Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 1

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 01


A ranar cikin su hudun säahar nadeeya taoufeeq da mai gayya me aiki fadeela babu wanda yayi wani cikakken baccin dadi, nadeeva ranta a jagule zuciyarta fal tambayoyi tare da neman dalilin tafiyar sãahar din lokaci guda,sai kuma yadda yaga zallae bacin rai daga fuskar ya moha,idan har kunnuwanta sunji mata dai dai da bakinsa yake gayawa fadeela

“Let her go,zaki ci gaba da rayuwa ko babu ita..” Sake juyawa nadeeya tavi tavi rub da ciki tana sake nazarin matsalar,a yadda idanunta suka karanci yaa moha din,kamar wata alaqar sanayya a tsakaninsu,to amma a ina ya santa ko kuma a ina sukasan juna? ,shine dai bata sani ba. Iska ta furzar daga bakinta,fatanta dai Allah yasa ba wani abu me muni bane va hadasu kwatankwacin na Ameesha. Sai ta girgiza kai da sauri tana gayawa kanta A’AH.

********Duk da kumburin idanuwan da basu samu bacci ba,da kuma ciwon kai da yakeson taso mata kadan kadan,amma hakan bai hanata shiga kitchen taya maama hadawa dr breakfast dinshi ba. Tana aikin amma yau so silent take,ba kamar baya da takanyi hira da masu aikin nasu ba. Afifa tun sassafe ta fice asibiti,saboda samun marasa lafiya da akayi daren jiya wadanda sukayi hadarin mota.

A daki ta iske maaman,ta gaya mata ta gama

“Ki shiryawa abbanku a dining na sashensa,fita zaiyi yau din yana da baqi,yanzu zan iso sashen” amsawa tayi da to ta juya tana fita, maaman ta bita da kallo. Tun jiyan datayi mata sannu da zuwa bayan dawowarsu da afifa ta karanci akwai wani abu dake damunta,to amma tasan halin kayarta da shegen zurfin ciki. Sannan tana zaune ma afifa zata gano musu komai. Sau da dama tana iya gayawa afifa damuwar da ita bata iya gaya mata ita,wannan din kuma wani haduwar iini ne da zumunci me qarfi a tsakaninsu fiye dasu iyayensu.

Ta gama shiryawa tsaf ta juya zata fita muryar dr girema ta sauka kunnenta,cikin kamilalliyar muryarsa yake sallama a falon.
Sai da gabanta ya fadi,amma ta tattara dukka nutsuwarta waje guda ta amsa masa sannan ta rusuna tana gaidashi

“Zauna muyi magana” ya fada maya shima yana laluben wajen zama,sai ta zame ta zauna daura dashi kanta a qasa.

“Jiya akacemin kinzo,ina fata ki dawo kenan,saboda ba zaki sake komawa ko ina ba,ladan da aka samu Allah ya amfanashi” a ladabce tace

“‘Eh,na dawo kenan abba,ina godiya kuma da dukka damar da aka bani”

“Bata haka nake buqatar godiyarki ba ummi na” sai ya gyara zamansa sosai yana dora hannunsa saman hannun kujerar

“Zuciyata ta gama nutsuwa da aminta da yaron nan,don haka ina me shaida miki,muddin kin bani dama kamar yadda musulunci ya tsara mu nemi izinin bazawara,to zan bashi damar turo magabatansa,yazo ayi a gama komai a wuce gurin,kema ki tattara hankalinki waje guda”

“Na baka izini abba” ta fada kanta tsaye, zuciyarta na qeqashewa,tana jin yanzun bata da sauran mafaka kuma,guje gujenta ya qare,babu wani abu da ya rage mata,
MAHMUD GANA yayi winning.
shuru dr girema yayi yana son karantar fuskarta,yadda tayi saurin amsawa yadan daure masa kai,saboda ya riga ya ajema ransa ko yaya zai ta dan ja,amma karon farko babu jaa babu komai ta sallama?. Kai ya gyada

“Shikenan kije,Allah yayi miki albarka,ko meye ake ciki zan sanya mahaifiyarki ta sanar miki”

“Ameen abba” ta amsa tana migewa, kowanne sashe na jikinta na qarasa sakewa yana mutuwa dukkan wani qwarin gwiwarta yana zagwanyewa,qarshen tika tiki tik,mai afkuwa zata afku a kanta.

