Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kurkukun Kaddara 2

*E2*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata’ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi


Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faÉ—akarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaÉ—antarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al’ummar Annabi ba.✍️_

GargarÉ—i

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_

 

The Begining Of The Story,(Farkon Labari)

ƙasa ƙasa Cikin baccinsa ya soma Jin sautin kukan Jariri acikin kunnuwan shi, tun abun bai damun shi har kukan Ya fara addabar shi, ya hana shi sakat wanda Hakan Yayi silar farkawar shi daga bacci, a hankali ya ɗan ware manyan idanuwan shi masu ɗauke da Bacci don da alama bai gaji da baccin ba, Ceilling Ya ƙurawa ido kamar mai karanto wani abu, a ƙoƙarin shi naya tariyo abunda kunnuwanshi ke jiyo mashi wanda Yayi silar farkawar sa daga Bacci,

Yana ƙoƙarin tunanowa Kwatsam Yaji kukan Jaririn Inya inya, mai sautin gaske, Zumbur ya ƙarasa Janye Blacket ɗin daya Lullu6a dashi Yayi wurgi dashi gefe ɗaya, kayan Bacci ne Ajikinshi Brown Colour Riga da wando, yayi mamakin ganin babu ita asaman gadon, ko ina taje ne? sauko da ƙafafun shi ya yi ƙasa ya yi, Cike da fargaba Ya miƙe yana mai tunanin Inda aka samu Kukan Jariri Acikin Gidansa, Shi dai A iya sanin shi Matar shi bata haihu ba,duk da cikinta nata yakai wata tara,

Gaba ɗaya ya ruɗe Yama rasa Ta ina zai ga Jinjirin dake kuka, Domin kuwa sautin ya karaɗe Ɗakin nashi,zukunnawa Ya yi tare da leƙa ƙarƙashin gado, wayam baiga komai ba miƙe wa ya yi da sauri ya nufi wardrobe Ya buɗe ya zazzago da kayan dake acikinta, duk a ƙoƙarin shi naya gano inda aka samu kukan Jariri aɗakinsa, Tuni ya haɗa uban gumi ajikinshi, aran shi harya fara tunanin kodai Aljanune!? abu kamar wasa idan jaririn yayi kuka sai ya lafa ƙasa ƙasa,wannan karan Yanayin kukan tamkar Ana zare Ranshi ne, har wani jan kukan akeyi inyaaaaaaa,

“Ka duba toilet”?zuciyar shi ce tayi mashi tambayar, shiru ya É—anyi kamar me tunanin wani abu,tun da yake arayuwar shi wani abu bai ta6a tsorata shi ba irin na yau, kukan jaririn duk ya firgitar da shi,har wani gumi ya haÉ—a,

Ja da baya da baya yayi a hanzar ce Ya juya gaban Faskeken Madubin É—akin, Wayar shi ya É—auko yana dannawa Call logs Ya shiga, missed calls Ya tarar Na Uzair, babban amininsa

Calling Layin yayi tana fara ringing, uzair ya É—aga kiran ko sallama baiyi ba ya soma magana”Uzair Akwai matsala Cikin gidan nan fa!” muryarshi na kerma yayi maganar,

On the other hand Uzair yace”Wata irin matsala kenan?
“Kukan jariri ne Ya tashe ni daga bacci,Bansan a ina aka samo kukan ba, kuma na tashi banga benazir ba”

“Ka kwantar da hankalin ka, Gani nan zuwa”
“Yawwa,dan Allah kayi sauri” rejecting call É—in yayi kafin Ya ajiye wayar saman bedside drawer,

Walking Slowly Ya nufi hanyar toilet ɗin Cike da fargabar abunda zai taras, cikin sanɗa yake yin tafiyar, jikinshi na kerma,a hankali ya ruƙe Handle ɗin ƙopar ya buɗeta

HaÉ—adÉ—en toilet ne Ko’ina Na Cikinshi Fari Æ™al atsaftace ba Æ™azanta, kamar ance Ya kalli Æ™asan tiles,Ba zato ba tsammani Yaga É—igon jini, Gaban shi ne Yayi wani irin mugun bugu ji kake daram! a firgice Ya É—ago da idanuwan shi yana kallon Cikin toilet É—in,Wani irin tsoro ne Ya kama shi lokacin daya hango Jikin Bathtub(kwamin wanka) jaga jaga da Jini kamar an yanka É—an akuya, a ruÉ—e ya soma ambaton Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un, kamkar a mafarki yake kallon Lamarin, Cike da fargaba ya Æ™arasa shiga cikin toilet É—in don ya gane wa idanuwanshi, a dai dai bakin kwamin wankan Ya tsara turus, Yana Kallon Jinjirin dake Acikinsa kwance,duk jini Ya wanke jikinshi Sai tsanyara kuka Yake yi,
Lokaci guda gabanshi Ya faÉ—i rass tunawa da wasu maganganu da suka tsaya mashi aranshi tun shekaran jiya

