Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tabarmar Kashi Book 2 Page 24

TABARMAR KASHI


Book 02 Page 24

Har suka isa company din babu wanda ya sake cewa da dan uwansa komai. Jibril nayi parking a parking lot na company din ya kashe motar sannan yayi magana ba tare da ya waiwayo ba

“Akwai employees da suka shirya welcoming naku,da tayaku murnar aurenku,suna entrance na main building” system din ya sauke daga saman cinyarsa yana ajiiveta gefe daya,idanunsa akan jibril

“‘Waye ya sanar musu da hakan?” Ya jefa masa tambayar da salon tambayarsa din nan me cike da dakewa. Cikin dan daburcewa jibril din yace

“Yallabai sajjad ne” dauke dubansa yayi daga kan jibril,ya gama gano abinda sajjad din ya shirya, sai kawai ya bada umarnin bude gofofin motar.

Kusan dukka manyan ma’aikatan company dinne suka jeru sahu biyu hagu da dama, kowanne dauke yake da gift a hannunsa,wasu flowers wasu boxes,mafi akasari sunyi hakanne saboda säahar din, don babu wanda baii cadin mu’amalarsa da ita ba,basu sake tantance muhimmancinta ba sai bayan tafiyarta,yanzun kuwa data dawo musu a karo na biyu sai hakan yayi musu dadi gwarai.

Ta tsakiyarsu suka fara takeaway a nutse,duk wanda zasu gifata sai ya ranqwafa cikin girmamawa. Mr hamza shine mutum na biyu a sahun, sunzo dab dashi ya ranqwafa idanunsa akan fuskarta

“Sir, congratulations, congratulations sir” ya fada da dan murmushi saman fuskarsa,sannan ya miqa flower din ga sãahar.

Baisan ya akayi ba,yadai tsinciki kansa da sanya hannu ya karba flower din daga hannunsa ya miqawa elyas tare da yi masa inkiya, sannan a hankali ya sanya hannunsa ya lalubi hannunta, ba zato ba tsammani sai jin tafin hannunta yayi ya manne da lallausan tafin hannunsa guri daya,ta waiwayo da hanzari tana dubansa idanunta kuma suka fada cikin zagayayyun fararen idanunsa. Zame hannunta taso yi cikin hikima da dabara amma ya matseshi tsam cikin nata,saboda ya fuskanci idanun mr hamza na kan hannayen nasu

“All eyes are on us” ya fada qasa qasa,a hankali itama tayi noticing hakan, musamman daga idanun mata da yawa da dama can ba huldarsu take shiga cikin company din ba, da masu goqarin shiga gonarta amma tayi musu iyaka irinsu saima.

A gaggauce suka dinga wucewa,hakan ta bishi saboda hannunsu na cikin na juna. Bai sakar mata hannu ba har suka isa bakin elevator.

Zame hannunsa yayi a nutse,abinda sãahar keta qoqarin yi kenan,ba tare da ya dubeta ba kuma ba tare da yace da kowa komai ba ya danna button ta bude.
Baya yaja kadan tare da yi mata nuna da hannu akan ta shiga. Cikin nutsuwa tabi ta gefansa,har kafadarta na gogar hannunsa saboda yadda ya tsaya yayi bake bake a bakin elevator din,wannan ya sake bawa turarenta damar bugun fuskarsa,ya damqe hannunsa da kyau kamar wanda ya boye wani abu. Waiwayawa yayi baya,kallo daya ya yiwa su elyas taga sun janye baya,ya taka da sassanyan takunsan nan ga shiga ya rufe dasu suka fara haurawa. Shuru elevator din yayi sai qamshin jikkunansu daya cikata. Yana tsaye daga gabanta dai dai bakin gofa,wannan ne ya bata damar gare masa kallo da kyau,duk kuwa da yadda taso dauke kanta,amma halin zuciva, sai taji a karon farko tana son yin hakan. Tun daga kan lallausar nannadaddiyar sumarsa,murdadden hannunsa dake boye a aljihunsa, daya hannun nasa dake rige da waga qawatacciyar briefcase dinsa zuwa bayansa da takalman dake gafarsa wanda suketa daukan idanu. Tana gama satar kallon dai dai sanda elevator din ta iso dasu floor din da suka nufa wato gini na garshe na kamfanin. Ya danns button din sannan ya taka yana shirin fita

