Breaking News

Kurkukun Kaddara 10

*E10*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata’ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi


Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faÉ—akarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaÉ—antarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al’ummar Annabi ba.✍️_

GargarÉ—i

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube don already na siyar da littafin, Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_

 

*South Korea*

Seoul City-Gangnam-Gu

Hamshaƙiyar Unguwace ta Attajiran masu kuɗi dake zaune a Seoul, Babban birnin korea ta kudu, babban birni ne mai manyan-manyan gine-ginen gargajiya dana zama ni masu matuƙar ƙayatarwa, ga manyan hanyoyin jiragen karkashin kasa da kuma Wuraren shaƙatawa, masu matuƙar jan hankali, A ɗaya daga Cikin jerin Modern apartments din dake a Gangnam-Gu Haɗaɗɗen masaukin Uncle abdallah ya ke, inda suke sauka duk in suka zo ƙasar.

tafi Æ™arfin awa É—aya a tsaye Tana Kallon hotonsu dake a manne Jikin bangon bedroom É—insu, Idanuwanta Sun Cicciko tab da Æ™walla, Har yau she ne wannan baÆ™in Cikin zai gushe acikin zuciyarta? taya zata Iya sakin jiki tayi rayuwa acikin duniyar nan batare da Ya’yanta ba? tabbas ta yi babban rashin, A kullum ta kali hoton su, sai ta zubar masu da hawaye, Almost 2 years kenan babu su babu labarin su, itace kullum Cikin zullumi da zarar wayarta tayi ringing, jikinta har 6ari ya ke yi don ta É—auka taga ko Jami’an dake bincike kan case É—in su tajuddeen ne suka kirata don su sanar da ita ko an gano inda suke,
Tun lokacin da suka dawo Seoul hajiya adama Bata Æ™ara samun kwanciyar hankali ba, Gangar jikinta gaba É—aya tana a nigeria, Sunan tana zaune a korea ne, duk irin Sabon da tayi da Æ™asar hakan baisa ta gundure ta ba, duk don saboda Abunda ya faru na 6acewarsu tajudden, Ita fa a ayanzu Tafi sha’awar su koma nigeria, Hankalinta sai yafi kwanciya koba komai Zata dinga ganin Æ´an uwanta,
Tsadadden leshi ne a jikinta, launin silver yabi shape ɗin jikinta, Ta kashe ɗaurin ɗan kwali, Yayin da ta goya hannayenta a saman ƙirjinta,
Sam ta kasa janye idanuwanta daga Kallon hoton nasu da take yi, bakowa tafi ji ba, face Angle ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalinta ba, taso ace tuntuni rainon yarinyar ya dawo hanninta da yanzu suna atare, Sai dai kash Ƙaddara ta riga fata,
Ziraran hawaye ne suka soma saukowa kan kuncinta,
Muryar me aikinta ce Ajumma ta katse mata Tunanin nata
Cikin harshen su na korea take sanar da ita cewa SaÆ™on ta ya iso, Share hawayen fuskarta ta yi, kafin tace”A shigo mun da su ciki,” itama da harshen nasu take magana, don tana ji ba laifi,
