Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 21

Page 21


Ta kusa mintuna talatin tsaye a bakin window dinta tana jiran feedback na abinda ta shirya,first plan dinta kenan. A gaggauce ta sauke labulen tana amsa sallamar masura me aikinta data aika ta sanya mata ido akan abinda zai biyo baya. Shuru tayi har masura ta gama labarta mata,taja wani numfashi me tsaho ta fesar da me zafi

“A taqaice kinason kice ba wani rashin jituwa daya gilma a tsakani?” Kai ta gyada

“Dukka ma suna sassan nasa,harda Dr raheema,kamar ma batajin dadi ne”

“Tashi kije” ta bawa masura umarni,sai ta miqe tsam ta fice. Hannunta ta dunqule tana dan dukan daya tafin hannun nata dashi. Tayi missing target dinta,a gobe meenal zata sauka a gidan kuma tun a yau taso ta haifar da gagarumin rikici gami da rashin fahimta a tsakaninsu,to amma ya akayi ta kuskure?. A mganganun data gaya masa game da yarinyar tayi zaton har sai ta shiga maganar wajen sasantasu.

Mamakinta da daurewar kanta ya sake qaruwa lokacin da taji tashin motarsa,ta sauke labulen nata ta koma ta zauna saman sofa din dake falon. Tayi nisa a tunani har bataji lokacin da me aikinta ke gaya mata ta gama gyaran dakin meenal ba har sai data maimaita

“Good,ki wuce sashen su nadeeya,cikin dakunansu ki sake gyara mata daya a can”

“Okay hajiya” ta amsa mata a ladabce tana fita. Tayi hakanne saboda ta samar da kusanci na mussamman tsakanin meenal nadeeya da kuma fadeela data tabbatar itace ruhin toufeeq.

Qarfe sha biyu saura na dare ya samu dawowa,sanda ya shigo falon babu kowa,har qwayayen lantarki duka a kashe sai masu qarancin haske da aka bari kada duhun yayi yawa. Dining ya duba,kusan a yanzu bazai iya cin komai ba,amma kuma yunwa yakeji,dole ya zauna ya tsakura abubuwan da basu cika nauyi ba,su dinma baici da yawa ba ya ture,inda zai samu wannan hadin coffee din da yafi kowa murna,zuwa yanzu ya fara fita a kansa,saboda yasan idan ma ya hada baya masa dadi kamar nata,abun ya zame masa kamar jarrabi.

Cike da gajiya data qarawa tafiyarsa nutsuwa yazo zai wuce,idonsa ya sauka akan qofar dakin nata. Tunda ya tafi meeting din hankalinsa ke a rabe gida biyu wanda shi kansa baisan ainihin dalilin hakan ba. Har ya gota sai kuma ya dawo,ko ba komai haqqinta ne a kansa ya kula da lafiyarta kamar yadda take qoqarin kula masa da lafiyar diyarsa.

Haske ne sosai a dakin,da alama bacci ya dauketa ne ba tare data shiryawa hakan ba,don fadeela na kife ne saman cikinta,hannuwanta zagaye da bayan fadeelan. Gabansu ya qarasa ya tsaya sosai yana kallonsu,suna rungume da juna tamkar uwa da ‘ya. A hankali ya zame ya durqusa daga gaban gadon inda suke kwancen,idanunsa saman fuskarta da take looking innocent cikin bacci,bayan a idanu biyu cikakkiyar matsiwaciya ce,sassanyan kyan nan nata da babu abinda ke sanyawa ya gushe shinfide akan fuskar tata. Da sauri ya dauke idanun nasa daga kanta ganin yadda suka fara yawo saman pink lips dinta,kwanyarsa nason tuna masa abinda yaji a wancan lokacin da ya nada lips din nata da nashi. Har zai miqe yaji alamun fitar numfashinta kamar ba dai dai ba,alamu suke nuna fadeela kenan tayi mata nauyi,sai ya zare duvet din data lullubesu dashi,ya soma zare fadeelan daga jikinta.

