Breaking News

Kurkukun Kaddara 63

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*

*Dedicated to Aunty kubra❤*

*Gargarɗi!!!*


_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E63 free pages

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

 

Ya jima tsaye jikin tagar ba tare daya motsa ba, zuciyarshi na raya mashi akan ya koma ya taimake ta, sai dai tsoro ya hana shi yin hakan, Ajiyar zuciya ya sauke tare nufar cikin toilet ɗin, wankan ma da ya shigo da niyar yi ya fasa, ƙopa kawai ya buɗe ya fito ya shiga ɗakin su.

A zazzaune ya same su saman gadajen su, angel ce kaɗai kwance saman nata gadon da alama bacci ya ɗauke ta, tunda Gabriel ya shigo idanuwanshi na akan kowannan su, damuwace danƙare akan fuskokinsu, In ka cire mutun uku, Majnun da jamima da ke ta yin rawa tsakiyar ɗakin su, yau ta biye mishi suna wasa a tare, duk da a shekaru Majnun ya girmi Jamimah.

bayan su sai Sarah dake yanke akaifar hannunta da nail cutter ɗinsu, tana zaune saman shimfidarta dake a ƙasan gado, don ita tuni ta yafe hawa gado, komai nata a ƙasa take zama ta yi shi, Hankalin ta kwance babu damuwa akan fuskarta, Danish yana daga kishingiɗe saman bed ɗinsa, ya ɗan lumshe eyes ɗinta, sam babu walwala akan fuskar shi, Azeeza tana zaune saman gadon parveen, ta ɗaura kanta saman shoulder dinta, magana su ke yi ƙasa ƙasa a takaninsu, haris da deeja suna fuskantar juna, sun nutsa cikin tattaunarsu duk dai akan Batul ne, idan muka koma 6angaren su Hanna ita da hibba da Yasmin da eve da rubina kowaccensu na kwance saman gadonta, sun yi likimo kamar masu yin bacci, Zuciya ce ba daɗi, dole jiki yai sanyi, yar gida daddy kuwa bacci ta ke yi sai dai ga dukkan alamu babu lafiya ajikinta, kamar zata faɗo daga saman gadonta, a cikin bacci take murza cikinta da hannunta na dama, idanuwanta sun kumbura, ga sahun marin da Danish yai mata gefen fuskarta kamar jini ya kwanta.

Zuciyarshi a hautsine Ya ƙarasa gefen gadon shi ya zauna, Ya rasa wa zai tunkara game da zancen haura war shi taga, so yake ya sami wanda zai faɗa mawa, ko don su je su ɗauko yarinyar nan da ya gani, tabbas yana ji aranshi cewa mutun ce ita ba Aljana ba, shiyasa abun ya tsaya masa aranshi, gani yake kamar bai kyauta mata ba, yanzu da ace sister ɗin shi ce, acikin wannan mawuyacin halin bazai ta6a ƙyale ta ba, duk runtsi duk wuya sai ya taimake ta, but why ya gaza taimakon ita wannan yarinyar, girgiza kai ya ɗanyi kamar wanda aka zunguri bayanshi ya miƙe Ya cigaba da yin zarya cikin ɗakin nasu, Ji ya ke kamar ya je ya faɗa ma Danish sai dai yana matuƙar kokwanto a kan shi, Kuma yana ji aranshi zaiyi wuya ya bashi haɗin kai don su shiga cikin kurkukun.

To waye zai iya faɗa ma zancen nan? Nutsawa yae cikin tunaninshi, nan take zuciyarshi ta Amabaci sunan ANGEL, tunawa yai da lokacin data watsa ma Giants ruwa a jikin su tana zazzaga musu masifa, hakan yasa shi yarda cewa Yarinyar ba ƙaramar jaruma ba ce, bata da tsoro kuma tana da ƙwarin gwiwa, dama tun ranar da aka kawo su ya lura da yadda take tafiyar da rayuwarta da kuma ta ƴan uwanta tamkar itace ta haife su, ta zama jagora acikin su, kuma ya fahimci cewa yarinya ce ita bata kai shekarunsu Hanna ba, amma tafi su wayau da hankali.

Tun da ya fara zarya acikin ɗakin, su parveen su ke ta kallon shi, hatta Danish ya ankara dashi, kamar akwai wani abu dake damun shi, sam bai lura da kallon na shi da suke yi ba, A ƙarshe zuciyarshi ta saƙa mishi cewa

_Ita kaɗai ce zata Iya taimaka maka wurin nemo ƴar uwarka, tun da itama tana neman tasu ƴar uwar da aka ɗauke, Idan ku ka haɗa hannu da ita, za ku iya cimma nasara, don haka karka kuskura ka faɗama kowa, Ita kaɗai zaka sanar mawa_

Muryar Azeeza ce ta katse mishi zancen zucin mashi ta hanyar yi mishi magana

“Ɗan uwa, me ka ke tunani ne? Tun ɗazu na lura da kai sai zarya ka ke yi mana acikin ɗaki, nace anya lafiya kuwa” Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi tare da juyar da kanshi Ya fuskanci inda azeeza take zaune ita da parveen. Kamar wasu tagwaye

“Ina tunanin rawar da zan koya ma ku ne ko ba ku so”? Ya faɗi hakan ne don kar su yi tunanin wani abun ne na daban ke damunsa.