Turo ƙopar ɗakin ajumma tayi, Babbar macace ta kwana biyu aduniya tsufa ya fara kamata, fara ce sol gashin kanta iya kafaɗarta ya tsaya, Jikinta na sanye da ƴar riga da gajeran skirt, Faffaɗan tray ne a hannunta, Saman shi kwalaban Soju ne (Giya) sun kusa Uku, tare da glass cup guda ɗaya,
A saman Round table É—in dake a kusa da gadon hajiya adama, ta É—aura tray É—in, Ta juya zata fita, har ta kusa kaiwa bakin Æ™opar fita muryar hajiya adama ta katse ta”Idan mutun yana so ya bugu sosai, har ya manta wanene shi, kamar yaya ya kamata yasha” shiru ajumma tayi tana tuna gargaÉ—in da Abdallah ya yi mata akan karta kuskura ta Æ™ara ba matar shi soju tasha, idan ba haka sai ya kore ta daga aiki, Yau É—unma don Abdalla baya a gari ne, Shiyasa ta kawo mata soju É—in,
“Kin yi shiru baki amsa mun ba”? Muryar na kerma tace”Kwalba É—aya, Amma ran ki shidaÉ—e ina jin tsoro, kada yalla6ai ya ritsa ki a lokacin da kika sha kika bugu, Zai iya korata daga aiki”
“Kada ki damu, Bazan faÉ—a ma shi cewa ke kika kawo mun giyar ba, Zance ni na fita na siyo ta, hakan yayi maki” jinjina kai ajumma tayi kafin ta ruÆ™e handle É—in Æ™opar ta fuce,
Zama Hajiya adama tayi a gefen katafaren gadonta, takai hannu ta Ɗauki kwalbar Soju Ta cire mufin, Abaki ta kwafata Cikin ƙanƙanin Lokaci ta shanye duka, wani irin biji biji tafara gani a cikin idanuwanta, Ajiye kwalbar tayi, tare da kai hannu ta ƙara ɗaukar wata kwalbar ta shanye duka, sauke kwalbar tayi saman table, Ta yunƙura zata miƙe duniyar ta soma juya mata, sha tara sha takwas ta dinga gani acikin idanuwanta, wani irin nauyi Jikinta yayi mata, Tangal tangal ta soma yi tana tafiya ta nufi hoton dake manne jikin bangon ɗakinsu, Ta curo hoton ta ƙura mashi ido tana kallon shi, har wani girgiza kai take yi,
Can dai ta rushe da wata irin mahaukaciyar dariya tamkar zararra, muryarta ashaÆ™e ta soma magana”Duniya juyi juyi, wohoho Kai ya É—au zafi, In ban da ta6ara da É—amsil basira Ta ya za’ace mutun ya 6ace tun 1960 Amma An gaza gano inda yake? Ƴan sandan nan basu san ciwon kansu ba, Gashin Hammata ma yafi su Amfani, Nayi fushi Allah Ni da kaina zan nemo abuna ahe, Ku zuba ido ku gani yanzun nan zan gano su,’ takai Æ™arshen maganar tare da ajiye hoton Æ™asa, tattare Zanin leshin jikinta tayi, ta zuÆ™unna Æ™asa tana rarrafe, SaÆ™o da lungu na É—akin ta shiga Bi tana sambatu Tana faÉ—in”Gasu Can sun 6oye, kamo su nan kamaso Sunan, Zo nan É—an É—ana Uzairu Yaron mamansa, kaima zo Tajuddeen É—ina, Kai na manta da Angela ta Yarinyata zonan in raira maki waÆ™a, Wacece Kumatu Angel ce kumatu, kumatutu kumatu, kumatutun mama, kumatutun baba……” tana raira waÆ™ar tana kuka, zama tayi tare da cewa”Yauwa, Ga abinci Nan Shekaran jiya na girka maku shi, nasan kuna jin yunwa, banda wawaso, duk wanda ka samu rabon ka ne,,” gaba É—aya ta haukace ita kaÉ—ai take ta sambatu, giya takai mata karo, ita fa ala dole su take gani acikin idanuwanta, tana magana tana sakin gyatsa,
