Breaking News

Kurkukun Kaddara 66

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

Dedicated to Aunty kubra💘🌹

*Gargarɗi!!!*


_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E66 free pages

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

 

 

💔PRISONERS💔

Kwance ta ke asaman gadonshi, hannunta rungume da pillow ɗin sa ta ƙanƙame shi a ƙirjinta, bacci take yi amma sam babu kwanciyar hankali atattare da ita, sai jan numfashi ta ke yi ga cikinta da ke ta yin kukan yunwa, hatta ƙirjinta wani irin nauyi yai mata, zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi, duk irin sanyin da yanayin ke da shi hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, saboda damuwa da kuma rashin cin abinci har rama ta yi fuskarta ta faɗa, sai uban hasken da ta yi, gashin kanta kuwa kamar na mahaukaciya, rabon da ta sharce shi tun lokacin da aka tafi da Danish, wankan ma sai in sun matsa mata ta ke yin shi akai akai, haka abinci sai sun mata dole sun tasa ta gaba tukunna take ɗan tsakurar kayan marmari tasha idan ta gama ta kora da ruwa, fruit kaɗai ta ke iya sha, duk ta takura kanta,Ta hana kanta sakat kamar wadda ta aikata zunubi, ga shi rayuwarta gaba ɗaya ta koma saman gadon Danish, idan kaga ta sauko to toilet zata shiga domin yin wani uziri amma bayan haka babu ruwanta da kowa, Saman gado take naɗewa ta addabi zuciyarta da tunane tunane na damuwa, depression tuni ya fara samun gur6i acikin zuciyarta, idan damuwa ta yi mata yawa kanta har sara mata ya ke yi da matsanancin ciwon kai, zuciyarta tai mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse saman ƙirjinta haka ta ke ji, wani lokacin idan abun yai mata yawa har amai take yi, Rayuwar Angel ta zama abun tausayi, kowa tausayinta ya ke yi acikin su, sun damu da damuwarta, suna matuƙar jin takaicin halin da ta shiga kamar ba Angel ɗin su ba……………..💔

Ƙasa ƙasa ta ke jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, sai surutu su ke yi duk sun cika ɗakin, tana ta faman ƙoƙarin buɗe idanuwanta amma sunƙi bata haɗin kai baccin ne bai ishe ta ba, ga kuma matsiyaciyar yunwar da ta ke ji, A hankali take motsa la66anta tana karanto addu’ar tashi daga bacci, kafin daƙyar ta iya buɗe manyan idanuwan nata waɗanda suka raunata sosai saboda kukan da take yawan yi akowani dare na Allah, bismilla ta furta yayin da ta ke yunƙurin miƙewa zaune ta jingina bayanta jikin bango, old uniform trouser ɗinta ne a jikinta baƙi, Sai jar vest ɗinta data sanya, don tafi sha’awar kwanciya bacci da ita, buɗe baki tai sakamakon hammar da tazo mata ba shiri ta ɗaura hannunta saman bakin nata Tana ambaton Alhamdulillah.

bayan ta sauke hannun ta ɗaura su saman pillow, kafin ta tsayar da idanuwanta kan ma su yin Surutun, kusan su Biyar, Zazzaune a ƙasa saman shimfiɗar Sarah, Hannah da Yasmin tare da Hibba da kuma rubina, sai Eve hada mai shimfidar Sarah, Hannunta ruƙe da nail cutter, Ita kuma Hanna tana ruƙe da nail filer, suna fira Sarah na yanke musu akaifa, idan tagama yi ma mutun ɗaya sai Hanna ta kankare mashi akaifar ta gyara mashi ita, idan ka gan su ahaka sai ka yi tsammanin basu da wata damuwa alhalin nan kuwa zuciyarsu a cunkushe take da matsananciyar damuwa.

tun da ta ɗaura idanuwanta akansu bata ɗauke ba, bakomai yake burgeta dasu ba, face yarda suke matuƙar ƙaunar junan su, Suna da kyakkyawar mu’amala a tsakanin su, Sau dayawa basu jin komai don su yi ma ɗan uwansu hidima, sa6anin wasu mutanan da zaka ga ƙashi ya hana su taimaki junan su, amma su waɗannan bayin Allahn suna da haɗin kai, tun da ta fara rashin lafiya basu ta6a bari ta wanke koda uniform ɗinta ba, hatta kayan marmarin da ta ke sha su ne suke kawo mata su har saman gadonta don ta sha, shiyasa take matuƙar ƙaunarsu.

Ɗauke idanuwanta tai daga kansu sarah, ta shiga bin kowani gado da Kallo, Parveen tana ƙudundune saman gadonta, bata farka daga bacci ba, sai juyi take yi saman mattress ɗinta kamar zata faɗo ƙasa, Sauran gadajensu Deeja tabi da kallo, Da alama idonta biyu, ta ƙurawa ceilling ido fuskarta ɗauke da damuwa, Haris ma Yana a zaune gefen gadon shi Ya zabga uban tagumi, gwiwowin hannayenshi asaman na ƙafafun shi, tasan bai wuci damuwar rashin ɗan uwansa bane, bawan Allah duk da irin juriyar shi hakan bai hana shi yin rama ba, sauran mazan duk suna a kwance saman gadon su basu farka daga bacci ba.