Tuni ya karaya hakan na nufin a daren Jiya ta haihu acikin toilet, saboda ƙarfin hali irin nata har ta iya haihuwa da kanta ta kuma Gudu duk da irin Jinin da ta Zubar, abun yayi mugun ɗaure mashi kai, ga wani irin ƙunci da yake Ji acan ƙasan Zuciyarshi, Tuni hawaye sun wanke fuskarshi, sam bazai juri ganin jaririn shi a cikin mawuyacin hali ba, sosai ya fashe da kuka tare da kai hannayenshi cikin bathtub ɗin Ya ɗauko Jaririn, bai damu da kayanshi su 6ace ba ahaka ya ƙanƙameshi ajikinshi yana shar6ar hawaye,

“Taj!taj!! muryar amininsa ce da alama sun shigo cikin gidan, Atare suka faÉ—o Cikin É—akin nashi a fujajen, Su Biyu ne shida Matarshi wadda ke sanye Cikin Jallabiya baÆ™a, Ta yafa mayafi akanta, farace tass doguwa,Shi kuma Uxair din, Jallabiyace ajikinshi brown color

Shigarsu keda Wuya Sai gashi Ya fito rungume da jaririn a ƙirjinshi,

AruÉ—e suke kallonshi, murya na kerma Aneelarh tace”Ta haihu ne”?
Tunkafin ta rufe baki Uzair ya kar6e da cewa”Meya ke faruwane taj?wannan Jaririn fa?Kodai ta sauka ne”?
DaÆ™yar ya iya daidaita natsuwarshi ya soma magana”Ita ce tabar mun shi, nima bansan meya faru ba, kawai naji kukan jariri, shine ma Ya tashe ni daga bacci,a toilet na sameshi cikin bathtub”
Atare suka haÉ—a baki suna salati, Kafin Aneelarh ta kar6i Jinjirin Tabi ta gefenshi ta nufi toilet don ta gyara mashi jikinshi,

Uzair kuma Yaja Hannun Taj suka fito falo, tsayawa Sukayi suna fuskantar Juna, ran kowannan su a6ace,
“Amma dai matar nan anyi Æ´ar akuya, dama can Ni bata kwantamun araina ba, In banda daÆ™iÆ™anci taya laifin ka zai shafi abunda ke cikinta”?

tun kafin yakai Æ™arshen maganar taj ya katseshi da cewa”Laifin me nayi mata Uzair!? meyasa wasu mutanan basu da tunani ne?sun É—auki duniya wurin zama,Suna manta cewa wata rana dole su koma Ga Allah, kuma zasu yi bayanin duk wani abu da suka aikata mai kyau ko mara kyau,” dakatawa ya É—anyi da yin maganar yaja numfashi kafin yaci gaba da magana,.
“Benazir Ta Æ™ona mun rai, bazan ta6a yafe mata ba, Allah ya isa tsakanina da ita,Ta nuna mun rashin imaninta Æ™arara akan Jariri na, In sha Allah Zata ga Sakayyar hakan……”kafin Uzair Ya kuma Furta wani abu, Sae ga Aneelarh Ta fito hannunta É—auke da jaririn cikin lallausan towel fari, wani irin farin Cikine akan fuskarta,tunkafin ta Æ™araso wurinsu ta soma ambaton”Tabarakallahu Ahsanul kaliqin, Tunda nake amsar haihuwa a asibitin mu ban ta6a Cin karo da kyakkyawar Jinjira ba, Irin wannan Hurul ainin dake a hannuna ba….

A sukwane Uzair da Taj suka kalli juna kafin suka mayar da idanuwansu kanta,
“Am just Speechless wlh, Ka gode ma Allah, Da Benazir bata yi tunanin kashe maka itaba, da kuwa munyi Babbar asara,”takai Æ™arshen maganar adai dai lokacin ta Æ™araso gabansu,.

