Kurkukun Kaddara 8
*E8*
Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom É—inta da ta bari a buÉ—e, dogon numfashi ta ja tare da
buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta.
Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu É—umi, harshenta ta sanya ta É—an lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta.
DaÆ™yar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko’ina ta yamutse.
A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet É—inta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta.
Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet É—in kayan su, buÉ—ewa ta yi tare da zura hannu ta É—auki hijab É—inta, ta sanya a jikinta.
Saman dardumar dake shimfiÉ—e ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta.
Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da É—aga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu’o’inta daga Æ™arshe ta rushe da matsanancin kuka tana faÉ—in. “Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge,” Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair.”
Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio.
Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio É—in saman bencin ya mike ya tunkare ta, “Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya.”Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta,
“Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi,” Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta.
Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta.
Cikin sanyin murya yace”Kiyi haÆ™uri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin Æ™oshin lafiya, babu abin da zai faru da shi.”
Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan.
Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin.
Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate É—in, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras!
Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, “Assalamu alaikum”
Tunkan takai Æ™arshen maganar taga ya É—an firgita, sai daya kalleta tukunna YaÉ—an saki fuskarshi yace”wa’alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?”
Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheÆ™ar kuka ta ce, “Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya,” Tana kai Æ™arshen maganarta baba maigadi ya ce, “Innallahi Wa’inna Ilaihir raji’un!”
A ruÉ—e ta ce, “Baba lafiya?” Cikin tashin hankali ya ce, “Æ´ar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin É—akina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren Æ™arfe É—aya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga É—akina, koda na fito naga gate a wangale, na leÆ™e banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi.”
Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi,
“Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a Æ™arkashin shi bai ta6a lekawa koda Æ™ofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya É—aure mun kai, ba shi kaÉ—ai ya tafi ba. Hada ANGEL!” A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa’inna Ilahir raji’in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!” GabaÉ—aya ta bi ta ruÉ—e, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati.
Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba.
Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna.
“Wai meke faruwane É—an ladi”malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse.
Baba maigadi ya ce, “Tun É—azu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daÉ—in ji.” Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi.”
Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, “Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya Æ™ure mana”!!
Jinjina kai baba maigadi ya yi” ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu É—an Æ™ara jira kaÉ—an zuwa anjima”
“Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station É—in” a cewar É—an ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buÉ—e bakowa
Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom É—inta ta shige, jikinta na kerma ta É—auki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,
Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka É—aga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, “Assslamu Alaikum daughter…” Tun kafin ya kai Æ™arshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita…”
Muryar Abie a ruÉ—e ya shiga kwala mata kira.” Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buÉ—e baki ki yi mun magana!”
Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheÆ™ar kuka”a…Abie..Uzair da Taj..” katse ta ya yi da cewa.”me ya faru dasu? Wani ya rasu ne’
“A’a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren Æ™arfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe É—aya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali.”
Lamarin ya girgiza abie sosai,”
Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, “ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle É—inki, ki É—an Æ™ara haÆ™uri.” Cikin shessheÆ™ar kuka ta ce”To Daddy, saina jika “ya ce” ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba” Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta.
Wuraren Æ™arfe huÉ—u na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la’asar bata cire hijabin jikinta ba,
jiniyar motor Æ´an sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faÉ—i, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan,
A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne,
Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai É—aukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin Æ´an sanda ba, Sai gashi É—ungurugum ya taho dasu Gidan,
Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace”Daughter Kece kika koma haka”? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta Æ™araso ya buÉ—e mata hannayen shi ta faÉ—a a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna”wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna,
Uncle Bash Æ™usa yace”Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba”?
Cikin shessheÆ™ar tace”Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe”
Jinjina kai yayi”okey, yanzu ki natsu ki faÉ—a mana taya akai yabar gidan without your knowledge”?
Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta,
Dco ya kalli Ramlat Jami’ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miÆ™e ta bi bayan aneelerh cikin bedroom É—inta,
Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje,
Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu,
Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta
“Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,”acewar Jami’ar binciken,
Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai É—umi tace”Bana jin daÉ—in jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu,”
Ramlat tace”Ki daure kici, lafiyar ki muke buÆ™ata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haÉ—in kanki wurin yin investigation É—inmu”?