Tana cikin bin gadajen su da kallo, ta soma jiyo sautin dariyar Azeeza ta cikin sashen toilet ɗin su, Da sauri takai idonta kan ƙopar, Majnun ne ya fito babu kaya ajikin shi sai gudu ya ke yi jikinsa duk lemar ruwan wankan da ta yi mashi, Gaba ɗaya su Hanna suka ɗago Suna kallon su, Lamarin ya ɗaure musu kai ganin yadda yadda ya fito babu kaya yana ta gudu acikin ɗakin su, hauka tuburan yana ta tiƙar dariya ko kunya bai ji ko da ya ke ina yasanta.

Azeeza ce Ta biyo bayanshi hannunta ruƙe da uniform ɗin shi, Sai zagaye cikin ɗakin nasu su ke yi tana ta Ƙwala mashi kiran tana faɗin”Wai ba zaka tsaya in sanya maka kayan ka ba? Salon sai ka faɗi ko, don ma ka samu na yi maka wanka shine ka ke min wulaƙanci, ba don zuciyar imani ba Allah da bazan yi maka wankan ba ƙazami kawai, mutun jiki duk ciwo, har tsoron ta6a fatar shi nake yi kamar zata fashe saboda haske……..” Su hanna sai dariya su ke yi musu, ita kanta Angel sai da ta ɗan murmusa ganin yadda take ta faman bin shi yana yi mata yawo da hankali, da ga ita har shi Sai ka rasa gane wanene babba acikin su, shiyasa duk suka rainata,

kamar sun samu tv haka suka dinga binsu da kallo, babu wanda ya lura da Angel ta farka da tuni sunzo wurinta.

Fitowa daga Cikin ƙopar sashen toilet ɗin su Jamima ta yi, hannunta ruƙe da rigar uniform ɗinta, daga ita sai ɗan wandonta ja, fuskarnan a murtuƙe ta sha mur, ƴan kumatuntu sun yi suntum dasu saboda tsabar fusata, Gashin kanta da aka ɗaure mata da ribbom Ya cika bayanta, kamar na ɗiyar roba, sai baƙin rai ta ke yi,

Hayaniyarsu Ce ta farkar da sauran da suke rage suna bacci, hatta haris daya zabga uban ta gumi da deeja dake kallon ceilling saida suka dawo da dubansu akan Majnun da Azeeza.

“Azeeza!” haris ne ya kira sunanta, hakan yasa ta tsaya tana haki, Ta waigo tana kallon shi.

Tun kafin ya soma yi mata magana, ta ɗan ɗaure fuskarta, muryarta tamkar za fashe da kuka ta soma magana

“Na gaji da raina min wayau da su ke yi, don sun ga na damu dasu, shiyasa suke yi min wulaƙanci dashi da waccan mai fuskar tumaturin, tsawon one week ba wanda yai tunanin yayi musu wanka, da yake ba hankali ne dasu ba, ko tsamin jikin su basa ji, a tunani na yi musu gwaninta, yau da safe na tada dasu daga bacci naja su muka shiga toilet na datse ƙopa don inyi musu wanka, nasa su ka fara yin brush, bayan sun gama nace toh su tu6e kaya in yi musu wanka, ba ku ga irin wulaƙancin da su ka yi min ba, Jamima hada ce min wai ita bazata tu6e kaya inyi mata wanka ba, saboda tsarata ce ita, ban fita da komai ba, daƙyar na samu shi majnun nayi mashi wanka ahaka ma saida ya dinga watsa min kumfa a ido ina wanke wa, ita kuma jamima kusan dambe mu ka yi da ita, taƙi yarda inyi mata wankan, hada cewa sai dai inyi mata da wando a jikinta don kada in gan mata jiki…………kasa ƙarasa maganar ta yi idanuwanta cike tab da ƙwalla, sai kace ba ita bace ta gama shan dariya tana bin majnun da gudu ba, ita babban baƙin cikinta, Jamima da take yi mata kallon tsararta, ta raina mata wayau, da ga ita har majunun sun raina azeeza saboda ƙarantarta, duk a tunaninsu tsararsu ce basu san cewa ta girmesu nesa ba kusa ba.

Dariya suka dinga yi mata, musamman parveen da bata jima da farkawa ba, Hada gabriel dake kishingiɗe saman gadonshi, farkawarshi kenan yaji azeeza tana kora jawabi.

Ganin yadda su ke ta yi mata dariya yasa ta bubbuga ƙafafuwanta ƙasa, ta zuƙunna tana kuka, Muryar Angel ce ta katse musu dariyar tasu da wani irin kasala take magana da busassun la66anta

“Ku daina mata dariya kuna ƙara 6ata mata rai, Azeeza ki daina kuka, yanzu fa ki ka gama shan dariya, ke kanki sun baki nishaɗi, sai kina yi musu uziri, kinga ke yayarsu ce, su kuma ƙannanki, dole sai ana haƙuri da juna…..’ ta kai ƙarshen maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jamimah dake ta faman ɗaure fuska tana tsino ƙaramin bakinta.

“Zo nan” jin kiran Angel yasa ta ɗan saki fuskarta, ta soma tafiya tana tunkarar gadon ta, a bakin gadon ta tsaya tana kallonta”ba nan nace ki tsaya ba, dawo nan gefe na” tai maganar tana nuna mata gefen gadon, dawowa tai daga gefen gadon ta tsaya tana faman mutsustsuka rigar hannunta,

numfasawa tai tare da juyawa ta kalli majnun dake tsaye yana ta faman raba ido, hannayen shi biyu rufe da gabanshi, Parveen tace”Abanza, bayan ka gama nuna mana abun na ka shine yanzu zaka wani sa hannu ka rufe, kai ɗin nan ba ƙaramun shaƙiyi bane, ae wlh da ace nice zan maka wanka, da duk saina gurje farar fatarnan ta ka, aljani kawai” Tana magana tana jifarshi da harara idonshi akanta sai murguɗa mata baki ya ke yi.

