Breaking News

Kurkukun Kaddara 5

A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure


rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,

A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara,

Tun tana da shekara Uku Ya sanyata nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu ƴa’ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control ɗinta ba, ga shi ya hana a dukar mashi ƴa ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi.

Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa’ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita,

Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa,

Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta.

Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan.

Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,

Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha.

Da gudu suka nufe ta gaba ɗaya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya,

Abunda Ya faru a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji,

Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa’aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faɗa idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka.

duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur’ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiɗaniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu’a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou

Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa,

Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,

Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali,

Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,

Saboda bala’in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,

Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,

Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,

Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi “Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,”

Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace”Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata” Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje”Kije ki nemi wani uban”

Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama’a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin “Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa”Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa’yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba

Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.

Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,

A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya’yan mutane,

A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,

Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.

Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,

Ba’a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.

Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin “Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin,”
Copral ne Ya bata amsa da cewa”Ana zargin su da sace Ƴa’ƴan mutane suna amfani da su”
Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace
“Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba…..”bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta”Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu,”
Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta”where’s the evidence”?

Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi

A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,

Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci,” yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,

Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami”You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce,” muryarta a disashe takai ƙarshen maganar,

“Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi,” acewar dpo,

Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel,
“Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne,”
Da buɗe bakin angel sai cewa”Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae”

Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa”You are under arrest” ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa
Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa”Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani.
Girgiza kai Dpo yayi”Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne”
Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution”
Jinjina kai dpo “Good idea Copral”Dpo ne ya kira sunan shi
“Yes sir” ya amsa mashi.
“Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku,”
“Consider it done sir” Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,

A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,

Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,

Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,

Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,

Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou ”

Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media,

Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi Wani sa’in yana ɗangya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta,

In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar dashi, dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair ɗin,

Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko’ina Yana gida, Wuraren ƙarfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baƙi, saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miƙe daga saman gadon ya nufi ƙopar ɗakin, Leƙawa yayi don yaga su wanene

Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa
“Allah ya jiƙan shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi,”
Can kuma yaji wani yace”A ina ne za’ayi jana’izar ta shi”?
Wani ya ba shi amsa da cewa”Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji,”
Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi”? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair.

Komawa Cikin ɗakin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya ɗauka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi ɗari uku na mutune, abun ya ɗaure mashi kai,

Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya ɗaga,
“Assalamu alaikum” batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa”Uzair kana ina ne”?
On the other hand Uzair yace”Gida mana”
Cike da damuwa yace”Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi ɗari uku na mutane wai meke faruwa ne”?

Muryar uzair da ɗan ruɗi yace”Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buɗe ta “tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call ɗin, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook, a ƙasa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don a yi jana’ixa da su.

jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na,

sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta’aziyar shi, daga ƙasan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma’anar hakan, Shine tayi mashi aika aika.

Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya ɗaga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki

A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine,
“Yanzu menene mafita”? taj ne ya yi maganar yana kallonsu,
“Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi,” acewar Uxair,
“Benazir ta tafi tabarmun bala’e” tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,.
“Me zai hana ka jaraba Bugunta”? a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar,
Cigaba da magana tayi”Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin ƙananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani”? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar,
Jinjina kai Uxair yayi”Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su ɗauko mun ƙadangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu,”
“Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki” acewar Taj,

Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan,

Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani,
A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata, magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba,

Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi,

Tunkafin ta ƙaraso Take nuna mashi gate ya buɗe mata, Sanin Tsiwarta yasa Ya buɗe mata ƙopar jikin gate ɗin ta fuce, Sai gidansu Aneerlerh lokacin da ta shiga Gidan, A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah, Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kuɗunɗu ne, Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,t ana daga zaune saman darduma ta kalleta”Angel Lafiyar ki kuwa”

Kasa ƙasa da murya tace”Zazza6i nake yi”

“kin sha magani”

“Eh nasha, daddy ne yace inzo wurin ki kiyi mun wanka,i n ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni”

Mikewa aneerlah tayi, bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe,

“Tashi muje nayi maki wankan”

Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon, rigar jikinta duk ta cukuikuye, hada manjan daya gogu agaban rigar,
“A haka kika hau mun gadona? Ina kika samu manja ajikinki”
Ashagwa6e tace” nace maki bana lafiya, Ni bana iya magana sosai”
Sam aneelerh ba ta yarda da ita ba ta ƙyale ta ne kawai,