Takai Æ™arshen maganar a lokacin sun dawo Cikin falon, Hankalin Dco da na sauran jami’an ya dawo kansu, mahaifinta kuwa jikinshi ba Æ™aramin sanyi yayi ba, ganin yadda É—iyar shi ta rame, tamkar ba neelerh É—insa ba,
A gefen abie ta zauna tare da kwantar da kanta saman kafaÉ—ar shi, Ramlat Ta kalli dco tace”Sir, bata da koshin lpy, kuma ta sanar dani cewa tun jiya bata Ci komai ba,”
Uncle bash yace”Idan har bata ci abinci ba, ba zamu iya samun bayanan da muke bukata ba awurinta,” Yayi maganar eyes dinshi akan Abie, kafin ya mayar dasu kan Ramlat yace”ki duba frigde nasan baza a rasa abunsha ba, Ki É—auko mata tare da ruwa me sanyi”Amsa mashi tayi”okey sir” kafin ta juya ta nufi fridge É—in dake A falon”
Hanmu tasa ta buÉ—e frigde din, Lemuka ne a jere masu sanyi, hada fura da youghurt, fresh milk ta dauko mata tare da ruwa”ta ruÆ™o bottles din a hannunta ta dawo ta É—aura su asaman C table din dake agaban sofa din da aneelerh take,
Uncle bash yace”Aneelerh ta shi kisha,”batare da musu ba, Aneelerh ta mike zaune, Takai hannu ta É—auki milk É—in ta buÉ—e ta kwafa abakinta, ta shiga É—aÉ—É—akarta, makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!!
Abie yace”Ki sha a hankali, kada ki shaÆ™e” janye bottle din tayi daga bakinta tana faman sauke ajiyar zuciya, lallai ba Æ™aramar yunwa take ji ba, bayan ta ajiye milk din Abie ya dauki bottle water me sanyi ya mika mata, hannunta na kerma ta buÉ—e mufin ta kwafa abakinta, A hankali take shan ruwan harta kammala, Sai gashi ta É—an samu natsuwa,
Uncle bash yace”Aneelerh kiyi mana bayanin yadda komai ya faru a daren jiya, muna sauraronki”
Ganin yadda zufa ke keto mata, abie yace ta cire hijabinta”hannu tasa ta É—ebe hijabin, dama akwai Kallabin data É—aure kanta da shi,
A tsanake ta soma Yi masu Bayani tiryan tiryan
“Ji wuraren Æ™arfe tara, nafarka ban samu uzair a saman gado ba, nayi tsammanin ko ya shiga toilet ne amma ko da na duba baya a ciki, na yanke shawarar zuwa na tambayi megadi,koda naje wurinshi yace mun Yaga lokacin da Uzair ya fita acikin motarshi, kuma har magana sunyi da shi kafin tafiyar shi, koda jin haka na dawo cikin gida na É—auki wayata na kira layin uzair tana ringing amma uzair bai É—aga ba, a ruÉ—e na ajiye wayar na fito na nufi gidan taj, ina zuwa na shiga gidan, A falo nayi mashi sallama, ya fito daga É—akin shi, harma yayi shirin kwaciya, nake faÉ—a mashi Game da tafiyar uzair Æ™arfe 9 na dare na farka banganshi ba, Nayi tunanin ko ya kirashi awaya, saboda kusancinsu dana sani, Uzair zai iya 6oye mun abun amma bazai iya 6oyema Taj ba, Shiyasa na tambaye shi,A wannan lokacin taj yace na jirashi ,Zaije room dinshi ya kira shi awaya, na tsaya ina jiranshi, koda ya dawo na tambaye shi ya kirashi,yace mun in kwantar da hankalina duk inda yake ayanzu yasan yana akan hanyar dawowa ne, ba don na yadda da kalamanshi ba, na dawo gida zuciyata duk a harmutse na kwanta, Ko a daren sai da taj ya kira layina, ya Æ™ara kwantar mun da hankalina, a wannan yanayin bacci yayi awon gaba dani,
Shiru ta É—anyi tana mayar da numfashi, kafin taci gaba da cewa”da safe na farka wuraren Æ™arfe tara, still uzair bai dawo ba, Nan ma hankalina ya Æ™ara tashi, Na yanke shawarar zuwa Wurin taj don inji idan sunyi waya da uzair, koda ace ya kirashi tsakar daren jiya, Ina fita daga gida na nufi gidan taj, tunkafin ma naÆ™arasa naga baba maigadin gidan atsaye ya jingina bayanshi jikin Gate din gidan fuskarshi da alamun damuwa atattare da ita……………”Komai daya faru saida aneelerh ta sanar dasu, lokacin da aneelerh ta kammala zayyana masu komai, Lamarin yayi matuÆ™ar girgizasu, ipo Yace”akwai matsala, Uzair ya fita gida Æ™arfe 9 na dare, Shi kuma taj ya fita tare da Æ´arshi Æ™arfe É—aya da rabi nadare? tabbas wani Babban al’amarine ya afku”
Ramlat tace”Kuma dukansu atare da wayoyinsu suka fita”?