“Zonan Majnun uban masu hankali” Angel ce ta kira shi, A hankali ya ke nufar inda take ba tare daya zame hannun shi daga gabanshi ba, a gefen gadon Ya tsaya dab da ita, Jamima tana a 6angaren dama shi yana a 6angaren hagu, kowa ya natsu yana jiran jin sasancin da Angel zata yi musu.

“Ku faɗamin meyasa kuka raina azeeza ne? Tsarar wasan ku ce ita? Daga taimako? Yau one week ba wanda ya kula da ba ku yi wanka ba, don ita ta taimaka zata yi muku shine kuke yi mata iya shege ko”! Tai maganar tana duban kowannansu,

Jamima ce tafara magana tana tsino baki
“Ae ni sai da nace mata, tabarnin inyi wankan ta ƙi bari inyi, bana son tayi min wanka, nafison su hanna su cuɗa min bayana ko ke….” tun kan ta ƙarasa maganar Angel tace”Oh saboda sune manya wanda suka isa dake, banda ita ko? Ɗaga mata kai tai alamar eh ta ƙara da cewa”azeeza fa ƴar ƙarama ce the same height as me, ta ya za’ai tayi min wanka.”

Mamaki ne ya kama su Hannah, Kowa ya ɗan zaro ido suna kallonta, Angel tace”Okey,” kafin ta maida duban ta ga majnoon”what about u? Meyasa ka rainata”? da buɗar bakinsa sai cewa yae”I don’t want her to bathe me because she’s so little, nafa girme ta, da ma ba ita ta ke yi min ba, Danish ne yanzu baya nan, Haris yana min da naufal”

Har cikin zuciyarta taji gabanta yaɗan faɗi saboda sunan Danish da majnon ya ambata, nan take taji wata irin kewarshi ta baibaye sassan jikinta, kasa magana tai, idanuwanta bakomai suke nuno mata ba face kyakkyawar fuskarshi, da sauri ta kwantar da kanta ta kifa fuskarta saman pillow, ganin hakan yasa suka fahimci dalilin shiga damuwarta, su kansu da Majnun Ya ambaci sunan Danish sai da zuciyoyinsu suka amsa.

Haris ne yaci gaba da yin magana yana duban su Jamima dake a tsaitsaye gefe da gefen na gadonta

“daga yanzu kada na kuskura na ƙara ganin wani a cikin ku ya raina azeeza, Ƴan ranin wayau, just because u saw her a little girl like u that’s why ku ka raina ta, Let me tell you that even Angel, whom you respect, is younger than azeeza.”

A matuƙar ruɗe Jamimah da majnoon suka kalli haris suna faman zare ido, Mamaki ƙarara akan fuskarsu, Hatta Gabriel da Sarah sai da suka jinjina maganarshi don basu ta6a sanin hakan ba, sai da ya faɗi yanzu,

Cigaba da magana haris yai,”Angel itace ƙaramar cikin mu kafin zuwan ku, tafi kowa ƙananun shekaru, ƴar azeezar nan da kuke rainawa yayarku ce,…….” muryar Jamima da kokwanto ta furta”amma ae ƴar ƙaramace ko, meyasa ita bata yi tsawon Angel ɗin mu ba”? Hada ruƙe qugu tana magana.

Kafin haris yabata amsa deeja ta kar6e da cewa”Saboda haka Allah ya halicce ta, baki ga banbancin da ke a tsakanin kowannan mu bane? Wani yana da tsawo wani Jiki wani mara ƙiba, ahaka kowa da shekarunsa” da alama jamima bata fahimci me take nufi ba, Majnun sarkin mahaukata yace”to itama taje Allah ya ƙara mata tsawon mana sai ta koma kamar Angel” bismilla parveen tai tare da yunƙurawa ta sauko daga saman gadonta, ta rarumi pilow, majnun na ganin ta yi hakan ranshi ya bashi cewar shi zata buga, aiko da gudu ya nufi sashen toilet ɗinsu yana dariya, Sai da tafara zuwa ta kar6i kayanshi da azeeza ta jefar ƙasa ta ruƙo su da hannu ɗaya, yayin ɗayan hannun ke ruƙe da pillown data ɗauko Tabi bayan shi Cikin sashen toilet ɗin, Bata jima da shiga ba suka jiyo sautin kukan shi yana zazzaga mata masifa.

Murmushi kowannan su ya saki, har lokacin Azeeza na zuƙunne ƙasa kanta saman gwiwarta, Saukowa daga saman gado Gabriel yai tare da nufar inda take, har ya kusa ya isa muryar haris ta katse shi”me zaka mata” Kallon shi Gabriel yai ba tare daya bashi amsa ba, Ya cigana da tafiya

“Kada ka kuskure kace zaka yi mata magana, shisshigin yayi yawa, wannan fa ba ƴar uwarka ba ce, yakamata kadaina manne mata” rai 6ace haris ke yi mashi magana, ko ta kanshi Gabriel baibi ba, damuwarshi akan Azeeza ne, baya son yaga tana kuka, saboda ƙaunar da ta ke yi mishi, zuƙunna yai agabanta tare da kai hannu ya ɗago da kanta fuskar nan sharkaf da hawaye ta ɗaura idonta akan nashi

“Its okey azeeza, stop shedding ur tears, i don’t know why ki ke son zubar da hawayen ki, akan abunda bai kai ya kawo ba,” hannayen shi ya ɗaura saman fuskarta yana goge mata hawayen, duk sun zuba ido suna kallon su banda Angel da ke ta shan kukanta ba tare da sauti na fita ba, An fama mata ciwon dake damun zuciyarta.