Har suna haɗa baki wurin cewa”Muna so mana, dama zuciyar mu duk ba daɗi wlh, kwanakin nan mun rasa farin cikin mu”

“Kada ku ta6a bari damuwa ta hana ku jin daɗin rayuwar ku, saboda kowa yana da damar da zai sanya kan shi farin ciki, yawan zama kuna tunanin zai iya haddasa muku matsala, just ku yi abunda ranku ke so, zaku samu farin ciki” acewar Gabriel

Parveen tace”Angel tana koya mana yadda zamu motsa jiki, da karatu sannan tana bamu tarihi da labarin gidan daddynta, har ma ce mata tayi wata rana zata yi ƙoƙari don mu fita daga cikin kurkukun nan………” natsuwa gabriel yai a yayin da yake sauraran maganar parveen, da alama ya ƙara samun wani abu da yake son ji agame da angel, da sauri ya nufi gefen gadon dasu azeeza suke zaune, shima ya zauna.

“Inaso ku bani duk wani labari da angel ta baku agame da rayuwar ta, da kuma abubuwan da ta koya maku” Buɗe ido sosai Danish yai daga can saman gadon shi yake kallon bayan Gabriel dake zaune gefen su parveen, Mamaki ne ya kama shi for what reason Gabriel zai dinga yi musu tambayoyi kan angel! Menene alaƙar shi da ita? Why yake son ji”? Miƙewa zaune Danish yai saman mattress ɗin, ya jingina bayanshi jikin bango, ya tsare su da ido, Tabbas da ace yasan dalilin da yasa gabriel ya tambayi su azeeza su bashi labarin angel da ya dakatar shi.

Parveen ce ta labarta mishi komai game da angel, tun zuwanta kurkukun da irin ɗawainiyar da ta yi masu, har zuwa ranar da aka kawo su Gabriel cikin kurkukun.

Jinjina kai gabriel yai alamar ya gamsu da labarin da parveen ta bashi na angel,

Azeeza tace”mu taso ka koya mana rawar? Idon shi akan fuskarta yace”nafi so mu yi tare da angel, mu bari ta farka,” su ka ce mi shi toh, zasu jira ta farka, Miƙewa Gabriel yae daga gefen gadon parveen, yana juyawa suka haɗa ido da Danish, ya ɗaure fuska, ta6e baki Gabriel yae tare da wuce wa Ya nufi nashi gadon ya zauna yana jiran farkawar Angel.

Lokacin da marece ya nutsa, suna zaune, Unaiza tafarka jikinta nata kerma hannayenta dafe da Cikinta, saukowa tai daga saman gadonta, da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, bayan ta shiga toilet ɗin agaban magudaji ta zuƙunna tana ƙwara amai, tamkar ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago, temperature ɗin jikinta ya yi zafi sosai, tana acikin mawuyacin hali, an rasa me zuwa wurinta ya taimake ta.

Tun daga cikin sashen toilet ɗinsu har izuwa cikin ɗakin su, Sautin kakarin amanta ne Ya karaɗe ko’ina, Ya addabi kunnuwansu, ganin sunƙi motsawa suje su taimake ta, yasa azeeza ta sauko daga saman gadonta, parveen hada cewa”Zuwa za ki yi? Baki ji abunda angel tace mana akanta ba? Salon saita shanye maki jinin ki ko”? abunda suke jima tsoro kenan shiyasa suka ƙi zuwa su taimake ta, shi kuma Danish abunda ya hana shi zuwa wurinta gudun kada yabar ɗakin Gabriel ya samu damar zuwa wurin angel, saboda ya fahimci cewa so yake yayi magana da angel.

“Ai bata da lafiya, ba zata iya shan jini ba, ni dai zanje na taimake ta ne, kada ta mutu” azeeza ce tai maganar tare da kama hanya ta nufi sashen toilet dinsu, Cikin toilet ɗin da take jin sautin shesheƙar kukan Unaiza, ta buɗe ƙoparshi tasa kai ta shiga, A zuƙunne ta same ta, Baiwar Allah taji jiki, Cikinta ya ɗame dama bata ci abincinta ba, jikinta sai kerma yake yi.

Ƙarasawa gabanta Azeeza tayi fuskarta da alamun tausayinta ta zuƙunna suna fuskantar juna, bata ta6a tunanin wani daga cikinsu zaiji tausayinta ba har yazo wurinta sai ga azeeza tazo, daƙyar take kallonta saboda nauyin da idanuwanta su ka yi mata, sunyi luhu luhu da su kamar ƙwayar cikinsu zasu faɗo ƙasa launin idon nata ya ciza, la66anta sun yi suntum, sai nishi take yi tana matse cikinta.

“Sannu sister, baki da lafiya ne”? Bata samu damar amsa mata ba, azeeza ta kuma cewa”Pls talk to me, I wanna help you.” Ganin taƙi tanka mata yasa azeeza ta Miƙewa tare da nufar inda bucket ɗinsu yake, ta tarba shi bakin fanfo ta kunna ruwa ya soma sauka acikinsa, Sai da yai rabi ta ja bokitin tana nishi don ba ƙaramin nauyi yayi mata ba, gefen unaiza ta ajiye bokitin, kafin ta karkatar dashi ruwan cikin ya kora aman da tayi dukan shi, Sauran da ya rage, ta taimaka mata wurin wanke fuskarta, ita kanta azeeza sai da gabanta ya faɗi jin irin zafin da jikin unaiza yae, lokacin da ta ke wanke mata fuskar da hannunta, kwata kwata babu ƙoshin lafiya atattare da ita, hada baki ta kuskure mata.