Slowly Taj da Uzair suka É—aura Idanuwan su kan Jaririyar, Saboda tsabar Kyanta har Razana saida Suka É—anyi, Babu wanda yayi tsammanin ganin jaririyar haka, farko ma sun yi tunanin Namiji ne saboda hankalinsu ba’a kwance yake ba, ashe ta maca ce,

Fara ce Sol har wani shining skin ɗinta take yi saboda tsabar haske, Natural Beauty ce, Bakomai yafi jan hankalin su ba, face Ƙwayar idonta (vivi gray) mai launin ruwan Toka ash Colour, ta ciza har ƙyalli take Yi, Sumar kanta Brown Colour ce Curly mai nannaɗa, har saman goshinta wani kwantaccen gashi ne, kuma kan nata acike yake da yalwataccen gashi, ga dogon hanci Allah ya bata, ga kuma Ƙaramin baki, mai ɗauke da siraran la66a Pink colour kamar an shafa mata jan baki,

Saboda tsabar farin Ciki,taj Ya kalli gabas Yay sujjada Yana kuka Yana Gode ma Allah.

“Ka fara tsarka ke jikinka mana,”Uzair ne yayi mgnr.

Murmushi suka saki gaba É—ayansu a ya yin da suke Kallon shi,
“Ina taya mu farin Ciki sosai, Aneelarh Wannan kyautar Allah ce agaremu, Naji dadi da Benazir batayi tunanin kashe jaririyar ba,
Murmushi aneelerh ta É—anyi”Ji nake kamar nafi mahaifin Yarinyar Farin Ciki, yau Rana ce me cike da tarihi, Ranar da Taj Ya zama Uba,
Murmushi suka kuma saki atare,A lokacin Taj ya É—ago daga sujjadar, hawaye sharkaf akan fuskarshi, Bazai iya misalta irin farin cikin da yake Ciki ba,

Miƙewa Yayi tsaye Ya koma gabansu, hannu ya miƙa ma aneelerh ta bashi babyn, maƙe mashi kafaɗa tayi, tare da yi mashi nuni da idanuwanta, sai lokacin ya tuna da yadda jikinshi ya ke, duk ya 6ace da jinin babyn sa daya ɗauke ta ɗa zu, Mirmishi ya sa ki da sauri Ya kama hanya zuwa bedroom ɗin sa, within mins sai gashi ya dawo jikinshi sanye da jallabiya, ya gyara jikinshi miƙa mata hannu ya yi batare da musu ba ta miƙa mashi ƴarshi, Yasa hannu biyu ya kar6e abunshi, sosai ya ƙanƙameta, Ya tsare ta da idanuwashi yana kallonta, Sae faman mutsu mutsu take Yi, ta tura yatsanta ɗaya acikin baki sai tsotsa take Yi,

Ba komai ya fi ɗaure ma shi kai ba a game da yarinyar face kwayar idonta, kaf dangin su babu mai irin launin ƙwayar idonta, sai dai ko acikin dangin mahaifiyarta,

Cikin sanyin murya ya soma magana Yana kallonta”ke kyautace agare Ni, Inasonki Sosai, Allah ya raya mun ke bisa tafarkin addinin islama, Allah Ya bani ikon kula dake Alfarmar annabi muhammad (SAW) Allah ya tsare mun ke, Allah kuma yasa ki xama silar farin Cikinmu,” haka ya dinga Jero addu’o’i, Suna uxair suna amsa mashi Ameen ameen

*SHIN WANENE ZAHEER TAJUDDEEN?*

Tajuddeen É—an asalin Wani Æ™auye ne da ake kira Buzaye wanda ke a Æ™arÆ™ashin Æ™aramar hukuman É—anja dake a jahar katsina, Haifaffen É—an garin ne, nan ne tushen shi, anan dangin su suke,mahaifin shi da mahaifiyarshi Auran Zumunci ne, Ƴa’Æ´an wa da Æ™anine, Malam Zahiru shine sunan mahaifinshi, Mahaifiyar shi kuma Yahanasu, tun da su ka yi auren Allah bai ba su haihuwa ba, abun tun bai damun su harya fara damunsu, mutanan garin har sun fara yi masu surutu kan rashin haihuwa, haka dangin su ma, sun fara tanka masu akan Haihuwa, musamman Deeje Mahaifiyar malam zahiru, kullum mitar rashin haihuwar matarshi take yi, Ita dai burin ta a haifa mata Jikoki, sun shiga mawuyacin hali,Har shirin zuwa asibiti su ka yi don a duba lafiyar su a gano inda matsalar take, A wannan Lokacin basu da babban asibiti A yankin sai da su ka yi tafiya zuwa cikin jihar katsina, Suka sauka agidan balaraba Æ™anwar Yahanasu da ke aure anan Cikin garin, sun samu kyakkyawar tarba a wurinta,haka mijinta ma, ya yi farin Ciki da zuwansu, domin kuwa malam zahiru Abokin shi ne ta silar shi Ya haÉ—u da balaraba, Kwanan su É—aya a gidan ta, a washe garin ranar Suka je asibiti aka duba su, A Æ™arshe dai Likita ya tabbatar masu da cewa Lafiyarsu qalou Lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, Su Cigaba da addu’a kawai in dai suna da rabon haihuwa aduniya to zasu ga jininsu duk mun daren da É—ewa, kwanansu Uku a katsina suka dawo nan buzaye, Koba komai hankalin su Ya É—an kwanta,tunda an tabbatar masu da cewa basu da matsalar Haihuwa,

