Inda Rai 9
*INDA RAI*...🥰🥰
*By*
*MARYAM ABDULLAHI*
(💔💋 Oum Shaheed💔💋)
https://chat.whatsapp.com/FI2ovuaHMbz0GBDNr2JeZX
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*✊🏼
Page 09
"Cikin farin ciki mai tsananin gaske Anjali ta baro ɗakin ta nufi office ɗinta, lalle ya kamata ta sanar da Ummy wannan abun farin ciki, ɗaukar wayarta ta yi ta danna number ɗin, daga bangaran Ummi ta ɗaga da sauri, dan tunda ƴarta ta sanar mata da taga Safras ta ke mamaki ta ya hakan ta faru? mutumin da ya ɓace sama da shekaru huɗu, hello! Ummy; yau dai ya farka, kitayani murna Anjali, ta sake faɗa dan gaba ɗaya ta kasa riƙe kanta, "Allah shine abun godiya, to har yanzu babu wanda kika haɗu dashi? daga cikin wa'ƴanda kika ce sun kawosa? hmmm Anjali ta sauƙe numfashi ta ce, "Ummy sai na dawo zamu ƙarisa magana domin nikan har yanzu banga wanda na saniba a cikinsu, daga wanda ya ke kiran kansa da ɗan uwansa har wanda ya zo yau a matsayin mahaifinsa, zamuyi magana leter, kit ta kashe wayar, ta jingina a jikin kujerar ta lumshe kyawawan idanunta ta lula duniyar tunani, sai sakin wani ƙayataccen murmushi ta ke yi, ita kaɗai tasan miye dalili, wannan sauyin nata, sake miƙe ƙafa ta yi a fili ta furta, "bazan sake bari kayi nesa dani ba, ka dawo gareni kenan har gaban abada.
Karaf maganganunta suka dira akan kunnen Sakku da Aliyu da doctor Anwar, sai bayansu wata ma'aikaciya da ta musu jagora, kallo kallo suka fara a tsakinsu, daga bisani ta basu umarnin zama, sai da suka ɗauki lokaci kafun ta ɓuɗe baki da kyar ta musu bayanin komi lafiya yanzu, sannan kuma ta sanar dasu ta na son ganin ɗan uwansa da kuma mahaifinsa. "Muna so ki bamu damar ganinsa" Sakku ta faɗa ta na mata kallon sama sama, kallonta likita Anjali ta yi ta ce, "ba yanzu ba, na sallemuku, kuna iya tafiya, Sakku zata sake magana Anwar ya dakatar da'ita ta hanyar ɗaga mata hannu sukayi waje, aransu suna jinjina wannan ƙarfin hali da nuna ikon da Anjali ta ke yi tun bayan dawo da Imran ƙarƙashin kulawarta.
Maryama ce zaune a ƙasan kafet kanta a ƙasa, sanye ta ke da wata dogowar riga kalar brown da ratsin milk, ta yane kanta da mayafin rigar, Mommy ta na zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon, sai wasu mutum shida daga gefe, ko wance ta hakimce sai kallon Maryama suke, kallo, kallo mai cike da raini, "ki tashi ki kawo musu ruwa Maryam" "Mommy ta bata umarni, Samha ta miƙe zafa bita Ammin Sahla ta mata daƙuwa a fuska, sai Sahla dake kwance a gefen Mommy ta ce, "ki haɗomin da abinci dan yunwa nakeji, kuma karkimin ƙazanta, dan natsaneta, ta ƙarisa maganar da tura baki tana hararar ta, jiki a saɓole Maryama ta ƙarisa shigewa, ta fi minfi goma a tsaye, sannan ta haɗa komi ta fi to, haka ta bi kowa tana miƙa masa har ta zo kan Sahla, a gadarce ta ƙarɓi abincin ta ajiye a gefe, zata nemi waje ta zauna Ammin Sahla ta daka mata tsawa ta ce wuce kibawa mutane waje, matar tushe kawai, ba Maryam ba hatta Mommy da Samha sai da ransu ya sosu, amma haka Mommy ta danne bata nuna ko akan fuskartaba, tashi Samha ta yi tabi bayan Maryam domin dama can basa shiri da Ammi, saboda macece mai matuƙar son kanta da yaranta.