Ganin yaƙi jin maganar shi hada share mata hawaye hakan yasa haris yunƙura ya miƙe zai nufe su, Muryar azeeza na kerma tace”dan Allah haris ka ƙyale shi, ni bansan meyasa ku ka ɗaura mashi karan tsana ba, koda ace Gabriel shine silar abunda ya faru da Danish, bai kamata kuna mishi haka ba, tunda ya nemi yafiyarmu ya gane kuskurenshi, shi kanshi fa bada son ranshi hakan ya faru ba, Angel ta riga ta yi mana bayanin komai……”

Tunkan ta ƙarasa maganarta, deeja ta katse ta da cewa”Azeeza kina da matsala! Tausayin ki bazai ta6a bari ki ga laifin shi ba, ke kowa naki ne, dame gaskiya da mara gaskiya, yanzu dik irin abunda Gabriel yai ma ɗan uwan mu Danish ke baki gani ba? Cikin mu ba wanda bai yi zazzza6in rashin Danish ba, wannan ƙaton Ya haddasa mana baƙin Ciki acikin zuciyar mu, ya naƙasa mana ɗan uwan mu, amma ahaka kike biye mashi, har wankin kayan shi ke kike yi kamar baiwarsa, kamar fa kina ƙara bashi damar da zai cigaba da cutar da mu ne” cikin nuna 6acin rai Deeja ta yi maganar, Dama sun fi kowa tsanar Gabriel ita da Haris, Su biyun nan sun zame mashi ciwon kai da masassara, Deeja da haris tamkar abu ɗayane, Kusan halinsu ɗaya, Idan suka tsani mutun sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya, kamar dai lokacin da Aka kawo Angel da suka addabe ta kafin asasanta, Zafin zuciya ne dasu, suna da wuyar sha’ani sai dai duk da hakan suna da kyakkyawar zuciya.

Ranshi bai ta6a 6aci ba irin na yau, Zame hannayenshi yai daga saman fuskar azeeza da yake share ma hawaye, Ya miƙe tare da juyawa yana kallon haris dake a tsaye yana jifar shi da kallon tsana.

“Bafa tsoron ku nake ji ba, sannan ba ƙarfi kuka fi ni ba, duk abunda ku ke yi min na ƙyale ku ne saboda nasan laifina ne, na rasa gane ku wasu irin mutane ne, sai kace ba kusan tsautsayi ba, nifa bada son raina na aikata mashi hakan ba! yadda ku ka ji zafi acikin zuciyarku bai kai kwatankwacin wanda naji ba, a lokacin dana naushi idonshi, ga Angel nan ku tambayeta irin tashin hankalin dana shiga ae ita tasa komai, har cewa nayi ta cire idona ta sanya mashi duk don saboda tausayin shi da naji………” kasa ƙarasa maganar yai, idanuwanshi cike tab da kwalla, jikinsu Hanna ba ƙaramin sanyi yayi ba, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalaman shi,

shigowa cikin ɗakin parveen tayi hannunta ruƙe dana majnun da ta sanyawa kaya, har sun shirya, Ganin Gabriel dake tsaye ido ya canza launi ga kuma haris agabanshi, hakan yasa ta dan dakata da yin tafiyar tana kallonsu,

“kuna ɗaukata tamkar wani maƙiyin ku, nifa ba bare bane acikin ku, kawai don bamu arayu atare bane sai daga baya na tsinci kaina acikin, da ku da ni duka prisoners ne da ƙaddara ta haɗa mu rayu a wuri ɗaya, akan me zan cuci wani acikin ku? Babu wanda yafi wani fa acikin mu! Bana jin daɗin juyamin baya da ku ke yi, nifa mutunne ba dutse ba, ina da zuciya a ƙirjina, dole in ji zafin ƙiyayyar da ku ke nuna min, meyasa nima baza ku soni ba ku ƙaunace kamar yadda kukeson junan ku? Yai tambayar cikin ƙunar rai yayin da ya ke bin kowannansu da kallo.

“Hatta azeeza da take ƙarama acikin ku tafi hankali, ita da Angel, sune waɗanda nasan ba za su ta6a juyamin baya ba, kuma ɗin rashin fahimta ne, a bun da baku sani ba, Danish shine silar da hakan ta faru, mun samu sa6ani dashi, ya sanya hannu ya shaƙe min wuyana, nayi nayi ya saki yaƙi saki kamar zan mutun a lokacin koda ace wani daga cikin ku ne yaji an shaƙe mashi wuya za’a kashe shi cikin fitar hayyaci zai iya yin komai donya ƙwaci kanshi, to nima shine abunda nayi at end nazo ina danasani, da ace da son raina na aikata mashi hakan ai baza ku ganni ina jinya ba,”

Haƙiƙa kalaman Gabriel sun yi matuƙar yin tasiri acikin zukatansu, duk sai su ka ji ba daɗi irin wariyar da suka nuna mashi.