“Mu koma ɗaki, kinji” a wahalce ta ɗago da ido tana kallon azeeza ta ɗan girgiza mata kai, yayin da take cizon lower lip ɗinta, wani irin raɗaɗin azaba take ji.

“Pls ki yi min magana mana, ni inaso na taimake ki ne” runtse ido unaiza tayi na ɗan wani lokaci, azeeza har ta gaji da tsayuwa, ba dan tana jin tausayinta ba da tuni ta jima da komawa dakin su,

Tana so ta yi ma azeeza magana sai dai ta kasa motsa la66anta, jini har ya fara bleeding ta hancinta, ganin hakan yasa hankalin azeeza ya tashi, da gudu ta nufi cikin ɗakin su, a sukwane ta faɗo Ciki, Hankalinsu Naufal ya dawo kanta, muryarta har tana shaƙewa wurin faɗin”Ƴar gidan daddy bata da lafiya, Hancin ta yana bleeding, dan Allah ku zo ku taimake ta” Shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata, duk da sun tsorata da jin abunda ta faɗi,

Ran azeeza ba ƙaramin 6aci yae ba, hawaye har sun fara wanke fuskarta, cikin ƙunar rai tace”wai ba zaku zo ku taimake ta ba”? Kamar kurame sai dai suka bi ta da ido, fuskarta a hautsine ta nufi gadon angel, tana bubbuga ƙafarta tana ambaton sunanta

“Angel wake up, ga ƴar gidan daddy can bata da lafiya, ina ta roƙon su akan su zo mu taimake ta amma sun ƙi saurarana”

tana kuka tana magana, Daƙyar ta samu Angel ta farka, tana faman yamutsa fuskarta da tayi jawur, saboda kukan da tasha, A hankali ta tsayar da idanuwanta kan fuskar azeeza dake ta kuka, Muryarta adisashe ta furta”meya faru ne”? Cikin shessheƙar kuka azeeza tace”Ƴar gidan daddy ce, tana acikin toilet bata da lafiya hada jini a hancinta, ina ta roƙonsu akan su zu su taimaketa amma sunƙi su saurare ni”

Ɗaya bayan ɗaya angel tabi kowannansu da kallo, ita Sarah bacci ne ya ɗauketa bayan ta gama yankar akaifar, amma sauran idonsu biyu, lokaci ɗaya ta fahimci dalilin dayasa suka ƙi zuwa su taimake ta, saboda tace musu ita mayyace, zata iya shanye musu jini, duk da ita ta yi hakan ne don ta sanya musu tsoronta acikin zuciyar su, gudun kada ta lalata musu rayuwa.

Saukowa Angel tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu azeeza tabi bayanta, Suna shiga Cikin toilet ɗin da Unaiza take suka same ta kwance ƙasa, idanuwanta sun juye, Hankalin angel ba ƙaramin tashi yai ba, zuƙunnawa tayi agabanta tare da sanya hannayenta biyu ta ruƙo kafaɗunta, ta ɗago da ita zuwa ƙirjinta, ta faɗa, nan take angel taji zafin da ke ajikin unaiza na fitar hayyaci, hatta nunfashinta da hucin zafi yake fita, ta rasa gane wani irin ciwo ne ke damunta, kamar hada zazza6i, raba jikin su tai daga na juna, ta sanya hannu ta tallabo fuskarta, muryarta na kerma tace”Unaiza meke damun ki? Wani irin ciwo ne wannan”? Biji biji ta ke kallon angel, duk da tana acikin mawuyacin hali, sai da tayi mamakin ganinta, don bata ta6a tsammanin wani daga cikinsu zai iya taimaka mata ba, motsi ta soma yi da la66anta, sunan allura ne take faɗa musu wadda ake yi mata agida, idan ciwon ya tashi, sai dai sun gaza fahimtar me take cewa, koda ace ma sun gane, basu da hanyar da zasu iya samo mata allurar,

“Azeeza ɗauko min mayafin nan na kayan mu,” ta amsa mata da toh, ɗaki azeeza ta shiga ta ɗauko Cotton scarve ɗinta, ta dawo ta miƙa ma angel bayan ta kar6a, tace ma azeeza ta zauƙunna ta ruƙe unaiza ajikinta, a cikin bokiti Angel ta tsoma mayafin cikin sauran ruwan da azeeza ta kora aman unaiza, sai da ya jiƙa ta matse shi, ta ɗaura shi saman jikin unaiza, ta dinga goga mata shi, ta ko’ina, ta yi mata hakan ne don ta samu relief ɗin zafin jikin ta.

sai nishi take yi tana fitar da numfashi awahalce, duk in ta ɗaura mayafin ajikinta sai ta zabura, alamar bata son ruwan jikin mayafin na ta6a jikin ta, bayan ta kammala, ta miƙe taje bakin igiyar toilet ɗinsu ta shanya Mayafin, Kafin ta dawo ta sanya hannu biyu ta ruƙo unaiza ta miƙar da ita, jikin ta babu ƙwari, dama ba wata ƙibar kirki ke gareta ba, a haka taja ta zuwa cikin ɗakinsu,

Suna shiga ciki, idanuwansu Hanna suka dawo kansu, gadon unaiza angel ta wuce da ita, tare da kwantar da ita sama, ta juya ta nufi akwati nansu, ta buɗe ta ɗauko tissue ta koma saman gadon unaiza.