Within minutes ta yo mata wankan, suka fito daga cikin toilet, ta shafe ma ta jikinta da mai, canza mata kaya tayi, dama Saboda Ita ta sayi kayan Yara dai dai Size dinta, saboda sun ɗauke ta tamkar ɗiyarsu, pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba, hada light make up aneelerh tayi mata,

“Aunty aneelerh,Z an koma saman gadon in kwanta, dan Allah ki hadamun fura, A sanya kwakwa da yogurt aciki da ƙanƙara”

Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace”Okey My daughter in law, je ki kwanta,”da gudu taje ta haye saman gadon,

Bayan Aneerlerh ta hado mata furar a cikin Cup ta kawo mata Nan ta zauna tasha ta ƙoshi, kafin ta koma ta kwanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,

A 6angaren Taj kuwa, Lokacin daya tashi toilet ya shiga, ya dauro alwala ya dawo Cikin ɗakin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet din shi Ya zura ajikinshi, Fitowa ya yi daga ɗakin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci,

Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba, Sai daya Dawo daga masallaci, wata irin yunwa ta farmasa, ba arxiƙi Ya nufi kitchen shigar shi keda Wuya Tun abakin ƙopar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro, A razane ya dago yana kallon cikin kitchen ɗin, har wani haya ki yake ganin cikin idon shi saboda tsabar 6acin rai, ashe bai ga komai ba sai daya Shiga Cikin store, Hannu ya ɗaura akai yana ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Nashiga Uku! Na bani!

Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel? wani zunubi na aikata, dafe baki yayi da sauri jin sabon da ya yi yana mai fadin astagfurullah…..” yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage, Aikuwa a harzuƙe ya juya ya kalli magen dake a bakin kopar store ɗin, Shaƙo wuyanta yayi tare da jijjigata Yace”Ke da ubanwa ku ka yi wannan”?
Ƙura mashi ido magen tayi tana Cigaba da yin kukan Yunwar da take yi, wurgi yayi da ita, tare da naɗe hannun rigar shi Ya fuce daga gidan, kaitsaye Ya shiga Gidan Uxair, tun a bakin gate mai gadin Gidan Ya soma tambayar shi”Yalla6ai Lafiya”

Baiko tanka mashi ba Idonshi Ya rufe, Angel kawai Yake nema Ko sallama bai tsaya Yi ba Ya faɗa Cikin Falon Gidan, Ganin bakowa Yasa shi fara kwala mata Kira”Angel!Angel!Angel!!’ tamkar makoshin shi zai 6allo,

Da gudun gaske Aneelerh ta fito daga bedroom ɗinta Jin muryar Taj Cikin tashin hankali,

“Me ya faru ne”?tayi tambayar tana kallon shi,
“Where is Angel”?
“Ɗazu ta shigo bata Jin dadin jikinta, yanzu haka bacci take yi adakin”bata kai ƙarshen maganar ta ba, Ya wuce ta a fusace Ya faɗa dakin, Can ya hangota saman gado a kudundune tana ta sharar bacci,”

Hannu biyu yasa ya Cakumeta, da sauri aneerlerh ta biyo bayan shi Tana tambayar shi Meya faru ne,

Da budar bakinshi sai cewa yayi”kashe ta zanyi,”

Yana faɗin hakan ya nufi hanyar fita da ita, gida Ya koma da ita a dakin su Ya jefar da ita saman gado, sai lokacin ta farka tana kallon shi da manyan idanuwanta,

“Daddy what”?

“Zaki Ci ubanki ne” ya faɗi hakan tare da Janyo pillow Ya hau saman gadon Ya turmushi fuskarta dashi, Mutsu mutsu ta shiga yi, tana kokawar fitar da numfashinta, sae faman harba ƙafafunta take Yi, tana neman Ceto,Amma Taj sam Babu alamar zai sarara Mata, Saboda Baya acikin Hayyacinshi Dagasken kasheta Zai yi,

Faɗowa ɗakin aneelerh tayi ko takalma babu a ƙafafuwanta, Anan ta same shi Saman Gadon Ya danne angel Da pillow, A gigice ta fasa ƙara, Tare da yin kukan kura Ta haye saman Gadon, Da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta cakumi wuyan jallabiyar jikin Taj tare da Yin Wurgi dashi gefe guda Ya faɗa saman mattress din,