Bayan tsawon Lokaci Da yin aurensu, Kusan shekera ashirin da biyar kenan, A wannan Lokacin Allah Ya kawo ƙarshen koken rashin haihuwarsu, wato Yahanasu ta samu Ciki, saboda tsabar farin Ciki har ƴar ƙwarya ƙwaryar walima suka shirya aka kira masu kiɗan kwarya, Aka ci aka sha,

A kwana a tashi, yahanasu ta haifi kyakkyawan jaririnta wanda yaci sunan shi Tajuddeen sunan Mahaifin Malam Zahiru, Tun yana yaro suka ƙwallafa rai akanshi, Kowa son shi yake yi, kuma tun daga shi Allah bai ƙara basu haihuwa ba har suka tsufa, a lokacin da taj ya fara girma, kawun shi ƙanin mahaifinshi Ya kwallafa rai akan subar mashi Yaron tunda basu da hali, Yanaso ya ɗauki nauyin karatunshi, acan inda yake aiki Jihar Jos, a lokacin ƙin yadda su ka yi saboda shi kaɗai ne ɗansu wanda suke kallo suji daɗi a duniyar nan, sunfi son ko da yaushe Ya kasance atare dasu, Babu yadda Uncle ɗin nashi ya iya dole yabar masu abunsu, Amma duk da haka sai da ya taimaka masu da abunda zasu kula dashi, don kafin tafiyarshi,Sai da ya tabbatar sun sanya shi makarantar Boko da islamiyya, tukunna Ya tafi,

Tajudeen tunda ya taso Yaro ne mai hankali da natsuwa akwai na annabawa wato haÆ™uri mutun ne maison Jama’a, ga son Ibada,ga tsafta sam baida wata damuwa a rayuwarshi, ga kyautata ma iyayen shi, tun yana É—an shekara Goma shabiyar aduniya yake Æ™oÆ™arin É—aukar nauyin iyayen shi,Wasu aiyukan na mata duk ya iya su, Share share wanke wanke,wankin kayan su da guga, ÆŠebo ruwa a rijiya,Hatta girki Mafi yawan lokutta indai ba makaranta, shi yake zama ya girka masu abinci, shiyasa a kullum iyayen shi suke Æ™ara sonshi, kullum Cikin sanya mashi albarka su ke yi.

Bayan Tajudden Ya kammala Secondry school, Wannan uncle É—in nashi dake a Jos Ya Æ™ara kawo masu ziyara, Ai tunda Yayi arba da tajuddeen yaga Yadda ya sauya, ÆŠan kyakkyawan matashi, nan fa ya Æ™ara sa naci akan subar mashi yaron Ya tafi dashi Can Ya sanya shi Jami’a dama yana da É—a É—aya Tilo mai suna Uzair burin shi ya haÉ—asu Wuri É—aya su yi karatu atare, Nan ma suka Æ™i amince mashi, haka shima Tahujudeen ya kafe akan baison zuwa yafi son zama da iyayenshi,

Babu yadda Uncle ɗin bai yi dasu ba, Amma suka ƙi yadda,a karshe Ya yanke shawarar zuwa wurin mahaifiyarsu deeje,

Lokacin daya je wurinta, Sosai ya Tunzurata, Ya nuna mata irin Albarkar da zasu samu da yaron idan ya tafi dashi birni,A ƙarshe dai hada Cin hanci Yaba uwar tasu, da yake tsohuwa deeje akwai shegen son kuɗi, Shiyasa Ko tsakaninshi da malam zahiru, tafi ji da shi saboda duk in zaizo Buzaye sai ya haɗo mata sha tara na arziƙi, haka idan zai tafi ma,