A firgice ta farka tare da sake qanqame fadeelan cikin zafin nama tana kiran sunanta. Cak ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,gaba daya ta firgita kamar ana zare numfashinta ne. Sakar masa fadeelan tayi a hankali bayan sun hada ido,sai ta tsuke fuskarta tana qoqarin gyara gabab rigarta da ya tattare saboda janye yarinyar da yayi yasa ya bude don rigar me santsi ce,saita juya right side dinta tana sake jan duvet din sosai tana lulluba har saman kanta,cikin ranta tana jin haushin yadda kowanne lokaci yake shigo mata daki ba tare da neman izini ba,dole tayi masa magana,ba zata juri wanann ba,a duk yanayin da kake ciki sai mutum ya ganka kenan a haka?. Shima yana gama gyarawa yarinyar kwanciya ya tofeta da addu’a sai ya juya ya fice,tabi bayansa da kallon harara ta cikin duvet din, cikin sa’a ya waiwayo don ya manta bai kashe musu haske ba,tayi hanzarin maida idanunta ta kulle,sai kawai ya basar amma cikin jikinsa tabbas yaji tana kallonsa,ya kashe wutar yaja qofar ya fice,yadda ta firgita da jin ana jan fadeela na tsaya masa a rai,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya sanda ya kammala shiga nasa dakin ya zare takalmansa a gajiye ya watsar dasu a gun ya zube saman sofa bed yana dage kansa saman bayan ya watsa hannayensa.

Yana fita ta waiwayo ta jawo yarinyar cikin jikinta,sai yau zasuci gaba da kwana tare,don kullum maji hanawa takeyi tazo,a nata nufin a barsu su sake,kuma fadeela tayi girma da kwana cikin iyayenta. Idanunta a rufe amma tana bitar abubuwan da suka faru wunin yau,bata jima tana wannan dogon tunanin ba bacci yayi awon gaba da ita.

***karfe biyar da rabi ta idar ta farka,a nutse ta sauka daga saman gadon,jikinta ya sake sosai,babu ciwon kan ko kadan,sai dan rashin qwarin jiki dan kadan. Bandaki ta wuce ta daura alwala ta dawo ta shimfida abun sallah,sai data idar sannan ta tashi fadeela,tana gamawa a nan gefanta saman abun sallar ta bingire bacci ya sake daukar yarinyar.

Tayi nisa wajen yin azkar dinta,yayin da gefe daya kuma qwaqwalwarta ke cike taf da tunani daban daban. Wayarta ce tayi haske kadan,ta jawota tana dubawa, afifa ce ta turo mata saqo,murmushi ya subuce mata tana girgiza kai,wato sajjad yana so ya sanyata ta manta da ita,lallai sunci bashi,bari a gama amarcin ta nemeta saita tsigaleta tas.

Tana shirin buda saqon sautin knocking ya ratsa kunnuwanta,ta tsaya tsam daga qoqarin bude saqon da takeyi tana son tantance daga inda sautin yake fitowa,don dai tabbas ba qofar dakinta akewa knocking din ba. Har ta basar jin cewa ba tata qofar ake bugawa ba,ta buda saqon afifa tana dubawa,wanda saqon sannu da jiki ne da kuma ban haquri,saidai har ta gama karantawa ta maida mata reply ba’a daina buga qofar ba. Maida idanunta tayi ta rufe bayan ta kalli agogo,duka duka yanzun qarfe takwas ne da wasu mintu na safe,to waye zai shigo har nan din yana irin wannan nacin qwanqwasa qofar?. A hankali bugun ke qara yawa,qaramin tsaki ta ja,ba kasafai ta fiyason hayaniya da safe ba,ta miqe a hankali tana gyarawa fadeela kwanciya ta nufi qofar dakin nata.

Cikin nutsuwa ta murda handle din ta bude qofar,ta kuma sanya kanta tana leqen tsahon hallway din don ganin me bugun da kuma dakin da ake bugawar. Hakan yayi dai dai da sanda shima ya buda qofar tasa,ya kuma sanyo kansa waje,fuskarsa tayi wani fresh da hasken sallar asuba tare da wani irin tarin nutsuwa da kamala da yake da ita.