Cikin shessheƙar kuka take fadin”Taj ban sanka da haka ba, meyasa zaka yanke hukunci Cikin fushi ne? Meye ribar ka idan ka kashe Angel?yarinyar da ba ta wuci 7years ba, idan ka yi hakuri Wata rana zata daina ne,

“Wlh bazan ƙyaleta ba Kafin ta kashe ni, Ni zan fara kashe ta,” ya ambaci hakan tare da yunƙurawa Ya miƙe Yana ƙoƙarin Cakumar Wuyan angel da ta sume, da sauri Aneelerh Ta sanya hannu ta ɗauketa, tana ƙokarin sauko wa da ita daga saman gadon, A ƙokarin Ya damƙo angel Ya janyo wuyan rigar Aneelerh gaba ɗaya aneelerh tayi baya ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi, Angel kuma ta yi gefe ɗaya saman gadon,

Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba, shi kan shi bai yi tsammani hakan zata faru ba, saboda ba ita yayi niyar Janyo ba, Angel da ke a hannunta Yaso Ya damƙo, hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta, wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowan nan su, ƙoƙarin miƙewa aneelerh ta yi sai dai ina wani magnet ne ya ruketa, Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a’uzubillahi minasshaiɗanirrajim, tun da ta ambaci hakan sai ga shi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj, aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon, ko mayafin ta bata tsaya ɗauka ba ta watsa da gudu tabar ɗakin,
A hankali taj ya lumshe idanuwan shi, ya yin da hancin shi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi, bakomai Ya tuna ba face Matarshi da ta gudu tabar shi, maca ce mai matuƙar son ƙamshi, shima kuma ma’abocinsa ne, baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi, da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan ƙamshin turaren ta,

Ganin Zuciyar shi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirrajim, Astagfurullah Ya Allah,

Miƙe wa Ya yi zaune Duk kasala Ta rufe shi, saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour, babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu, frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi ya dawo bedroom din shi, daga gefen gadon Ya zauna, buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta, nan take Taja dogon numshi,

Slowly ta buɗe idanuwanta akan fuskar shi, Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka,

Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukan nata ba, tun da ya lura Ba son shi take Yi ba,

Cikin shessheƙar kuka tace “You want to kill me because you don’t love me, yanzu da na mutu Allah zai kamani, so kake in shiga wuta ko? ta yi tambayar tana kallonshi, har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba,
“Kana Jina ka share ni ko”

Gyaran murya ya ɗanyi can kasan makoshin shi ya furta”Dama kina tsoran Mutuwa”!
A tsiwace tace “Eh mana,malamin mu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba, A wuta za’a babbaka shi……”

Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa”So you know that but u keep hurting me ko”?

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan, Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi, cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwan su ke kallon Cikin na Juna,

“Angel, zan sanar dake wani abun da baki sani ba ba ki da wanda yafi ni a duniyar nan, ba ki ta6a tambayata mahaifiyarki ba, Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne, Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki, Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifin ki,” shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu, ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi,

Cigaba da magana yayi”Angel, mahaifiyarki a wulakance ta haife ki, Cikin bathtub tabar min ke, Cikin Jini kina ta kuka, Ni ina bacci kukan ki ne Ya tashe ni haka naje na sameki, Na ɗauke ki na rungume ki ajikina, duk da jinin da ke ajikin ki, Ni ban gudu nabar ki ba, kuma ban bari kin wulaƙanta ba, Sai da na tsaya akan ki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin, Tun da ki ke ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba, kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba amma angel……”kasa ƙarasa maganar Ya yi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita, ɗagowa Ya yi zaune yana kallonta.