Aneelerh tace”Shi uzair da wayarshi ya fita, Amma shi Taj banda masaniya akan hakan”
Dco yace”Aneelerh zaki yi mana jagora zuwa gidan Taj don mu fara gudanar da binciken mu”Amsa mashi tayi”toh” kafin suka miÆ™e gaba É—ayansu suka É—unguma zuwa gidan Tajuddeen, A bakin gate Dco Yace ma malam Garba yabi bayansu, Don shima zasu buÆ™aci jin Æ™arin bayani awurin shi, Lokacin da suka Æ™araso bakin gate É—in gidan Tajo, Baba maigadi Na zaune saman benci cikin zullumi, Dco yace shima Yabiyosu Cikin gidan,Ya miÆ™e yabi bayansu,
A falon Gida Taj, Abie ya zauna, baba maigadi da malam garba suka zauna saman Carpet suna jiran tambayoyin da za’ayi masu,
Aneelerh ce ta yi masu jagora zuwa bedroom É—in taj, A bude suka samu É—akin, Da sallama tashiga ciki, Dco da ic da ipo suka mara mata baya,
A tsakiyar Dakin suka tsaya suna bin ko’ina da kallo, Karaf idanuwan Aneeleeh suka sauka akan wayar Taj dake yashe Æ™asan tiles, A ruÉ—e tace”Uncle ga wayar shi anan” A tare police men din suka kai idanuwansu kan abunda aneelerh ke nuna masu,
Hanky Ic ya curo daga cikin aljihun shi, a hankali ya taka zuwa inda wayar take a ƙasan tiles,ya zuƙunna tare da ɗaukota,Ya dago da ita ya juyo da ita, Screeen ɗin wayar ya fashe, sakamakon Bugun tiles da Tayi,
Juyowa Yayi tare da kallon Dco yace”Sir, A hasashe na, Jiya Bayan aneelerh tabar gidan nan, Tajo Ya dawo Ya kwanta har bacci ya É—auko shi, Wuraren Æ™arfe É—aya da rabi na dare, An kira wayar shi, kuma ya É—aga kiran, tabbas an gaya mashi wani abu daya É—aga mashi hankali, wanda yayi matuÆ™ar razanar da shi, har baisan lokacin da yayi wurgi da wayarshi ba, Ya fito daga É—akinshi Yaje ya É—auki É—iyarshi ya gudu da ita,tabbas anyi mashi barazanane, kuma zai iyayiyuwa anyi amfani da uzair wajen razanar da shi”
Jinjina kai dco yayi”tabbas akwai wani 6oyayyen Al’amari, daya faru a daren Jiya, taya za’ae mu gano ainihin meya faru?