Da gyar ta tattara nutsuwarta tayi wanka,batason duka wannan bacin rai qunci da damuwar da take yawaita samun kanta a ciki,ga tunanin fadeela cunkushe cikin zuicyarta,duk wani motsi da zatayi sai taji kamar sautin muryar fadeela ne keci gaba da kiranta. Wannan ya sanya ta shirya ta nema izini wajen maama,ta wuce gidan yaa muhyi ta dauko khaleefa,daga nan suka zarce gidan ya Saifullahi ta dauko fadeel,ta sauka gidan yaa zaid ta dauko zaahid. Tana Sanya ran kasancewarta tare da yaran zaiyi matuqar debe mata kewa,duk da cewa yara maza ne ba mata ba,amma tana da yaginin zai dauke mata damuwa me yawa,ya kuma rage mata zaman kadaici.

********Dukka manyan idanunsa ya ware a kanta,yana ci gaba da sanya spoon din abincin a bakinta cikin tsare gida tare da sake tsuke dinkakkiyar fuskarsa. Hakan ya qara ta’azzara rashin fara’arsa tare da garawa fuskarsa kwarjini.

Duk sanda zata karba abincin saita kalli idanunsa sannan,ya sake kawo spoon din bakinta,sai taqi bude bakin bare ta amsa.a maimakon haka ma ruwan hawaye ne ya biyo baya.

Ajiye spoon din yayi yana tsareta da idanu

“Meye kuma?”

“Anty N” ta fada hawaye na sake sauka a idanunta. Sosai ranshi ya sosu,don ko sunanta bayason yaji daga bakin fadeelan

“Idan kika sake yimin maganarta.
.. saina zane
bakinki tas” ya fada yana zare idanunta cikin
baraza

“Oya,gate up” muryar sajjad ta ratsa tsakaninsu ya fada yana migawa fadeela hannu. Da hanzari ta miga masa hannun nata hawayen da suka magale suna garasa zubowa,ya tayar da ita tsaye yace

“Muje ki gayawa sister nadeeya ta canza miki kaya,ki barshi yaci kansa shi daya,ya
Allah.
..ina rogonka ka danqara masa
soyayyarta azababbiya naga ya zaiyi da wannan zafin kan da zafin zuciyar” ya fadi maganar yana wucewa gaba abinsa.

Ji yayi kamar ya tashi ya shago sajjad ya nannausheshi,adduar da yayi masan yazun jinta yayi bata da maraba da mutumin daya rogar maka saukar ajalinka a kurkusa. Shima sajjad din yasan me ya aikata,don haka ya dauki fadeela cak suka fice da sassarfa daga sashen,yana jiyo muryarsa yana sake kira masa wani alkaba’in na zurmawa soyayya.

Sumar kansa ya shafa yana furzar da iska,zuciyarsa tana gogarin bashi nutsuwa ta hanyar jaddada masa babu ta yadda zaiyi a yanzun yaso wata diya mace, babu wata d’iya mace da zata iya galabar tsallakawa takai ga zuciyarsa,an gama yiwa ruhi da zuciyarsa barna,bazai kuma sake bari hakan ta faru ba,kai kwata kwata ma yanajin cewa a yanzun babu wani abu waishi SOYAYYA dake existing,zaifi kyau a canza masa suna da sha’awa ko son zuciya.