Hannu ta ɗaura akai tana faɗin “Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!” hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,njin yadda babyn shi take Kuka,

Lallashinta ya soma ƙokarin”Am really sorry daughter, I don’t mean to hurt u darling, Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci, don ki san cewa Ina sonki, kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki,” bata tsaya sauraronshi ba, Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,

A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta,

Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta”My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki”

Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin”I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona……”
Runtse idanuwan shi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗinshi Calmly ya kira sunanta”Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki,
Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan
“Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata”
Shiru bata tanka mashi ba,
“Ki buɗa mun ƙopar”
Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa”daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai”
Cikin matsananciyar damuwa Yace”idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,”

Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta

“I made a mistake daddy, I won’t hurt you anymore,”

Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,
“I love u daddy” ya kuma Jin ta furta mashi aruɗe yace”Repeat it pls”
“I love u daddy”
“sake maimaita mun naji”fuskar shi ɗauke da murmushi Ya yi maganar,
Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi,

“I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan”
Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su,

A ƙagare Yace”Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina”

Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,’ dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba,
daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha’awar kallon Cartoon da kuma zombie,

Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaɗar shi ya ɗauke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar ɗakin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin”I luv u daddy” murmushi ya ɗan saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta
“Luv u too My own daughter”

Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya ɗauka,
“Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka”
“Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah”
“Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka, Ae ni har na yi shirin zuwa ɗaukar rahoto”
Fashewa Taj yayi da dariya”Ta
6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,”
“Yanzu Ina virus ɗin taka take”?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus,
Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki,”
Uzair yace”Meya faru”?
Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi,”
Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,
“Ja’irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki,

“Ameen mutumina”
Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa,
“Muyi video call mana”acewar uzair,
Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci,
“Show me her face” murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci,
Dariya uzair yayi”waya ga mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu,”
Fuskar Uzair ɗauke da murmu shi yace”cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa”
Jinjina kai Uzair Yayi tare da ɗan yatsina fuska yace”Virus ɗin”?
Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta,

Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,

“Me kake tunani ne”? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace”Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu,” da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama,

Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi,

Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su.

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki, dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa’azi, jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,

a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,
“Wake up My lovely daughter” Cikin kunne yayi mata raɗa,
Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji,
“Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina

Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth ɗinta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su,

Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta,

A saman mirror chair ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?

ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,

“Daddy ni da kai wa ya fi kyau” ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi
Dungurin kanta yayi”Kinfi kowa sani ae” ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari,

bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado”Am coming now” ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,
Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,.
Harara ya ɗan jefa mata”Zansa kaya”
ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba,
Gyaran murya yayi mata”Can’t u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya”.
Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace”Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya’

Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,

“Angel don’t waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo,”
Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit, Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon,

Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita,

Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana,

Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel”Ƴan mata makaranta za’a tafi”?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh”
“Allah ya bada sa’a Angelata”maƙe mashi kafaɗa ta yi”Ni ta daddy ce”dariya su ka yi gaba ɗayansu,

Taj yace”Bari mu wuce kada mu makara” baba maigadi yace “Allah ya tsare adawo lpy” ya amsa ma shi da ameen kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buɗe ya zauna a driver seat,

A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan,

A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta,
“Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa”
“Ba bacci nake ba,Ina tunani ne”
“Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku”
Murmushi ya ɗan saki”Karatun naki fa”?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,
Shiru bata amsa mashi ba,
“Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake”?

“Inaso” ta amshi amsa a takaice,
“To faɗamun me kikeso ki zama”?
Da buɗar bakin ta sai cewa tayi”house wife” ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar,
“Daddy why are u laughing? did i say something wrong”?
Girgiza kai yayi”a’a,May be u did’nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,

Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata murfin motar “baki amsa mun tambayata ba”?
Ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi
“Daddy my answer is the same, I wanna be a house wife” Sakin baki yayi galala yana kallonta, Ya rasa taya ya akai tafara tunanin zama house wife, dududu fa primary school ta ke,
Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba, Ɗauko mata food basket ɗinta ya yi kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar, kamar kullum har Cikin class ɗin su Ya kai ta, English teacher ɗinsu ya taras a jin Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa da shi, ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motar shi, Zuciyar shi a cunkushe duk ya rasa sukuni, tunani ya shiga yi taya za’ae ya canza mata ra’ayinta na zama matar aure? don wannan ba ƙaramar matsala bace agare shi, ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure,

Karasa shige wa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key, Ya nufi gate ɗin makarantar mai gadi ya buɗe mashi ya fuce,

Harya haura saman titi, Hankalin shi na akan Kalaman angel, shi da yake da burin ta zama babbar ma’aikaciyar gomnati, ashe ita sam Ba wannan bane agaban ta, A ƙarshe dai ya yanke shawarar idan ya ta shi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida, Zai zaunar da ita ya yi mata karatun ta natsu, Ko ya samu ya canza mata ra’ayinta,