A ɗaikinta ta samu Maryam a zaune a bakin gado sai kuka take mai cin rai, Allah sarki Innata, Allah ya miki rahma innata, kuka ta ke yi sosai, wanda rabon da ta yi irinshi tun bayan mutuwar Innarta, ƙarisawa Samha ta yi ta zauna daf da ita tana share mata hawaye, domin itakan hakanan take sonta, jitakeyi kamar ciki ɗaya suka fi to, haƙuri ta ke bata da kalamai masu daɗi, har ta samu ta daina kukan, hira suke kamar dama can sun saba, da Samha kawai ta ke samun nishaɗi, kullum da soyayyar mijinta ta ke kwana ta ke tashi, gashi tunda ya ta fi ko a waya ba sake jinsa ba, soyayyar mininta a jininta ta ke yawo, tana addu'ar Allah ya dawo mata dashi lafiya, "wai nikan Aunty Maryama a ina ki ka tsaya da karatune? ta faɗa mata iya aji biyar ta tsaya, amma ta na son karatu sosai, ana ta bata labarin haɗuwarsu da Sudais da kuma yadda ya ke ƙara mata karatu, sunata hira har sun manta da abunda ya faro a falo.
Zaune Daddy da Sudais su ke a office ɗin likita Anjali, bayan gaisuwa da godiya da suka mata office ɗin ya ɗauki shiru, sai duba wasu tarin ta kaddu da takeyi a gabanta, jin shirun ya yi yawa kuma da 'alama bata san matsayin Daddy ba, Sudais ya yi gyaran murya ya ce mata muna jinki, domin muna buƙatar ganinsa, ya ɗaura da faɗin, "tunda jikin ya yi sauki yamu ta fi dashi.. "zuwa ina? Anjali ta tambaya tana kallonsa, mamaki ƙarara akan fuskarsu suka kalli juna, Daddy ganin rainin hankalin nata ya yi yawa yasa cikin fushi ya ce, "zuwa gida Nigeria, tunda ai nanɗin ba mahaifarsa ba ce, idan wani abu ki ke buƙata to ki sanarmin ko nawane, sannan ina miki godiya a bisa ceto mini rayawar ɗana da ki ka yi, saboda haka ki gama duk wani stari naki zuwa gobe zan ta fi da ɗana, ya ƙarishe maganar da buga hannunsa aka table ɗin dake gabansa.
Tunda ya fara magana likita Anjali ta ke kallonsa, lalle wannan koma waye ƙarfin halinsa ya burgeta, murmushin gefen baki ta yi sannan ta ɗauki tarin takaddun da ke gabanta ta miƙa masa, saka hannu ya yi a gadarce ya warce ya janye idonsa ya mayar kan takardun, ai da wani irin shork ya mike, take gumi ya fara tsere a duk wata ƙofa dake fidda gashi na jikinsa daga bisani ya yanke jiki ya faɗi agun, cikin matuƙar razana Sudais ya ƙarisa yana jijiga Daddy, amma ko motsi bai yi ba, likita Anjali ko motsi ba ta yi daga inda take zaune ba, danna wata ƴar ƙaramar na'ura ta yi babu ɓata lokaci akazo aka fita dashi zuwa ɗakinda za'adubasa, gaba ɗaya Sudais ya rikice, shin miye Daddy ya gani a takaddun? wanda har ya yi silar faɗuwarsa? sunkuyawa ya yi ya hau tattare takaddu ya fara dubawa, babu abunda ya himta sai takaddar shedar haihuwa da ta shedar zama ɗan ƙasa, sannan sai wasu pics na mace da namiji daga gefen pic ɗin wani yaro ne fari tas, dukansu fararene tas kasancewarsu indiyawa, to mai hakan ya ke nufi? suwaye wa'ƴannan ɗin? mai ya firgita Daddy? tambayoyi ne fal a ransa amma babu mai amsa masa su, kallon Anjali ya yi sai danna waya takeyi ko kallonsa ba ta yi ba, fita ya yi ya nufi ɗakin da Daddy ya ke, samu ya yi har sun gama dubasa ansa masa dirip.