Dashi tai amfani wurin goge mata sauran jinin dake a hancinta, bayan ta kammala ta nannaɗe wanda ta goge jini da shi ta cusa su acikin wanda ta kuma yagowa, ta miƙa ma azeeza tace taje ta zuba a acikin trash can, ta amsa mata da toh, bayan ta kar6a ta juya ta nufi toilet dinsu, bada jimawa ba, Azeeza ta dawo ɗakin, gefen gadon unaiza ta koma ta zauna, ya kasance su biyu ne akusa da ita, jikinta ya ɗanyi sauƙi, ta ɗaura kanta saman pillow, still bata daina nishi ba, hannayenta na asaman mararta, addu’o’e angel ta karanto mata ta tottofa mata saman fuskarta da jikinta.

Hankalin Gabriel gaba ɗaya yana akan angel, yayin da shi kuma Danish nashi hankalin ke akan Gabriel, Ya kafe shi da ido ba tare da ƙyaftawa ba, sarai gabriel ya lura da kallon tuhumar da Danish ke yi mishi, amma sai ya basar.

Saukowa yai daga saman gadon shi ya nufi angel, da sauri Danish Ya miƙa shima Ya nufi gadon Unaiza, atare suka tsaya bakin gadon, har suna haɗa kafaɗa, Kallon mamaki Gabriel yai ma Danish, fuskar angel a yamutse ta kalle su, harara ta watsa ma Danish, muryarta ƙasa ƙasa tace”Shi ne ku na ganin bata da lafiya amma an rasa wanda zai taimaka mata acikin ku sai Azeeza”? Gabriel ne yace”Bansan time da ta farka daga bacci ba, hankalina baya akanta,”Danish yace”saboda ke yasa ban je wurin ta ba” ta6e baki ta ɗanyi, tare da juyar da kanta, Ta kalli su Hanna tunkafin ta yi magana parveen tace”ae kin hana mu zuwa wurinta saboda mayyace zata shanye mana jini, shiyasa mu ka ƙi taimakon ta”

Numfasawa tayi yayin da take kallonsu, Acan cikin zuciyarta tana tunanin taya zata fahimtar dasu cewa ba mayya ba ce? Kada su ɗauke ta maƙaryaciya, tun da ita ta faɗa mu su hakan da bakinta.

“Ae bance kada ku taimaka mata ba, idan bata da lafiya, a bun dana hana ku shi ne ku daina bari tana ta6a jikin ku, saboda babu kyau, wani ya kalli tsiraicin ka koya ta6a shi, Itama don batasan babu kyau ba ne shiyasa take yi, amma in muka ja ta ajikin mu mu ka fahimtar da ita zata daina ne…..” tun kan ta rufe baki, Rubina tace”Hada jinin zata daina sha”? Ɗaga mata kai angel tai alamar eh, su ka ce toh zamu dinga taimakonta daga yanzu, amma itama kija mata kunne ta daina rashin jin magana, kuma ta daina yi mana gorin ƙirji,” angel tace musu toh, zata ja mata kunne.

Mayar da idanuwanta ta yi akan su Danish dake atsaye, kowannan su ita ya ke kallo, ta rasa gane dililin yin tsayuwar na su akanta.

“Lafiya”? Tai tambayar tana jiran jin amsar su, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa ba komai,” juyawa gabriel yai tare da komawa gefen gadon shi ya zauna, shi ma danish ya koma nashi gadon ya zauna.

Duk wani motsin Gabriel Akan idon Danish, Ya hana shi sakat, Abu kamar wasa, Ko toilet Angel zata shiga sai Danish yabi bayanta, lamarin ya ɗaure mata kai, a bakin ƙopar toilet ɗin zai tsaya har saita fito sannan yaja hannunta su koma ɗaki, hakan ba ƙaramin 6ata ma Gabriel rai yai ba, shi burin shi su zauna da ita su tsara yarda zasu ɗauko ƴan uwansu, da kuma yarda zasu gudu daga Cikin kurkukun tun da yaji cewa itama tana da wannan ƙudirin aranta, Sai dai ga dukkan alamu, akwai mutun ɗaya da baison hakan ta faruwa, shiyasa ya hana shi sukuni, dama can bai yarda da Danish ba, tun zuwanshi, daga gani yana da wayau, akwai abunda yake 6oye musu, kuma yasan komai akan gidan kurkukun kallon su kawai ya ke yi.

Lokacin da dare ya yi kowannansu yai shirin kwanciya, mutun biyu ne babu alamun zasu runtsa.

Jikin Unaiza ya ɗan lafa, da taimakon su azeeza taci abinci kaɗan, tun ɗazu bacci yayi awon gaba da ita.

A tsakiyar ɗakin Gabriel ya dinga sintiri yana jiran bacci ya ɗauki Danish, Ko ya samu yaje su yi magana da Angel, amma ɗan tahalikin nan Yaƙi kwanciya, ƙarshe ma daya ga dagaske Gabriel ba bacci zaiyi ba, sai ya ɗauki pillow ɗinshi, Ya koma saman gadon Angel da ke kwance tana yin bacci, Ya ɗaura pillow ɗinsa saman mattress ɗinta, ya hau ya zauna tare da jingina bayan shi jikin pillow ɗin,’ mamaki ƙarara akan fuskar gabriel, Ganin wani iko na Allah, a dole ya haƙura ya koma kan nashi gadon ya kwanta zuciyarshi acunkushe da tunani kala kala,.