“Ki ringa kame ganinki,karki manta ni dan iska ne me yiwa mata fyade, muddin kika cika kallona zan iya dauka cewa ranki ya biya ne da ni, komai kuma zai iya faruwa”.

Idanu ta fiddo waje cikin mamakin maganarsa,sai tasa hannunta guda daya ta dafe kanta haushin kanta yana kamata,meye ma ya kaita tsaiwa ta kalli wannan mutumin idan ba jawowa kai matsala ba ta fahimci shi kullum baiso a zauna lafiya,batasan meye tayi masa ba,wai shi kunyar furta kalmar fyade ma baya jinta sam?. Gani tayi idan ta barshi ba shakka ya sha da ita, saita tako itama tana biye dashi sanda yake scanning key din a jikin qofar

“Wai shin me ma zan kalla hala? wannan kodaddiyar fatar ko kuma wanna gashin mara kyan gani?” Ta furta tana nuna singalilin hannunsa dake riqe da handle din gofar. A karon farko dariya taso qwace masa amma ya rage kaifinta ta hanyar murmushin gefan bakiya kalli hannun nasa data nuna sai ya sanya daya hannun yana shafarsa

“U’uzubi kalimatillahit taammati minsharri ma khalaga, da gasken dai qaremin kallo kikeyi, banda haka ta ya kika san da zaman gargasata iyee?” Ya jefa mata tambayar data sanyata fara raba idanu amma ta basar

“Bayan gashina mara kyan gani sai kuma meye kika gano?,oya tell me” ya fada yana murza handle din tare da tura gofar baya ta bude.

“Eheenn, ina jinki da meye da meye?” Ya kuma jefa mata tambayar yana matsota idanuwansa akan lips dinta da suke haifar masa da wani irin abu a jikinsa wanda yake sanya tsigar jikinsa zubawa,a duk sanda yaga lips din sai ya tuna da santsi da kuma laushinsu. Ba zato ba tsammani taii va cafketa ya kuma finciketa zuwa office din ya maida murfin da qafarsa guda daya. Jefata yayi jikin bango yana bin bayanta
“Saifa kin gayamin, kada naje wadan nan marasa kunvar idanun naki sun ganemin sirri na” yadda ya matseta da bango ya sanyata jin kamar iskar dake wajen tayi mata kadan,ta tabbatar ko da wasa ta motsa ba shakkan qirjinta shine abu na farko da zai fara gogar jikinsa.

Qangame jilkinta tayi guri daya tana rufe idanunta sanda taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta, ta gama taga ya taho da hannunsa saitin fuskarta,ta gama saddagarwa may be maruka zata sha,sai taji yatsunsa guda biyu saman lips dinta suna zagayasu.
Tsigar jikinta ne ya zuba lokaci daya taji kamar wayar wuta ta jata

“‘Waye ya baki izinin shafa wannan abun?” Kusan daukewa numfashinta vayi, saboda a saman fuskarta yayi maganar muryarsa can gasa kamar me shirin rad’a mata, hucin furucin bakinsa dake cakude da mint scent ya daki fuskarta. Bata gama kokawa da wanna ba ta tsinci lausasan lebunansa masu dan tudu a saman nata siraran labban, ta gama fahimtar abinda yake shirin yi mata, saita tattara dukka qarfinta ta sanya hannunta saman girjinsa ta turashi baya tana gocewa gefe cikin bacin rai.