Wuraren ƙarfe biyu na rana, Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam’i, tukunna Ya nufi school ɗinsu, Lokacin daya karasa makarantar, tunkafin ya fito daga cikin motar, maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa,

Ba ƙaramin daɗi yaji ba, kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba, yaci gaba da da driving, har ya ƙarasa Gida Tun a bakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel, Yace mashi a’a, hakan na nufin tana a gidan su,

Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan, Bedroom ɗinsa ya shiga, Shaf shaf Ya rage kayan Jikin shi Ya fada toilet don ya yi wanka, ko yaji daɗin jikin shi,

Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan, ɗauke da angel da alama ta yi bacci, lokacin da ta shigo falo tana ta kwala sallama ba’a amsa mata ba, kawai sai ranta ya bata cewar ko bai kaiga dawowa gidan bane, don bata lura da motar shi da ke ajiye ba, hakan yasa ta nufi bedroom ɗin shi kai tsaye, ta tura ƙopar kafin tasa kai Cikin ɗakin, Asaman gadon shi ta kwantar da angel, short gown ce ajikinta daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta ɗanyi daga tsaye tana shafa sumar kanta,

Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short a jikin shi,

Burki yaci lokacin da yayi arba da ita, duk tabi ta ruɗe a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin, Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota, ta dawo jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya, taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa za ta yi ba.

Sam ta manta Jikin wa take, ta ƙaƙameshi sosai, har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta, ta yi saurin raba jikinta daga na shi, duk kunya ta rufe kowannan su,

Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana
“Sai ka ce kin ga dodo, kawai daga gani na kin zabura zaki gudu, yanzu da kinji ciwo fa? so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko”?
Murmushi ta ɗan saki ba tare da ta ce uffan ba, idanuwanta na akan yatsun hannunta,
“Thank u so much aneelerh, kina ɗawainiya da angel ɗina, tamkar mahaifiyarta, naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin naki sai dai kash ni ban yi sa’ar mata ba,”
Juyawa ta ɗanyi jiki a sanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar, A tsanake ta soma magana,
“Zan ta ya ka addu’a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini” tana kai ƙarshen maganarta, da sauri ta fuce daga ɗakin,

Murmushi taj ya ɗan saki, tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi, juyawa ya yi tare da koma wa gaban mirror, lokaci guda kasala ta baibaye shi, ƙamshin turaren aneelerh ne, Ya cika mashi hancin shi, ita koda yaushe Cikin ƙamshi take, Zama ya yi a saman chair din gaban mirror, Ya kura ido yana kallon fuskar shi ta cikin mirror,

A 6angaren aneelerh kuwa, Da sauri ta fuce daga Cikin gidan, Tana shiga falon gidanta, A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu, tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin da ta ci karo da taj,

A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans ya feshe jikinsa da turare mai kamshi,

Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba, Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba,

Wayarshi ce ta soma ringing, da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer,

Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai, murmu shi ya ɗan saki tare da yin picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi”Assalamu alaikum, ɗan uwana rabin raina”
On the other hand Uzair yace”Ka koma gida lafiya”?
“Lafiya lou, Yanzu na fito daga wanka ma”
“Ka ci abinci”?
Dariya taj yayi sosai, jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro,
“Meyasa ka ke mun dariya? yau nafara tambayarka hakan”?
Tamkar yana agaban shi Ya girgiza kanshi”Nop, just naji abun wani irine, kana tunamun rayuwar mu agidan Uncle”
Muryar shi ya jiyo da sautin murmushi “Unforgettable momeries, Allah Yabar ƙauna aminina, Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima”

Taj yace”Okey, take care of ur self for me pls”
Uzair yace”U too” fuskarshi ɗauke da murmushi ya yi rejecting call ɗin,

Yana ajiya wayar saman drawer, Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo, Yana kwala sallama,

A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, Yayin da yake amsa mashi sallamar”Wa’alaikum Salam”

Cikin falon Ya nufa, A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye, ƙarasawa Ya yi yana kallon shi,
“Barka yalla6ai”ya amsa mashi da “yawwa barka”
“Dama baƙo ne ka yi”
Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace”baƙo kuma”? yayi tambayar ne don shi a iya sanin shi, ba su yi da kowa zai zo gidansa ba,