Dare Ya nutsa sosai, Sunyi nisan kiwo acikin baccin su, har time ɗin Danish na zaune saman gadon angel, ahaka bacci yai awon gaba dashi, Ba zato ba tsammani, Unaiza tafarka tana ihu tana daddafe cikinta, wata irin kururuwa kamar ana zare ranta, a matuƙar firgice masu bacci suka soma farkawa Kowa Yana faman zazzare idanuwanshi, Haƙiƙa sunyi matuƙar firgita, ɗaya bayan ɗaya suka soma saukowa daga saman gadonsu suna tunkarar gadonta, mutun biyu ne basu farka ba, Jamima da majnun, kamar matattu sai sharar baccin su su ke yi, A kewaye da gadon unaiza suka tsaitsaya curko curko suna kallonta hankalin su yai matuƙar tashi, suka dinga tambayarta lafiya meke damunta, amma ta kasa buɗe baki ta basu amsa, Sai cizon la6en ta take yi, yayi suntum dashi, Angel tafi kowa shiga damuwa tsoranta, har ga Allah bata son wani abu ya samu unaiza duk da baƙin halinta tana ƙaunarta.

“Yanzu ya zamuyi da ita? Danish ba wani taimako da zaka iya yi mata? Angel ce tai maganar tana kallon shi, yae shiru bai ce mata komai ba,

Haris yace”ni fa inaga kamar kalar ciwon da su Hanna suka ta6a yi ne” gabansu ne yai wani irin mugun bugu jin abunda Haris yace, muryar deeja na arude tace”In sha Allah ba shi bane,” Azeeza tuni ta fashe musu da kuka, tana zaune saman gadonta, ta kasa saukowa gudun kada ta faɗi ƙasa saboda lalurarta, tana jiyo muryoyinsu acikin kunnuwanta

Suna Cikin yin maganar nan, sautin motsin buɗe ƙopa ya karaɗe kunnuwasu, hankalin su ya ƙara tashi, nan take ransu ya basu cewa Anzo atafi da ita ne’ jikin su duk yai sanyi, lokacin da su ka yi arba da Giant ɗin dake saukowa saman benan, basamudan ƙato, Mai ɗauke da star 1 agaban rigarshi, tunkan ya ƙaraso ciki, suka bashi hanya, Ya sanya hannu biyu ya ɗauki unaiza saman kafaɗarshi ya juya ya fuce da ita daga Cikin ɗakin, kamar wasu sakarkaru haka suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin nasu da akayi, shi kenan an tafi da Ƴar gidan daddy, Gabriel yaso ya tambaye su ina za’a kai ta? Sai kuma ranshi ya bashi cewar wata’ƙil zasu kaita inda zasu duba lafiyarta ne, hakan yasa shi dakatawa da yin tambayar tashi, dama bai shirya yinta ba agaban Danish, don zai ƙara sa mashi ido ne.

Ba su ta6a tunanin zasu zubar mata da ƙwalla ba, saboda babu shaƙuwa atsakanin su da ita, Amma sai gashi yau saboda ita sun gaza runtsawa, a gefe da gefen gadonta matan su ka zauna shiru babu mai magana, Babu yadda haris baiyi dasu ba akan su koma su kwanta saman gadajen su, amma suka ƙiya, A ƙarshe nan suka kwana.

A washe garin ranar da safe, suna ta sharar bacci, wasu sun jingina bayansu jikin bango wasu kuma sun ɗaura kawunansu saman cinyoyin ƴan uwansu, Waɗan da suka kwana asaman gadonsu, mazan ne duka sai Jamima da azeeza, Cikin sa’a Gabriel ya riga Danish farkawa daga bacci, Ae yana buɗe ido ya hango Danish baje saman gadon shi, yai wuff ya duro daga nashi gadon Cikin sanɗa ya nufi bakin gadon unaiza inda suke zazzaune suna bacci, A hankali ya zuƙunna inda angel ta jingina bayanta jikin bango, hanna ta ɗaura kanta saman laps ɗinta, haka su kai bacci jiya, saitin kunnanta yakai bakin shi cikin raɗa ya shiga kwala mata kira “Angel! Angel” har cikin dodon kunnanta, ganin tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta yasa shi yin sauyin ɗaura tafin hannun shi saman bakin ta, gudun kada ta razana ta saki ƙara Danish ya farka, tsantsar mamaki ne ya kamata ganin Gabriel, Zuƙunne agabanta, hada ƙoƙarin toshe mata baki, zazzare mishi idanuwanta ta soma yi, tare da kai hannu zata ka6e mishi nashi hannun daya toshe mata baki.

Da sauri yace”ina son magana dake, tun jiya, bana so kowa ya sani, pls ki bani haɗin kai, ki taso mu shiga sashen toilet ɗin mu” yana ƙare maganar ya zame hannun shi daga saman bakinta, Ya miƙe cikin sanɗa ya nufi 6angaren toilet ɗinsu, yana tafiya yana waiwayon shimfiɗar Danish, wata irin kasalace ta baibaye Jikinta, A hankali takai hannu ta ɗauke kan Hanna daga saman laps ɗinta ta kwantar da ita ƙasa, kafin ta miƙe ta bi bayan Gabriel, tana shiga sashen toilet ɗin ta same shi atsaye ya jingina bayan shi jikin bango.

Yana ganinta yai saurin ruƙo hannayenta biyu acikin nashi, kamar wani mara gaskiya, yana magana yana kallon bakin ƙopar shigowa sashen toilet ɗin, Nan take ta fahimci cewa akwai wanda baya son yaji abunda zai faɗa mata.