Ido suka hada shi da ita,manyan fararen idanunsa da bacci yadan qara musu haske da girma,a tare suka janye dubansu sannan ta sauke kallon nata akan matashiyar dake tsaye gaban qofar dakin. Sanye take da skinny jeans da wata t.shirt da iya tsahonta qugunta,qafafunta dogayen takalma ne masu tsini da igiyoyi a jikinsu,sai qaramin Scarface dake kanta wanda iyakarsa wuyanta,ba wani abu da ya rufe mata,bata iya ganin fuskarta,amma duk da haka zaka iya gane tsananin sirantar da take dashi da kuma hasken fata.

“Yaa moha” ta fada da muryarta me tsananin sirantaka, muryar na dan rawa kadan alamun kuka takeson saki. A nutse ta maida jikinta ta kuma maida qofar dakin nata ta kulle,kwanyarta nason tuna mata wacece ita?. Gefan gado ta koma ta zauna tana qarshe cikon hailalarta da take guda dari duk rana safiya da maraice 200 kenan. Gefe daya kuma yarinyar na mata yawo a idanunta

“Haseena,’yar hajiya qarama” wani lungu daga qasan zuciyarta ya cillo mata amsar,bayan ta gama qirga kwanakin da hajiyan tace mata zata dawo,haka yake,indai lissafinta yayi dai dai kenan. Qaramin murmushi ne ya qwace mata a fuskarta,tadan girgiza kai kawai,wanann itace haseena din da hajiyar keta kururuta zuwanta?,saita girgiza kai kawai,ta sauka a hankali ta dauke fadeela ta maida saman gadon itama ta koma ta kwanta tana jan musu duvet. Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,tana ci gaba da salati qasan ranta idanunta a lumshe,dukka hallway dinma shuru,babu alamun motsin mutum kwata kwata.

Sanda ta maida qofar ta rufe duka akan idanunsa,a nutse yana kuma qarawa fuskarsa rashin walwala ya sauke dubansa akan yarinyar. Idanunta cike suke taf da qwalla,ta ritsashi da idanunta tana kallonsa da kyau,sai kawai ta zame jakar dake rataye a kafadarta ta ware hannunta da zummar rungumarsa. Da sauri yaja da baya yana jifanta da wani kallo

“Meenal,meye hakan?” Ya furta a mugun dake,tsaiwa tayi sak tana kallonsa,hawayen da take maqalewa na gangarowa

“I want to be in your arms yaa toufeeq please” ta furta tana sake sakar masa kuka. Tsaiwa kawai yayi yana kallon ikon Allah,yadda qanqanuwar yarinyar da aka haifa ta taso a gabansa ta zama haka,totally ma ta canza,tun daga yanayin halittarta kawo dabi’unta,tayi wani irin girma kamar sa’arsa,duk da cewa ‘yan watanni ne tsakaninsu da nadeeya,amma sai ka rantse gaba take da nadeeya. Ganin baice komai ba sai hannunsa sa ya goye kawai a qirji yana mata wani kallo da batasan inda ya dosa ba,saita sulale a gurin ta duqa saman qafafunta tana sake sabon salon kukan

“Yaa toufeeq,i can’t take it anymore,duk tsahon wanann lokacin da naqi kula kowa kai nake jira,na saka raina da duka burina a kanka” sai taci gaba da gaya masa abinda ke ranta kai tsaye ba kunya ko kwana kwana,gaba daya kansa sake daurewa yayi,yaushe ta zama mara kunya haka?.