“yalla6ai, Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yi ma angel ruƙiya?’ cike da son fahimtar da shi baba maigadi ya yi maganar,
“Kana nufin maisalati”?
Da sauri baba mai gadi yace”kwarai kuwa shi ne”
“Okey, Ka ce ma shi ya shigo”
“To yalla6ai,” Yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar falon,

Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Ya ji sallamar shi, Fuskar nan dauke da murmushi, Jikin shi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai idon ƙafar shi ba, Hannunshi na ruke da cazbaha Kanshi yasha uban rawani, Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,

Sakar ma shi fuska taj ya yi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa
“Allah ya gafarta malam, barka da rana Ya iyali ya jama’a ya ƙoƙari, Allah yataimaka, Allah Ya kara ɗaukaka”
“Ameen ameen tajo, Fatan na sameka lafiya ya aiki, ya kuma ɗiyar mu”

Taj yace”Alhamdulillah, Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki,” ya ruƙo hannunshi, suka nufi sofa ɗin falon, maisalati ya zauna asaman 2 seater, Sae faman sakin murmushi yake yi, Dama shi haka yake kullum fuskar nan a washe, Da wuya kaga bakin shi a ƙulle.

“Bari na kawo maka ruwa” da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi”samu wuri ka zauna tajo, Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni,”

Tunda Taj yaji hakan, Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalin shi a kan maisalati yana sauraron shi’

“Game da ƴarka injila” da sauri taj yace”Angel sunan ya ke”
“Oh toh, eh ita ɗin dai” shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi ma shi jawabi.
Taj kuwa ya tsare shi da ido, Jikin shi har tsuma yake yi, don a ƙagare ya ke ya ji me angel ɗin ta yi,

Gyaran murya malam maisalati Ya yi kafin ya soma magana a tsanake,
“ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya, nayi wani laifi laifin kuwa shine bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyar ka ba, bama hasashe bane inanda tabbaci kan shi,”
Tunda taj yaji hakan,nGabannshi ya faɗi rass aruɗe yace”malam wani abu kenan”?
Numfashi ya ɗanja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan
“Akwai abunda na gani a tattare da yar wurin ka, A lokacin da nake yi mata ruƙiya, Sai dai tsoro da firgici ya hana in faɗa maka, gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina na kasa tantance sihiri ne a jikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani a jikinta babbar al’amari,
Tuni jikin taj ya soma kakarwa, muryar shi na kerma yace”Malam dan Allah ka yi mun bayani, hankalina a tashe Yake wlh”

Cigaba da magana malamin ya yi”Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba, Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta …….”,

Muryarshi na ɗan rawa yace”am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta ƙalau, yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci a tsakanina da ita, Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba”

Murmushi maisalati ya yi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi, jinjina kai yayi tare da cewa”Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambaye ta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa? kuma bata ƴan gane gane haka”?

Shiru taj ya ɗanyi, Shi kaɗai yasan halin da zuciyar shi ta ke aciki, duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancen shi ya zama gaskiya,” girgiza kai yayi alamar aah, gyara zama ya yi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru da ita ta hakane xamu samo bakin zaren”
“Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta,”

Maisalati yace”Yawwa ko kaifa, Sannan kuma shawarar da nake so na baka, Ka tabbatar kana Yi mata addu’o’i akai akai, idan bata iya ba ka koya mata, hada azhkar na safe dana marece, ka kuma koya mata addu’ar shiga toilet, idan zata kwanta da dare ka yi mata addu’oi’in neman tsari, kuma a koda yaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali, ka lullu6e mata gashin kanta, Hatta kaya idan zaka sanya mata ka yi mata addu’o’a, Daso samu ne ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al’qur’ani mai girma ku kwana da shi,” sosai malam maisalati ya ba shi shawarwari a ƙarshe yace”Idan Allah yasa ƙarshen wahalar ta kenan sai kaga Allah ya yaye mata, Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu’a akoda yaushe, na manta ma ban tambayeka ba, Tana zuwa islamiyya”?