“Tun jiya nake son na yi magana dake amma ɗan uwanki ya hanani sakat, na rasa gane dalilin dayasa baya son na tunkare ki”

“You mean Danish”? Ɗaga mata kai yai alamar eh”

Tace mai ka ke son faɗa min ne”? Har ya buɗe ba ki zai yi magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa”Oh wai kana magana akan Unaiza da aka tafi da ita jiya? Nasan ka tsorata da ganin an ɗauke ta, bawani abu zasu yi mata ba, za’a kai ta treatment room ne aduba lafiyar jikinta” tun da angel tai wannan maganar nan take Gabriel ya fahimci cewa DANISH yazo wurin, shiyasa tai saurin tarar numfashi shi, Saboda ita ta hango shi, kamar walkiya, ko yaushe ya tashi daga bacci.

ta wutsiyar ido Ya hango shi tsaye bakin ƙopar shigowa wurin ya goya hannayen shi saman ƙirjin shi, ya kafe su da ido.

Yatsina fuska Gabriel ye ba tare daya kalli fuskar Danish ɗin ba, yaji takaicin bayyanar shi, ɗan hana ruwa gudu, sauƙin ma Angel ta gan shi da baisan me zai biyo baya ba, idan ya faɗa mata ya shiga cikin kurkukun.

“Zan shiga toilet in yi wanka, yakamata kaima ka shiga ka yi” tana magana kamar batasan da zaman Danish a wurin ba, Ta juya ta nufi toilet ta buɗe ta shiga, duk akan idon Danish, Shima Gabriel ya nufi ɗayan toilet ɗin ya shiga Ciki, Ya datse ƙopa.

Sun so ace ya koma cikin ɗaki amma yaƙi tafiya, kowannan su sai da yae wanka time da suka fito daga cikin toilet ɗin, Yadda suka barshi haka suka same shi, Gabriel bai tanka mishi ba ya wuce ɗaki, Angel ce ta tsaya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi tace”ya ka ke? Fatan ka tashi lafiya”?

Wani irin kallo taga yanayi mata, kamar ba zai amsa mata ba, muryarshi da alamun kasala ya amabaci sunanta

“Angel, na tashi lafiya, ina fata kema haka” matsawa tai kusa dashi, jikinta da lemar ruwan wankan da tayi, Tace”jiya nashiga damuwa da aka tafi da unaiza, banma san time da bacci ya ɗauke ni ba, zuciyata ba daɗi” ta ƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka, Ruƙo hannunta yae acikin nashi, ya ɗan janyota kusa dashi,

“Fuskarki harta kumbura, yakamata ki koma kiyi bacci, ko kin samu relief,” girgiza mishi kai ta yi “a’a, baccin ya ishe ni, zan jira abinci ne, ka shiga toilet ka yi wanka zan jira ka anan”

(Angel sarkin wayau, tana so ne ya shiga don ta samu damar yin magana da Gabriel, ta ƙagara amatse take da taji me zai faɗa mata)

Maƙe mata kafaɗa Danish yai tare da cewa”Bana buƙatar yin wankan, mu koma ɗaki mu zauna, mu jira abinci nima yunwa nake ji,” kallon shi kawai ta ke yi, wato ta fahimci wani abu agame da Danish, shegen wayau ne dashi, mutun sai yana da kaifin basira zai iya gane hakan.

“Dan Allah ka shiga ka yi wanka, inaso ne kaima ka ji irin daɗin da naji ajikina, idan ka kammala sai mu koma ɗaki,”

kamar maroƙiya haka tadinga yi mishi magiya akan yaje yae wanka, hada bubbuga mishi ƙafa da shagwa6a, sai taga ya saki ƙayataccen murmushi akan fuskar shi, ta yi tsammanin zai amince ne hakan yasata sakin murmushi tace”Ka amince zaka shiga ka yi wankan”? Ɗaga mata gira yai tare da cewa”Eh amma atare zamu shiga, sai kiyi min, idan har baki amince mun shiga atare ba, to ki daina roƙona akan yin wanka don ba inda zanje INA ATARE DA KE!” takaici ne ya isheta

A ƙule tace “ai ni nayi wanka akan me zan bi ka mu koma toilet”? Tai maganar tana gatsina mishi hanci, yace”nasan kinyi ae, ni zaki yi mawa yanzu” tsoki taja tare da bi ta gefen shi ta wuce cikin dakin, Ya juya yabi bayanta, Suna shiga Ciki suka sami Gabriel zaune gefen gadonshi ya zabga uban tagumi, Takaicin Danish ne ya ishe shi, sam baya son aja tsawon lokaci ba tare da yayi gaggawar sanar da angel game da yarinyar nan ba, zata iya rasa ranta.

Saman gado Danish ya zauna, angel kuma ta nufi akwatin kayansu, ta ɗauko red vest ɗinta, tare da dogon wandonta baki, Ta nufi sashen toilet dinsu ta shiga, acan ta canza kayan jikinta, ta cire tsaffin ta maida sabon, Vest ɗin tabi jikinta ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, duƙunƙune tsohon uniform din ta yi a hannunta.