Idanunsa da wani abu ya sirka a cikinsu ya daga yana dubanta

“Duka wannan baya cikin sharudanmu,koma meye zanyi ko zan sakawa fuskata ba damuwarka bane, na kula kawai da fadeela,i will do my very best, that’s all” ta fada muryarta tana rawa. Kafin yace komai yaji qofar na bada alama na shigowar wani,don haka ya juya da dan hanzari kai tsaye ya wuce cikin office dinsa.

Saima ce rungume da files, gaba daya fuskarta zuwa zuciyarta babu wani sukuni ko annuri, ido suka hada da säahar, sai säahar din ta dauke kai tana gyara rufin lafayarta sannan ta durfafi office din itama kai tsaye,cikin ranta tana jin kamar ta zura da gudu tabar office din, a karo na biyu ta sake dawowa aiki da wannan mutumin da bashi da kirki ko kada,ko yaya zata kasance musu?.

A nutse ta buda ta shiga da murtukakkiyar fuskarta,har hanzu office din yana nan kamar yadda ta sanshi,saima sake qawatashi da akayi da gyare gyare.
Guri ta samu ta tsaya tana harde hannuwanta a girji, bugun zuciyarta har yanzu bai daidaita ba. Bashi a office din,amma taji qarar ruwa daga toilet, sai ta zabi taci gaba da tsaiwa kawai.

A galla mintuna kusan goma sha biyar ya shafe kafin ya fito,kallo daya ta masa ta dauke kanta, gaba daya fuskarsa ta sauya,ya koma real MT JARMA dinsa data sani,kamar ba shine yanzu yanzu yaso matseta yayi mata mugunta ba,ya jade fuskarnan da kyau,abinda ya sake qara masa kwarjini kenan

“Have a seat” ya fada yana jan tashi kujerar baya tare da shirin zama a kai,har yanzu bai kalleta ba.

Batason suia magana da vawa,don haka ta garaso ta zauna din, ya buda wani file dake gabansa ya ciro wata takarda ya ajiye saman file din

“As my new P.A,aikinki zai zama a qarqashina ne, zai kuma zamana kan umarnina,na baki access da duk wani kira mo email da ya shafi office dina, sauran abinda zakiyimin idan ta kama zan sanar miki, koda ya fita daga tsarin aikin PA”

•_HAJIYA QARAMA_*

Ita da masu aikinta biyu suka isa makarantar, kai tsaye har zuwa office din shugabar makarantar.

“Abincin jikata ne FADEELA Muhammad jarma” dubanta headmistress din tayi

“Cute angel,ko ba ita ba?” Ta fadeta da sunan da yawanci ake kiranta dashi a makarantar. Murmushi hajiya garama ta saki tana gyada kai “Eh ita fa”

“‘Amma dazu mamarta ta kawota da kanta,kuma da abincinta tazo kamar yadda aka saba” kai hajiya qarama ta jinjina,tana jin dacin kiran sãahar da sunan mahaifiyar fadeela

“Ba itace mamarta ba,matar ubanta ce,nanny dinta kuma ada” ta qasan glass matar ta dubeta

“Eh amma ita muka sani a yanzu,don ko last week da za’a shiga sabon session itace tazo tayi updating data na fadeela,da sunanta muka cike komai,so ko yanzun ba zamu iya karbar abinci daga hannunki mu bata ba,sannan koda daukarta ma a yanzu ita ke da alhakin hakan,idan fana da uzuri kuma zata kiramu da kanta ta bamu shaida akan wanda ta turo din”.

“Turqashi!” Ta furta tana dukan hannun kujerar da take zaune a kai ba tare da tasan ta aikata hakan ba

“Madam kinsan da waye kike magana kuwa? hajiya fauziyya ce ni fa qanwa ga Dr mahmud JARMA, uwa ga MT JARMA, sannan kaka ga fadeela,kinaso ki gayamin matsayin matar uba ya wuce na kaka?” Ita kanta matar mamaki sai daya darsa mata a rai, saboda bataga meye abun tashin hankali ko bacin rai ga gin karbar abinci ba,amma duk da haka ta basar ta girgiza kai