Hannu yasa ya share hawayen dake akan fuskarshi, Idonshi akan na haris yace”ina ƙara baku haƙuri, idan ma hakan bai yi maku ba, zan duƙa saman gwiwowina in roƙe ku akan ku yafe min, kai idon ma kuna so ku cire min idona ne don ku huce takaicin abunda nayi maku to gasunan, ku yi abinda ku ka ga dama, amma karkuce zaku raba ni da azeeza, saboda tana bani kulawa, ina jinta tamkar ƴar uwata Gabriella,”

Yana kawo nan a maganarshi, Ya zube saman gwiwowinsa, Da sauri azeeza ta miƙe tana roƙonshi akan ya tashi tsaye ya daina zubar da hawayen shi.

“Kada ka damu, komai ya wuce awurina, koda ace su basu yafe maka ba ni na yafe maka” acewar Hannah. Tana rufe baki parveen ce”tunda dai ya riga ya faru, bamu isa mu canza komai ba, don haka nima na yafe maka” Ɗaya bayan ɗaya suka dinga cewa sun yafe mashi, Mutun ukune basu tanka mashi ba, Haris da deeja da kuma Naufal, Su sunce sai an dawo musu da ɗan uwansu sun ga awani hali yake ciki tukunna zasu Yafe mashi, a ƙalla ya ji sanyi aranshi ganin dayawan su sun yafe mishi sunce zasu cigaba dayi mashi magana bazasu ƙara nuna mashi wariya ba, Yaji dadin hakan ga kuma Azeezar shi mai sanya shi farin ciki, itama tana Atare da shi, bayan komai Ya lafa, Gabriel Ya miƙe ya nufi sashen toitet ɗinsu, don yayi wanka,

ƙarasa shigowa cikin ɗakin parveen ta yi hannunta ruƙe da na majnun don tun ɗazu tana a tsaye tana sauraronsu Gabriel ganin sun samu maslaha atsakanin su yasa ta motsa, sai da ta fara wurga pillown hannunta saman gado tukunna ta nufi jamima da ke a tsaye gefen gadon Angel ta damƙo hannunta, ta haɗa su duka biyun takaisu gaban Gadon azeeza a lokacin harta koma ta zauna.

“Ku bata hakuri idan ba so kuke ranku ya 6aci ba,” acewar parveen, Ɗagowa su kai suna kallon fuskar azeeza da tayi jawur.

“Idan har baku bata haƙuri ba, Yau babu wanda zan bari yaci abinci acikin ku, kunsan dai halina tau,” jin haka yasa suka haɗa baki wurin furta”We’re really sorry sister azeeza ba zamu ƙara ba”

hada kama kunnansu kamar zomaye, hakan da su ka yi ba ƙaramin dariya yabata ba, Miƙa ma Jamima hannu tayi”muje inyi maki wankan tun da mun shirya” Ba musu ta amsa mata da toh, Saukowa azeeza tayi daga smaan gadon ta ruƙe hannun Jamima acikin nata, suka nufi toilet, Bayan shigarsu, Parveen ta koma saman gadonta tana yi musu sambatun yunwa take ji, majnun kuma ya nufi tsakar ɗakin su Yanata Yin ƴan tsalle tsallen shi.

Ɗakin yai tsit na ɗan wani lokaci, Fitowa daga cikin sashen toilet dinsu Gabriel yai su azeeza na a biye da bayanshi ita da jamima da ta yi ma wanka, Sai murmushi suke saki Shigowasu yayi dai dai da turo ƙopar ɗakin su da aka yi, Gaba ɗaya hankulan su suka koma akan benan, Banda Angel data mannewa pillow, ta kammala shan kukan nata, ta lallashinta kanta ta yi shiru, Ajiyar zuciya suka sauke ganin Giants ne masu kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da Wooden trays kamar yadda aka saba, A jere suka nufi ɗakin bayan sun ajiye su saman carpet, suka ja da baya tare da ƙamewa,

“Abinci ya iso, wanda bai wanko bakinshi ba, yai sauri yaje toilet muna jiran ku” Hannah ce tai musu magana, su ka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya su ka dinga miƙewa suna shiga sashen toilet ɗinsu, within minutes kowannansu ya dawo suka zauna saman carpet domin cin abinci, ganin taƙi tasowa tazo suci yasa Deeja ɗaga murya ta ƙwala mata kira”Angel Ki taso muci abinci” shiru bata tanka mata ba, haris ma yai magana amma shiru taƙi tasowa, naufal yace su ƙyale ta, inyaso sun ajiye mata nata acikin kwando,

Har sun yi nisa da fara cin abincin, kowa ya natsu yana ci, Majnun sai cusawa ya ke yi abankinshi Parveen nata jifar shi da harara ganin yadda yake yin cin mugunta.

Babu wanda ya lura da ita, Saukowa tai daga saman gadonta fuskarnan sharkaf da hawaye ta yi jawur da ita, tafiya take yi kamar zata kife ƙasa saboda rashin kuzarinta, bata nufi ko’ina ba sai wurin Giants dake a tsaye kamar dakarun Yaƙi.

Dab dasu ta tsaya kamar zata faɗa musu, fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin, zuciyarta a bushe take, muryarta a sanyaye ta soma yi musu magana

“Bawani abu ya kawo ni wurinku ba, so nake ku faɗamin, yaushe zaku dawo mana da ƴan uwanmu? Batool shiru har yau, Danish kuma bansan awani hali yake ciki ba, ni dai don Allah na roƙe ku, ku taimaka ku faɗamin awani hali suke ciki, shin suna raye ko sun mutu ne, idan naji sai in haƙuri in fidda rai……” tun da Angel ta soma yi musu magana Hawaye nabin fuskarta, gaba ɗaya muryarta ta janyo hankalin su Mubeen akanta, tuni sun dakata da cin abincin suna kallonta, an rasa me buɗe baki ya dakatar da ita.