Babu Yadda Yahanasu da malam zahiru suka Iya, Ba da son ran su ba, A wannan lokacin suka rabu da tajuddeen, Suna kuka yana kuka, gwanin ban tausayi duk da Uncle ɗin ya yi masu alƙawarin duk In suka samu hutun makaranta zai turo masu shi, hada mai aiki ya ajiye masu agidan wadda za ta ci gaba da kula dasu kamar yadda tajuddeen yake yi masu, hatta Ginin gidansu sai daya sabunta masu shi,

Bayan tafiyarsu Jos, Rayuwar Tajuddeen ta canza sosai, Yana samun kyakkyawar kulawa a wurin Uncle É—inshi da kuma matarshi Hajiya Adama, ga kuma aboki daya samu É—an uwan shi Uzair, wata irin shaÆ™uwace a tsakaninsu, kullum suna atare, dare da rana a tare Uncle abdallah ya sanyasu A university kuma Course É—aya suke karanta 6angaren jarida, da yake ra’ayinsu yazo É—aya, duk in lokacin hutu ya yi Sukan shirya shi da Uzair su tafi Buzaye wurin danginsu, Har hutunsu ya Æ™are tunkunna suke dawowa gida,

Bayan Wani Lokaci, Tajuddeen da Uzair Su ka kammala degree É—insu, dama kuma tunkafin Su yi graduation, kowannan su yana da budurwar shi wadda yake da burin aure, Taj dai Wata É—iyar hamshaÆ™in mai kuÉ—ice É—an siyasa Allah Ya haÉ—a shi da ita, Kyakkyawar gaske Asalinta ma half cast ce,mahaifiyarta balarabiyar Egyp ce, mahaifinta kuma Bahaushe ne gaba da baya, Sunanta Benazir Sam bata da sauÆ™in kai, maca ce mai matuÆ™ar Ji da kanta, Sam bata mu’amala Da mutun idan har mahaifin shi ba shahararren mai kuÉ—i bane kamar mahaifinta, kuma ba’a ta6a ta a zauna Lafiya, shiyasa kowa ke shakkar shiga gonarta, Æ™awarta É—aya kwallin kwal wadda Jinin su ya haÉ—u da ita, amma kuma halinsu yasha banban, Aneelerh maca ce mai sauÆ™in kai, ita kanta Æ´ar masu kuÉ—i ce amma bata É—auki duniya da zafi ba, Tana bin komai asannu, Ga tarin ilmin addini da take dashi, Dukkanninsu kowa da Course É—in da ya karanta,Ita Benazir Business administration ta karanta, Aneerlerh kuwa Medicine ta karanta, tunkafin ma ta kammala karatu mahaifinta Ya gina mata Privet hospital mallakin ta, atare su ka yi karatunsu Æ™asar germany ita da aneelerh, farkon haduwar su A cikin jirgi ne suka fara sanin juna, A lokacin zasu tafi Germany Æ™aro karatu, sun zauna a seat É—aya cikin jirgin, kasancewar aneelerh bata cika shariya ba, ko batasan mutun ba, takan gaida shi harma taja shi da fira, ita ta fara yi ma benazir magana suka fara fira sama sama, tana ta shan Æ™amshi, sai ga shi daga baya da suka isa Æ™asar germany sun kuma haduwa a University É—aya, Sunyi mamaki daganan kuma suka Æ™ulla zumunci,

Bayan sunyi degree suka dawo Nigeria, Sati É—aya da dawowar su suka shirya zuwa Shopping Mall domin yin siyayya, anan Allah ya haÉ—a su da Su tajuddeen suma ranar sunje yin siyayya, basu sha wahala ba, wurin samun amincewa daga wurinsu, In a short time soyayya mai Æ™arfi ta kullu atsakaninsu, har takaisu ga yin aure, Wannan shine farkon haÉ—uwarsu, Taj bai tashi sanin wacece Benazir ba, Sai bayan da aka shafa fatihar auransu, Aka kaita Gidanshi, ta hana abokan ango shugowa Siyen baki, dama Ko time É—in da aka kaita gidan, Family É—inta ne zalla babu Æ™awaye don bata HulÉ—a da mutane, Aneelerh ce kawai Aminiyarta da akayi masu aure rana É—aya, Sati É—aya su ka yi suna shan soyayya, Ta iya tarairayar miji da bashi hakkin shi akan lokaci, sai dai bata Iya girki ba, kuma bata iya Gyaran gida ba, dai dai da gyaran gado wannan batasan Ya zata yi shi ba, saboda tsabar sangartata da akayi, ranar da ya yi mata complain kan cewa Tayi mashi girki sai cewa tayi, ba’a halicci Hannayen ta donsu girka ma Æ™ato abinci ba, tsabar 6acin rai kamar Ya rufeta da bugu bata iya komai ba, sai danne dannen waya ko salla sai taga dama take yinta don wani lokacin Sai dare take hada sallar Azahar da isha’e da magrib duk tayi su a lokaci É—aya.Salatul fajr kuwa, Sai Æ™arfe goma na safe take Yinta, idan ya yi mata nasiha sai tace “Ae ba a Æ™abari É—aya za’a binne mu ba, mommy ta sanar dani cewa in yi sharholiya ta son raina Aljanna tamai rabo ce,”