“Ko kadan kuma wannan ai family issue ne ma hajiya,abinda na sani dai kawai, duk wanda aka sanyashi cikin data na dalibi shine zaici gaba da juyawa da kulawa da komai nashi,dama kusan ita fadeelan ce kadai bata da wannan record da muke dauka a duk shekara,so wannan karon kuma ta samu,haqginmu ne mu kula da lafivar dalibi da tsaronsa, ki koma da abincin hajiya idan kuka sasanta a gida sai kuzo asan sunan wanda za’a cike dashi, ko kiyi kiranta muji hakan daga bakinta”.
Tsantsar bacin ran da take ciki ya hanata sake cewa komai sai kawai ta miqe tana fita dava office din, adama na biye da ita da lunch bag din. Sai data kusa minti ashirin a tsaye jikin motar tana juya abun a ranta, ita yarinyar zata dinga shigewa rayuwa haka? lallai zata nuna mata kurenta,amma kafin sannan bari taje ga mataki na gaba.

“Gida zamu koma hajiya?” Driver dinta ya tambayeta,saita girgiza kai

“Gidan yaaya zaka kaini”

•_DR MAHMUD JARMA RESIDENT_

Yana duge gaban garamar luggage dinsa, daya daga cikinsu wadda duk sanda tafiya ta kamashi yake amfani da ita. Yana tsaka da zugewa hajiya mansura ta shigo dakin dauke sa tray data shiryo masa kayan abinci a ciki.

Idanunta a kansa har ta garaso ta ajiye,ta koma gefan gado ta zauna

“Kwanaki uku kenan inatason yin magana da kai, amma sai nake ga kamar baka da lokacin kanka a ‘yan kwanakin nan” ba tare da ya dago ya dubeta ba va iiniina kansa

“‘Inata shire shiryen yin tafiya ne kuma a galla tafiyar zata dan iya daukana lokaci wala’alla me dan dama kafin na dawo,duk da bana fatan hakan” ya bata amsa yana tsaida luggage din bayan ya gama rufeta. Sosai take kallonsa,cikin kwanakin gaba daya kamar ma cikin nutsuwarsa yake ba,to amma ita abinda yake gabanta a yanzu yafi tasa a damuwar a gunta

“Labiba gaba daya na kasa gane kanta,yini take ta kwana tana kuka,ta daina fita ko ina,ta daina walwala ta daina magana da kowa”

“Duka akan me?” Yayi mata tambayar yana zama saman stool. Mamaki yadan kama hajiya mansura yadda yayi kamar baisan komai a kai ba, duk da haka ta hadiye cikin lanqwasa murya da karyar da kai

“Akan yayanta toufeeq mana, tunda yayi auren nan ita kuma ta koma haka” idanunta yake kalla kai tsaye,yama rasa abinda zaya fada, baisan me yasa daga mansura har fauziyya kowacce idanunta ya rufe akan batun hada auren toufeeq da ‘yarsa ba,duka duka ma yaushe yaron yayi auren da har za’a tsaya rakito masa wani auren?,shi yasan abinda su basu sani ba yadda haseena take zabin fauziyya,labiba take zabin mansura, haka säahar take
ZABINSA, ya riga taoufeeq nema masa auren sãahar ba tare da shi kansa ya sani ba. Bayan ya samu dukkan labarin aurenta da adam daga bakin muhyiddeen,ya tabbatar ya kuma yi imanin SÄAHAR itace macen da tafi dacewa da toufeeq,itace kuma madadin AMEESHA data sanyawa rayuwarsa dafin da yasa yake kallon mata amatsayin ABU GUDA. SAAHAR itace tayi masa kamanceceniya da SHIFA, dabi’unsu suna gogayya da juna,yafi kowa sanin wacece shifa da halaccinta a garesa,wannan ya sanya ya yiwa toufeeq sha awar mallakarta.
[21/09, 9:16 am] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

 

Post a Comment for "Tabarmar Kashi Book 2 Page 24"