Bata fito ba, sai ta tsaya tana leƙen Cikin ɗakin su daga cikin sashen toilet ɗin, bakowa take kallo ba face Gabriel, ranshi ne ya bashi cewar ana kallon shi, hakan yasa shi juyowa don ya tabbatar, Cikin sa’a su ka haɗa ido da ita, Da hannu ta dinga yi mishi alamar ya iya rubutu? Ta kwatanta mishi biro ta hanyar yin amfani da hannunta na dama kamar tana rubutu, nan take ya gane me take nufi, bai amsa mata ba saboda Danish daya tsare shi da ido, shiyasa ya kawar da kanshi gefe ɗaya, Fitowa angel ta yi daga cikin toilet din ta shiga ɗakin ta zauna gefen gadonta, ta daura idonta akan Gabriel, so take ya bata amsar tambayarta idan ya iya rubutu, tana so ta sanar dashi akan ya buɗe backpack ɗin Unaiza ya ɗauko jotter dinta da biro yae mata rubutu, Ya jiye mata, ta hakanne kaɗai zasu iya magana da juna, if not Danish bazai ta6a bari su ke6e ba, sai dai batasan koya iya rubutun ba, zaiyi wuya ma ace bai iya ba, tun da a hasashenta ba rainon kurkukun ƙaddara ba, Akwai wayewa atattare da shi.

Yaso ya bata amsa amma Danish Ya kafe su da lumsassun idanuwanshi, Su uku ne idonsu biyu acikin ɗakin, Sauran har yanzu basu farka ba, Sai daga bisani ne Ɗaya bayan ɗaya su azeeza suka soma tashi daga bacci, da tunanin unaiza suka farka, suna ta jimamin halin da aka tafi da ita jiya, abun ya ta6a zuciyoyinsu, Angel tace dasu suje suyi brush suyi wanka, idan suka fito zasu motsa jiki yau, hakan yasa suka miƙe atare suka nufi sashen toilet ɗinsu, kafin wani lokaci duk su kayi wanka, kowa ya sanya red vest din shi da dogon wandon shi na sabon kaya ba ƙaramin kyau, su ka yi musu ba.

Ba su kai ga fara motsa jikin nasu ba, Giants suka kawo musu abinci, Dama da yunwa suka farka, Kowa ya samu wuri ya zauna, tsiren nama ne aka kawo musu da kayan marmari, hada robobin lemu dana ruwa, suna cin abinci idon Gabriel akan fuskar angel, yana so ya bata amsar tambayar da ta yi mishi ɗazu shiyasa ma ya zauna yadda zasu fuskanci juna, ko da ta ɗago suka haɗa ido dashi, saboda rashin gaskiya atare suka saci kallon Danish, shi da yafi su iyawa, ashe tun ɗazu ya ajiye cin tsiren naman don kada ya janye mishi hankali daga kansu har su samu damar yin wani abu ba tare daya gani ba, kyawawan idanuwanshi na akan faces ɗin su.

Danish bai ta6a bata mamaki ba irin na yau, ashe dama yana da wayau? Yake nuna kamar sakarai ne shi? yau dai ta shaida hakan, har tambayarshi ta yi meyasa bazai ci Abincin shi ba? ya ce mata kada ta damu, zai ci ne zuwa anjima.

tasa naci akan saiyaci, yace idan har tana so yaci, to ta dawo saitin inda yake zaune, don yaji daɗin ganinta da kyau, ba tare da ta yi mishi musu ba, ta miƙe tabar saitin Gabriel ta koma saitin inda ya ke ta zauna, Sai gashi ya sanya hannu yana ci yana kallonta, a haka har suka kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan kayan abincin suka bar ɗakin, fitarsu ke da wuya, Angel ta nufi toilet, Da sauri Danish yabi bayanta, tana shiga ya fado ciki, murmushi ta sakar mashi tare da cewa”My bodyguard, wankan zaka yi ne”? yace mata a’a, ita ya biyo tace mashi toh, su shiga dama tazo duba furenni ne taga awani hali suke ciki, ta kuma basu ruwa, Atare su ka shiga, da kanshi ya ɗabo mata ruwa a bucket yazo da shi gaban tukunyar fulawar, har yanzu dai furen batul Yana nan yadda yake, ya bushe Ganyan sun tsamure, suna a tsaye ta kalle shi tare da cewa”furen batul ya nuna alamun bata da ƙoshin lafiya, amma banji ka ce komai ba”? Ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba, ya bata amsa da cewa”bani da masaniya akan yanayin ganyan jikin shi, zai iya yiwuwa ruwa furen ke buƙata” ya ƙarasa maganar tare da kwarara ruwan da ya ɗabo saman furennin, bayan ya kammala ya sauke bucket ɗin,

Kallon juna su ka yi ita da shi, ba tare da ƙyaftawar ido ba,

“Irin wannan kallo haka, me kake gani akan fuskata”? Tae tambayar tana dan harararshi,

Bai bata amsar maganarta ba, sai ce mata yai
“Pls angel, bana so in gan ki tare da yaron can, ni ban yarda da shi ba, kuma na lura kamar yana son shisshige miki ne……” dariyar da tayi ne ya sa shi dakatawa da yin maganar, sai da tayi mai isarta tukunna ta dai dai ta natsuwarta.

“Ka faɗi min dalili ɗaya da zaisa in janye jiki da shi, in banda abun ka ni menene alaƙa ta dashi? Ko ka ga wani abu ne”? Shaking head ɗinsa yai “just ni bai kwanta min araina ba” fuskarshi ayamutse ya bata amsa, ta6e baki ta ɗan yi, tana ƙoƙarin motsa lips ɗinta da niyar ta yi magana, ɗan juyi da zatayi keda wuya ta hango wani sabon tsiron fure kyakkyawan gaske a gefen na daddynta, waro ido waje tayi cike da mamaki, Ta zuƙunna gaban tunkunyar fulawar, a gefen ta Danish ya zuƙunna, launin ganyen furen pink colour, tsabar kyau kamar ka cinye, A ruɗe ta kalli Danish Alamar tana son ƙarin bayani game da sabon furen daya fito, girgiza makai yai alamar shima baisan ya akai ya futo ba, wani irin kallon rainin wayau tayi mashi tare da cewa”Ni dai ka faɗa min ran wanene akan sabon furen nan” shiru yai still idonshi akan fuskarta, sam baiso ta canza musu firar da su ke yi ba, Yaji haushin fitowar sabon furen da bai san Ran wa ke akanshi ba, saboda ya katse musu maganar da su ke yi.