A lokacin ne ya samu damar shiga toilet yayi wanka,duk yadda yaso ga yaci jerin abincin alfarmar da Jacob ya saba dafawa ha ajiye masa amma yau ya kasa dora komai saman harshensa,kukan da fadeela keta faman yi a kwanakin ya tsaye masa a rai,yau ta bugaci wani abu da yakejin bazai taba iya bata shi ba,sai kuma rashin walwalar nadeeya,duk gidan sun maidashi wani so silent, damuwa ce fal cikin zuciyarsa,wadda har sai data taba kuzarinsa.

Yana tsaka da duba wasu ayyuka a system dinsa,ya shanya abincin da tun daxu Jacob yayi serving nasa amma ya kasa ci,aka gaya masa baaba ramatu nason ganinsa. Kafafunsa ya sauke yana bada izinin shigowarta,ta shigo cikin kamala da nutsuwarta,yayi mata da nuni ga saman kujera,ta koma ta zauna

“Barka da yamma” baaba ramatu din ta fada,cikin girmamawa yace

“Barka kadai,ya aiki?”

“Alhamdulillah ” ta amsa shi tana murmushi

“Idan babu damuwa shawara ce dama nazo da ita” ta furta a nutse tana dubansa.

Kansa kawai ya gyada mata alamun ya bata dama,ta danyi gyaran murya kadan tana tauna abinda zata fada

“Nikam nace me zai hana kayi haquri da korar nannies din fadeela,saboda dole sai ana haquri da halaye da dabi’un mutanen da kake rayuwa da su,ba ta yadda za’a yi kowa yayi maka abinda kakeso dari bisa dari,yarinyar cikin watannin da tayi qalilan tayi aikin da babu wanda ya taba yiwa fadeelan shi,tana da kula da takatsantsan da iya raino,idan ba damuwa kayi haquri ka dawo da ita taci gaba da kula da fadeela don Allah” kansa ya dago ya kalleta,sai kuma ya maida kan abinda yakeyi, kamar bazaiyi magana ba kafin daga bisani yace

“Ba zata taba dawowa ba,ta tafi kenan,so ku koya mata haquri,tunda tun farko dama ba da ita ta saba rayuwa ba,dole zata ci gaba da rayuwa ko bayan babu ita” tunda baaba ramatu taji ya fadi hakan ta tabbatarwa kanta saahar ta tafi kenan. Kaifi daya ne shi,wanda tsanani baya sakashi sauya zancansa ko
dawowa da baya. Migewa tayi sali alin ta fice a gurin,cikin ranta tana jin matugar kewa da takaicin subuce musu da yarinya kamar sãahar tayi,ta tabbatar ba za’a maida kamarta
ba.

Sai yamma sosai sajjad suka dawo da fadeela,ko bayan sun dawo din bata ma shigo sashen toufeeq din ba. Tana lafe jikin nadeeya,wanda kafin kace meye wannan wani mugun zazzabi yayi ram da yarinyarnar wani irin rawan sanyi takeyi. Sosao hankalin nadeeya ya tashi,ta dauki waya ta sanarwa toufeeq. Daga masallaci ya dawo, kwanakin tunda suka fara wannan rigimar saboda tafiyar sãahar din shima baya fita ko ina,a gida yake wuni,duk wani aiki ta system dinsa yake gudanarwa.

Hankalinsa yafi na kowa tashi,saidai zuciyar ‘yan maza wadda bata bari aga rauni a tattare da ita. Mota ya kaita,ya sanya baaba ramatu ta shirya tazo su kaita asibiti.

Nadeeya na zaune tana sharar qwalla har suka fice,zuciyarta a mugun karye,ta tabbatar wannan zazzabin na fadeela yana da nasaba da yadda tayi mugun sanya sãahar a ranta,da qulafucinta da takeyi. Gaza jurewa tayi ta mige ta isa daki,ta cire wayarta dake saman dressing table ta budeta,ta zauna bakin gado tana lalubar number sãahar.