Girgiza kai ta yi tare da lashe hawayen daya gangaro saman la66anta da harshenta, kafin taci gaba da cewa”wai ku ba zaku ta6a aikata abun kirkiki ba arayuwarku? Haka zaku ƙare wurin aikata zalunci…….” muryar Haris ce ta katse mata maganarta

“Angel, pls ki matsa daga wurinsu! Kodan saboda mu, idan wani abu ya same ki mu zata shafa, mun rasa mutun uku acikin mu yanzu idan kema wani abu ya faru da ke ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance’? Fashewa tayi da matsanancin kuka, azeeza tuni ta kama yin kukan itama.

Cikin shessheƙar kuka Angel tace mashi”don bakasan yadda nake ji acikin zuciyata bane, ni ƙwara ma su kashe shi in huta, da irin wannan rayuwar mara amfani…..” daƙyar ta ƙarasa maganar saboda wani irin jiri da ta soma gani acikin idanuwanta, ƙirjinta yai mata nauyi tamkar zai dare biyu, hannu ɗaya tasa ta dafe kanta, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Gabriel saurin miƙewa shi da yake a zaune ƙarshen carpet din dab da inda suke hannu biyu yasa wurin tarbeta, Ya ɗauke ta Ya nufi Gadonta, a sama ya kwantar da ita, hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, abincin ma ya fita aransu, duk suka miƙe da sauri suka nufi Gadonta don ganin meke faruwa da ita, Mutun biyu suka rage kan abincin, majnun da Jamima, kallon juna su ka yi kowannansu ya cunkusa abinci abakinshi, Suna tauna suna magana

“Ki ɗauko kwandon batul mu ɗibar masu abincin kada waɗannan dodonnin su tafi dashi,” Majnun ne yai mata magana, harara ta wurga mashi”Kai bazaka je ka ɗauko ba, saini,” ƙarasa cinye abincin bakinsa yai tare da yunƙurawa ya miƙe ya nufi gadon batul hada ɗan gudunsa, Ya zuƙunna a gaban ƙarƙashin gadon ya zaro kwandon da sauri ya dawo ya zuƙunna kamar mutumin kirki, Ya dinga kwasar abincin Yana zubawa ciki komai Ya haɗe musu kusan Duka ya kwasar musu har saida kwandon yai soro, ya ɗago ya kalli Jamima dake ta tura plaintain chips abakinta.

“Tun da ni na ɗauko kwandon, Ke zaki maida yanzu” ta6e baki tayi”ae bani da ƙarfin iya ɗaukarshi, faɗuwa zanyi ƙasa, kai ka ɗauka mana” Girgiza kai majnun yai kamar babban mutun Yasa hannu ya ɗauki kwandon, Ya nufi ƙarƙashin gadon Ya tura shi ciki, yana ƙoƙarin miƙewa Yaji muryarta abayanshi”Gashi na ɗauko” kallonta yai, Robobin ruwa ne ta rungumo guda uku a ƙirjinta, sai yatsina fuska take yi, Hannu yasa ya kar6a Ya tura a ƙarƙashin gadon, yace mata ta kwaso sauran, Ta koma ta daukosu, Ta miƙa mashi ya kar6a ya ajiye musu, babu wanda Ya tuna da abinci ba su san ma sun ajiye musu ba, Hankalinsu gaba ɗaya yana akan Angel sun kewaye gadonta damuwa ce danƙare akan fuskokinsu, sai kiran sunanta suke yi tare da jijjiga jikinta don ta farka amma taƙi motsawa, hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankalin yai ba,

“Angel! Pls ki tashi! Dan Allah ki farka!’ azeeza ce keta magana tana matsar kwalla, Deeja tace”Allah yasa ba waɗancan mugayen bane su ka yi mata wani abu ba,” haris yace”nima abunda na ke hasashe kenan”

muryar Gabriel ce ta janyo hankalinsu akan shi” Ba abunda ya same ta, Yunwa ce take ji, ku miƙo min ruwa” yatsina fuska Naufal yai”kawai saboda tana jin yunwa saita yanke jiki ta faɗi? A ina ka sami wannan ilmin” Banza Gabriel yae dashi bai tanka mashi ba, Haris yace”Shisshigi ne kawai,” Dogon tsoki Gabriel yaja tare da kallon Azeeza da ke ta yin kuka yace ta ɗabo mashi ruwa, Kafin tayi yunƙurin zuwa ɗebowa Sai ga majnun bakin gadon hannun shi ruƙe da bottle water yaji suna nema shine ya kawo musu, karo nafarko kenan da majnun ya ta6a yi musu abun kirki.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Gabriel ya kar6i robar ruwan, ya samu wuri daga gefen gadonta ya zauna tare da sanya hannun shi ɗaya ya ɗago da kanta ya ɗaura shi gefen chest dinshi, azeeza ce ta buɗe mashi murfin robar hannun shi ta ruƙe a hannunta, Ya kanga ma Angel robar abakin ta, Duk suka baza ido suna jiran ganin in zata motsawa, aiko kamar jira take taji an daura mata robar ruwan abakinta, ta dinga kur6arshi kamar zata shaƙe maƙoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!