“Look meenal” ya kirata yana sake hade ransa da kyau,a hankali ta daga idanunta da suka jagale da hawaye ta kalleshi

“Dama ina wasa dake?” Ya fadi da wani irin tone da ya fidda kwarjininsa har ya kusa bugar da ita,qoqarin tattaro dukka dauriyarta tayi,da gasken gaske takeson toufeeq fiye da lokacin baya kafin dawowarta da ganin da tayi masa yanzu,a wannan lokacin da tayi ido hudu dashi,bawai cikin hotunansa da take faman wallafawa ba,ta sake jin cewa a shirye take ta karba toufeeq din daga hannun kowacce mace

“Kaga alamar da wasa nake yaa moha?,kaga alamun wasa cikin soyayyar da nake maka?” Ta tambayeshi idanunta cikin nasa hawaye na sake wanke mata fuska. Abun sai ya koma bashi mamaki qwarai,yayi shuru yana karantarta

“Yaa toufeeq please say something,kayi magana mana,da gaske nake maka,bazan iya jurar rasaka ba,i can do anything a kanka,ciki kuwa harda kashe kaina muddin na rasaka!” Cikin ‘yan mintuna qalilan ya gama fahimtar da gasken take fa,duk abinda take fadi din da gaske ne zata aiwatar,shi sai yake ganin ma kamar ba cikin saitinta take ba.

“Muje parlor” ya fadi yana nuna mata hanya,dole tana buqatar guidance and council,ya kamata ta fahimci shi din a matsayin yaaya yake a wajenta bawai masoyi ko mijin aure ba. Kamar ba zata tafin ba har sai da ya maimaita mata yana sake hade fuska,sai tayi gaba tana qoqarin tsaida hawayen nata.

A hankali ta bude idanunta saboda gajiya da tayi da rufesu din,baccin kuma da take sanya ran zuwansa baizo ba,batasan me zuciya da kunnuwanta suke jira ba,sai ta miqe a nutse tana gyara top din rigar baccin jikinta me rubi biyu,ta jawo dankwalinta me santsi daya dace da rigar ta daure kanta ta zuro qafafunta ta sauko daga saman gadon. Gaba daya ta manta da batun shan ruwan duminta,ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofa. Duk yadda taso ta dauke kai daga kallon qofar dakin da a dazun yarinyar ke tsaye amma ta kasa controlling din idanunta. Ba kowa yanzu a qofar dakin,saidai kamar a bude take bawai a rufe yadda ta saba ganinta ba kullum. Batasan dalili ba amma sai ta samu kanta da jan qaramin tsaki,ta juya tana fita a gurin.

Muryarsa a tausashe kunnuwanta suka fara jiyowa,a lokacin da yake magana da haseena cikin son kwatanta mata abinda ke cikin zuciyarta ba me yiwuwa bane

“Ka fahimceni yaa toufeeq,nima ba yin kaina bane,bansan lokacin da zuciyata ta kamu da matsanancin sonka ba,a yanzu kuma ba abinda kunnuwana zasu iya fahimta sai yaren sonka kawai” daidai lokacin idanunsa dana sãahar dake qoqarin wucewa kitchen suka hadu waje daya. Har tsakiyar kanta taji kalaman yarinyar da muryarta me bala’in sirantaka,ta lumshe idanunta tana daukesu daga kan toufeeq din,wani tsanarsa na darsuwa a ranta. Shikenan shi bashi da aiki sai jefa soyayya a zukatan ‘yan mata?,su kuma basu da aiki sai zub da kima da martabarsu?,shin wai basajin kunyar roqon soyayya daga gurin namiji?, namijin ma irinsu toufeeq din me zafin kai izza da jin cewa shi din wani ne?.

Bata sake bari kunnuwanta sun jiye mata komai ba ta daga qafarta ta shige kitchen din da dan sauri kadan,sai a lokacin ya dauke idanunsa daga kanta,baiga komai saman fuskarta ba kamar yadda ya saba gani a baya akan fuskar AMEESHA a duk lokacin data fahimci wata mace tana ra’ayinsa,koda kuwa bata furta ba,a ranar babu zaman lafiya ko kuma kwanciyar hankali. Idanunsa dake dauke da wani irin maganadisu wanda ke sake dasa mata kakkaifar soyayyarsa cikin zuciyarsa ya zube mata cikin kowanne lungu na jiki da zuciyarta.
[21/09, 2:02 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

 

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 21"