Dai dai lokacin da suke zaune a falo ita da afifa suna hada fruit salad din abincin dare,cikin kwanakin gaba daya itama ta sake zama so silent,babu wani karsashi ko kadan a tattare da ita. Duk da yadda fadeela ke tsaye a ranta,amma taqi bawa zuciyarta damar da zata karaya. Har a ranta tana jin hukuncin data yanke shine dai dai,babu gudu babu ja da baya,ta yadda sabo turken wawa ne,amma idan tayi haquri wataran zuciyarta zata rusuna,taji tamkar ma bata taba rayuwa da fadeelan dama duk wani ahalin gidan ba. Gefe guda kuma dukka kunnuwanta na kan motsi da kai kawon gidan,duk da ta tattara lamarinta ta miqashi ga Allah,saboda ta tabbatar tunda har ta bawa Dr girema wuga da nama akan lamarin mahmud,to tasan fa babu fashi aure ne zai zama tabbatacce a tsakaninsu. Abu mafi razani dake jijiga zuciyarta,kaddarar auren adam me daci ce da hallaka dukkan buri da gusar da fata ko sha’awar ci gaba da rayuwa ta aure dama ta duniya gaba daya..
…ita kuma qaddarar auren mahmud fa? yaya zata zo mata?. Tambayar kenan dake barazanar fasa mata zuciya a duk sanda tazo kanta. Ta sani cewa saidai suyi zaman haquri ita da mahmud kawai,amma babu ta yadda za’ayi ya samu yadda yakeso daga gurinta,ta gaya masa wannan ta sake nanata masa,ya shaida masa yes……a shirye yake yayi haquri da ita ya kuna zauna da ita koma a yaya ne.

Wani sashe a zuciyarta kowacce rana nana ya mata cewa JINSIN MAOARYATA
NE,JINSIN MAHA’NTA NE,duk abinda suka gaya maka bashi kake tararwa ba bayan aure,yaudara da cin amana da karya alqawari sun lullube zukata da harsunansu, bata tunanin akwai wata kalma ta soyayya da jan hankali, nuna zallar kulawa da rayuwa yare har bayan mutuwa wadda adam bai furta mata ba,amma yaya sakamakon hakan ya kasance?. To auren me zatayi? ‚AUREN BIYAYYA kenan ko me? tunda dai ita din batakai lokacin da za’a ce tayi auren kai buta da ruwan wanka bandaki ba.

Tsakiyar wanann tunanin wayarta tayi burari,ta waiwaya a nutse tana duban me kiran,zuciyarta na gaya mata mahmud ne, wanda zuwa yanzu ta fara tsanarsa tare da tsanar komai daya shafeshi, yana yaiwata kiranta da sunan caring,caring din da ita kuma bata sonshi, don duk abinda yayi sai taga kamar yana bin footprint na adam ne.

Mamaki yadan kamata gain sunan nadeeya.
Bawai bata kiranta ba,a’ah,tun daga randa ta baro gidan,har tayi kwanaki bakwai babu ranar da bzata fito ta fadi bata kirata ba tana roqonta akan ya dawo. Randa tayi alqawarin ba zata sake kiranta ba tayi fushi ne saboda ta tabbatar mata ba zata dawo ba,suyi haquri ta kula da fadeela,tun daga ranar bata sake kiranta din ba,saidai kullum zata bar mata good morning massage through watsapp dinta.
Wugar hannunta ta ajjiye ta miga hannu ta dauki wayar,ta daga kiran ta karashi a kunnenta. Gabanta yayi mummunar faduwa jin sautin kukan nadeeya,tayi saurin kama sunan
Allah sannan ta samu qwari gwiwar tambaya

“Sister nadeeya,me ya faru?”

“Fadeela ce.

” Sai kuma maganar tata ta
tsaya,abinda ya haddasawa sãahar wani irin muguwar faduwar gaba,ta sake kiran sunayen
Allah

“Karki cemin wani mummunan abu ya faru da ita”
[11/09, 3:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*6

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 1"