka tafi babu wanda ka kari kaji lafiyarmu bare ka tambayi ƴar mutane daka ta fi ka bari cikin wani hali, " runtse idanu yayi jin ta ambaci wannan batu, inama mafarki ya keyi, da yafi kowa murna, amma inaaa aikin gama ya gama, "daga ƙarshe ina baka umarni ko wanne aiki ka keyi ka bari zuwa gobe ka dawo gida, kit yaji an kashe wayar kafun ya samu zarafin magana, dafe kansa da ke barazanar tarwatse masa ya yi, ya zama dole ya sanar musu halin da ɗannasu yake ciki, idan ba haka ba to ya zama dole ya tafi yabar ɗan uwannasa, wanda yasan bazai taɓa iya ai kata hakan ba.
Yau de a
Alhamdulillahi jikin Imran da sauƙi sosai, har an fito dashi daga ɗakin tearter, amma duk da haka likita Anjali ta hana kowa ganin sa, a cewarta wannan aikin tane, kuma yana buƙatar hutu sosai, wannan kenan.
"Salati kawai Daddy ke yi bayan ya gama sauraron ɗannasa, subhanallahi, kana nufin har aiki a kamasa a zuciya,? ya ilahi, "Sudais yace ka kwantar da hankalinka, na faɗa mukune saboda ganin kuna sonna dawo, alhalin bazan iya barin sa a halin da yake ciki ba, " HMMMM Daddy yaja dogon numfashi kafun yace, "yanzu kace jikin da sauƙi sosai ko? idan akwai matsala ka faɗamin sai na taho yanzu, "ah a Daddy, da sauƙi sosai, dan har muna sa ran ganinsa yau ɗin, wata likita muka samu mai mutumci, ta kula da bro sosai, nasoma na gan ta na mata godiya amma har yanzu bamu haɗuba, "To shikenan, zan bari har zuwa goben tun da da sauƙi, and baka tambayi iyalin naka ba? kuma kasan haƙƙi ne a kanka, "kayi haƙuri, shine kawai abun da ya iya faɗa, " ka kyauta, sannan kada ka gayawa mahaifiyarku wannan batun, kasan dai halinta akansa, sosai suka tattauna kafin daga bisani sukayi sallama akan sai gobe idan ya taso.
Samha wai dan Allah nikan bazaki kirasa kiji ko yana lafiya ba? kodan kin ga ina binki a sannu,? kin deji abun da Mommy tace miki, kimin biyayya kamar yadda zakiyiwa shi wan can, "dariya Samha ta kwashe dashi jin ƙarshen maganarta, wai wan can, to waye shi wancan ɗin,? ta tambayi aunty Maryam ɗin, "turo ɗan mitsitsin bakinta ta yi gaba, kafun tace ai kema kin sani, Samha tace to ai shikenan, dama bro Imran kika ce na kiramiki da tuni na kirasa, waye kuma Imran,? ta tan bayi Samha, au wai kina nufin baki san shiba? tab lalle kinyi missing, domin kaf gidannan an fiji dashi, sai dai bayi da kirki idan kika haɗasa da mijinki, Allah sarki, ya kasan ce mutum mai son ahalinsa, ya na sommu muna sonshi, kwatsam ƙaddara ta faɗa masa, wanda har yanzu babu wanda yasan makasoɗin mafarin lamarin, amma dai kamar akan soyayya ce a yadda na fahimta, ya sanja gaba ɗaya, ya zama shiru shiru, sai yawan faɗa da baƙin hali, a dalikin wanda yake so yabar zaɓin su Daddy da Mommy na karantar business domin tallafawa Daddy a harkar kasuwanci, ya zaɓi harkar zane, tun a wancan lokaci Mommy ta tsani yarinyar, tsana mafi muni, duk da bata taɓa ganin ta ba, amma tayi silar wargaza mata rayuwar ɗanta mafi soyuwa a ranta.
Ƙuriii Maryama tayi tana jin labarin da Samha take bata, take taji tausayinsa dana Mommy ya kamata, Allah sarki yanzu yana ina? "yana india, acan yayi karatu, bayan ya gama kuma yaƙi mai da hankali kan abun sonnasa, wato ZANE, "hmmmm Maryama ta sauƙe wata dogowar ajiyar zuciya, har cikin ranta takejin wani irin fargaba, ko miye dalili, nan Samha taci gaba da bata labarin yayan nata, wanda a zahiri sam ba tama jin mai take faɗa hankalinta ya kuma kan mijinta abun sonta, wanda ji ta keyi kamar sun shekara tare, shafa fusakarta tayi tana tuna daran farkonsu kafun daga bisani ta saki murmushi.
Yanzu Alhaji wace kalar tafiya zakayi lokaci ɗaya, ? babu kowa a gidan ka sani, kuma ni gaskiya kasan bana jure rashin ka kona minti ɗaya ne sai dole, Mommy ta ƙarisa maganar tana mai shigewa jikinsa,, numafashi ya sauƙe a saitin kunnenta, a ransa yake raya da tasan in da zaije da yanzu zaiga zallar bori, domin yasan halinta akan Imran sam bata wa kowa kara, ciki kuwa hadda shi kansa, karan hancinta yaja yana wasa da jelar gashin yace " haba zumata, kinsan nima ba'a son raina zanyi wannan tafiyar ba, kawai sai dole, taya zan iya kwana a wani wajan ni kaɗai babu, kema kinsan sai dai gangar jikina, amma zuciyar ta nanan tare dake tauraruwar mata, haka ya yaci gaba da mata kalamai masu sanyi har dai ta haƙura ta lamunce masa tafiya a goben.
bayan komi ya lafa a tsakinsu ta kwance a jikinsa tana wasa da kwantaccen gashin dake ƙirinsa tace, "yanzu haka zamubar rayuwar yaronnan a gargarce, ? kana ganin yanzu ko zuwamman da yakeyi akan lokaci ya daina, sannan a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya mafarkaina a kansa ne, na tsani yarinyar nan, bazan taɓa bari ya aureta bako da kuwa zai mutune akan sonta, na tsananeta, ta sake mai maitawa tana mai fashewa da kuka mai tsuwa zuciyar mai saurari, da kyar ya samu ya lallabata tayi bacci, shima a ransa yanajin zuciyarsa ta fara tsanar yarinyar da ko ganita basu taɓa yi ba.
Writing by Oum Shaheed🩷🩷
Post a Comment for "Inda Rai 7"