Dakyar ya iya buɗe baki yace”Eh amma ta jima ba ta je ba,

Girgiza kai maisalati yayi”Banso haka ba tajo, kanaso ka yi mana buƙulin samun Hafizar al’qur’ani, wadda zata yiwa addini hidima nan gaba, kamar yadda nake fata, Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla, ga hali kamar na manyan mutane, bai kamata kayi wasa da wannan damar ba, Gaskiya ina mai baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta, idan da hali harma tahfeez ka sanyata,”

Ajiyar zuciya taj ya dan sauke”in sha Allah zanyi hakan, Nagode sosai malam, Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka, Allah ne kaɗai zai iya biyanka, Allah dai yasa ka maku da alkhairi,” sosai taj ya yi ma shi godiya, Koda ya miƙe zai tafi saibda taj ya ƙara tambayar shi ya kawo mashi ruwan sha,
Yace a’a, Shi dai burin shi ya yi ƙokari wurin ceto rayuwar ƴar shi, Shi ma kuma zai taimaka mata da addu’o’i shida ɗalibansa,daga haka su ka yi sallama dashi Yabar gidan,

Tofa, Bayan tafiyar malam maisalati, kasa zama taj ya yi saboda ruɗanin da zuciyar shi ta shiga, Zarya ya shiga yi a falon, Zuciyarnshi a cunku she take, wani irin faduwar gaba yake ji, tabbas yanyi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali ya yi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin”

A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinnshi, tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon)

Ƙura mata ido ya yi yana kallonta, ganin ta lumshe i danuwanta, tamkar mai tunanin wani abu,

Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantar ta,

“My daugher” da buɗar bakin ta sai cewa tayi”Daddy, Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini ko” idanuwan ta a rufe ta yi maganar,

Da mamaki akan fuskarshi yace”Taya akai kikasan yazo ke da kinke acikin ɗaki”?

Bude idanuwanta ta yi a hankali,

“Tun dazu nafarka daddy, har leƙa ku nayi,”

“Kinji me muka tattauna dashi” girgiza kai tayi”ae ka hanani yi maka la6e, shiyasa ban tsaya ba, nadawo na zauna”

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa”aunty aneelerh ce ta kawoni gida”? ɗaga mata kai ya yi alamar eh,
“ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina”?ta kuma jefa mashi tambaya,
“A’a,zanje na kar6o maki su anjima”

Jinjina mashi kai kawai tayi,

Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin na shi,
“My daughter”!
Ware ma shi manyan idanuwanta tayi”na’am daddy”

Murmushi ya ɗanbsaki, ya rasa ta ina zai taro zancen, kamar maijin tsoron ta,

Can dai ya daure Ya soma yi mata magana antsanake”Nasan kina sona sosai,bkuma kina kyautatamun, koba haka ba?

Da sauri tace”Hakane daddy”

Jinjina kai yayi”um..Yanzu kina sona,nba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddyn ki ba ne, Pls inaso na tambaye ki, a wannan lokacin ke ki ke ƙuntata mun da kan ki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanya ki kina yi mun”?

Cikin rashin fahimta tace”daddy i don’t understand me ka ke nufi”?

“Ina nufin, A time ɗin da kike 6ata mun rai, Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason, babu yadda za’ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya,”

Wurga eye balls ɗinta sama ta yi tana kallon ceilling, ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi, wai ko zaiga abunda take gani,

Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Pls explain to me kin ji babyna”

Mayar da idanuwanta kan shi ta yi taɗan turo baki irin na shagwa6a66u,

“Nidai bansani ba, Amma bani nake yi ba, kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi” takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido,

“Magana a ke yi maki acikin kan ki ko kuwa”? ya kuma tambayarta,

“Daddy nifa bana ganewa”

“Angel kina mafarki”? ya kuma tambayarta, bubbuga hannuwanta ta yi saman Mattress ɗin”Wlh daddy ni ka yi disturbing ɗina, kana rikita ni”

Lallashinta ya shiga yi”Am sorry, wannan ce tambaya ta karshe, idan ki ka bani amsa, Zan ba ki wayata, kiyi game,” yasanta mayyar wayace, aikuwa da sauri ta soma kora ma shi jawabi
“Daddy, ko yanzu dana kwanta,na yi mafarki kuma kullum ina yin mafarki,”

“Faɗamun meke faruwa acikin mafarkin”?a ƙagare ya yi maganar,

Angel tace”Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro, kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya, Bana iya ganin fuskar su, hannunsu zako zako da akaifa, Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya, riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara, Kuma suma red uniform ne a jikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin Kuma babu alkairi a cikinsa”

Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi, tamkar zata faso daga kirjinshi,

“Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki ta6a sanar mun ba”?