Ipo yace”Abu na farko daya kamata muyi shine, mu fara tambayar masu gadin gidajensu A wani yanayi sukayi rabuwar Æ™arshe dasu, sannan Wayar taj, Yakamata A gyarata, kodan mu samu damar bincikar last Call da yayi recieving awannan daren! Sannan zamu duba messages É—in wayarshi, koda ace sun tattauna game da wani sirri dake atsakaninsu shida uzair”
Gaba É—aya sunyi amanna da maganar ipo, aneelerh dae Jikin ta Æ™aura yayi la’asar,Tunda taji hasashen Ic gabanta Ya dinga faÉ—uwa rass rasss! Daurewa kawai take yi,
Cikin falon suka dawo Kowa ya zauna, Ipo Ya kalli É—an ladi baba maigadi na gidan tajo, yace”lokacin da taj zai fita A daren Jiya! Kaine ka buÉ—e mashi gate”Da sauri baba maigadi ya girgiza kai”a’a yalla6ai, Wlh ni bansan ma Ya fita ba, Kwatsam Ina Cikin Bacci sama sama Naji alamun buÉ—e gate, kafin inyi wani yunÆ™uri in miÆ™e inzo in duba,Tuni Ya fuce, Babu shi babu alamar shi, har waje na leÆ™a banga komai ba, na dawo cikin don in duba wurin ajiye motocin shi anan naga ya fita da É—aya daga cikin su, Bayan haka kuma na shiga cikin gidan don inga ko Æ´ar shi angela na nan, sai naga babu ita, nan na gane cewa da ita ya tafi, Wannan shine iya abunda nasani,
Jinjina kai Ipo ya yi kafin Ya mayar da idanuwanshi kan Malam garba me gadin gidan Uzairu,Yace”kaifa?Me ka sani game da tafiyar Uzair”?
Malam Garba yace”Naga lokacin da uzair ya fita, har magana mun yi da shi, Abunda ya faru ina zaune saman benci ina sauraron radio, Sai ga Uzair ya fito daga Cikin gidan, Sai faman sauri yake yi, Ya buÉ—e mota ya shiga yayi mata key,Ya Æ™araso da motar Yana yi mun hon in buÉ—e mashi gate, Na taso Na buÉ—e mashi, har ina tambayarshi ko lafiya, naga zai fita a lokacin da bansaba ganin ya fita ba, ya ce mun babu komai, bazai jimaba yanzu zai dawo, Nayi ma shi Allah ya kiyaye hanya, wannan shine maganarmu ta Æ™arshe da shi,’
Jinjina kai ipo yayi”bayan wannan ko akwai Wani wanda ke yawan zuwa gidajensu?
Har suna haÉ—a baki wurin cewa a’a,
Dco yace”Yanzu Idan munason ganawa da iyayen kowannansu taya zamu same su”? ya yi tambayar yana kallon aneelerh,
Cikin sanyin murya tace”surukaina basa Æ™asar nan tun da jimawa suka tafi suwa south korea amma kwanan nan zasu dawo, Shi kuma taj Iyayen shi Suna zaune a Buzaye, Sun tsufa sosai, Ni aganina baikamata asanar dasu ba, Hankalin su zai tashi sosai,’
“Bazamu sanar dasu ba, Amma Shi taj ina matar shi? Ipo ne yayi mata tambayar,
Abie yace”ae shi Taj tunda matarshi ta haifi Æ´arshi ta fari, ta gudu tabar gidan, Kamar yadda aneelerh ta sanar dani, Acikin bathtub tabar mashi jinjirar,Itace ANGEL yarinyarshi,”
Dco yace”Okey, Shine Yake auran Æ´ar gidan tsohon gomna, Alhaji Ubaid Sani wadata” Jinjina kai abie yayi eh shine,
Ipo yace”Abunda za’ae yanzu, zamu fara bincikar wayar taj, wata’Æ™il asamu wata shaida, Sannan zuwa gobe in Allah yakai mu, Zamu Kira Surukanki, don yakamata asanar dasu halin da ake Ciki, Shima Alhaji ubaid Zamu tuntu6e shi, Sannan Zamu Je gidan Radion da suke aiki, Dole mu binciki kowa dake atare dasu, idan Akayi sati É—aya ba’aji É—uriyarsu ba,Za’a YaÉ—a labarin 6acewar su ta kafafan sada zumunta, Wata’Æ™il adace”
Sun jima suna tattaunawa Da ƴan sandan kafin su tashi tafiya, Sai da suka ƙara kwantarma Aneelerh hankalinta, Sukayi mata alkawarin zasuyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, sosai suka bata baki, kafin Ƴan sandan suka tafi, Ya rage gidan daga ita sai Abie sai su baba maigadi, Umarni abie Ya basu dasu Cigaba da kula da gidajen, Kafin a ƙare Binciken,