“Magana fa nake maka, inaso nasan furen wanene wannan mai kyan gaske,” motsa lips ɗinsa ya soma yi

“Angel, bansan na wanene ba, Amma tabbas mallakinsa, zai iya kasancewa wani ne daya maye gurbinki a wurin daddynki, ina nufin wanda daddynki yake matuƙar ƙauna kuma yake atare dashi” kallon harara angel ta jefa mashi,

“Lier, Ae daddyna baida madadina a duniyar nan, Ni ɗaya ce tak, babu wanda zai iya replacing ɗina acikin zuciyarshi, balle ma baya araye da har za’a samu wani ɗan shisshigi ya amshi matsayin da nake dashi awurinsa” murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish maganar da ta yi ba ƙaramin nishaɗi ta sanya shi ba,

Cigaba da magana tayi”daddyna da kanshi yace min ko aure zanyi bazan iya rabuwa dani ba, sai dai mijin ya dawo gidanmu ya zauna, ko kuma shi daddyna ya koma gidan shi da zama idan har yace bazai zauna a gidan mu,” gaba ɗaya ta manta atare da wa take magana, surutu take ta zubawa kamar radio mai jini.

“shi kanshi daddyna yasan irin burin da nake dashi, Ni nan da kake gani Hamshaƙin mai kuɗi zan aura, wanda ya shahara a duniya, ko Jinin sarauta, Hatta aunty aneelerh tasan da wannan maganar, wai hada ce min banson talaka nace mata Annabi ma yace mu nemi tsari da talauci, atoh, wa zai kai kanshi inda zai sha wahala, ae wlh ƙwara inda zanyi rayuwar hutu, adinga take min baya…….” shiru ta ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, shi ko mutumin ya tsareta da ido yana jiran ta ƙarasa sambatun nata, don ya lura kamar bata acikin hayyacinta ne.

“Kurkukun ƙaddara Ya canza min rayuwata, na ɗauki darussa sosai na zaman duniya, a yanzu bani da wannan burin da nake dashi a lokacin da nake agidan daddyna, na faɗi maka ne kawai, ni da ma bani da tabbacin zanyi tsawaicin kwana” yanayin fuskar Danish ne ya sauya ganin ƙwalla sun tarar mata acikin idanuwanta,

“Burin da nake dashi A yanzu shi ne, In taimaki ƴan uwana mu fita daga cikin wannan Kurkukun ƙaddarar, Su yi rayuwar ƴanci kamar kowa, wlh Ni ban damu da in tsira ba, su kawai nake so su ku6uta, bayin Allah ina amfanin ma iyayen da zasu sadaukar da ya’yansu don neman wata biyan buƙata ta duniya, yanzu jibi Unaiza, mugun ubanta da ya ke yasan bayar da ita zaiyi shiyasa bai bata tarbiya ba”

sosai ta fashe da kuka, har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata, hannu biyu ya sanya wurin janyota jikin shi ya ɗan kwanto da ita saman ƙirjin shi, yana lallashin ta.

*PRISONERS✍️*

Tun lokacin da Angel ta shiga toilet Danish yabi bayanta, Gabriel yae saurin miƙewa ya nufi saman table din dakinsu inda unaiza take ajiye backpack ɗinta, Sai da ya tabbatar babu mai kallon shi, dama already ya ɗauke musu hankalinsu, ta hanyar basu training ɗin rawar da za su yi, Sun dage sai tiƙar rawa suke yi atsakiyar ɗakin,

Zuge zip ɗin jakar yai, Jerin text books ne da jotter hada diary ɗinta, wanda ke ƙunshe da tarihin rayuwarta, biro ya ɗauko tare da jotter ɗin ya ɗaura saman table, bayan ya buɗeta a tsanake Ya soma rubutu cikin harshen turanci, kusan shafi ɗaya ya cika, ya yagi paper ɗin da yayi rubutu akanta, Ya maida jotter ɗin da biron cikin jakar, Ya zuge mata zip ɗinta.

Sai da ya ninke takardar, tukunna ya doshi gadon angel, Haris da deeja idonsu na akan Su parveen dake rawa, Haka zalika su naufal da mubeen duk hankalinsu akansu yake, Tsabar iyayi hada Majnun da Jamima cikin masu yin rawar uwa uba, Sarah, kamar macijiya sai karkarɗa ƙugu take yi, ita ala dole rawa take yi,

Ya rasa a ina zai ajiye mata takardar inda zata gani, fargabarshi kada ya ajiye inda Danish zai iya ganinta, don zai iya yage ta ne. A ƙarshe ya yanke shawarar tura mata ita Cikin rigar pillow, ɗaukar pillow ɗin yai ya zuge zip ɗin jikin shi, ya saƙa takardar aciki, ” kafin ya ajiye mata shi, a hankali yake ja da baya, cike da saran Allah yasa Angel ta karanta saƙon nashi.

💌

*Idan Allah yakaimu next week zan Kammala Free pages of Takun farko, zan ɗauki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ƴar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

No comments