“Banaso na tayar maka da hankaline, Aunty aneelerh tace in dinga faranta maka rai, kada na 6ata maka rai, Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka, sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta” fashewa tayi da matsanancin kuka,

Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta, baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskar shi ba, yana jin kukanta har cikin zuciyarsa

“In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na ceci rayuwarki, Bi’iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne, Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake, akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya, Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani, Kuma zai bayyanar mun dashi ne, duk mun daren daɗewa”!

Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya a wurin aikin shi, masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu, kuma har akan idon shi suna nuna mashi ƙiyayya, shiyasa ya yi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage, shine a kayi amfani da ita wurin cutar dashi,

Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita, sai da aka fara kire kirayen sallar la’asar, tukunna Ya ɗago da ita daga Jikin shi, Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata, firgit ta farka”time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah, kinji ko’?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa”Addu’ar shiga toilet kin iya”?ɗaga mashi kai tayi”Eh”yace to karantamun, nan ta shiga karanto mashi, ya kuma tambayarta addu’ar kafin a kwanta bacci da kuma in an ta shi daga bacci duk ta karanto mashi Yace”masha Allah, haka nake son ji My daughter, Sannan kuma zan koya maki azhkar da zaki dinga yi na safe dana marece, pls ki bani haɗin kai, ki dage kin ji indai bakyaso a rabani dake”da sauri tace” zanyi daddy,”yace that’s good, yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki”

Amsa mashi tayi”toh” da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, harta kusa shiga ya dakatar da ita”wait” ta tsaya tare da waiwayowa tana kallon shi, saukowa daga saman gadon ya yi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu, buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi, asaman gadon ya ajiye mata hijabin shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi a kanta, sosai ya lullu6e mata gashinta”yawwa daga yanzu haka nake so gashin kanki ya kasance a lullu6e, sannan kuma idan kin kammala sallah, ki dinga karanta surorin da nake koya maki” amsa mashi tayi”toh”kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki,”

Tsayawa ya yi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet, lokacin daya fito salla ya same ta tana yi, baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ran shi,

Da sauri ya fuce zuwa masallaci, a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki, dama biyo ma shi yayi don su tafi masallaci atare,

Bayan tafiyarshi, Angel ta kammala sallah ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irin su falaki da nasi, su ta yi ta biyawa, duk don saboda yace tadinga yi indai bataso a rabasu, Tana cikin yin ƙira’ar, Wayar shi daya manta saman gadon su ta soma ringing,

Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauke ta, Sunan Uncle ne Ya bayyana, Kafin ta ɗaga kiran ya katse, ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata, dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayar shi, Zama saman gadon ta yi ta dinga buga game na spider man,

Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba’a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba’a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran,

Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba’ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta”who is on the line”?

Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace”Angel ce,”

Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta”kinsan dawa kike magana”?

Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace”a’a,”

“Ur age”? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama,

“7yrs” voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita”7yrs? ina mai wayar yake’?

“Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya”

“Can i call u video”?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen ɗin sai duhu sosai, Amma shi wanda take wayar dashi da alama yana kallonta,

“I can’t see u” ta yi maganar tana faman gwale ido,

Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta,

A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,

Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,

“Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,”acewar uzair,
Jinjina kai Taj ya yi”Yanzu menene mafita”?
Uzair yace”Mu tayata da addu’a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za’a dace ne,”

Taj yace”Allah Ya yarda, duk na damu wlh,”

Uzair yace”ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi,

Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida,

Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko’ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za’ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta,

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall,

Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba.

A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama’a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai,

A washe garin ranar ya kasance Juma’a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani’an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu

Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma,

jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a ɗaya daga Cikin ɗakunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall ɗinne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu’a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiɗa, ko ƴan zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta,

Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi,

har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari,

a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba’a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi,

sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya ɗauke mata hankalinta daga yin karatu,

Acikin waɗannan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su ɗunguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi,

Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko’ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo

Wannan kenan,

a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan,

Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba’a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon,

Motsa lips ɗinsa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon

No comments