Ita kuma aneelerh yace Ta tashi su tafi gida, don bazai barta ita kaÉ—ai agidan ba, ba don taso ba tabi bayanshi, A motarshi suka tafi,drivern gidansu ne ke tukasu,
Tsawon One Week Ƴan sanda suna Bincike akan case É—in, Basu samu komai ba,Har gidan radion su taj sukaje,ÆŠaya bayan É—aya Aka fiddo da ma’aikatan gidan radion suka yi masu tambayoyi,
A Ƙarshen Satin Cikin Weekend Uncle abdallah Ya dawo ƙasar tare da Hajiya adama, duk arana ɗaya Suka shigo garin tare da Alhaji ubaid,
Sun girgiza da jin abunda ya faru na 6acewar Su tajudeen Hajiya adama tasha kuka tamkar ranta zaifita, Haka Alhaji ubaid ya shiga matsananciyar damuwa Musamma da ya ji cewa tare da jikar shi Taj ya tafi adaren Ranar, yarinyar da yake gani tamkar ƴarsa benazir data gudu tabarshi tsawon shekaru, kasancewar shi babban mutun Wanda yasan mutane da dama, tun ranar daya shigo ƙasar Ya kira Cp(Commisioner Of Police)Sukayi zama na musamman Akan case ɗin 6acewar Su tajo,
Gaba É—aya Cp ya tattara Jami’an da suke akan aikin Binciken case É—in, don yaji bayani daga garesu, Bakomai yafi É—aure ma kowa kaiba, face Yadda aka rasa samun wata hujja da zata tona asirin abunda ya faru dasu adaren ranar,
Wayar Taj da suke tunanin zasu samu Wata shaida atare da ita, koda Akaba me gyaran waya ya canza screen É—in, Cikin rashin sa’a suka samu komai na wayar Ya goge, Duk zurfin binciken da Jami’an sukayi, Basu samu koda motocinsu ba, SaÆ™o da lungu na garin da bayan garin dare da rana haka sukayi binciken amma basu samu wata shaida ba, A Æ™arshe binciken ya koma CID,
Labarin 6acewar Su taj ya karaÉ—e social media, Ta ko’ina zancen 6acewarsu a keyi, Mafi rinjayen mutane sunfi tunanin An kashesu ne a 6oye, Tunda kowa yasan su da son fiddo da gaskiya, kota halin Æ™aÆ™a, Wannan yasa mutane su ke Hasashen kodai an kashesu a 6oye ne Allah shine mafi sanin dai dai!!!
Rayuwar Aneelerh gwanin ban tausayi baiwar Allah, Ta jigata sosai, ta shiga mawuyacin hali na rayuwa, ta rame sosai ta Æ™anjame hatta aiki Abie ya hanata zuwa tunda ba Æ™oshin lafiya gareta ba, Rashin Uzair da taj da kuma ANGEL ba Æ™aramin nakasa rayuwarta yayi ba,Tayi kewarsu sosai,a kullum addu’arta Allah ya bayyanar dasu aduk inda suke, saboda su takan tashi tsakar dare tayi nafilfili, tayi masu addu’a Tana kuka,Haka rayuwarta taci gaba da kasancewa, Abinci kanshi sai abie da mami sun tasata gaba tukunna take Cinshi, a karshe da ciwon nata yayi yawa, Dr ya duba ta, Ashe hada laulayin Ciki, Allahu akhbar Abunda suka jima suna rokon Allah ya basu ita da uzair, Ga shi Yau Allah ya kar6i addu’arsu a lokacin da shi uzair É—in Bayanan, Allah sarki rayuwa kenan.
A 6angarensu Hajiya adama kuwa, basu koma south korea ba, Anan suka Ci gaba da zama, saboda halin da ake Ciki na 6atan Ya’yansu ,kullum Cikin zullumi suke,
Akwana Atashi Yau wata É—aya cuff da 6atansu tajuddeen, A lokacin Kowa ya fara sarewa, Tuni Æ´an sanda sun sallami su baba maigadi, makullan gidajensu Yana a hannun jami’an CID, sun ruÆ™e su har zuwa lokacin da zasu kammala bincikensu,
Tun Uncle abdallah Yana 6oye wa Mutanan Buzaye game da 6atansu Tajo, harya yanke shawarar zuwa buzaye don ya sanar dasu halin da ake Ciki,
A ranar da suka shirya tafiya tare da hajiya adama suka Bi jirgin asubahi zuwa katsina state, A hotel suka sauka, A washe gari su ka wuce zuwa buzaye, Lokacin da suka isa garin da safe, a ƙopar gidansu Malam zahiru suka risƙi mutane zazzaune saman tabarma, nan fa hankalinsu ya tashi, Sunzo da mummunan labari Sun riski labarin dayafi nasu ɗaga hankali .