YunÆ™urawa tayi ta miÆ™e tsaye tana faÉ—in”Zan Binciko ku duk inda kuka 6oye ja’iran yaran, harni zan girka maku abinci ku Æ™i ci? Kai tajo hada cewa ba daÉ—i? Ni da ku ne” hannu tasa ta zuge zip É—in rigarta, Ta cire rigar tare da yin wurgi da ita Æ™asa, Ta warware zanin shima ta jefar da shi Æ™asa, ya rage daga ita sai undy, Ƴar duma duma da ita, ga uban tumbi, wurgi tayi da kallabi leshin kanta, Ta koma mahaukaciyar Æ™arfi da yaji, dambe ta shiga yi ita kaÉ—ai, sai da ta Tarwatsa komai na É—akin, da sunan tana neman Su Uzairu, itace har cikin toilet, gaban toilet seat taje tana leÆ™awa, Hankali Ya gushe,
A karshe ta zube Æ™asa tana birgima tana faÉ—in”Ya Allah kota sama ne, A jeho mini su, Nasan kasan inda su ke, tunda kai kana ganin komai, ko karkashin Æ™asa mutun ya 6oye…….”
Ta jima tana sambatu, kafin Allah ya kawo bacci ya yi awon gaba da ita, Lokacin da Uncle abdallah ya shigo Cikin gidan, Jikinshi sanye Cikin Suit sun zauna ma shi,
Tun a palour suka yi kici6us da Ajumma, Sam ba ta yi tsammanin Aranar zasu dawo ba, A tsorace ta gaishe dashi muryarta na kerma, Kota kanta bai bi, kaitsaye ya nufi bedroom É—insu Ya tura Æ™opar ya shiga, tun daga kan Kayan Hajiya adama data tube ya fara Cin karo da su yashe a Æ™asan tiles, Ko’ina na É—akin ta hargitsa shi, tsayar da idanuwan shi yayi akan hajiya adama da ke kwance Æ™asa ta baje sai sharar bacci take yi hada minshari, Ga kwalaban Soju É—in da tasha nan Ajiye saman table,
“YA SALAM” rai a6ace ya ambaci hakan, kutsa kai yae cikin É—akin A Æ™asa yayi toxali da hotonsu Uzair, wanda hajiya adama ta jefar Æ™asa, zuÆ™unnawa yayi tare dakai hannu ya É—auki hoton nasu yana kallo,
Nan take ya gane dalilin shan giyar nata, in har zata cigaba da kallon hotonsu uzair, to kuwa bazata ta6a daina shaye shaye ba, ba irin faɗan da baiyi mata ba akan tadaina amma taƙiya,
Takawa yayi zuwa jikin bangon ya liƙa hoton, kafin Ya nufi inda take a kwance ya zuƙunna, ya jima yana kallonta, hannu yakai saman ƙafarta yaɗan bubbuga, Shiru bata farka ba, Sai da yayi dagaske Sannan Ta buɗe idanuwanta waɗanda sukayi jawur dasu, Tana kallon shi,
“Get up, Ina son magana da ke” da alama har yanzu wine É—in bata sake ta ba, daÆ™yar ta lalla6a ta miÆ™e zaune tana faman yin hamma,
