Breaking News

Soldiers Family 59-60

Page 59&60

 


__”sunlula sararin samaniya sunata ratsa hazo tafiya sukeyi hankalinsu kwance se fira sukeyi cikin farin ciki yayinda alyasat hankalinshina duniyar tunanin sahibarsa,,,kawai sesukaji ana bayadda sanarwa akwai matsala ajirgi kowa yayishirin kotakwana,,bakaramin tashi hankalin duk Wanda ke jirgin yayiba musamman dasukaga ana Raba rigunan iska.

 

Acan wajen jirgin kuwa tawagar jaguss ce suka sako wani,irin duhu meban tsoro kamar irin bakin hadarinnan Wanda ko hannunka dak’yar zaka gani gashi sunhana kowanne abun dake jikin jirgin yin,aiki gabaki d’aya computer dake ciki basa aiki sun tsaya cak,,,ma,aikatan jirgin nata iya k’ok’arinsu naganin sunseta komai Amma abun yaci tura domin basumasan ta,Ina zasu faraba gawannan bak’in duhun har acikin jirgin,,,anacikin hakan ne wata irin guguwa tataso mebala,in k’arfin gaske kamar zata tada duniya atake tashigayin majau,jauwada jirginnan kamar alkwato,,juyashi takeyi kamar juyin waina.

 

Cikin tashin hankali da rud’ani mutane dake ciki suka fara Kiran Allah suna kalmar shahada wasu Kuma na kuka domin sunga mutuwa afilin Allah,,rigunan da,akabasuma Basu samudamar sakawaba sabida juyin wainar da,akeyida jirgin gabaki d’aya mutanenda keciki sun hautsine wuri d’aya sun duk’unk’une Idan jirgin yajuya seya makasu wuri d’aya iya jigata sunyita domin kowa yasadak’at tasu tazo karshene,,,ana cikin wannan tashin hankalinne wani irin haske yawulga kamar walk’iya wulgawarshi keda wuya aka kifojirgin zuwa kasa dagayya,,Amma kamun yakai k’asa Kuma seya tsaya cak kamar abunda akarik’e kamun sama,u tafara wayewa kamar safiya duk wannan duhun yayaye hakan yabani damar ganin jarimin namu wato bibibo cikin tawa arniyar shigar yak’i shida wasu abayanshi suna rik’eda wasu igiyoyi ga dukkan alamu ajikin jirgin suka d’aurasu,,,figo igiyoyin sukayi dak’arfin gaske jirgin yadawo Dede yadda kowaze,iya zama wurin zamanshi.

 

Ai mayarda jirgin keda wuya Sega jaguss shima ya bayyana dawasu manyan aljanu ataredashi kowanne d’aukeda miyagun makamai,,gadan gadan sukayi kansu bibibo Amma kamun suk’arasa ne gimbiya halila da maheerah suka bayya suma cikin shigar yak’i tareda wasu manyan mayak’an Masarautarsu suma sukayi kansu jaguss,,,aiki inbakayi bani wuri wani irin gumurzun yak’ine akeyi tsakanin adilci da zalunci yak’ine me,abun ban Al,ajabi da mmki gabaki d’aya inba ruwan tsafiba Babu abunda su jaguss keyiwasu gimbiya halila yayinda sukuma suke yak’arsu da ayar Allah.

 

Bibibo kuwa datashi zuga suna,Nan wurin k’ok’arin bawa bayin Allah dakecikin jirgin kariya dudda basa ganin Mike faruwa Amma sunajin artabon da,akeyi awaje saboda gunji da gurnani da ihun dake tashi me amonsauti kamar ze tsaga duniya,,domin Allah yabawasu gimbiya halila nasara akansu sunjigatasu sosai Kuma sun raunatasu ganin suna nema galaba akansune yasa jaguss komawa kaiwa jirginsu Hari tako Ina muradinshi kawai yakashe alyasat da mama dudda yanzu yafahimci Bata ciki Amma gara yakashe alyasat daga baya yakoma kanta,,,ganin hakan yasa bibibo tunkararshi sukayi gaba da gaba kowannensu najida k’arfi da zallar zuciya,,,hakan yasa suka fara yak’i irinna k’arfi da k’arfe kowannensu burinshi yakashe abokin karawarshi amma bawanda yayi nasara akan wani.

 

Gimbiya halila naganin hakan yasa tashiga k’ok’arin gyara jirginda suka B’ata domin tafahimci nufin wannan aljanin sedaime jirgi ya gyaru Amma wujijjigar dayasha ana tadashi zekamada wuta sibada k’arafunanshi sunyi zafi gakuma fetur d’in dake ciki shima ya hautsineda bak’inmai shima yad’auki zafi sosai,,,,azabure tajuya tana kallon hadimanta tace “jirgi yanzu yanzu,,aikamun ma tarufe bakin wani babban bafad’e yazama katon jirgi Wanda ze,iyad’aukarsu Baki d’aya.