Mutanan da suka samu a ƙopar gidan, Ƴan zaman makoki ne, Allah ya yi ma iyayen tajuddeen rasuwa su duka Biyun, Malam Zahiru ne Ya fara Rasuwa sakamakon Hatsarin Da yayi, Yana Cikin tafiya gefen titi ya dawo daga gona zashi gida, Wata mota ƙirar dab,Ta biyo ta titin da gudun gaske kaitsaye tabi takanshi, Ashe burkin motar ne Ya samu matsala, Duk yadda drivern dake tuƙa ta yaso Ya yi control ɗinta abun Yaci tura,Gaba ɗayansu suka mutu a wannan lokacin,
Tunda labarin mutuwar shi ta riski Yahanasu mahaifiyar tajuddeen taji mummunar mutuwar da Mijinta yayi,nan take Zuciyarta ta buga ko shurawa batayi ba, innalallahi’wa’inna ilahirraji’un!!!Uncle abdallah yaji mutuwar É—an uwansa,duk yadda yaso ya jure hakan ya faskara tamkar Æ™aramin yaro haka ya dinga kuka,mutane suna lallashinshi,
Hajiya adama saboda tsabar kiÉ—ima har suma saida tayi, Ciwo gadan gadan Ya taso mata, A nan gidan deeje suka xauna mahaifiyarsu Uncle abdallah, ita kanta deeje batasan inda kanta yake ba Tun bayan rasuwar malam Zahiru Ta kamu da ciwon paralyse, Laraba Æ™anwar yahana su Ce ke yin jinyarta, da wasu daga cikin Æ´an uwansu na nan buzayen, Kafin Barin su uncle abdallah buzaye, Itama deeje Allah yayi mata rasu wa, Wa’iyazubillah Babu wanda bai tausaya ma Uncle abdallah ba, lokaci É—aya ya rasa ya’yan shi da suka 6ace,Ya rasa ya’yan shi da matar sa yanzu kuma Yayi babban rashi na mahaifiyarsu deeje, Lamarin dai babu daÉ—in ji!
Kusan wata É—aya su ka yi A buzaye kafin suka tattara yanasu yanasu suka koma Jos,
Zaman Æ™asar gaba É—aya ya gagaresu, Babu wani Labari me daÉ—i, a Æ™arshe suka tattara suka koma south korea, Cike da zullumin Me zai biyo baya, Don sunyi magana da Ipo, ya yi masu alÆ™warin duk halin da ake Ciki game da bincikensu taj zai kira su awaya ya sanar dasu, Shima Alhaji Ubaid, Sun Æ™are magana da Jami’an dake bincike a kan case É—insu Tajuddeen, sun yi mashi alÆ™warin zasu yi iyakar bakin Æ™oÆ™arinsu,wurin Bincikar ainihin abunda ya faru da su,kuma zasu binciko su aduk inda suke muddin suna a doron duniyar nan!,kuma duk halin da ake aciki zasu dunga tuntu6arshi akai kai,
A 6angaren Aneelerh kuwa,Komai Ya hargitse mata baiwar Allah, Ga rashin da ta yi Ga kuma Laulayin Ciki da take fama dashi, kullum cikin yin kuka take, tsananin tausayinta ya kama su Abie, Kowa lallashinta yake yi, Akan tayi hakuri tabarma Allah komai, tun daga wannan lokacin ta hana idonta bacci,Takan tashi tsakar dare tayi nafilfili duk don saboda su Angel,idan tafara nafilfili har sai kafafunta sun fara yi mata zogi tukunna take dakatawa, idan kaga aneelerh tayi bacci to da rana ne, domin kuwa ta maida dare lokacin yin ibadarta, kullum rana ta Allah sai ta yi masu sadaka, bayan haka ta yi magana da abie akan A nemo manyan malamai su taya su da addu’a kuma ayi masu sauka, batare da 6ata lokaci ba, Abie Ya aiwatar da duk wani abu da Aneelerh ta bashi shawara akai,
Ƴan sanda Sun Dage damtse wurin Yin Bincike,Yayin da malamai suka Bada himma Wurin taya su addu’a da kuma yi masu sauka, Haka zalika su aneelerh Sun taka rawa wurin Yi masu addu’a, da sadaka, akan Allah ya bayyanar dasu,wannan kenan..