“Waya kawo wannan abun Cikin gidan nan”? Ya yi tambayar yana nuna kwalaban Soju É—in da ta sha, fuskar shi a murtuke,
“Ni na kawo su, don su É—ebe mini kewa,”
“Narasa gane meke damunki? Meyasa kullum burinki ki 6atamun rai? Kin manta sharuÉ—É—an da dr park ya gindaya maki akan lafiyarki? Kina tunanin shan wine É—in da kike yi shi ne mafita agare ki? Yakai Æ™arshen maganar yana kallonta,
Sai faman lumshe ido take yi,”magana fa nake yi maki? Harara ta wurga mashi”To Ubana Alhaji Adamu, Zaka fara faÉ—an naka ko? nasan bai wuci kace haramin bane shan giya, Zan illata lafiyata, bayan shi sai kuma me”? A harzuÆ™e tayi maganar tana kallon shi, har saida gabanshi ya faÉ—i ras! Saboda yadda ta rufe ido tana gaya mashi magana, lallai har yanzu bata dawo Cikin hayyacin ta ba,
Sassauta muryarshi yae, Cikin sigar lallashi yace”Allah ya huci zuciyarki, ni ba faÉ—a nace zanyi maki ba, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan baida amfani, idan damuwa ce tayi maki yawa Ki É—auko qur’ani ki karanta mana”
“Ka yanke shawara game da komawarmu nigeria? nifa na lura kamar baka damu da 6acewarsu ba, harkokin kasuwancinka kawai kasa agaba, NikaÉ—ai ce nasanya damuwa akansu, almost 2 years ban ta6a ganin ka tashi tsakar dare kayi Nafila a kansu ba,
Jinjina kanshi yae”Adama kenan, Ae duk cikakken musulmi wanda yayi imani da Allah, ya kuma yi imani da Æ™addara mai kyau ko mara kyau, Bazai ta6a zama ya Æ™untata kan shi ba don Allah ya jarabce shi, Nasan cewa aduk inda suke Allah yana atare dasu, Kuma inayi masu addu’a, wannan ma ya wadatar ba dole saina tashi tsakar dare ba, bansani ba ko so kike in ajiye harkokin kasuwancina, In sanya damuwa araina a Æ™arshe Nima in koma É—an giya,’ hannu tasa ta dafe gefen kanta, hawaye masu É—umi suka soma shararowa mata,
RuÆ™o hannayenta ya yi Cikin nashi”Ki faÉ—amun kome kike so zanyi maki, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan kodan saboda lafiyarki, bana so kema in rasa ki kamar yadda narasa iyaye na, da kuma ya’yana,” cikin shessheÆ™ar kuka tace”Mu koma Nigeri, Nagaji da zama a Æ™asar nan, Æ™wara idan ina acan zanfi samun kwanciyar hankali,”
“Shikenan, Zanyi abunda kike so amma ki É—an bani lokaci, In kammala wani aiki da nake yi, da zarar na gama zamu koma can É—in kamar yadda kikeso,”
GyaÉ—a kai tayi”wannan karan idan har baka Cika min alÆ™awarina ba, sai dai kawai kaji labarin Na tafi,”
“In sha Allah hakan bazata faruwa,” sosai ya kwantar mata da hankalinta, Har ya samu Ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya, Da kanshi ya gyara masu É—akin, ya tattara kwalaban Soju É—in ya fita yaje ya jefar dasu, Sannan hankalin shi ya kwanta,