Sai da Daddy ya shafe kusan awa uku sakamakom allurar baccin da aka masa kafun ya farka da salati a ɗauke a bakinsa, "sannu Daddy, ya kakeji yanzu? "kallonsa Daddy ya yi ya ce ka shirya mana zama da wannan likitar yanzu ko ta halin ƙaƙa, " wai lafiya kuwa Daddy? "kayi abunda na ce maka yanzu.
Tashi ya yi ya nufi office ɗinta, gaba ɗaya ji ya ke idan xai samu dama zai iya shaƙeta ta mutu, norking ya yi a ƙofar babu jiran izini ya sa kai ya shiga, ɗago fararan idanunta ta yi ta bisa da kallo ganin iya gudun ruwansa, "Daddy ya nason zama da ke yanzu.
"Murmushin gefen baki ta yi ta ce, " ka ce masa ba yanzu ba, kallon agogon hannunta ta yi ta ga ƙarfe 1:45 pm zuwa ƙarfe 5:00 pm saboda yanzu lokacin bawa Safras abinci ya yi, sannan kuma a bangaranku kamata ya yi kuyi sallah tukunna, ta na ƙarisa maganar ta miƙe har ta yi hanyar waje ta tsaya ta ce masa, "idan ka gama tsayuwar kajamin ƙofa, ta fice ta barsa a tsaye kamar an dasashi, shi ya rasa da me wannan lokitar ta ke taƙama.?
Jiki a mace ya je ya sanarwa Daddy abunda ta ce masa, jinjina kai kawai Daddy ya yi, a ransa ya ke faɗin tabbas lokacin tonuwar asirinsu ya yi, ya zama dole ya yiwa tufkar hanci tun kafin abubuwa su kwaɓe masa.
Kallonsa kawai Sudais ya je yi, kasan cewarsa lawyer mai kaifin basira har ya faimci rikicin da ke kwance a fuskar Daddyn nasu, amma bazaiyi gaggawar son jin komi ba, zabi komi a sannu har sai ya gano miye ya ke shirin faruwa.?
Tun bayan farkawar Imran ya ke son yaga ɗan uwansa, da kima Daddynsu kasan cewar Imran ya sanar masa da zuwansu, amma har yanzu babu wanda ya gani daga cikinsu.
A hankali ta boɗe kofar ɗakin ta shigo, matashiyar likita mai kimanin shekaru talatin a duniya, kyakykyawace ajin ƙarshe, tana da manyan idanu masu maiƙo farare tas, sai dogon hanci har kusa ca baka, wanda ya sake ƙawata mata fuska, kai a taƙaice komi ya ji a jikinta, tunda ta shigo ya ke binta da kallo, ƙarisa shigowa ta yi cikin sakin fuska ta ce "barka da tashi my Ladka, "Saurayinta kuma? Imran ya tambayi kansa, "ina waƴan da aka ce min sunzo dubani,? ɗan uwana da kuma Daddymmu,? da sauri ta kallesa jin cewar shima wai ya sansu, matsawa ta yi ta zata riƙe masa hannu ya janye da sauri, a ranta ta ji cewar tabbas ya samu matsala a kansa, tinda har ya kasa ganeta ba rai ya tambaye ta gudan jininsa abun sonsa Arshad.
Post a Comment for "Inda Rai 9"