Shin ya rayuwar Angel ta ƙare a cikin ruwan da mahaifinta ya jefa ta? Ta rayu ko ta mutu?
Bayan wasu Æ´an kwanaki da Tajuddeen ya jefa ta a cikin ruwa, hadari ne Ya haÉ—u bakikkirin a sararin samaniya, kafin wani lokaci yayyafi Ya soma sauka a doran Æ™asa. Daji ne mai manya manyan bishiyoyi da tsirrai, kowane ganye ka kalla yayi kore shar da shi, gwanin ban sha’awa, musamman ciyayin da ke cikin dajin masu tsayi da cukowa, a daidai wannan lokacin garken shanu suka shigo cikin dajin. AÆ™alla sun kai talatin da biyar, suna tafe suna Cin ciyawa.
Wucewarsu keda wuya cikin dajin,Wata kyakkyawar bafullatanar daji, fara tass Jawur da ita, sanye cikin kayansu na al’ada, Ta bayyana hannunta ruÆ™e da sanda, siririyace Bata da Æ™iba ko misÆ™ala zarratin gata doguwa sam6al, Amma akwai dukiyar fulani cike tab da Æ™irjinta, ga yalwataccen gashin kai dake gareta mai tsayin gaske, anyi mata kitson kalaba,Wanda yasha ado da duwatsu,wutsiyoyin gashin sun sauka har tsakiyar bayanta, ga wasu da suka zubo ta gefe da gefe na fuskarta,
Tabarakallahu ahsanul khaliqin,Wasu dara daran idanuwa gareta Farare Ƙal kamar fatar farin Cikin kwai, Launin Idon nata Brown Colour ce, tana da kwarin ido sosai,Ga ziraran Eyelashes, Jagirarta tamkar anzanata saboda tsaruwarta, Ga wani dogon hanci da Allah yayi mata, siraran la66anta jawur dasu, Akwai kwalliyar ɗige ɗige asaman fuskarta har goshinta, Wuyanta na sanye da sarkoki, Haka hannunta ma akwai awarwaro,Tana da hujen hanci mai shegen kyau, idan tayi dariya kuwa wayyo Allah madarar kyau, Kai kace gonar audugace, Saboda kyan fararen hakoranta masu tsari, wani ƙarin kyan dimple biyu gareta wanda ko magana take yi, sai sun lotsa,A ƙalla Bazata Wuce shekara Goma sha Shida ba,
Tafiya take Yi a bayan shanayen tana Korasu da sandar hannunta, Wani Lokacin Har rawa take Yi tana jujjuya Jikinta, Da alama ba ƙaramin daɗin yanayin garin take ji ba, ko kusa bata jin Sanyi, Burinta A ruwan sama ya sauka sosai don tayi rawa acikinsa, kamar yadda ta saba,
Fararen kafafuwanta na sanye Cikin takalma, Cikin harshen fulatanci ta soma raira waƙa,
Tana cikin yin waÆ™ar ruwan sama ya soma sauka tamkar da bakin kwarya, Wani irin farin Cikine Ya lullu6eta, Cikin harshen fulatanci tace”Ni É—in Jinin nasara ce, Mai nema mai samu,Mai nasara mai sa’a, Daga Yin magana Gashi ruwa ya sauka wuhuhu Sai ni DANEJO”
Rawa Tashiga Yi acikin ruwan Yayin da shayenta suka duƙufa Cikin dajin suna kiwo,
Juyi ta dinga yi tana karkaɗa qugu, ruwan saman duk ya jiƙe kayan jikinta sharkaf, sun manne mata,Ƴar rigar jikinta bata rufe Cibinta ba, Sai ɗan zanin data ɗaura, kallabin kuma taci ɗamara dashi,
Tana Cikin Yin rawar nan Cikin rashin sa’a ta É—aura Æ™afarta saman wani dutse dake a bakin Ramin da wannan tafkeken ruwan yake, Gaba É—aya Dutse ya jirkice, A gigice Ta fasa Uwar Æ™ara, duk yadda taso Ta hana kanta faÉ—awa Cikin ramin amma hakan ya faskara, Domin kuwa gaba É—aya Ta rufza Cikin Ramin, Tsulum Ta nutse Cikin ruwan,
Within Seconds Ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman haki kamar wadda tasha gudu, Gaba É—aya gangar jikinta tana acikin ruwan, Iya kafaÉ—arta Ya tsaya, Idanuwanta sunyi luhu luhu dasu, Ƴan hanjin cikinta sun kaÉ—a, Hankalinta ya É—unguzuma, Ba ruwan bane damuwarta, don tun tana Æ´ar Æ™arama Baffanta Ya koya mata Ruwa, Babbar damuwarta shine taya za’ae Ta fito daga Cikin Ramin?