*UAE*

HaÉ—aÉ—diyar Daular Larabawa

Abu dhabi,

Alhaji Ubaid ne zaune A cikin Hamshaƙin falon gidansa, Wanda yaji Hadaddun furniture tsadaddun gaske, ga wani sanyin A.c dake ratsa sassan Jikin mutun,
Ya ɗau wankan Shadda, Ya hakimce saman 3 seater, Hannun shi na ruƙe da jarida, A gaban shi table ne mai ɗauke da mug na coffee,
Ya natsu yana Karanta Jaridar, kamar daga sama yaji An fisgeta, kafin ya É—ago ya kalli wanda ya kwaci jaridar daga hannun shi, tuni tayi tearing É—inta into pieces,
Bakowa bace face Laila, Mahaifiyar Benazir, doguwar balarabiya tasha wankan Abaya launin royal blue, yalwataccen gashin kanta har tsakiyar bayanta, Ƙafafunta na sanye da High heels,
Zuba mata ido yayi batare daya ce mata ƙala ba,
“Idan har zaka cigaba da kallon waÉ—annan gantalallun Ni kuma bazan gaji da yage duk wata jarida da zaka kawo A cikin gidan nan ba, tunda na lura bakasan ciwon kanka ba, Menene alaÆ™arka da su? Ga Æ´arka ta cikin ka da ta 6ata shekara da shekaru Baka damu da ita ba, sai wasu can rainon talauci,” rai a6ace takai Æ™arshen maganar, tare da juyawa ta nufi bedroom É—inta, Sai gata ta dawo hannunta ruÆ™e da newspaper me É—auke da sunan khaleej times, ta wurga mashi saman fuskar shi”Ita ce jaridar dana amince maka ka karanta, tun da karantun jaridar ya zamar maka dole”
Hannu yasa ya janye jaridar daga saman fuskar shi, still idonshi na akan fuskarta,
“Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da Æ™ima a idona, dake da Æ´ar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin É—a’a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,”?
Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba,
Sai da ta mula tasha iska tukunna tace”bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba,”
Murmushin takaici yasaki kafin yace” Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saÆ™o a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waÉ—annan bayin Allahn, Rana É—aya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata É—aya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, Æ™aramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki”?
Ta6e baki Laila tayi”Laifinsu ne ae, kasan Æ´an jarida da kafiya, ga shegen naci da bin Æ™waƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi Æ™arfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,”? Yadda tayi maganar ko ajikinta,
Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta”Hada jikarki fa a cikinsu,”
“Jikarka dai, Ni ban haÉ—a komai da su ba, Auran benzir da yaron nan Æ™addara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi Æ™arfin shi, Ni nayi tunanin ma É—an Abdallan ne shima ashe É—an wani faÆ™irin mutunne dake zaune a karkara…..” rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita”Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya’yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi,”
Murmushi tasaki tana kallon shi,”Nifa komai zaka faÉ—i akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee É—inka nan Yana huce wa yakamata ka sha” tayi maganar tana nuna mashi Mug É—in dake ajiye saman table,
Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba,
Kashe murya tayi tare da cewa”Habibi fushi ka ke da Nooril Æ™albin taka”? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta Æ™ura mashi ido tana kallon shi,
Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing,
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan,
Girgiza kai lailah tayi”É—an siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuÆ™a shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon Æ™afar ta shi yayi sauÆ™i, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban Æ™asa, Wannan shi ne burin da nake da shi,’ takai Æ™arshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a Æ™alla takai shekara arba’en, jikinta na sanye da kayan aiki,
Cikin harshen labaraci tace”ki sanar ma Sauran maids É—in Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt”
Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da”Toh, in sha Allah za’a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya,”
Laila ta amsa mata “ameen”
Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu,
“Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya Æ™afa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin Æ™oÆ™arina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana,”
On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana” Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi É—aya ne, wani irin bauÉ—aÉ—É—an mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci,”
“zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba É—aya yana a nigeria, nadamu da su,” fuskarshi É—auke da matsananciyar damuwa yakai Æ™arshen maganar, abokin nashi da suke waya yace”Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne,” muryarshi da alamun mamaki
“kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce,”
Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi,
Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buÉ—e mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faÉ—in”Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo Æ™asar” Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani Æ™amshi dake fita a jikinshi,
Rungume juna su kayi kamar zasu haÉ—iye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden É—in gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu ShimfiÉ—a Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su,

Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota?

Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko’ina duhu, babu haske ko misÆ™ala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an É—aura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza É—agawa, Wani baÆ™on yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko’ina, numfashin ta kanshi daÆ™yar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu’a da tazo bakin ta,
Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haÉ—a uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda Æ™uncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faÉ—in”Wai ba kowa ne a kusa, Ku faÉ—amun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness……” cikin shessheÆ™ar kuka takai Æ™arshen maganar,
Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas,
Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta,
Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo,
tamkar hostel na kwanan É—alibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(Æ™arfe) A Æ™alla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun É—aya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a É—aya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta É—akin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there’s a table an É—aura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar É—akin akwai shimfiÉ—aÉ—É—en red carpet,
Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu,
Lumshe idanuwanta ta É—anyi tare da buÉ—e su akan Æ™opar dake a rufe, saman Æ™opar taga an rubuta “Toilet” nan take ta gane makewayi ne, É—akin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garÆ™ame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi,
A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1,
Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta,
Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce,
Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziÆ™i ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko’ina a kan fuskarta,
Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail É—in benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye Æ´an hanjin cikinta,
Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buÉ—e Æ™opar É—akin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls É—in ta kan Æ™opar tana jira taga wata ja’irar ce ko wani ja’irin ne xai shigo, domin kuwa ta É—aura É—amarar yin yaÆ™i da duk wanda ya yi silar É—auko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison.
Cikin Æ™anÆ™anin lokaci aka buÉ—e Æ™opar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon Æ™afar mutanan da suke Æ™oÆ™arin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaÉ—an Æ™irji, Wata kalar Æ™ira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baÆ™aÆ™en kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, Æ™afafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko’ina arufe ya ke, motsa lips É—inta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunÆ™urin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan Æ™afar matashin saurayin da ke Æ™oÆ™arin shigowa, kalar uniform É—inta ne ajikinshi baÆ™aÆ™e masu É—auke da No 1 A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes É—in shi farare Æ™yal da su, Yana da dogon hanci, full lip É—insa red colour ne, yana da dimple É—aya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips É—insa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back É—insa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba,
ta yi tunanin shi kaÉ—ai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips É—inta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta,
Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya,
A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar,
Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace”wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaÆ™ata da ku!”nuna matasan Æ´an matan ta yi da yatsan hannunta “ku faÉ—amun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na” a harzuÆ™e ta yi maganar,
É—aya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci”kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu É—aya na sani shi ne, kurkukun Æ™addara gida ne na marayu wanda basu da gata,’
girgiza kai angel ta yi’ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave……..” kafin takai Æ™arshen xancen nata wata matashiya me É—auke da uniform jajaye no 4 baÆ™a siririya tace”ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun Æ™addara shi ne gidanmu”
Uwar harara angel ta wurga mata”prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za’a sato mutun akawo shi wani baÆ™on wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faÉ—o ba,” yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta,
Takun tafiya suka jiyo daga cikin É—akin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faÉ—in”Ina Magana”da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin É—akin hada angel,
Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma,
Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo?
Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace”ko É—aya! ta Æ™opa na shigo ciki” ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata Æ™opa dake a É—aya daga cikin kusurwowin É—akin,
“Nan É—aki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da BATOOL!” ta kai Æ™arshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faÉ—i, masu kalar uniform É—in angel,”
Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saÆ™awa acikin zuciyarshi”?
“Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace, Ko da ace ni marainiya ce taya za’a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka É—auko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh?
“Gidan kurkukun Æ™addara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison É—in nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa’annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi” tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin,
Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin É—aga murya tace”If it’s an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won’t believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka É—auko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku” takai Æ™arshen maganar tana haki ta harzuÆ™a sosai,
Sauran prisoners É—in duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baÆ™uwar yarinyar da su kayi tare da tsohuwa, tun da suke a gidan prison É—in ba’a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baÆ™uwar da suka tsinta yau acikin su,
“Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!”
A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi,”
“Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa É—an wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!”
Tana huci takai Æ™arshen maganar tare da É—auke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar” ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka É—auko ni, Kuma a faÉ—a mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naÆ™asa rayuwar shi”
Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya,
Sassauta murya ta yi”idan kun saba rainawa mutane hankali kuna É—aukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buÆ™atar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah,”
Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace”buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke É—iya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya”
Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata,
“Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu É—aya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damÆ™a mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaÆ™in É—aukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu….idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki,”
Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheÆ™ar kuka tace”kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma Æ™arya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun,”
Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa”Æ´ar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buÉ—e baki ki kace mun Æ™arya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa Æ´an uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa’annan ina mai Æ™ara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki”
Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta,
Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba É—aya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waÉ—annan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta,
Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton”Innallahi wa’inna ilahirraji’un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka É—auki raina nima in huta………”sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina,
Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu,
Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faÉ—i a sume.
Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips É—insa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me É—auke da no 2 haka kowani gado yake da number,
Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun É—aya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta,
Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a Æ™asa ta É—aura shi saman cinyarta, juyawa ta É—anyi tare da kallon kowannan su dake kishingiÉ—e saman gadonshi, tsayar da Æ™wayar idonta ta yi akan Hannah ta É—an É—aga murya tare da cewa”abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta?
Ta6e baki hanna ta yi”rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaÉ—ai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta,” Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace”nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, “yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa”bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba’a gama rainon ta ba,”
Gaba É—aya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci,
“Is enough, kunsan bana son hayani ya” wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow,
Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai,
Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana”SISTER” har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buÉ—e idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta É—auke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa”bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa,”

❤dedicated to Aunty kubra❤

*Daga alÆ™alamin Boss Bature✍️*

No comments