Bawan Allah taj, da yake yana sonta, haka yaci gaba da zaman haƙuri da ita, kullum shi ne Zarya zuwa restaurant Cin abin, daga bisani ne da abun ya dameshi, ya samu Uxair Ya kwashe komai game da zamanshi da Benazir Ya sanar mashi, Ba ƙaramin tausayin shi Yaji ba, a ƙarshe Yace mashi Ya daina zuwa restaurant Cin abinci, Ya dinga zuwa gidanshi suna ci, idan ma bai iya zuwa kullum zai dinga kawo mashi,

Tun daga ranar duk in Aneelerh zata Yi girki hada Taj take haÉ—awa, daga baya kuma Aneelerh ta fara zuwa aiki, hakan yasa suka nemi Æ´ar aikin da zata dinga yi masu aikin cikin gida kada abun yayi mata yawa, koda uzair ya sanarma Mahaifiyarshi hajiya adama game da neman masu aikin da zasu dinga yi masu aiki a gidanshi dana Tajuddeen, Cikin sa’a Hajiya adama tayi ma mai aikinta Esther magana akan ta nemo masu masu aiki mutun biyu, Batare da 6ata lokaci ba, Esther ta samo masu Æ™annanta dake cikin buÆ™atar aikin yi, dama su ukune Kuma marayu, suna a Cikin buÆ™atar abunda zasu tallafi rayuwarsu dashi, Sai gashi Allah ya kawo masu aikin yi, Sunan Æ™annan nata Ana da Janet Ana itace take aiki agidan Uzair janet kuma agidan tajuddeen,

Rayuwar Janet a gidan Tajuddeen,Ta aikatu kamar jaka a wurin benazir, Gashi abu kaÉ—an saita rufeta da bugu saboda tsabar Zalunci, haka ta jure zama da ita, kodan saboda albashin da take samu mai tsoka awurin Taj, Yana ji da ita mutunne mai kirkin gaske,

Tun bayan auransu da Sati biyu dai dai da rana É—aya Taj bai ta6a jin dadin zama da benazir ba saboda baÆ™in halinta mahaifinta kanshi kuka yake da ita, duk Cikin ya’yanshi babu mai irin halinta, ga shegen yawon tsiya,da auranshi haka take fita Night club kuma ba yadda zaiyi da ita kusan kullum sai sunyi sa’insa da ita, hatta Cikinshi data É—auka, ba irin maganin da bata shaba don ta zubar dashi amma Abun ya faskara, Allah ya riga daya Æ™addara zuwanshi duniya, ita fa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata faÉ—a taji, wata irin bauÉ—aÉ—É—iyar macace, mai wuyar sha’ani hatta Aneelerh ta sha yi mata nasiha akan tagyara rayuwarta a karshe ma saita yaki ce aneelerh daga rayuwarta, ta É—auki gaba da ita ko magana bata haÉ—a su, lokacin da Cikinta ya soma Girma kamar tayi hauka saboda ba ta san Ganin shi ajikinta, kamar ta sanya hannu ta danna shi ya baje haka take ji, Taj yasha kamata tana kokarin shan maganin don ta zubar dashi,Wanda hakan yayi silar da har su ka yi faÉ—a da ita kaca kaca, kuma Tace mashi koda ta haihu kada yayi tunanin zata shayar mashi da abunda ke acikinta, ashe dama jira take ta haihu tabar gidan, Shine ta tafi tabar mashi jaririya cikin kwamin wanka, dama kuma tunkafin tafiyarta, Ta kori mai aikin gidansu Janet, Batare da saninshi ba wannan kenan………

 

Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 2"