Saboda tsabar kunyar da ta kama su haris da Naufal Sai gashi sun sadda kansu Ƙasa, Kusan rabin ruwan ta shanye, wani irin yunƙurin amai ne yazo mata, saboda rashin ƙwarin jikinta bazata iya miƙewa taje toilet ba, asaman rigar Gabriel ta shiga kwara aman, tsananin tausayinta duk ya kamasu sai sannu suke yi mata, kamar zasu ɗauke mata ciwon haka su ke ji, duk da irin aman da ta ke yi ajikinshi bai ji komai ba, ko irin ƙyanƙyamin nan, saima ƙara ruƙe ta da ya ke yi da hannayenbshi don tuni ya miƙa ma Azeeza robar ruwan, bakomai ke fita acikin bakin nata ba face kayan marmarin data sha tun jiya da zallar ruwa, Sai nishi take yi tana faman lumshe idanuwanta.

“Sannu sister, Allah ya baki lafiya” acewar javed, Suma saura suka ƙara yi mata ya jiki, sam ta kasa motsa la66anta donta amsa musu, daƙyar tafara magana kamar ma sambatu ta ke yi musu tana ambaton sunan Danish da batul, miryar deeja ce tasa ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta

“Angel ki daure kidaina sanya damuwa aranki, Idan kina yin hakan ba ƙaramin raunata mata zuciyoyin mu kike yi ba, ke da kika saba ƙarfafa mana gwiwa, amma yau kece kike neman zaucewa saboda rashin su, kowa ya jure amma kin gaza, Ya ki ke so muyi”? Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi mata maganar.

Cizon la66a ta ta yi ba tare data iya furta mata komai ba, ruwan hannun Azeeza ya kuma kar6a Ya kuskure mata bakinta dashi, tare da wanke mata fuskarta, Kafin ya miƙa ma Azeeza robar tasa hannu ta kar6a,

“Akwai sauran abinci”? Yai tambayar yana kallon su, har suna hada baki wurin rabka salati suna faɗin”Mun manta Bamu ɗebi abincin ba, gashi giants sun tafi dashi” Kamar zasu fashe da kuka.

Chinonsu dake sauraronsu shida jamima, jin suna neman abinci yasa Suka nufi ƙarƙashin gadon Batul atare suka ruƙo hannun kwandon, suka nufo wurinsu, tunkan su ƙaraso Ƴan uwan nasu suka ga uban tulun abincin da suka ajiye musu, Wani irin farin Cikine ya lullu6e su, Ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, Bakin parveen washe da annuri tace”Kai ba dai kune ku ka ɗebi abincin nan ba”? Har suna haɗa baki wurin furta”Mune nan muka ajiye shi” with proud su kai maganar, suna ƙarasowa parveen ta kar6i kwandon daga hannunsu ta ruƙe shi, tace da Azeeza ta ɗauko Mayafi da zasu goge aman da Angel tay, ta masa mata da toh, ta juya ta nufi akwatin kayansu kafin ta dawo Gabriel yace ta miƙo ma shi abunda zai fara bata ta ci.

Zura hannu tayi cikin kwandon ta ɗauko meat balls ta miƙa mashi, ya kar6a ya soma bata abaki tana ci, ba ƙaramin daɗin shi su ka ji ba ganin yadda ta zaƙe tana ci.

Dawowa Azeeza tai hannunta ruƙe da ɗan mayafi ta shiga goge mashi aman da Angel ta yi a jikin vest dinsa, da saman laps ɗinsa, bayan ta kammala tace mashi ya curo mata taje ta wanke mashi, murmushi yaɗan saki tare da kallon ta yace”bakya gajiya da yi min wanki Azeeza, kibar shi zan wanke da da kaina” maƙe mashi kafaɗa tai alamar bazata bari ba, yace toh bari na ƙarasa bata abincin, sai na baki rigar,

sai da ya kammala bata ya kwantar da Angel kamar me bacci ta lumshe idanuwanta, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, Kowa ya nufi gadon shi ya zauna, parveen ta ɗauki kwandon taje ta ajiye musu a ƙarƙashin gado, miƙewa Gabriel yai daga gefen gadonta, Ya tu6e rigar jikin shi ya miƙa ma azeeza tasa hannu ta kar6a, ta nufi toilet shima yabi bayanta don ya watsa ruwa ma jikinsa.

Bacci mai daɗi ya ɗauki Angel, Su majnun dake shirin yin wasa atsakar ɗakinsu, parveen ta lalla6asu akan su yi shiru kada su tada Angel tunda sun ga bata da lafiya, suka amsa mata da toh, Kafin marece yai kowannansu na zaune, wasu sun ɗan kishingiɗa da niyar bacci ya ɗauke su, rabi da kwatansu idanuwansu arufe yake, duk don saboda Angel sunyi tsif babu mai magana, gudun kada su katse mata baccin ta.

💔PRISONERS💔

Kunnuwansu ne suka soma jiyo musu motsin buɗe ɗakin su, Ras gabansu Ya faɗi ba tare da sanin dalilin hakan ba, kusan atare kowannansu Ya buɗe idanuwanshi Hankalinsu gaba ɗaya ya koma Kan staircases ɗin, Jira suke suga waye zai shigo ko wani ne za’a dawo musu dashi tunda an riga an kawo musu abinci, Yadda suke zazzare idanuwansu akan ƙafafuwan masu shigowa tamkar ƙwayar idanuwansu zasu faɗo ƙasa,

Bakowa bace face tsohuwa Zafreen Hannunta ruƙe da sanda cikin shigarta ta jajayen kaya, Rabin fuskarta rufe yake, Iya idanuwanta ne awaje, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, Abayanta Wasu Gabza gabzan Giants ne Su biyu garada masu ɗauke da Star 2 agaban baƙar rigar jikinsu, Takun tafiyarsu yadda kasan na wani namun dawa.