Rushewa tayi da kuka cikin harshen fulatanci ta soma Kiraye Kirayen Sunayen Ƴan uwanta donsu kawo mata ɗauki,
“Inna wuro,Adda!Nanne!bawuro!Wayyo Allah Na babu wani akusa da zai kawo mun É—auki”? tana Cikin wannan yanayin Shanayen ta Suka LeÆ™o Cikin Ramin Kamar sunji abunda take cewa, sun kewaye ramin suna ta kuka Emmoh !emmoh!
Nuna su Tayi da yatsan hannunta”Banga amfaninku ba, Ciyawa kaÉ—ai kuka Iyaci,”cike da takaici tayi maganar,Tana Cikin sambatun nan, Aka kwatsa Tsawa mai sautin gaske a gigice Ta nutsar da kanta Cikin ruwan don ba Æ™aramin tsorata tayi ba
sosai ruwan saman Ke safka da ƙarfinshi,
Lokacin da danejo ta nutsa kanta Cikin ruwan a tsorace sakamakon Tsawar da aka kwatsa, Ba zato Ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Kyakkyawar Yarinyar dake kwance saman dutsen dake a ƙasan ruwan mai girma da faɗi, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, rigar Jikinta duk ta nannaɗe ta manne mata, biji biji take iya hangenta saboda ƙasan Ruwane
Waro ido waje daneju tayi a matuƙar tsorace take kallon Yarinyar, Shin mutunce ko aljan, Abunda ta fara sakawa aranta kenan, tunawa da wata tatsuniya da Nannensu ke basu, Akan macen kifi, nan da nan tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, A gaggauce ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman Mayar da numfashi,
Waswasi ta shiga yi acikin zuciyarta,Anya Yarinyar data gani Acikin Ruwan Mutunce? kodai ta macen kifi ce ko ɗan ruwa? ta jima tana wannan zancen Zucin Kafin Ta kuma nutsa kanta Cikin ruwan, Cike da fargaba ta nufi inda Yarinyar take saman dutse har Allah ya kawota Saitin Inda yarinyar take, Hannu biyu tasa Ta ɗaukota, Sama tadinga yi Har ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan, Natsuwa tayi tana kallon kyakkyawar yarinyar, Daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba, Allah kaɗai yasan Tun wani lokaci take kwance a ƙasan ruwan, Cikinta yayi 6ul6ul dashi,Da alama Ta shaƙi ruwa sosai,
Mu haÉ—u a next Page don jin yadda zata kaya, Jama’a an rasa shaidar da zata bayyana abunda ya faru? taya kenan za’a san meya faru dasu Taj?Su wanene waÉ—annan Mutanan masu haÉ—arin gaske? shin danejo zata taimaki angel? Idan ta taimake ta kuna tunanin angel yarinya mai Æ™iriniya zata juri zama a hannun fulanin daji? ya zata rayu batare da mahaifinta ba? Duk dai acikin littafin kurkukun Æ™addara zaku samu amsoshin tambayoyinku, Tafiyar ta dabance salon ma na daban ne, a kullun burina in kawo sabon salo wanda ba’a ta6a ganin irin shi ba, Allah dai ya taimaka, WaÉ—anda suka shirya yin payment na kurkukun Æ™addara 500 ne, Suyi mun magana ta layi na 08103884440.*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*dedicated to Aunty kubra❤*
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara 8"