 

 

Cikin sauri tashiga kiciciniyar bud’e k’ofar jirgin Amma andatseta ga dukkan amalu tsafetane akayi,,hakan yasa ta haura saman jirgin tareda yimai duka d’aya yahude akasamu hanya se kawai tadira ciki,,dayawa wasu daka cikin jirgin sun suma wasu Kuma ganinta ya sumardasu,,,shiko jalaludeen Yana ganinta yace alhmdllh yayinda Zaid da tind’azu yake karkarwa yak’ara matse jikinshi se zare Ido yakeyi dudda suke sojoji Amma arayuwarsu Basu tab’a ganin tashin hankali kamar wannan ba.

 

Itako batama damuda kallon tsoron da wasu kemataba gun alyasat kawai taje tareda rik’o hannunshi,,se alokacin yabud’e idonshi domin tunda abun yafuru yake lumsheda idanuwanshi dudda cewa zuciyarshi na bugawa sosai Kuma yanajin yadda Yusif da lateep kesalati Amma hakan besashi yabari firgicinshi ya bayyana ba yaso zuwa gun mahaifansu Amma ganin su alhassan sun kanannad’e ammy da abbe d’in yasakashi bejeba,,,kallo yabita dashi,,itako komai batace masaba kawai sama tayi dashi sukabar jirgin…gabaki d’aya Wanda Basu sumaba dasu abbe da Ido suka rakasu kowada abunda yake sak’awa azuciyarshi fatansu kawai Allah yafiddasu daga wannan had’arin dasuke ciki.

 

Acikin wannan aljanin dayazama jirgi tasanya alyasat tareda juyawa tafita tad’auko jalaludeen,,hakan tarik’a d’auko mutanendake wancan jirgin tana maidawa wannan itada maheerah da wasu dagacikin hadimanta ahakan har suka d’auke kowa hadda masu tuk’in jirgin,,kana wannan aljanin yayi sama cikin azabar gudu yanufi India dasu,,, jaguss be Ankara da,abunda kefaruwaba seda yaga dagawar aljaninda yad’aukesu,,cikin bakin ciki rasa wannan damar dayasamu tawuceshi yad’auko wata sharb’eb’iyar wuka zesokawa gimbiya halila cikin sauri maheerah takara yasuketa agefen cikinta ihun datayine ya ankararda maheer da gimbiya halilan,,,cikin tashin hankali gimbiya halila tayi kanta yayinda maheer tadamk’i wuyan jaguss yayi Masa mirda d’aya segashi yaraba kanshi da gangar jikinshi atake yafad’i matacce.

 

Dukkansu kan Maheerah sukayi ganin yadda ta raunata cikin sauri gimbiya halila tad’auketa tareda nufar masarautarsu da,ita shiko bibibo da tawagarshi suka nufi India..

 

Kodasuka Isa Masarautar Bata tadda mahaifiyarsu ba da mama hakan yasa itada memartaba dakanshi sukashiga bawa maheerah temakon gaggawa Kuma cikin ikon Allah sunsamu nasarar ceto rayuwarta.

 

India

 

Wani irin girgiza d’akin tsafin Didi yayi alokacinda jaguss yamutu,,dudda batasan mutuwa yayiba Amma tasan ansamu matsala babba kuwa hakan yasa tashiga Kiran wasu yaranta domin tak’arawa gidanta tsaro,,bayan tagama wannan sulkullen natane tafito domin ganin yadda tashirya komai yatafi yadda takeso,,,tana fitowa taga wannan dattijuwar k’anwar tata zeenah tana zaune a perlon da itada wasu yaranna didi wato k’anen ma,Isha (ammy) d’aure fuska sosai Didi tayi kamun tace mikizoyi anan zeenah?

 

Kawarda fuska zeenah tayi gefe kamun tace tarbon y’ata da ahalinta…”ok sekije gidanki kitarbeta badai ananbako? “Anan dai Zan tarbeta domin anan zata sauka Kuma bamani kad’ai ba nida duk Wanda kikasan yanada hakki akanta Kuma yanada muradin ganinta yanzu hakan sauran Y’an uwanta sunjed’aukosu ne banmasan Miya tsayardasuba domin ya,Isa yanzu ace jirginsu yasauka.

 

“What?? Zeenah mikike nufi? Nizan saka doka kikaryata? Wato seda kikagaya musu zatazoko? Good keyi naki kingama saura nawa..”eh nagayamusu Didi duk abunda zakiyi kindad’e bakiyiba kewai wace irin zuciyace dake mutin sekace ba Imani aranshi waye baya kuskure arayuwa waye bayayin laifi Kuma ayafe masa? Amma kin d’auki kiyayyar duniya kind’orawa Yar cikinki daba,agabana Kika haifi ma,ishaba da nace wlh ba y’arki bace haba wannan wanne irin abunne?

 

Shiru kawai Didi tayi tana kallon zeenah tamarasa mizata cemata tad’auki tsawon lokaci atsaye kamun tajuya fuuuu zatabar wurin kenan taji k’aramar jikarta nafad’ar yeeer gasu uncle Nan sunzoda Bak’i didi,,ai cak tatsaya..!

 

 

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08107819124

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

*S F*

No comments