Wahalallan yawu kowannansu Ya haɗiya, hakanan suka dinga jin bugun zuciyarsu na hauhawa, Chinonso dake ta tsalle tsalle ganinsu yasa shi yin saurin nufar gadon parveen ya haye ya zauna gefenta hada ɗaura kanshi saman kafaɗar ta, Azeeza kuwa cikin sanɗa ta duro daga saman gadon ta faɗa ƙarƙashinsa ta la6e jikinta nata kerma, ganin ta 6oye yasa jamima lalla6awa itama ta sauko daga saman gadonta, ta shige ƙarƙashi. sauran kuwa ba wanda ya motsa kowa yasha jinin jikinsa.

Lokacin da mai girma tsohuwa Zafreen ta ƙaraso Tsakiyar ɗakin nasu, Sai kowannansu ya sadda kanshi ƙasa ba tare da sun furta komai ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, duk sun kame kansu.

“Fatan na same ku lafiya” tai tambayar tana kallon fuskokinsu, wasu daga cikinsu ne suka samu damar amsa mata da cewa”Muna lafiya” tace”tsawon lokaci banzo na duba jikokina ba, saboda uzurirrika da suka yi min yawa, sai yau na samu damar leƙo wa, hope you’re happy to see me”

kamar waɗanda aka ma dole haka suka furta mata”eh” Jinjina kai ta ɗanyi yayin da take cigaba da binsu da kallo kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar haris Ya ɗaure fuskarshi sosai, Idonshi na kallon ƙas

“Zuwan nawa ba lallai bane yayi maku daɗi ba, domin kuwa nazo ne na raba ku da zaratan samarin dake a cikin ku” a firgice suka ɗago suna kallonta la66ansu na kerma ba tare da wani ya iya furta wani abu.

“Haris, Mubeen, Naufal, Javed, and Gabriel, A kan ku nake magana, Ba’a ta6a zuwa an ɗauke ku ba, wannan karan kurkukun ƙaddara ya buƙace ku, Don haka ba tare da 6ata lokaci ba, kowannan ku ya sauko daga saman gadon shi, A jere zaku tafi,” A matuƙar ruɗe su parveen ke kallonsu, wani iko na Allah babu wanda ya musa acikinsu, Kamar yadda ta basu umarni haka suka sauko a jere suka nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, Sai waiwayon ƴan uwansu suke yi, idanuwan kowannansu cike tab da kwalla kai daga gani bada son ransu suke yin tafiyar ba, Sarrafa su aka yi, Hankalin Deeja idan ya yi duba toh ya tashi, Ba ita kaɗai ba hatta sauran matan da ke acikin su, Gashi sun gaza ɗaga koda yatsan su, Sai hawayen da ke gangarowa ta cikin idanuwansu.

“Albino, Follow their back” tai maganar ba tare da ta juya ta kalli inda chinonso yake zaune gefen parveen, Jikinshi nata kerma ya sauko daga saman gadon idon parveen akanshi, Yana tafiya yana waiwayonta kamar zaiyi tuntu6e, ahaka harya haura saman starcases ɗin Yabi bayansu Haris, Tashin hankalin da ba’a sama shi date! Kaf an kwashe mazansu, Cikin su 20 yanzu saura mutun goma sha ɗaya, Shin Ina za’a kai su haris?

Tsayar da idanuwanta ta yi akan gadon Angel dake ta sharar bacci, babu alamun zata farka,

“Ba’a san ƙaddarar kurkuku da rauni ba, tana bacci gwanin ban sha’awa, nan badajimawa ba, zamu buƙace ki” Tayi maganar tare da matsawa dab da gadon Angel Ta ɗaura sandarta asaman ƙafarta, Nan take angel tayi wani irin juyi ta fuskanci ceilling ba tare data farka daga baccin ba, A saman ƙirjinta zafreen ta ɗaura sandar hannunta Saitin zuciyarta, Wani irin numfashi Angel ta shiga fitarwa ahargitse, Su Deeja dake kallon abunda ke faruwa kamar su ɗaura hannu aka su fasa ihu, Sai dai kash babu mai iya motsawa a cikinsu, Sai da Angel tagama banƙarewa kamar zata koma zombie, tukunna tsohuwa zafreen ta sauke sandar daga saman ƙirjinta.

*Yayin da ni kuma na ajiye alƙalamina✍️ *

*This week posting sai a slow, cos ina fama da ciwon hannu, abunda yasa ban dakata da yin free ba, saboda book one baizo inda zai ƙare ba, shiyasa nake ta ƙoƙari ina yin long page don in samu in ƙare shi, idan kunga banyi update ba already na faɗa maku, zanyi iyakar bakin ƙoƙarina idan abun yaci tura zan dakata in tafi hutun da nace zanci, inyaso daga baya ko cikin days na hutun ne zan sakar maku sauran free pages na part one, Fatan za’ayi min uziri a kuma tayani da addu’a Allah ya bani ikon kammala shi lafiya,Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

No comments